GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

” Sannan sai muga ta wasan kwaykwayo kuma ko naga a lokacin wanne wasa kuma zaka juya, inga ta inda zaka kuma b’ullo da tsabagen tsagwaron rainin hankalinka, duk wani mahaluk’i dake duniyar nan matuk’ar yasan EL-MUSTAPHA FAMILY yasa koyaya aka had’a jini dasu sai mutu yayi CINDO gami da MARK a gefen cikinsa ina nan ina jiran lokaci da kuma ranar da ABU A DUHU zayya bayyana, sai muga ta k’arya ranar da ruwa zai k’arewa d’an kada.

Ta juya ta mayar da kallan ta wajen Zarah dake ta faman kukan zuci, tana zuciyar ta kamar zata tsaga k’irjinta ta fito saboda tsananin bak’in cikin duniya gami da tsananin takaicin rayuwarta, saboda tsananin b’acin rai gaba d’aya jikinta kerrrrrma yake yana rawa, zuciyar ta bugawa da matsanancin k’arfi tana yi mata soya gami zafi, k’irjinta sai suya yake yana mata k’ona yayinda gaba d’aya taji ta tsani rayuwarta da duniyar ma gaba d’aya, Zainab ta kalle ta tun daga k’asa har sama sannan tayi murmushin takaici tace.

” Banza sakarya shashasha, wawiya kawai wacce bata san ciwon kanta da darajar kanta ba balle tasan mutunci da k’imar kanta, kina tare da makashinki amma baki sani ba, kin d’auki so da yarda gami da amanar duniya kin d’ora masa, amma banga laifinki ba dan masana halayar d’an Adam sunce matuk’ar akaga mace ta lik’ewa Namiji awai wani abu a k’asa a b’oye, to ke naki dayake ya fito ya bayyana kansa duniya sani zai iyayiyowa abinda yake miki ne kike jin dad’insa wannan alama ce ta Naseer ya iya wasan sa amana yasan kansa amatsayin sa na cikekken namiji, hakan ya k’ara tabbatar da gaskiyar abinda nake zargi dan gashi saboda tsabar jin dad’in ZINAR dayake yi dake gashi kin biyo shi har gidan dan nasan yanzu kema kinsan dad’in namiji kin ji yadda ake ji shiyasa kika kasa hak’ura ki jure kika biyo shi har gida, JARABABBIYA kawai, HARIJA, MASIK’A MAZINACIYA.

Dady da Momy na zaune akan sofa babu wanda ya motsa balle yayi magana ko yayi k’ok’arin dakatar dasu, a hankali Dady ya mik’e ya kalli Momy yace ” tashi muje ciki ko, babu musu Momy ta mik’e tabi bayan sa, dan matuk’ar El-Mustapha yaci gaba da zama a wajen za’ayi b’atacciya dan ranshi yayi masifar b’aci, dan dama yana da bak’ar zuciya zamu iya cewa a wajensa Naseer ya gado zuciya, mutum ne shi mai wasa da dariya, amma kwata-kwata baya d’aukar raini, musamman yadda Mannir ya zubawa matarsa ido take zazzaga rashin mutunci da tsabagen rashin kunga gami da fitsara a gaban idansu amman ya kasa hanata balle yayi k’ok’arin dakatar da ita kodan kunyar idansu, amma ya tsaya yana kallan yadda ta zage take tijara.

Ta juya ta kalli Naseer dake ta faman huci kyamar zaki in banda Zarah ta hana shi da tuni ya sumar da ita day duka, tace ” banga laifin ka ba dan kanata rawar kai da rawar k’afa gami rawar jiki kanta, banga laifinka ba dan kana iya rufe ido akanta kayiwa makusanta turaja ka zazzga musu tsantsar rashin mutunci ba, zai iya yiyiwa kai ma kaji abinda baka saba ji a wajen matan banza da aka saba huld’ar banza dasu ba, da sauri ya yunk’ura zayyi kanta cikin hanzari Zarah ta rik’e hannu shi had’i da girgiza masa kanta aalamar a’a, idansa ya runtse da k’arfi saboda tsananin zuciya dan zuciyarsa takai mak’ura, idan Aunty Zainab ne ya sauka akan hannun Zarah dake rik’e dana Naseer tayi murmushi tace ” ai basai kunana ba an rigada an sani, gata nan sai kai ta rik’on abokiyar FASIK’ANCIN naka hannu bibbiyu, MAZINATA kawai, banzaye FASIK’AI.

” Haba Momy abinda kike yi fa kwata-kwata bai dace ba, baya cikin tsari da tarbiyya da kike tunk’aho da ita, a gaban Dadyn Dadyn mu, da Momyn Dady kina irin wad’annan abubuwan haba Momy wallahi bai kamata ba, surukan ki ne fa, zaki zubarwa da kanki da Dady da kuma mu kan mu mutunci da k’imar ahalin mu, wannan bake bace Momy, wani shaid’ainin ne ya shiga zuciyar ki yake sarrafa miki ita, dan wannan ba ainahin Momy dana sani bace, please karki bari shaid’an yayi tasiri da k’arfi a zuciyarki da gangar jikinki gami da ruhunki, Momy ki shaid’anin dayake san juya akalar rayuwarki da zuciyar ki daga kyawawan halaye zuwa ga munana hab…… k’au Zainab ta d’auke Ikram da wani gigitaccen mari mai tsananin k’arfin gaske wanda yasa saida ta hantsila da baya, dole yasa Ikram yin shiru badan ta gama fad’ar abinda yake ranta.

A fusace Zainab tace ” dan ubanki ni kike gayawa irin wad’annan maganganun ni zaki gayawa abinda ya dace dani, ko abinda ya dace inyi, lalle Ikram kin isa, tunda hantsarki ta kawo ai dole kiyi min rashin kunya da fitsara, ai kin girma zaki iyyin fiye da haka ma zaki iya yin duk yadda ransa ke so, tunda ga ‘yar uwarki nan ma ta zab’i nata zab’in, tabi hanyar data ke, yanzu Ikram dama irin wannan tarbiyyar na baki, oh ni dai Zainab na shiga uku naga ta duniya ina ganin bak’in cikin rayuwa dai-dai gwargwado, me nayi ne?

“Wanne laifi na aikatawa Allah dayake jarrabata da iftila’i kala-kala haka, “yanzu ke wannan tarbiyya kikayi, ko kina ganin kinyi dai-dai ko abinda ya dace ne kikayi,, ki tsaya a gaban iyaye na mahaifa na wad’anda suka haife ni kina zazzaga rashin mutunci gami da tsabar rashin kunya da tijara, haba Zainab idan rai fa ya b’aci hankali baya kushewa, haka idan nutsuwa ta gushe tunani ake sawa ya nemo ta, cewar Mannir, murmushi tayi had’i da cewa ” ok yanzu na fahimta, na fahimci cewar ni bare a cikin ku yaran dangi zaku yi min, tunda Naseer d’an uwanka ne, Ikram kuma ‘yar ka sannan kuma wacce ta nuna Zarah farkar d’an uwanka ce.

A hankali Zarah ta shiga kokawa da nufashinta dake niyyar d’aukewa gaba d’aya saboda tsantsar bak’in ciki da takaici, a hankali taji numfashin nata ya d’auke gaba d’aya yayinda idanta ya fara gani dishi-dishi, daga k’arshe ma ganin nata ya d’auke gaba d’aya dakyar ta fusgo magana ta kira sunan NASEER!!!! da k’arfi, a kid’ime Naseer ya juya indatake, ai a firgice ya k’arasa inda take, dai-dai lokacin data k’ok’arin sulalewa k’asa da sauri ya tare ta kiran sunanta da k’arfi ZARAH!!!! amma ina bata ko motsi, a tsorace Ikram ta nufi saman su Dady ta sanar dasu hankalin da ake ciki.

Hankali a tashe Naseer ya sure ta yayi harabar gidan da ita, a kid’ime yake kwalawa driver kira da k’arfi cikin tashin hankali, shima driven jiki na rawa ya taso, tun daga harabar asibitin yake kwarawa Doctor kira, da gudu Doctor da nursing suka k’araso d’auke da gadan tura marasa lafiya, kasancewar private hospital ne kuma tana buk’atar taimakon gaggawa yasa basu wani tsaya b’ata lokaci ba aka shiga da ita ciki aka fara aiki, a k’ofar d’akin da aka shigar da Zarah Naseer yake ta zarya ya kasa zaune ya kasa tsaye, yana cikin wannan halin Dady, Momy, da Ikram suka k’araso cikin tashin hankali, tamabayar Naseer Dady yake halin da ake ciki amma ina Naseer ba baka sai kunne, da ido kawai yake binsu.

Wata baturiyyar likita ce, kyakykyawar gaske matshiya dan bazata wuce 35 yrs ba ta fito cikin matsanancin tashin hankali da gudu Naseer ya nufe ta, a kid’ime take masa bayanin, ba haihuwa bace amma ta fara nak’uda, kuma gashi kasancewar tana cikin matsanancin tashin hankali da matsananciyar damuwa ya haifar mata da hawan jini, kuma zuciyar ta ta kumbura sosai, dole sai dai ayi mata aikin gaggawa a curo d’an matuk’ar ana san duk su biyun su rayu, da sauri Naseer yasa hannu aka shiga da Zarah Operation room, Dady Naseer ya rungume had’i da fasa kuka mai cin zuciya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button