Gangar Shedan Hausa Novel
Gangar Shedan Hausa Novel
Gangar shed’an
MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION
Labari mai taba zuciya da ban tausayi.Wannan labari ya kumshi darusa dadama da ilimantarwa yana kuma nuni da irin halayan da mata sukan jefa kanunsu ciki a sakamakon biyewa *ruɗun zuciya*
*Note* ban yarda wani/wata ba su sauyamin labari ba.idan kuma kika sauyamin labari ba tare da amincewata ba banyafe ba.
Page 1&2
Gida ne wanda yake d’auke da ɗakuna wajan 20. Daganin tsarin gidan ko ba’a fada maka ba hakan ze taba tar maka da cewa gidan kwaruwai ne. A tsakar gidan na iske maza da mata suna zaune a cikin katuwar rumfar gidan, sunata faman yin modi wasu daga cikin su na hura hayaƙin taba, wasu kuma shaye-shaye suke yi hankalinsu a kwance, babu ɗaya cikin su wanda yake da shigar musulunci dukanin su kayan jikin dasu gara babu musaman ma matan dan su mazan daga me gajeran wando, sai wanda ya ɗan suturta ya sa boxers .
Wata mata ta fito daga cikin wani ɗaki ba ƙaramar mace bace tana da jiki, uwa uba hips ɗinta da suke rinjaya ta dan da ƙyar take ɗaga su uwar daba kenan, uwar ƴan iska ina yaron daya gagari uwarsa da ubansa yazo ga uwar sa,
idan ka gagari uwarka kazo uwar daba zata d’auke ka tabaka daki ka z’auna ta mayar dakai ɗanta(wa iya zubila Allah kayi mana tsari da wannan mata).
Suna ganinta aka soma yimata kirari ita kuwa sai juyi take tana ƙara ɗaga kanta sama, ana tafiyar kasaita.
Wani daga cikin su ya d’auko mata kujera ta zauna tana faɗin, “wai ina yarinyar nan take yau ban ganta ta fito a gidan nan ba gashi ha ƙarfe 1:00pm ta kusa” tana maganan tana tauna cingum. Wata daga cikin su, ta mayar mata da amsa cikin maye”ai tun jiya bata fito daga ɗakin ta ba, kinsan fa jiya ta ɗuri ruwa dayawa( tana nufin wai tasha giya da yawa) kwaɓe ta uwar daba tayi tace”ke rufe min baki kin wani karkace baki kina magana magana da wata fuskarki mumuna”(ni kuwa nace to kaji fa karfin hali ɓaraho da sallama, bata fiki kyau ba duk dama kin sha bleaching )tashi tayi ta nufi wani ɗaki dake jerin ɗakunan da ta fito daga cikin shi, soma bugun dakin tayi tana kiran”Teema, Teema”shiru kake ji ba’a amsa mata ba sake bugawa tayi tare da kiran sunanta,a matuƙar fusace ta buda ɗakin tace “wai uban waye yake bugamin kofa haka”, masha Allah na faɗa yayinda wata yarinyar ta fito kyakkyawa ce ba ƙarya fara ce ba sosai ba, tana da tsayi ba sosai ba, tana da shape sosai, gata da boobs ga hips masha Allah, gashinta har bayanta ga d’an bakinta pink da dara-daran idanunta, tana sanye cikin riga da wando black batada d’an kwali a kanta, uwar daba ta kalle ta tace”haba teema meyasa kike min haka ne wai, naga baki tashi bane shiyasa nazo naga Lafiya”, hararar ta tayi tace “ina ruwanki da lafiya ta ni na saka ki kizo ki tashe ni, wai bana faɗa miki ba, kada ki sake zowa ƙofar ɗaki na ba”, hakuri uwar daba ta bata ta fice ta koma ɗakinta, Ita kuma wannan yarinya da aka kira da Teema taja ƙofar d’akinta ta rufe…..
Tofa yanzu labarin yasoma
~shin menene tsakanin Teema da uwar daba da bata tsoranta haka?
~menene maƙasudin zaman Teema a cikin wannan gida ?
~shin wai wacece Teema?
Duk wannan zaku samu wannan amshoshin ku dai cigaba da bibiyar labarin
Daga taku har kullum
Y’ar lelen d’an lele
Name: | [GANGAR HAUSA NOVEL ] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books, Complete Hausa Novels |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | November, 2021 |
[ad_2]