GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ganin za’ayiwa Zarah CS yasa Dady sanar da mahaifinta da kuma amininsa Alhaji Abdullahi, ba’afi 30 minutes ba sai gasu a lokaci d’aya da hanzarinsu, sai da suka nutsu Dady yayi musu bayanin duk abinda ya faru bai b’oye musu komai ba, take zuciyar Alhaji Abdullahi ta shiga tafasa tana azalzala kamar wuta.

Ba’afi 2hrs da shiga da Zarah Operation room d’in ba, aka fito da ita da hanzari Naseer ya nufi har suka k’arasa wani k’ayataccen bedroom, bakin gado Naseer yaje ya zauna had’i da k’ura mata ido yayinda su Dady, Momy, Ikram, Abban Zarah, Alhaji Abdullahi duk suka zagaye bakin gadon suna kallan yadda take bacci, kallo d’aya zakayi mata kasan tana yin baccin ne dole badan ranta ya so ba, kana dubanta kasan tana cikin matsananciyar damuwa.

Babu wanda yafi takan abinda aka haifa balle a tambayi tana ina, dai-dai lokacin Baturiyyar nan mai suna Jennifer ta shigo d’akin d’auke da Baby tana murmushi ta mik’ewa Naseer tana cewa ” congratulations Mr cry, Babynka yayi tsananin kama dakai, you an him they’re look like twice, da k’arfi k’irjinsa yayi muguwar bugawa, hannun Dady na rawa ya karb’i yaran yakai idansa kan yatsunsa, gaban Dady yayi mummunan fad’uwa ganin CINDO a hannun yaron, sannan ga tsananin kamar da yaron yake yi da Naseer kamar an tsaga kara bakin Dady na rawa yace ” yaron yana da CINDO, cikin kerrrrmar jiki ya d’aga rigar Babyn nan ma yaci karo da MARK a gefen cikinsa, Dady bai san sanda yace ” still Mark ba, a fili Dady yace ” Innalillaihi wa’inna ilaihirraji’un.

MOMYN ZARAH

GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

52

Cikin tsananin firgici had’i da kid’ima Naseer ya mik’e had’i da karb’ar yaron daga hannun Dady yana dubawa, kallo d’aya ya yiwa yaron ya kau dai yana ambaton ” Innalillaihi wa’inna ilaihirraji’un, tabbas shi kanshi yasan yana tsananin kama da yaron, a fili yace ” ta ya haka ta faru?

Da k’arfi ya runtse idansa jikinsa na tsuma, had’i da muguwar kerrrma duk ilahirin jikinsa rawa yake, yayinda zuciyar ta tsinke, zuciyar sa ta shiga bugawa da tsananin gaske, yayinda k’irjinsa ya shiga yi masa soya, mak’ogwaran sa ya fara d’aci yana yi masa mak’ak’i, yayinda zuciyar sa ta ci gaba da harbawa da tsananin gaske tana tsalle kamar zata tsaga k’irjinsa ta fito, gaba d’aya jikinsa ya d’auki mugun zafi lokaci d’aya , shi kansa yanzu ya fara zargin kansa yana mamakin taya hakan ta faru, had’i tuhumar kansa, shi dai a iya sanin sa bai tab’a kusantar Zarah ba, iyakacinsa d’an shan minti (romance) take yaji ya tsani kansa da kansa, ashe duk wannan abu daya samu Zarah shine sanadi, a hankali ya share hawayen dake zubo masa, ya kasa koda motsa hannunsa dan yasan yanzu bashi da bakin magana balle ya samu abin cewa, dan yasan shi kowa zai zarga.

Shi babban tashin hankali ma ita kanta Zarah, tayaya zai kuma had’a ido da ita bayan tarin yardar daya mishi, d’azu-d’azun nan ta gama fad’ar yadda matsayinsa yake a gunta, yanzu idan ta farka taga yaron nan ya zayyi mai kuma zai ce mata, Alhaji Abdullahi ya mik’e a hankali gami da d’aukar yaron ya k’ura masa ido cike da tsananin tausayawa take hawaye suka fara zuba daga idanuwansa, a hankali ya shiga furta ” kai kuma taga k’addarar kenan, haka Allah ya tsara maka, ta wannan hanyar zaka zo duniya, amma Allah yafi mu sanin dalilin dayasa yayi haka, dan Ubangiji baya tab’a yin abu babu dalili, duk abinda kaga Allah yayi to akwai dalilin yinsa, sai dai muyi addu’ar Allah ya kiyaye gaba, kallan Naseer yayi daya zama kamar wani tab’abb’e yace ” wanne suna za’a saka masa, idansa ya k’ara runtsewa da k’arfin gaske had’i da furta “Innalillaihi wa’inna ilaihirraji’un, shikenan mai afkuwa ta auko ya yanzu kowa shi yake zargi, bashi da wata mafita, maganar Aunty Zainab ta tabbata.

Sake maimaita masa tambayar Alhaji Abdullahi yayi, kasa magana Naseer, a hankali ya d’ago kai ya kalli Dadynsa yaga shima shi yake kallo yana watsa masa wata uwar harara gami da kallan tuhuma, da sauri ya sunkuyar da kansa k’asa, Dady yace ” baka ji ana yi maka magana ne?

Cikin rawar murya Naseer yace ” wallahi Dady yaron nan ba d’ana bane, ni bama Zarah kad’ai ba, ni da kowacce mace ma ban tab’a aikata ZINA ba, wallahi Dady ban tab’a sanin wata ‘ya mace ba, a matuk’ar hasale Dady yace ” to d’an ubanka ne idan ba d’an ka bane? da uban wa yake kama? sannan duk wasu shaidu sun nuna tabbacin yaro nan d’anka ne, ga CINDO sannan ga MARK, kuma kace zaka zo mana da maganar banza, ko akwai wanda kaji ya tuhume, koya yayi maka fad’a? “Dady aje ayi NDA test amma wallahil azim yaron nan ba d’ana bane dan ban tab’a yin zina a rayuwata ba, ran Dady ab’ace ya wanka Naseer kyawawan marika guda hud’u a jere, da sauri Abban Zarah ya rik’e Dady yana cewa ” a’a Alhaji duk abin bai kai ga haka ba, shima yana da dama gami da hak’k’in gare kansa, daga b’acin rai yasa ka yanke hukunci cikin fushi wanda daga baya kazo kana danasani, ” a fusace Dady ya kalli Abban Zarah yace ” wanne danasanin zanyi bayan ga hujja da shaida nan Allah da kansa ya bayyana GASKIYAR AL’AMARI, sannan zaka d’aure masa gindi, dai-dai lokacin da Zarah ta farka tana tari had’i da salati, a hankali ta fara kiran sunan Naseer.

Wani irin razananniyar fad’uwa gaban Naseer yayi jin Zarah ta farka kuma sunansa ta fara kira, da hanzari Naseer ya mik’e ya nufi bakin gadan, a fusace Dady ya ka mishi tsawa yace ” karka sake ka k’arasa inda take, a hankali Zarah ta yunk’ura ta mik’e zaune, cikin sanyin murya irin ta marasa lafiya tace ” Dady please let him come to me? ido Dady ya runtse gami da yin tsaki da k’arfi ya kawar da kansa gefe, Naseer na ganin haka da sauri ya nufi Zarah, cikin kuka yace ” please Zarah ki sanar dasu bani ne baban yaron nan ba, ki fad’a waye ainahin mahaifin sa, ki gaya musu MEKE B’OYE, dan Allah ki sanar dasu GASKIYAR AL’AMARI da SIRRIN B’OYE please kona fita daga zargi, ke kad’aice kawai duk duniyar zata iya kub’utar dani daga zargi.

Hannunsa ta rik’o cikin nata tana zubar hawaye, tace “wallahi Naseer nima kai na ban san waye uban yaro nan ba, ban ya akayi na samu cikinsa ba, amma ni dai abu d’aya na sani shine nasan bazaka tab’a yimin haka ba, nasan bazaka tab’a iya cutar dani ba, Naseer koda duk duniya zata yarda kai ne mahaifin yaron nan ni bazan tab’a yarda ba, ta rasa mai yasa zuciya ta tak’i yarda da aminta akan cewar kai ne kayi min ciki.

Amma nasan komai daren dad’ewa gaskiya zata bayyana kanta koda bama rai raye mun bar duniya ne, Allah ne ya jarrabe mu daga ni har kai sai dai mu karb’i jarabawarsa hannu bibbiyu muyi addu’a Allah ya bayyana GASKIYAR AL’AMARI, ajiyar zuciya Naseer ya sake da k’arfi gami da k’ara damk’e hannunta cikin nashi yace ” Alhamdulillah tunda baki yarda da hakan ba, dama ni tsoro na da fargaba ta d’aya kema karki yarda da abinda mutane suka yarda dashi, sannan karki aminta da abinda duniya zata ce, dan bana san kema ki rink’a yi min wani irin kallo kamar yadda sauran mutane zasu rink’a yimin, karki rink’a yi min kallan mugu, azzalumi wanda ya cuci rayuwarki ya gurb’ata miki daniyaki, ya musanya miki farin ciki da walwalar ki izuwa bak’in ciki da damuwa kuma ya….. jin an banko k’ofar d’akin da k’arfi yasa Naseer yin shiru batare daya k’arasa maganarsa ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button