BAKAR INUWA 40

……….Ba sai an mata wani explanation ba tasan shine. Dan mayataccen ƙamshinsa tuni ya ƙara ƙarfi a ƙofofin hancinta. Kasa buɗe ido tayi ta kallesa dan kunya, ga shi bata da ƙarfin da zata ƙwace jikinta a nasa.
“Kina ganin jiri ne?”.
Ya faɗa a hankali yana tallafo fuskarta cikin tafin hanunsa. Bata yarda ta buɗe idanunta ba, sai ta jinjina masa kanta, zuciyarta babu abinda take sai luguden daka kamar zata fito waje, ga tsigar jikinta sai yamutsawa take. Dan wannan shine karo na farko da ya taɓa mata irin wannan riƙon a cikin jikinsa sosai kamar haka. Shi kansa danne yanayin kawai yake a zuciyarsa, yay ƙoƙarin kaita zaune a bakin gadon….
Dai-dai lokacin Mama Ladi da batai zaton samunsa a ɗakin ba ta turo ƙofar da sallama ta shigo saboda tasan Raudha ɗin ma ta barta ne tana wanka batai tsammanin ta fito ba. Shigowar tata baisa ya janye jikinsa da ga na Raudha ba, sai ma itace data ɗan dabirce har ta samu ƙarfin yin mutsu-mutsu amma sai ya shareta. A ɗan rikice Mama Ladi ta juya zata koma ya dakatar da ita
“A gafarce ni ranka ya daɗe wlhy bansan kana ciki ba”.
“Is ok”. Ya faɗa tamkar baya so yana matsar da jikin nasa daga na Raudha ya zaunar da ita da ƙyau ya miƙe akan ƙafafunsa, nuni yayma Mama ladi data ajiye kayan hanun nata. Cikin girmamawa ta ƙaraso ta ɗora tray ɗin saman table da alama abinci ta haɗoma mata.
“Babu dai wata matsala zuwa yanzu ko?”.
“Eh ranka ya daɗe Alhmdllhi. Likitama da tazo ɗazun tace komai ya dai-daita sai dai a cigaba da kula da maganinta, ta kuma dinga cin abinci sosai dan ƙarfin jikinta ya dawo”.
Baice komai ba sai kallon Raudha da yayi. Sosai ta rame, ƴar ƙibar da tayi duk ta zube. Idanun ya janye yana ɗan furzar da iska. Sai kuma yace, “ALLAH ya ƙara lafiya”.
Mama Ladi ta amsa da “Amin”. Raudha ma data kai kwance saboda rashin ƙarfin jiki ta amsa a laɓɓanta.
Bai sake cewa komai ba ya fita a ɗakin ya barsu, dan Taura house yake son zuwa amma a ɓadda kama zai fita gidan. Ɗakinsa ya koma ya ɗaura jacket saman kayansa da p-cap ya fita, odilan ɗinsa dake jiransa dan dashi kaɗai zasuyi fitar yay saurin risinawa yana masa barka da fitowa. Kansa kawai ya jinjina masa.
“Saifu muje lokaci yaja”.
“Okay sir, odilan Saifudden ya faɗa da sauri yana buɗe masa back sit.
★★TAURA HOUSE★★
[indeed-social-locker sm_list=’fb’ sm_template=’ism_template_6′ sm_list_align=’horizontal’ sm_display_counts=’true’ sm_display_full_name=’true’ unlock_type=1 locker_template=2 sm_d_text=’
This content is locked
Share This Page To Unlock The Content!
‘ enable_timeout_lk=1 sm_timeout_locker=40 delay_lk=1 sm_delay_lk=4 reset_locker=1 locker_reset_after=1 locker_reset_type=’days’ ism_overlock=’default’ ]
Gaba ɗaya ranta a ɓace yake tun jiya a gidan, tsabar bala’in dake cin ranta ko barcin kirki batayi ba da daddare. Yinin yau kuwa babu wanda zai ce yama ganta a gidan har ƴaƴanta, sai Adda Asmah data shigo da yamma ta ƙara fanfata matuƙa saboda cikin nan na Raudha ya matuƙar tsaya musu arai duk sun san ya zube kamar yanda sukaji bakin su Lubnah da Anne. Ɗazun da rana Hajiya Shuwa da Hajiya Mufida sunje har government house sun duba Raudha. Koda Anne taga babu gimbiya Su’adah batace komai ba, saboda ɗaukar hakan matsayin kawaici ga abokan zaman nata.
Knocking ƙofar bedroom ɗin nata ya katse mata wayar da takeyi da Fulani. “Ammy zan kiraki inaga gashi nan ma yazo mara mutuncin”. Daga haka ta yanke kiran da miƙewa ta buɗe ƙofar dan a kulle take kasancewar bata buƙatar kowa ya shigo mata.
Barin wajen tai, Ramadhan da yaga tsantsar ɓacin rai a yanayin nata ya ɗan furzar da iskar bakinsa yana ambaton sunan ALLAH a zuciyarsa. Ko ɓangaren su Anne bai shigaba ya wuto nan. Koda ya kai zaune yana gaisheta bata amsa masa ba, sai kawai ya saki ɗan murmushi da zame p-cap ɗinsa ya ajiye shima yay shiru.
Tsahon mintuna uku ɗakin ya ɗauka shiru, sake ɓaci ranta yayi fiye da wanda take ciki. A zafafe ta watsa masa harara tana magana a kausashe, “Yanzu ai ka fara ganin abinda muketa nuna maka akan wannan shegen auren, matarka tayi yanda take so na zubar da ciki saboda ta fito a gidan marasa tarbiyya. Tunda ta nuna bata shirya haihuwa ba kasani ni bazan amince ba. Dan haka dole ne ka ƙara aure nan da wata ɗaya, kuma Aina’u zaka aura…..”
“Maah!. Aina’u?”.
“Eh ita, idan kuma ban isa ba kamar yanda ubanka da kakaninka suka isa har suka aura maka zaɓinsu ka amsa ba tare da bijirewa ba sai naji.”
Iska ya furzar da ƙarfi yana ɗan rumtse ido da buɗewa lokaci guda. “Maah Please calm down. Kibar zancen wata Aina’u a beg. S…….”
“Anƙi a bari ɗin, kai yanzu Ramadhan dan baka da mutunci har kana da bakin faɗamin nabar zancen ɗiyar ƴar uwata akanka? Aka saka kama auri karuwa….”
(Ya ALLAH) ya faɗa a zuciyarsa yana rumtse ido da murza goshi. Cikin zafin rai gimbiya Su’adah ta cigaba da sauke masa takaicin Raudha da shi kanshi da dama take ƙullace da shi tun lokacin first night da suke tunanin ya faru tun a waccan ranar. “Ita ga ƴar iska mara mutunci, tasan bata shirya haihuwa ba miyasa ta yarda da kai dan ubanta, nama godema ALLAH data zubar ɗin kuma mahaifar tata bazata sake ɗaukar wani cikin ba. Bani da rabon haɗa zuri’a da jinin karuwai!!”.
Sosai ransa a dagule yake. Amma ya daure dan mahaifiya ta wuce wasa. Babu abinda yake sai haɗiyar zuciya. Babbar matsalarsa auren Aina’u da ta ambata, koma mizai faru sai dai ya faru babu auren Aina’u a cikin tsarinsa. Yariyar daya gani da idanunsa a cikin tsakkiyar club a America ana lesbians da ita, ƴan iska na ihu suna ɗauka a waya (Wa’iyazubillah). Ta rufe fuska da mask, shiyyasa tai tunanin babu mai ganeta, sai dai tayi rashin sa’a shi ya ganetan da idonsa. Dan ya tabbatar mata ya ganeta ɗin kuma ya cire mata mask ɗin. A wannan rana baiyi barci ba dan tashin hankali, dan koba komai itaɗin jininsa ce. Da uwarta da tashi fa uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Sannan mahaifinta shima ɗan masarautar su Maah ɗinne ɗan uwa na jini matsayin Uncle yake garesa. Amma itace yanzu Mahaifiyarsa ke tabbatar masa zai aura. Ji kawai yake ana ambaton Raudha da ɗiyar marasa tarbiyya amma shi har yanzu bai tabbatar ba tunda bai taɓa ganinta tana aikata wani fasiƙanci ba. Itako Aina’u da idonsa ya ganta ba labari ba…….
“Tunda ga ƴar iska ina magana kamin shiru ko!!”.
Gimbiya Su’adah ta faɗa cikin dawo masa da hankalinsa gareta. Ajiyar zuciya ya sauke yana gyara zamansa. Cikin tausasa harshe yace, “Maah Please relax. Ki bari ki huce sai muyi magana daga baya. Indai dan haihuwa ne insha ALLAH jikoki har sai kin rasa yanda zakiyi da su a gidan nan…..”
“ALLAH ya tsareni samuwarsu da ga wannan jinin karuwan da talauci. Dan haka karka sake min irin wannan maganar zan ɓata maka rai”.
“Ok. ok!. shike nan kiyi haƙuri Please”.
Tsaki taja tana ɗauke kanta gefe. Kaje dare yayi, amma ka tabbatar ka samu kakaninka da mahaifinka da maganar Aina’u dan wlhy babu fashi saika aureta, sai dai in mutuwa kayi ko ita ta mutu”.
(Oh oh, shikam yau ya zaiyi da tsohuwar nan) ya faɗa a ransa yana dafe kai.