GIDAN UNCLE 49
*G.U*
Bata iya yimasa musu ba ta miqe suka shiga kitchen din basuyi wani abu me wahala ba jallop din taliya ce sukayi ta zuba masa takai masa sama ta hada
masa lemukansa da komai takai masa ya zauna zaman cin abincin itakuma ta sace jikinta ta koma parlour sukaci gaba da hira da baqinta dauriya kawai takeyi tana yaqe saboda bataso tabada qofar da zaa fahimci rauninta amma zuciyarta cike take da fargaban zuwan Salma gdan yau hakanan dai suka yini har dare sannan duka suka watse suka tafi suka barta saida ta rakasu har inda suka aje motarsu sannan ta dawo ta kwanta a parlourn tana tunanin wadanna irin mutane ne dangin Salma da bazasu iya zuwa inda take ba saidai idan ta fito su rinqa binta da kallo kalma wata Mata ta tuna lkcn data rakasu Aunty Jameelan bayan sun tafi ta juyo zata dawo sukayi karo da ita ta fito daga bayan dakinta taja baya da sauri kawai sai taga matar tayi murmushi tace “Umaimah kike ko?”
Daga kai tayi da alamun mamaki tace “eh lfy?” Sake fadada fara’arta tayi tace “aa to lfyr kenan dangin kishiya kam ai bakya tambayi lfy a gurinsu ba koda yake meye ma na bata bakina abuda saura qiris” wannan kalamai sune sukeyi mata yawo a zuciyarta “saura qirin meyene to saura qiris din?” Tambaya ce da bata da amsa saboda haka tayi luf a kujerar tanata zuba hailala da salatin annabi har akayi sallar insha ta tashi ta shiga dakin qasa tayi sallah ta haura saman harta nufi dakinta sai kuma ta juya ta shiga dakinsa ta bude ta shiga yana kwance da Shurafah rungume a qirjinsa idanunsa a bude suke ya zubawa pop din dakin ido har ta qarasa kusa dashi ta zauna baiji ba saida ta tabashi sannan ya dawo hayyacinsa ya sauke idanunsa akanta tare da sauke ajiyar zuciya tayi murmushi tace.
“Kowanne ango a daren da zaa kawo masa amaryarsa baya samun zama balle ya kwanta harsai yaga an shigo da ita gdansa amma kai gaka a kwance banga kana shirin zuwa ka daukota ba yakamata ka tashi kayi wanka ka fara shirin tarar amaryarka nasan tanacan tana daukin zuwanta gareka da tarin alkhairanta da kyautukanta masu muhimmancin da ko labarinsu bazanji ba” tana mgnr tana sake sauke idanunta a kansa yanda taga idanunsa sun kada sunyi jawur ne yasata tabbatar da cewa kuka yayi kawar da kanta tayi ta miqe ta shiga bathroom ta hada masa ruwan wanka ta dawo ta janye Shurafah dake jikinsa ta ja hanunsa ya bita kamar raqumi da akala suka shiga bathroom din ta rufe ta matso gabansa tace.
“Zakayi da kanka ko nayi maka na qarshe?” Dubanta yayi da sauri tayi saurin yin murmushi ta lakace masa hanci tace “ina nufin zuwa ranar da amarya zata sake bani aronka tunda yanzu itace take riqe da kambun ka sarautar tatac….” rufe mata baki yayi da sauri yace “banida wata sarauniya a fadata bayan ke bloody wlh bazan iya yiwa kaina komai ba duk jikina a sanyaye yake” hadiye wani yawu tayi me ciwo ta fara balle bottle din rigarsa ta cireta ta zare masa wandon tajashi har komin wankan ya shiga ta rinqa diban ruwan a hanunta tana zuba masa a sumarsa saida ta jiqata ta dauko shampoo ta matsa ta wanke masa ita tsaf ta sake daukan shaver tayi masa shaving na qasa da sama har qashin qirjinsa saida ta rage masa kasancewar yanada suma sosai a jikinsa kuma tunda ya kwanta jinya bai rageta ba garama na qasan shine take tunanin ya rage bayan yaji sauqi dagowa tayi ta shafa gefen fuskarsa kawai sai taji hawaye ne yakebin kuncinsa batayi masa mgn ba saboda tana cewa zatayi masa mgn itama kukan zatayi hqrnta ya fara qarewa wai ita Umaimah itace take gyara mijinta saboda wata ajiyar zuciya taja da qarfi wadda tasashi bude idonsa ya zubasu a nata yanajin zuciyarsa kamar ana hura masa wuta ya janyota cikin bath din ya matseta a qirjinsa yace.
“kinajin abinda nakeji a qirjina kuwa bloody bana sanin sanda hawayennan yake zubomin duk dauriyata na kasa daurewa nisa dake wlh Umaimah ajiye mace sama da daya bai kamace ni ba saboda bazan taba kwatanta adalci akan wata mace ba indai inada ke Umaimah…” Rufe masa baki tayi tace ya isa bloody don Allah ka daina banaso abinda ya faru ya riga ya faru kuma koma mene kaine ka jawo mana da bakaje kakai kanka gurin Salma ba da bata ganka harkun fara soyayya ba” dagowa yayi da sauri bakinsa yana rawa yace “wal….” daga masa hanu tayi da sauri jikinta na rawa tana neman rikice masa tace “ya isa haka banason jin komai a game da matarka Abu Shurafah ka tashi ka shirya ka tafi gurinta tanacan tana jiranka” tana fadin haka ta miqe ta nufi qofar fita daga bathroom din tana fita ya fito shima ya dauki wasu riga da wando na jeans dake lkcn sanyi ne yasa ko mai bai shafa ba ya dauki key din motarsa ya fita yana shirin bude motar yaji anayi masa mgn ta baya ya juya da sauri fuskar Salma ya gani taci uban ado harda su eyelashes kamar wata aljana dama ita ba fasali ba ya yatsina fuska tare da tsartar da yawu yace.
“Lfy?” Mgnr ta daketa amma dake yar duniya ce sai tayi raurau da idonta tace “amma dai kanada masaniyar tun shidda nake cikin gdannan yanzu har takwas da rabi bakazo ba bayan kasan nice baquwa ni yakamata kabawa lkcnka” wani kallon wulaqanci ya watsa mata kallon data tsana a duniya kenan koda yake dama an fada mata zata fuskanci wulaqanci indai matarsa tana cikin gdan a qaryar bokanta yace mata wai zuciyar matarsa itace take control din tasa bayajin komai baya ganin komai sai ita shiyasa taso tun kafin ta shifo gdan ta rabashi da soyayyar Umaimah amma haqanta ya gaza cimma ruwa qarshen zancen akace sai ta shigo gdan ta kwanta dashi ta debo sperm dinsa sannan zaa hada mata laqanin rabashi da matarsa.
_Wa’iyazubillah Allah ka tsare mana imanin mu qalubale garemu mata Allah ka kiyashemu tabewa ameen_
Jan motar yayi da sauri ya fice daga gdan ta tsaya sororo tanabin inda yabi da kallo a fili tace “banza jahili zaka shigo hanuna talala nayi maka daga kai har matar taka da kake wani fasa kai da ita harda wani cewa matarka halin Nana Fadima ne da ita to saika fadamin me halin yar gdan paparoma wani Illiteracy dake wlh da sannu zaka kwashi kashinka a hannu saika gane baka da wayo Hameed nice fah Salamatun Hajja Talatu”
Juyawa tayi ta koma bangarenta ta fara bunka turarukan sihirinta tana tsibbace tsibbacenta bayan ta gama ta kunna turaren wuta qaurin maganin ya hade da qamshin turaren yabada wani qamshi mara dadin ji ta koma daki ta dauki wata matsiyaciyar rariyar rigar bacci tasa ta hada gashin kantin da tasa a kanta ta daure ta nufi jikin mudubi ta dauki turare ta fesa a jikinta ta kalli kanta gaba da baya tayi murmushi ita a dole tayi kyau Salma kenan irin qananun matan ne batada tsayi kuma bata da jiki qirar tsadidi amma tanada fuskar girma sosai don idan ka ganta ta fuska bazaka ce saar aunty Jameelah bace yayar Umaimah koda yake babbace tun shi kansa Hameed zasu iya zuwa sa’anni koma ta girmeshi.
Sai goma ya dawo gidan kai tsaye bangaren Umaimah ya shiga ya haura saman tana zaune kan sallaya baiwar Allah tana karatun qur’ani tana kuka saboda ita ta zaci ya tafi bangaren Salman zama yayi a gabanta har saida ta sanya aya ya dago fuskarta yace “kukan me kikeyi bloody kin yimin alqawarin bazaki bani matsala ba don Allah ki daina kuka tashi kici hanta naga kinasonta ko?” Girgiza masa kai tayi saboda batajin zata iyacin komai a yanzu amma saida ya takura mata taci kadan tasha madara ya kamata suka shiga bathroom tayi brush shima yayi sannan yace “to zo na kwantar dake kiyi bacci kinji uwargidana farin cikina” kawar dakai tayi fuskarta a daure tace “nidai na roqeka kayiwa Allah ka tafi gurin matarka wlh Hameed dauriyata ta kusa qarewa ka matsamin na daina ganinka nayi maka iyakar karar da zan iya idan kuma ba gawata kakeson gani ba”
Miqewa yayi a sanyaye ya kamota ya rungumeta a jikinsa yana shaqar qamshin jikinta feeling dinta na taso masa ya lumshe idonsa tare da sauke ajiyar zuciya yace “zan tafi da wannan dumin jikin naki da wadannan zafafan kalaman naki nasan yau bazan iya bacci ba Umaimah jikinki kawai nake buqata” yana fadin haka ya saketa ya fice da sauri yaja mata qofar da qarfi tabi bayansa ta sanyawa qofar key ta zube a gurin ta dora hanunta a kanta ta zunduma wani uban ihu da batasan sanda ya qwace mata ba da sauri ta tura hanunta ta toshe bakinta tana maimata “ Innanillahi wa innah ilaihir raji’un Allahummah ajjirni fi musibati wa’akalifni khairin minha shikenan ya tafi Hameed ka tafi gurinta Abu Shurafah ka dawo gareni don Allah nafi kowa sonka a duniya wlh………”
*UMMUH HAIRAN CE…✍????*