GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sake jan bargon tayi tana sauke ajiyar zuciya tana cewa “nidai Uncle ka kyaleni don Allah jiya fa baka barni nayi bacci ba wlh kana qarawa mutuwa zany…” Rufe mata baki tayi tare da dagota tace “uwar shirme har yanzu kinanan da nauyin baccinki to bashi bane bude idonki ki gani” fara bude idonta tayi a hankali harta budeshi tar akan Aunty Jameelah ihu tayi ta rungume ta tana dariya tace “wayyoh dadi Aunty na wlh nayi missing dinki over” jan hanunta tayi ta sauko da ita daga gadon tace “wayyoh Aunty zafi Allah bazan iya tsayawa ba” kallonta takeyi tana cajeta sosai tace “meye yakeyi miki ciwon?” Kuka ta saka mata kawai ta shige jikinta murmushi tayi tace “kekam shirmenki bazai qareba to muje su Hajiya suna parlour suna jiranki kallonta tayi da sauri tace “kayy kuma saina fita ni wlh kunya nakeji” dariya tayi sosai tace “haka zaki fito kuwa kigani abinda mikiba a canza miki” kama hanunta tayi tajata suka fito parlourn tana binsa da kallo tana murmushi tace “lah Aunty yaushe akayi aikin nan lallai nayi bacci da yawa” Hajiya ce tace “yanzun ma Mijinki cewa yayi kada a tasoki zubewa tayi akan kujerar da yake zaune three sitars tana dariya tace “amma Hajiya tare zamu tafi ko?”

Haushine yasa Hajiya yimata daquwa tace “qaniyarki da tafiyar Jameelah kinga rashin kunyar da yarannan suka rinqa yima harfa binsa takeyi cikin mota suyi tsotse-tsotsensu amma don rashin kunya yanzu wai kinji mu tafi tare ai kinanan indai Hameed ne gakinan gashi wataran sai kinyi kamar ki gudu da qafarki” turo baki tayi tace “nifa ba binsa nayiba raka Sa’ud nayi muka hadu dashi a hanya ko Uncle?” Ta fada tana kallonsa ya kuwa karkace yace “aa nikam Ina zaune a mota tazo tace na taimaka na sake yimata ciki ko zaku barmu mu taho gdanmu ko ba haka akayi ba?” Idonta ne ya kawo ruwa ta kama zubar da hawaye tana dukansa tana cewa “Allah Hajiya ba haka bane wlh bazan iya fadar hakaba niba mara kunya bace irin…” Damqar bakinta yayi yace “waye mara kunyar to” girgiza masa kai takeyi tana kuka tace “nifa bance Kaine ba” dariya suka kwashe da ita yace “Allah ya ceceki yarinya da kinga irin rashin kunyata yanzun nan yarinya” zamewa tayi ta rarrafa ta koma kusa da Hajiya ta kwantar da kanta a cinyar Hajiya tace “Hajiya idan kika barni dashi wlh akwai matsala kasheni zaiyi bashida tausayi ko kadan kuma ko na bashi hqr baya hqr sai yayi kamar bayaji na wlh Hajiya jiya bai barni nayi bacci ba kaina har ciwo yakeyi”

Ajiyar zuciya Hajiya tayi tace “yaje da safe ya fadamin ai shine kema kike maimaita min Oh ni Zulaiha naga marasa kunyar yara wato ku babu wanda kuka raina saini ko?” Sunkuyar da kanta tayi tana shassheqar kuka harga Allah ita da gaske takeyi da Hajiya zata tafi da ita so takeyi saboda taji maza maza sun bata kashi, kallonsa Hajiya tayi tace “kaje kawo muku repiling gas dinku zamuyi amfani dashi” yasan korarsa akeson yi don haka ya miqe ya shiga dakinsa ya canza kaya ya dauki selinder ya fita kallonta Aunty Jameelah tayi tace “raguwa kawai daga ihu daya har murya ta dashe me akai da maza ma inji karya inma zaki ware gara ki ware wlh” kallon Jameelah Hajiya tayi tace.

“Kayyah Jameelah zama da namiji irin Hameed sai jarumar mace kudai ku gyarata kawai yanda zata dan qara kuzari Umaimatu hqr zakiyi da yanda Allah ya halicci dan’uwanki Mijinki” baje fasaharsu sukayi suka rinqa dirka mata magunguna harda kaza da kowanne tarkace ranar Umaimah taga abu bai dawo gdanba sai wajen magaruba lkcn Hajiya tasata tayi wanka ta shirya cikin wani pepar less dinkin doguwar riga saida suka shiga dakinta Aunty Jameelah ta bude Jakarta ta dauko mata wani jarka ciki da wani abu me masifar kauri jarkar faro ce babba tace ta zuba a kofi qarami tasha bayan sati ta kumasha haka zata rinqa shansa sati sati harsai ta shanye sannan ta bata wata takarda tace idan kina buqatar wani abu na warin kuzari ki duba wannan zaki samu kiyi hqr da mijinki Umaimah kada ki bashi kunya don Allah ki riqeshi amana kamar yanda ya riqeki run kina qarama Umaimah ni shaida ce wlh duk wata mace data samu soyayyar Hameed burbushin wacce yake miki ce tun bakisan kanki ba yake dawainiya dake kema yakama yanzu ki zama masharin kukansa kada ki bani kunya Baby kuma ki kama kanki ki riqe maraicinki Allah zai dafa miki kafin na tafi zan dawo naga yanayin zaman naku Allah ya kade muku fitina”

Tunda Aunty Jameelah ta fara mgnr Umaimah take kuka tasan itadai ta kade a gurin Uncle din nata saida Jameelah ta tabbatar da tasha hadin tsumin nasu na shuwa’arab sannan tayi mata sallama ta fita zama tayi a gefen gadon tayi tagumi tana tufka da warwara gabanta sai faduwa yake daidai lkcn shigo gdan dakinta ya shiga ya tarar da ita ta zabga uban tagumi gabansa ya fadi sosai saboda yasan bai wucce tunanin takurarsa ne yasata tagumin ba tsugunawa yayi ya kamo hanunta cikin nasa yana murzawa a hankali yace “tunanin me amaryar Uncle Hameed takeyi haka?” Ajiyar zuciya tayi tare da kawar da kanta gefe tanason fara koyon danne tsoronsa ta fuskanci sabuwar rayuwar data tsinci kanta a ciki.
Kwanciya tayi rigingine a saman gadon hakan ya bashi damar haurowa ya kwantar da kansa ha qirjinta tare da sanya hanunsa saman tudun breast dinta yace “bai wucce tunanin irin mijin da kike aure ba ko?” Lumshe idonta tayi ta budesu a kansa tare da girgiza masa kai murmushi yayi yace “ta yaya zan tabbatar da hakan?” Turo bakinta gaba tayi cikin sigar shagwaba tace “toni na fada maka ba tunanin da nakeyi kenan ba” dariya yayi sosai yace “lallai yarinya ashe kema kin iya shagwaba lallai yau akwai kallo a gdannan dan saikinyimin kuka da ido daya zan qyaleki”

Kallonsa tayi da sauri tace “amma dai ba irin abunnan na safe zanyi makaba ko?” Yanda tayi mgnr ne yasashi baisan sanda ya kwashe da dariya ba yace “inta kama sai kiyimin irinsa dinma” raurau tayi da ido zatayi masa kuka yace “wlh duk digar hawaye daya karin awa daya kinsan zan iya kuma” mirgina kai gefe tayi tace “Eh zaka iya amma dai kasan hukuncin wanda ya cuci maraya” sai take bashi dariya yace “saboda ragwanta yau ko girki bakiyi mana ba yanzu me kikeso muci mu kwanta” kallonsa tayi tace “ai su Hajiya sunyi girki na zaci kaje gdan Aunty kaci shiyasa ban baka ba” miqewa yayi ya nufi kitchen din ya zubo cous-cous din da vegetables soup ya dauko fresh milk ya ajiye a dinning din ya kulle qofofin sannan ya koma dakin ya dagota cak ya fito da ita ya ajiyeta a stool din ya kuma shiga kitchen ya dauko babban tire yazo ya zazzage kajin da ya shigo dasu guda hudu ne yaba su Hajiya biyu suka tafi dasu ya daukar musu biyu dama shida ya siya ya kaiwa Sadiya biyu ta jefeshi dashi tana tuhumarsa inda ya kwana ya yini bai tsaya bata amsa ba ya manna mata hauka ya kuma ficewa.
Kamo hanun Umaimah yayi yace “ni zan ciyar dake yanzun anjima ke kya ciyar dani ko?” Saurin girgiza masa kai tayi alamar aa yayi murmushin da yake qara masa kyau har dimples dinsa ya lotsa yace “idan baki ciyar dani ba ya zanyi Babyn Uncle ki daina tsoron mijinki zaki saba a hankali” itadai batace masa komai ba ya fara bata abincin a haka suka qoshi bata wani naman na kirki ba ta fara miqa ya zuba mata ido yanajin wani mugun feeling dinta yana bijiro masa shafa wandonsa yayi abarsa harta miqe yayi ajiyar numfashi tare da ruqo hanunta data miqe zata bar gurin yana qare mata kallo a-z tsorone ya cikata itakam yau taga boni “wai duk wata amarya dama haka akeyi mata ko kuwa ni kadai ce?” ta tambayi kanta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button