Labarai

Gaskiyar magana akan “yan Ta’adda da akace an gani a jihar Kano a unguwar Kuntau

Hukumar “Yan Sandan Jihar Kano taja hankalin mutane akan wannan labarin dake kasa da ya ya mutsa hazo,ga sanarwar da hukumar ta fitar kamar haka.

Ga labarin karyar da aketa yadawa kamar haka:

Yaya Kuke Ganin Wannan Zance Na Dr. Fatima?

Yadda Nayi Kacibus Da ‘Yan Ta’adda A Daren Jiya Asabar

Misalin 2:45am na daren jiya asabar na dawo daga halattar mauludin wani kanina dana sami gayyata a kano, sai hanya ta biyo dani ta wani yanke wanda zai sadani da babban titin gwarzo road.

Na biyo bye pas na sabon titi wanda zai hadani da wani yanke ta tsakiyar unguwar kadawa, na goto junction na makaranta me zaman kanta data shahara da suna (KUNTAU) dedai wani tsohon rami da aka cike a unguwar ta kadawa da ake cewa RAMIN KASA nayi kacibus dasu.

Goyon uku-uku sukai a machine kirar boxers, fulanine zunzurutu adadin mashinan da suke kai ya haura 100, na jijjiga matuka dana ga sun kewaye abun hawan da nake kai, yaren danai musu na fillanci shine ya kwaceni a hannunsu, kana suka dunguma suka nufi inda suka dosa.

Lallai ina jan hankali ga gwamnati da dukkan Jami’an tsaro, akan suyi kokarin daukar mataki a jahar Kano tare da tsaurara sa idanu musamman ga baki masu shige da fice in dare yafara turawa.

Wallahil’azeem batagari na amfani da sula-sainin dare wajan nemawa Kansu mafaka, masu unguwanni da da mazauna garuruwan dake gefen birni, lallai mu maida nutsuwarmu ga harkar data shafi tsaron kai, Dan tabbas wadanda na hadu dasu a Daren jiya bakine.

Ya Allah ka kyautata rayuwarmu, ka rufa asiranmu ka bamu lafiya da zama lafiya a kasarmu da jihohinmu, ka tsare rayukanmu da lafiyarmu da dukiyoyinmu da iyalanmu.

Dr. Fatima Sani
20/Nov/2022

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button