
Zainab ta shigo cikin d’aurewar fuska ta had’e rai sasoi tace ” Alhamdulillah, Masha Allah, yau dai anyi walk’iya munga gaskiya, kuma anyi iska munga d’uwawon kaza, GASKIYA AL’AMARI ya fito fili, ABU A DUHU ya bayyana kansa da kansa, yau kuma Naseer me zaka ce? da wanne kalar wasan kwaykwayon zaka kuma rainawa mutane hankali, ga yaro yayi kama da ubansa sak, sannan ga CINDO & MARK, Allah ne ya kawo k’arshen dramar ka Naseer, dubunka ta cika munafuki mak’iyin Allah, mik’ewa Naseer yayi duk da Zarah na k’ok’arin hana shi, amma zuciyar sa taje sama bazai controlling kan sa, daf da daf yaje kusa da ita ta yadda suna ina jiyo bugun zuciyar junan su ya kalle ta ido cikin ido ransa a matuk’ar b’ace zuciyar sa nayi masa ambaliyar wuta gami da k’una yace.
” Yes Zainab yaron can d’ana ne, jini nane halak malak na kuma karb’e shi hannu bibbiyu, babban abin takaicin shine ace ba’a san ubansa ba, to yanzu an san waye ubansa tunda gashi tsaye a gaban ki, kuma ubansa yakai uban daza’a iya nunawa duniya, saboda yakai duk inda wani namiji yakai, kyau, kud’i, ilimi, gata duk ina dasu, mu kalar tamu k’addarar kenan, ke ko ku an san kalar taku k’addarar da zata zo muku a nan gaba, kuma sannan ina miki albishi a yau d’in nan zan auri Zarah, kuma yanzu-yanzu anan ba’a wani waje ba, sannan na karb’i d’anta daga yau ya zama d’ana kuma na saka masa sunan uban rik’on ta mijinki wato MANNIR, hannu yasa a aljihu ya ciro kud’in dashi kansa bai san konawa bane ya risina ya mik’ewa Alhaji Abdullahi yace ” ka dubi girman Allah ya aura min Zarah yanzu kuma anan take, da sauri ta d’ago kai ta kalle shi tana hawaye, kallan ta yayi yace ” eh Zarah yanzu zan aure ki, in ga wanne d’an iska ko shege ne zai kuma nuna min iko da gadara a kanki, naga wanda ya isa ya kuma tab’aki matuk’ar ina raye, ya juya ka d’auki jaririn yace ” daga yau sunansa MANNIR NASEER MUSTAPHA.
Murmushin farin ciki Zarah ta rink’a yi yayinda hawaye ke zubo mata daga idanunta, sosai Alhaji Abdullahi da Abban Zarah suka ji mugun dad’i da tsananin farin ciki ya gauraye musu duka zukatan su, Alhaji Abdullahi ya kalli Abban Zarah yace ” kaje waje ka nemo mutane biyar suyi shaidu, sannan ni zanyiwa Naseer waliyyanci, ya kalli Dady dake tsaye yace ” kai kuma sai kayiwa ‘yar waliyyanci, ba musu Abban Zarah ya mik’e ya fita, zuciyar Aunty Zainab kamar zata fashe saboda tsananin bak’in ciki da takaici, kallan Zainab Naseer yaci gaba dayi ido cikin ido yayi tsaye kawai yana aika mata da silent killer smile, bak’in ciki ya k’ara turnik’e ta, AbbanZarah bai jima ba ya dawo da mutane wajen guda 10,nan take ranar a lokacin aka d’aura auren NASEER MUSTAPHA & FATIMA MUHAMMAD ZARAH.
Cikin nishad’i da fara’a gami da tsananin farin ciki Naseer ya kuma takawa har gaban Aunty Zainab yana murmushi yace ” Alhamdulillah suruka ta tunda kinga k’arshen wason kwoykwayo na, kin san sai cikekken namiji mai kafin basira da tunani ne kad’ai dai iya tsara irin wannan wasan kwaykwayon, sannan GASKIYA AL’AMARI, da kike yawan fad’a gashi Allah da kansa ya bayyanar dashi cewar NASEER MUSTAPHA shine mijin Zarah, ABU A DUHU shima ya fito fili cewar NASEER MUSTAPHA shine mahaifin d’an ZARAH MUHAMMAD, sai me kuma kike cewa? ya fad’a yana karkata kai sama alamar tunani, sai kuma yayi murmushi yace ” yawwa SIRRIN B’OYE da kuma MEKE B’OYE, hmmmmm suna duk ga sunan kin gani yanzu a gabanki sai kuma idan yaro ya girma yazo gidan kakaninsa cin tuwo ya k’arasa maganar idansa tarrrr cikin nasa yana silent
smile.
Cikin muryar kuka Zarah tace ” please Uncle stop is, she is still my Mom like no other, wata gigitacciyar tsawa Zainab ta dakawa Zarah ” dallah can rufewa mutane baki, sai bayan da kika bari ya gama fad’ar duk abinda zai fad’a yakai inda yake san kai, ya dasa aya sannan zaki yiwa mutane bariki da hanzari Naseer yasha gabanta yana girgiza mata kai had’i da cewa ” no! no! Zainab, shi is now Mrs NASEER not miss Zarah, you have to be understand Mrs Mannir, dai-dai lokacin Mannir ya shigo cikin matsanancin farin ciki da walwala mara misaltuwa had’i da annushuwa direct wajen Zarah ya zarce bai ma lura da wad’anda ke wajen ba, sannu ya shiga yi mata yana shafa kanta had’i da k’ok’arin rungume ta, cak yaji an d’auke hannunsa daga jikin Zarah had’i da cewa ” sorry Mr man, wannan ba Zarah’n daka sani da bace, wannan Zarah matar aure ce yanzu, kuma mijinta yana da tsananin kishin matarsa, dan haka don’t ever touch her again if not, ya cije lab’ensa na k’asa da k’arfi.
“What cewar Mannir a kid’ime, “yes she is Mrs Naseer, a matuk’ar firgice ya juya yana yiwa mutanen wajen kallan tambaya, sai a sannan Dady yayi magana ” yanzu muka d’aura auren Naseer da Zarah, a hargitse Mannir yace ” what kamar yaya Dady, “eh kamar dai yadda kake ji, kamar Mannir zayyi kuka yace ” but why Dady?
“Saboda Allah ya rigada ya tsara cewar Zarah matar Naseer ce, sannan ka d’auki matarka kubar wajen nan yanzu, tun kafin ran ku ya b’aci, wajen Baby ya nufa yasa hannu ya d’auke shi yayi hanyar fita dashi, tsawa Dady ya daka masa had’i da cewa ” ina zaka kai yaron? “zan tabi dashi inda ya dace ne, dan ya samu ingantacciyar tarbiyyar gami da kulawa ta musamman ne, ” baka da hankali ne, ya zaka raba yaro da uwarsa, d’ayen jaririn zaka raba da nonon mahaifiyarsa?
“Eh Dady bazan bari su lalata shi kamar yadda suka lalace, murmushi Naseer yayi had’i da nufar inda Mannir yake, cikin tsananin fitsara yake kallan shi k’uri, murmushi yayi masa had’i mik’a masa hannu yace ” bani d’a na, k’in bawa Naseer Baby Mannir yayi, da k’arfi Nasser yasa ya b’anb’are hannun Mannir daga jikin Baby ya kwace yaro, cikin tsananin b’acin rai yana ta faman huci kamar zaki, yayi hanyar fita yana cewa ” Zainab zo mu tafi, har sun kai bakin k’ofa suka jiyo muryar Alhaji Abdullahi na cewa ” Mannir daga yau mun din kasan ba alkhairi zai kawo ka kai da fitsararriyar matarka wajen mu ba karku kiskura ku k’ara zuwa inda muke, bai jiyo ba yayi ficewarsa Zainab ma ta rufa masa baya.
Alhaji Abdullahi ya yiwa yaro hud’uba da sunan da ubansa ya rad’a masa MANNIR, yace a rink’a kiransa da Na’eem, ranar aka sallame su suka koma gida, da farko k’in Zarah k’in shayar da yaron tayi sai da Naseer ya nuna b’acin ransa a fili sannan ta fara Breastfeeding baby, sosai Momy ke kula da Zarah tana yi mata duk abinda ake yiwa wata ‘ya mace ‘yar gata idan ta haihuwa, kulawa ta musamman Momy ke bawata tana kuma gyara mata jikinta sosai had’i da tsumata da ingantattun magungunan mata, dan tasan muddin ta gama bik’i Naseer bazai tab’a d’aga mata k’afa ba, musamman yadda yake rawar kan nan.
Hmmmmmm Ashe k’addara ta rigayi fata
BAYAN WATA BIYU
Sosai Na’eem nake samun kulawa a wajen Momy, yaron yayi kyau yayi b’ul-b’ul dashi kamar d’an larabawa, gwanin ban sha’awa, yayinda Zarah ta tsane tayi kyau, tayi wani so fresh da ita, sai dai kallo d’aya zakayi mata kasan tana cikin matsananciyar damuwa, kwata-kwata Zarah bata cikin kwanciyar hankali tunda ta rabu da Zainab take cikin tunani da bak’in ciki akan rashin ganinta, gashi yanzu ko wayar bata kiran su, ta had’asu daga ita har Ikram tayi watsi dasu, dan ma Ikram tana matuk’ar k’ok’arin kwantar mata da hankali, haka ma Momy duk wani abu datasan zai faranta ran Zarah shi takeyi dan tana jin mugun tausayinta, tasha zama tayi mata kuka akan k’addarar da Allah ya jarrabe da ita gata yarinyar k’arama wacce har yanzu bata cika 18yr ba, kullum Momy sai ta markad’awa Zarah fruits ta zuba mata pick milk da honey aciki ta had’e ta bata tasha, sannan ga tsumi kala-kala da ingantattun magungunan mata data ta mafan d’irka mata, dana gyaran jiki, fata, breast, aiko cikin k’ank’anin lokaci tayi d’au da ita, tayi mugun kyau da shek’e duk da matsananciyar ramar datayi, dan tana cikin matsananciyar damuwa.