GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

A parlor suka iske Momy, Dady, Naseer da Zarah, Ikram zaune, jin sallamar Mannir yasa Zarah mik’ewa dakyar tana cewa ” Dady yau ma Momy bata zo ba ko, har yanzu tana fushi dani akan abinda ni kai na ban san asalinsa ba ko? tayi maganar hawaye na zubo mata, har lokacin Zarah na masifar son Mannir da Zainab, kuma ko sau d’aya bata tab’a ganin laifin d’ayan su ba, tana jin su a ranta kamar a baya dan babu abinda ya ragu daga san da take yi musu, kuma tana d’aukar su a matsayin iyayenta, data kallansu a matsayin duk duniya bata da kamar su, hab’arta Mannir ya kama ya d’ago kanta yana murmushi yayinda yake yi mata nuni da bakin k’ofar parlor.

Zainab ta hango tsaye tana kallanta idanta yana zubar da hawaye da sauri Zarah ta saki Mannir ta nufi Zainab tana tafiyar dakyar, tana k’arasawa ta rungume Zainab had’i da sakin rikitaccen kuka mai ban tausayi, tana cewa ” Momy kiyi hak’uri ki yafe min wallahi nima ban san asalin cikin nan na jikina ba, Momy har rantsuwa nayi miki da Qur’an dan ki yarda dani amma har yanzu kin k’i yafe min balle ki fahimce ni, Momy kin san fushin iyaye ba k’aramin bala’i bane ga rayuwar d’a, Naseer yayi dan har a lokacin babu wanda yake yiwa magana tsakanin Mannir da Zainab, yana k’ok’arin mik’ewa yaji Zainab cikin kuka tace ” bazan tab’a yafewa masik’in da yayi miki cikin nan ba wallahi ko waye shi tayi maganar tana kallan Naseer, murmushi had’i da girgiza kansa ya mik’e yayi shigewarsa d’aki a hankali Zainab ta b’anb’are Zarah daga jikinta niyyar yi mata magana tayi arba da turtsetsen cikin Zarah wanda kwata-kwata bata lura dashi ba sai lokacin, take taji zuciyar ta tayi mata bak’i k’irin k’irjinta ya fara yi mata zafi yana tafasa yayinda mak’ogwaronta ya shiga yi mata k’una take taji tsanar Zarah ta sake dirar mata zuciyar ta, da sauri ta hankad’ata baya, Zarah tayi baya taga-taga zata fad’i Naseer yayi saurin tare ta,take idanuwanta sukajyi jajir kamar gauta cikin zafin rai ta nuna Zarah da yatsanta tace ” Allah ya isa tsakani dake Zarah, bazan tab’a yafe miki ba, kin cuce ni kin tozarta ni a idan duniya kin wulak’antar da duk tarbiyyar dana baki.

A matuk’ar hasale, zuciyar sa nayi masa tururin zafi gami da rad’ad’i cikin k’onar zuciya ya je daf da Zainab ta yadda suna iya jiyo numfashin juna ya d’aga hannu zai yarfa mata mari yaji anyi sauri rik’e masa hannu ta baya yana juyawa yaga Zarah a matuk’ar hasale tana kalan shi ido cikin ido babu alamar tsoro ko fargaba a zuciye cikin matsanancin b’acin ta. d’aga hannunta ta……………..

MOMYN ZARAH

GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

51

Ta nuna shi da d’an yatsanta cikin kakkausar murya tace ” karka soma, karka fara, a gaba na ka marar min uwa, sannan ka saran zanci gaba da huld’a dakai ko ganin mutuncinka, Naseer bari kaji idan ma baka sani gwara sani duk duniyar nan bani da kamarsu bani da wanda suka fisu a waje na, duk wanda yake so a bayan su yake, haka duk wani mahaluk’i dake duniya dazan so kona saba dasu a bayan su.

” Har yau har gobe suna nan a matsayin su babu abinda ya canja ko ya ragu daga yadda suke a zuciya sai ma abinda ya k’aru, har wa yau ina kallan su da mutunci da k’ima had’i da darajar da ba kowanne d’an Adam nake gani da ita ba, har kullum, ina nan ina ci gaba da kallan su a matsayin iyaye na, kuma har k’arshen rayuwata zanci gaba da yi musu wannan kallan, duk abinda ya faru a tsakani ko zai faru nan gaba babu ruwanka, kar ka kuma shiga, su kashe ni in sun so.

” Ni nayi musu laifi na kuma cancan duk wani hukunci daga gare su a matsayina na ‘yar su, sannan na cancanci fiye da haka a yadda suke kalla na a matsayin MAZINACIYA (My new novel) masik’a suna iya yin min hukunci mai tsananin gaske san ran su, tun ABU A DUHU (my upcoming novel) ne, babu wanda GASKIYAR AL’AMARI (my novel ) balle yayi min adalci.

” Idan suna ganin irin tarbiyyar da suka bani kenan, suna iya yi min komai tunda duk abinda zanyi musu dan su fahince ni su kuma yarda nayi musu, har rantsuwa nayi musu da mafi girma da darajar littafi Qur’an, amma sunk’i gaskata ni, duk duniya bani da kamar su sune mutane na farko daya kamata su fahince ni su kuma gaskata ni, amma sunyi watsi dani da lamura na, ta k’arasa maganar cikin matsanancin kuka mai cin rai kai daga jin sa kasan kuka bak’in ciki da takaicin rayuwa ne, Naseer zayyi magana tayi saurin dakatar dashi tace ” please Uncle karka ce komai, bana san ka shiga tsakanin dan kana da baban matsayi a waje na, wanda idan ka d’auke Momy da Dady bani da tamkarka.

Wani irin sanyin dad’i Naseer yaji ya ziyarci duk wata gab’a dake jikinsa, a hankali ya fara jin duk wani k’unci da bak’in cikin dayake ciki ya fara gushewa yana rikid’ewa izuwa farin matsanancin farin ciki marar misaltuwa, murmushi yayi yana kallan fuskar Zarah da ita shi take kalla ido cikin ido, yace ” da gaske Zarah ina da wani matsayi da daban a wajen ki, sansayan murmushi ta sakar masa had’i da lumshe idanuwanta dake zubar hawaye ta bud’e su sauke su akan shi tace ” Uncle bama a waje na kad’ai ba har ga zuciya ta da rayuwata duka kana da babban matsayi na musamman, kai ka zame min tamkar d’an uwan da muke ciki d’aya uwa d’aya uba d’aya, ka maye min gurbin wad’anda na rasa, sannan ya sanya farin ciki marar misaltuwa ga rayuwata, ka maye min gurbin bak’in ciki da damuwar dake ciki da farin ciki.

Naseer ka so ni a lokacin da kowa ya k’ini, ya tausaya min a lokacin dana rasa tausayawar kowa, ka yarda dani alaokacin kowa yak’i yarda da aminta da ni, a tsayawa rayuwata a lokacin dana rasa gata, ka zame min uwa da ubana lokacin da suka guje ni, ka kusance ni a lokacin da duk duniya ke guduna, lokacin da wad’anda nafi so nafi kusa dasu suka k’i ni, Naseer zame zan iya saka maka, wallahi da ina da ikon cire zuciya ta da rai na dana dad’e da cirewa na mallaka maka su kyauta, dariya Zainab ta tuntsere da ita tana tafa hannu, cikin isa da tak’ama ta tako har gaban su tace.

“Weldon Mr Naseer and Mrs Zarah Naseer Mustapha, gaskiya kun matuk’ar iya wasa kwaikwayo, da tsantsar rainin hankali sannan da wasa da zukutan al’umma, kun yi matuk’ar rainawa kanku hankali, idan zaku iya yin wasa da zukatan mutane kusa su raunana izuwa gare ku to ku sani banda Zainab Muhammad (da sunan Abban Zarah take amfani shiyasa tace Muhammad sab’anin tace Abdullahi ) domin ni kasan kai na ina da wayo da hankali gami da lura, na dad’e da wucewa da tunaninku balle sanin ku, sannan nasan ainahin kalar ku, nasan su waye ku, bayan ka d’irka mata ciki kazo kana rainawa duniya da mutanen cikinta masu k’aramar kwakwalwa irinka tunani.

” Kana wani pretending kamar mutumin kirki kai wai ga na Allah, mazinaci fasik’i kawai, Naseer koda kowa bazai yarda da cewar cikin dake jikin Zarah naka bane, kai kan kasani cewar ni nasan cikin naka ne, sannan koda duniya zata yarda da wannan wasan kwaykwayon naka kasan ni tar kuma k’arrr nake kallanka, ko da ita Zarah bata sani ba bakuma ta yarda cikin jikinta naka bane, amma akwai lokaci na nan zuwa wanda da kansa zai tabbatar mana da GASKIYAR AL’AMARI, ABU A DUHU ya fito fili, SIRRIN B’OYE ya bayyana kowa gani ya sani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button