NOVELSUncategorized

NIDA AMARYATA 1 & 2

NIDA AMARYATA
Na
Khadeeja Usman
A’uzubillahi minasshaidanir rajeem
Bismillahir rahmaneer Raheem
Astagafirullah wa’atubu ilaik
ina matukar Nuna godiyata ga Allah subahanahu wata’ala,Daya nufeni da kasancewa a raye Kuma cikin koshin lfy,a da naso in huta da typing zuwa lokacin da Allah zai budi idona lfy,amma dayawa sun bukaci in Inada damar yin Dan Allah inyi koba yawa,to Alhamdillah tunda har zaku iya hakurin bina sannu a hankali,bakuda matsala,Ina matukar sonku da kaunarku kamar yadda Kuma kuka nunamin soyayyar gaskiya,nagode Allah ya Kara kauna.
Ina Mika godiyata ga dukkan admins na groups Dina,Ina yabawa da kokarinku Kuna burgeni sosai wallahi nagode nagode Allah yakara zumunci.
idan har kinsan in kin karanta sai dai kicemin tnx,to ki rike abinki na yafe,idan kin San Zaki turamin hoton zuciya ko fulawa,Suma ki rike kayanki na yafe,dukkan marubuci Yana bukatar sharhi ne Akan abinda ya rubuta,tanan zai fuskanci abinda yake rubutawa ta Yaya ya Isa ga al’umma,masu addu’a gareni Kuma Ina matukar farin ciki, Allah ya Sanya farin ciki a rayuwarku,kamar yadda kukasa a zuciyata.
1-2
   Hall din cike yake da mutane,yayin da kowa ke zaune gurin da aka tanadar Masa domin kashe kwarkwatar idanu.Amarya NIHILA ansha kyau,an kame a kujera tare da angonta Alhaji Sani,Wanda daka kalleshi kasan Yana cikin farin ciki sosai.
 
An gabatar da dukkan abinda ya kamata ace anyi a gurin,yayin da manyan abokan ango masu takama da nera suka taso danyin hoto da amarya da angon,inda aka dinga kashe hotuna,Wanda inka kalli fuskar angon zakaga Sam babu walwala kamar dazu, sakamakon ganin da yayi amaryarsa nata bude baki da gantsarewa,harda irin cuno bakin Nan Wai ita a dole danta burge.Wasu a gurin sun dauka tsananin wayewa ce,yayin da wasu Kuma suka dauka tsabar rashin kunya ce kawai.Haka aka gama duk abinda ya kamata, sannan aka Fara bawa amarya da ango gift dinsu,Wanda idan angon yaji dai dai,da an bayar sai yaji amarya tace “think”amma Saiya maze yake ganin,kamar shine baiji dai-dai ba,Dan haka ya share a haka aka Gama taron aka firfito,domin tafiya Kai amarya,domin daga Nan aka shirya wucewa da ita.
    Sun iso gidan Alhaji Sani,gida ne Daya amsa sunansa gida,gidane Wanda daka gani kasan Mai gidan ya Tara citta da yawa,Koda motocin suka Gama parking,kowa ya hau firfitowa,tare da rangada guda,Nan da Nan gida ya kacame da hayaniya.
   Hajiya Hafsa dake daki ita da yaranta,tanajin karasowar ‘yan kawo amarya,tahau karanta addu’oin da suka zo bakinta,dukda inda sabo ta Riga ta Saba,amma shi kishi halitta ne,domin duk tsufan mace saita yishi,su Amira dake zaune a gefenta,Suma dukansu daka gansu zaka San suna cikin damuwa,amma dukansu sanye suke da Hijabai tare da carbi a hannuwansu suna lazimi.Suna a haka kowa yana saka nashi abin a zuciyarshi,sukaji sallamar ‘yan kawo amarya,duka amsawa sukayi,tare da kokarin tashin ‘yammatan nata suna yiwa bakin sannu da zuwa.saida suka Gama shigowa da amarya a tsakiyarsu lullube da mayafi,bayan sun karasa suka nemi gurin Zama,sosai Hajiya Hafsa ta Nuna musu karamci,inda suka Bata amanar Nihila, kasancewar ta Karamar yarinyar,ta dai ce musu zatayi iyakar kokarinta,haka sukayi sallama suka nufi sashen amarya,sun tafi suna yaba karamci da mutunci irin na Hajiya Hafsa.
Bangaren amarya Nihila Kam barakallah Masha Allah,domin ba karamin kudi aka kashe ba.Anyi duk abinda ya kamata kafin kowa ya watse,har ‘yammatan amarya,aka barta kuri ta bude fuska tana karewa dakin kallo.mikewa tayi ta ajiye gyalen a gefe,tare da rike kugu ta shiga tika rawar murna,Wai tazama amarya.Jin alamun motsi.kamar an nufo dakin nata,yasata saurin Zama da rarumo gyalenta ta yaa ta rufe fuskarta.Da takunsa na kasaita ya nufo bangaren,yayin daya Sha kyau iya kyau sai baza kamshi yakeyi.
Da sallama ya shiga dakin,inda ya hangota zaune tsakiyar gadon, murmushi ya saki tare da nufar gadon,bayan ya ajiye ledar Daya shigo da ita a kasan,ya haura wajen tare da jawota jikinshi ya sauke boyayyiyar ajiyar zuciya.tabbas Allah ya jarabceshi da son Nihila,Dan haka cikin dabara ya dagota tare da yaye lullubin fuskar tata,sosai ya Kara ganin kyanta fiye da ko yaushe.Sata yayi ta dauro alwala,suka gabatar da sallah,inda yayi addu’oin da duk suka kamata,sannan ya mike da kanshi ya dauko plate a kitchen dinta.Sosai ya ciyar da ita,inda Saida ya tabbatar ta koshi,sannan yaci shima,bayan ya dawo ya sameta inda ya barta, murmushi yayi tare da Zama kusa da ita Yana fadin,
“Amarya bakya laifi”
Bata amsa shi ba,illa dago kanta da tayi ta kalleshi,amma saita komar dashi kasa, sakamakon Jin zuciyarta na kokarin karaya.Jin muryarshi Yana fadin “amaryata ko Zaki iya karantamin suratul fatihatul kitab?
Shuru tayi har Saida ya Kara maimaita Mata tambayar,sannan ta dago Kai tare da murguda baki,Wanda karaf akan idonsa,Bai Gama mamaki ba,yaji tace,
“Ai dai kasan Ni ba jahila bace,Danmu daga Alhamdu aka Fara Mana karatu,mun dade da wuce inda kake tambayata ,inma danka kureni ne to nayi maka nisa”.
Cike da mamakin Jin furucinta yasashi Kara kallonta,duk da tsantsar kuruciyar dake tattare da ita Dan yasan yanzu haka bazata wuce shekara Sha uku ba,inma tayi din,Amma yayi duba da yadda yanzu ilimi ya mamaye ko ina,an daina Zama cikin duhun jahilci,Amma Bari dai karya yanke Mata hukunci,Bari ya dai yaci gaba da gwadata,Dan haka ya Kara jefo Mata wata tambayar.
“Ko Zaki fadamin ya ake wankan janaba? Sannan ki fadamin farillan alwala guda nawane,sannan ya sharrudan tsarki suke?”
“Hmmmm kajika Kai baba sanin Nan,to Wai dama har wani wanka akeyi idan mutum zaiyi jaraba,to wallahi ka ganni Nan ba Karamar jarababbiya bace Ni, Amma ba ruwana wallahi,dambena nakeyi Kai tsaye,to Banda ma rashin wayo in mutum yaje aka damalmala shi a kwata fa? Har Saiya Kuma asarar sabulu da wani ruwan,Kuma ai farillan arwalla kowa yasan adadinsu,kaima dai baba sani,Dari da hamsin ne fa, sharrudan tsarki kuwa,guda uku ne,na Daya zuba ruwa a buta ,na biyu yin Kashi ko fitsari, na ukun Kuma tsarkin shi kanshi”,ta karasa maganar tana me
Mikewa da cire gyalen gaba daya,tayi tsalle kan gadon tare da fadin,
“Sorry Choco! Wlh me u see I very gajiya like doki,I try yin bacci Dan haka don’t tashina kaji baba”!
Wani mugun bakin cikine ya ziyarci zuciyashi,badan komai ba sai dan Jin Kiran sunanshi da takeyi  Wai baba,to ba gara ta kirashi da sani Kai tsaye ba,Amma ko yarinyar Nan lallai in haka ne tayi kyan Dan maciji,to Amma ai Alhaji nura kamata yay yayi Masa bayanin yadda yarinyar take,duk da son aurensa na Karamar yarinya,amma duk da haka Bai shirya Zama da jahila ba,ba arabi ba boko,ganin girman jikin yarinyar yasashi tunanin zai more yayi kara’i,ya Kuma dauka a waye take
Zai barje haushinsa,Ashe  ba haka abin yake ba, tirkashi,lallai akwai aiki Dan shi Daya Gama tsara yin tafiye-tafiyensa da ita,zuwa kasashe daban -daban to ya kenan,Dan bazai dauketa gurin da zaiji kunya ba,musamman abokansa turawa,da Kuma wadanda sanabe yasa ko magana zasuyi,sai sunsa turanc,ya zaiyi to idan ya tafi da wannan jahilar ta kunyata shi,cike da takaici ya mike ya fice ya buga kofar,yayin da Yana fita Nihila ta mike tare da durowa tahau murnar ganin Wai yau anyi Mata aure,aikuwa saita hau leke-leke,Saida ta Gama zagaye dakin har zuwa falon sannan ta mike ta cire kayanta,daga ita sai under’s ta haye gado ta kwanta,a fili ta furta.
“Allah sarki,ko Ina su Anty Hama suke yanzu,ko me sukeyi oho,nidai nayi muku wayo gani Nan kwance Ina shagalina,Akan gadon masu kudi yeeeehh ta furta,zuwa can Kuma ta bingire ta kama bacci, sakamakon Jin laushi da sanyin A.C.
***. *** ****
Hajiya Hafsa ce ta fito,domin Fara aikace aikacen gida,çaraf ta idonta ya sauka Akan karfen benen,Nihila ce keyin sililu inda data zo karshe saita sheke da dariya,saita koma sama da gudu.
Ganin kartaji ciwo yasa Hajiya fadin,ke yarinya Bari kinji kada kiji ciwo,Ina ita Aunty’n taki ta barki Kika fito da sassafe,Dan ita a zatonta ta dauka ma ta dauka kanwar amarya ce.
Dai dai Nihila ta karasa silalowa,da gudunta ta karaso gaban hajiya,harda Dan hakinta,ta furta,”Ai Aunty na can gida na barota,tace yanzu Ni kadai zan dinga kwana a dakina Wai Amma  ranar girkina tare da baba sani zamu kwana,niko nace to ai Ni ban iya girki ba,shine tace Wai duk zan koya sannu a hankali harda karatu ma,Kuma fa Ina zuwa makarantar,shiyasa jiya da daddare da baba sani ya….Sam basuji alamun sakkowarshi ba,illa ganinsa da sukayi a gabansu kawai Yana kallon Nihila,irin kallon dayake Mata yasata sunkuyar dakai tare da fadin,
“Ai bance Mata komai ba,Naga kanamun kallon ka Kama munafuka,Dan Allah mama ai ban fada Miki komai ba ko?” Ta karasa maganar da sigar tambaya.
Hajiya da mamaki ya cika Mata zuciya,kaddai ace wannan itace amaryar Alhaji?
Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un ta furta kawai….
Na fada muku na yafe tnx comments dinku shine kwarin gwiwa ta
Alkalamin khady

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button