Hausa Novels

Lu’u Lu’u 22

*22*

 

Da sauri ta d’aga kanta ta kalli sarki Wudar ita ma da shi ma yake kallonta, cikin raunatacciyar murya tace “Ina so na had’u da mahaifina yallab’ai.”

A tsorace suka kalleta sai sarki Wudar da yayi saurin fad’in “Me kika fad’a? Kinsan me kike nufi kuwa?”

Jinjina kai tayi tace “E, na sani yallab’ai, ina so na ga fuskar mahaifina.”

Girgiza mata kai yayi yace “Saboda me? Gimbiya Zafeera kasheki zai yi idan kika fuskance shi.”

Jinjina kai ta sake yi tace “Na sani, amma kafin ya kasheni ina so na kalli fuskarshi, ina so nayi musayar numfashi da mahaifina, komai lalacewarsa shi dai ya kawoni duniya, kai kan ka da kake neman aure na a yanzu zan iya amincewa ne idan mahaifina zai saka min albarka.”

Da mad’aukakin mamaki ya kuma kallonta irin duba na tsanake, Umad dake kallonta hankali tashe ne ya matsa daf da ita ya kalleta yace” Hakan fa ba zai yiwu ba, akwai had’ari sosai.”

Mak’ale kafad’a tayi tace” Ba wani had’ari, kuma ma me ye asararku dan ya kasheni?”

Rumgume hannaye tayi ba alamar wasa tace” Ina so na je.”

Numfashi sarki Wudar ya sauke yace” Kin tabbata idan har na sadaki da shi zaki amince da buk’ata ta?”

Tsurawa fuskarshi ido tayi na sakanni sai kuma ta d’aga kai tace” Na yi alk’awari.”

A mugun tsorace ba tare da sanin yayi ba ya damk’i wuyan hannunta da bala’in k’arfi saida tace” Aouch!”

Kallonshi tayi a tsorace ita ma cikin siririyar murya tace” Yallab’ai you hut me.”

Rintse idonshi yayi ya cije leb’en k’asa, a hankali ya shiga sauke numfashi yana daidaita nutsuwarsa tare da sassauta rik’on daya mata har ya saki hannunta gaba d’aya, bud’a idonshi yayi a sauke a kan ta, da k’yar ya k’ak’aro maganar yace” Kuskure kike aikatawa, karki aikata haka Ayam.”

Cikin rad’a tace” Me yasa? Da matsala ne?”

Kawar da kan shi yayi yace” Babba ma kuwa.”

K’ura masa ido tayi tace” Wace iri yallab’ai.”

Sarki Wudar ne ya katsesu da fad’in” Tunda kin min alk’awarin haka ki shirya, zuwa wayewar gari zan sa a rakaki zuwa fadarki tamkar sarauniyar k’asar nan.”

Da farin cikin zata had’u da mahaifiyarta ta saki murmushi, ita har zuciyarta a uba take kallon tsohon nan, musamman ma daya tara farin gemun nan kamar na kakanta, uwa uba kuma mahaifin malaminta ne yallab’ai, sai kawai ta bud’e hannaye tsabar jin dad’i ta nufi sarki Wudar zata rumgume shi.

Tana daf da kai wa Umad ya daka wani k’arajin ta hanyar fad’in “What?”

Cak ta tsaya ta juya ta kalleshi inda sarki Wudar ma ya d’aga hannaye zai rumgume ta da farin ciki sai kuma ya kalli d’an na sa, a duburburce ya canza harshe zuwa yaren Italy yace “Ki gaggauta barin nan malama.”

Turo baki tayi tana kallonshi ita bata ji dad’i ba, bubbuga k’afafu tayi k’asa ta juya ta shiga haurawa sama. Da gudu, satar kallonta yayi ya d’an dafe saitin zuciyarshi yana sauke numfashi mai nauyin gaske, idonshi ne suka k’yallara suka had’u dana mahaifinshi, ganin wani tuhumammen kallo da yake masa yasa shi juyawa da sauri ya fice a falon yana godiya ga Allah da basu had’a jikin nan ba, a gaskiya rasa nutsuwarsa yake wasu lokuta, gashi bai san e ke damunsa ba da yake jin haushi haushin mahaifins1 wasu lokuta a game da ita, shin niyyarsa ce a kan ta ba mai kyau ba? Ko kuma dai kishinta ne yake?

Saidai tashin hankali shi ne da ta ce zata had’u da mahaifinta kuma mahaifinshi ya amince da haka, me kuma zai faru a gaba? Me hakan zai janyo musu ko kuma zai janyo mi shi? Da wannan tunanin ya k’arasa b’angaren shi gaba d’aya jikinshi ba k’wari, da haka yayi alwala yayi sallah ya zauna kan sallayar yana jiran ya ji me zai faru.

 

*Khazira*

Kamar ba mahaifiya wacce ta haifeta ba, haka ta tsaya gabanta tana girgiza kai da murmushi d’auke a fuskarta tace “Mah, me yasa kika aikata haka? Ni dama na zargeki tun a waccen ranar, to me ye ribarki a yin hakan?”

Girgiza kai sarauniya Juman tayi cike da takaici tace “Kaico Zafreen, hak’ik’a ubangiji yayi gaskiya da ya ce yana fitar da rayayye a jikin matacce, sannan ya fitar da matacce a jikin rayayye, ko da yake zan iya cewa sak halin mahaifinki kika d’auka, amma ina bak’in ciki da haka, dan na so a ce kin d’auko ko da kad’an daga halina ne, ki sani kuma wannan banzan halin na ki shi zai nesantaki da burinki.”

A wani wulak’ance ta kalleta tace” Me kike nufi Mah? Kin kuwa san girma da cin muradin burina? Shin kin ma san me ye barin na wa?”

Ita ma a gadarance ta kalleta tana gyara zamanta tace” Me ye burin na ki daya wuce ki gaji mahaifinki, duk fafutukar da kike Zafreen kina yi ne saboda idan ya mutu ki hau kujerar mulkinsa.”

Cikin jin haushi ta kalleta tana mai d’aga murya tace” Kinsan da haka kuma shi ne kike min fatan rashin cikar burina, a kan me? Me yasa kike nuna min banbanci ne tsakani na da waccen banzar yarinyar da kika haifa?”

D’auke idonta tayi a kanta tace” Ni ban nuna banbanci tsakaninku ba, saidai nasan na yi abinda kowace uwa zata iya yi ne, sannan abinda na mata ko kece a halin da take ciki zan mata.”

Tsugune tayi irin na mazan nan ta had’e hannayenta tana murmushin mugunta tace” Kinsan wani Mah? Na fita neman yarinyar nan ne dan na kasheta, sanda na fara had’uwa da ita da nasan ita ce, hak’ik’a dana fara canza mata kamanni, a ranar data mari fuskata kuma da ina da sanin ita ce, tabbas dana shak’e wuyanta har sai na tabbatar ta daina numfashi.”

Wani shu’umin kallo ta mata tace” Kinsan me zan aikata yanzu da nasan wacece ita?”

Murmushin gefen labb’a tayi tace” Idan har muka sake had’uwa da ita saina kasheta ko ta wane hali, ba zan tab’a bari ta zama silar dakushewar rayuwata ba, na rantse miki sai na kasheta.”

Malalacin kallo ta mata tace” Na so a ce kan iyalina a had’e yake tamkar tsintsiya, ba zan hanaki yunk’urin d’aukar matakin da kike ganin shi zai kaiki ga cimma ga ci, amma ki sani zakiyi dana sani wata rana, yar uwar ki kuma ba zaki iya kasheta ba, dan rayuwarta ba a hannunki take ba.”

Mik’ewa tayi ta harareta tace” Ni kuma na miki alk’awarin zan nuna miki gawarta ganin idonki, sannan idan har burina ya cika, ke da masu bin addini irin na ki duk sai na hukuntak…”

Bata bari ta dire maganarta ba saboda haushi duk da bata da kuzari haka tayi azamar mik’ewa ta d’auke fuskarta da lafiyayyen mari.

A gigice ta kalli mahaifiyar ta ta tana rarako idonta hannunta dafe da kunci, rai a b’ace sosai sarauniya Juman ta nuna mata k’ofar fita tace “Fita ki bani wuri tun kafin na sab’a miki kamanni.”

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button