GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVEL

Tun cikinta nada wata bakwai Hajiya tayima Hameed mgnr siyayyar kayan haihuwa yace Mata shi ya gama siyan komai da ake buqata Aunty Zarah zata kawo.
A cikin satin Aunty Zarah ta kawo kayan daya gigita tunanin kowa Kaka kam sallallami ta hau yi tana cewa “wannan yaro wanne irin mahaukaci ne ina zaakai kayannan haka saikace wanda zaa haifama yaya goma”

A haka kwanaki suka rinqa turawa ranar wata laraba da yamma Umaimah tana kitchen ita da Hajiya da titsetsan cikinta a gaba suna girki taji bayanta ya bada wata qara qass tare da riqewa tayi qasa da sauri tana dafe cikinta da bayanta tana fadin “way…yohhh uwata wayyoh ub…ana wayyoh Hajiya bay…ana cikina shikenan mutuwa tazo Hajiya ki yafeni????……

UMMUH HAIRAN CE…✍????
[1/20, 3:00 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍????: GIDAN UNCLE

Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:

PAGE THIRTY-SEVEN

Kamota Hajiya tayi da sauri na hadata da jikinta tace “subhanallahi haihuwar tazo Umah bari mu tafi Asibiti” riqota tayi a jikinta suka fito parlourn inda Kaka take zaune tana duba jarida miqewa tayi da sauri daidai lkcn da Hameed din ya shigo parlourn ganin yanda Umaiman take yatsina ana rirriqeta ai baisan sanda yayi watsi da ledar shop din dake hanunsa ba ya nufi Umaiman da gudu ya ruqota Hajiya tace “yawwa maza sata a mota haihuwa ce…”

Ai bata I rufe bakinta ba ya sunkuceta yayi waje har yana tuntube yanakiran sunanta, sata yayi a sit din baya yashiga ya tada motar bai jira fitowar su Hajiyan ba saboda gani yake zata bata masa lkcn yaja motar a mugun guje ya fice daga gdan.

Suna fitowa sukaga tashin qurar motarsa suka shiga wata driver yaja suka rufa masa baya bai iya hqrn kaita asibitin nassarawan ba saboda nisansa yake gani daga unguwar tasu wani asibitin kudi ya nufa aka karbeta aka shiga da ita larbour room sai bayan an shiga da ita sannan su Hajiya suka qaraso Hajiya ce tabada katinta tare da fada musu matsalarta shikam gogan sai safa da marwa yake yana hada gumi kamar shine yake naqudar duk sanda ya juyo nishinta shima sai yayi kamar shine me haihuwar lamarin ba duk da halin tararrabin dasu Hajiya suke ciki basu kasa yimasa dariya ba amma shi ko a jikinsa bin likitocin kawai yakeyi da suketa kaiwa da komowa idan kuwa yajisu shiru ya rinqa leqe kenan ta window.

Cikin ikon Allah baa bata wani dogon lkc ba Allah ya sauki Umaimah lfy ta haifo kyakkyawar yarta mace me kama da ubanta da uwarta dake dama kamar tasu dayace kowanne ka kalla sai kace yarinyar tana kama dashi tsakanin Hameed din da Umaimah.

Kukan jaririyar ne ya ankarar dashi aikuwa tun kafin a bashi izinin shiga ya danna kai dakin ya hango Babyn tanata wutsil² a hanun wata nurse ko takan Babyn baibi ba ya nufi inda Umaiman take ya tsugunna yace “wayyohhh Allah Babyn Uncle sannu kinsha wahala ko da wahala haihuwa ko? Ni nama yafe kawai wannan kadai ta ishemu”

Wani kallo da takeyi masa ne yasashi miqewa a sanyaye ya matsa inda nurse din take riqe da Babyn take shiryata ya tsaya ya zubawa yarinyar ido kawai sai yaji wasu hawaye sun zubo masa Allah kenan duk cikin yayansa babu wacce take tsananin kama dashi kamar jaririyar ajiyar zuciya yayi ya miqa hanu ya karbeta daidai lkcn dasu Hajiya suka shigo dakin.
Da sauri Hajiya ta nufi Umaimah ta dagota ta nufi toilet din da taga wata nurse ta fito tace “akwai ruwan da zata gyara jikinta?”

Amsawa tayi da “eh nama hada mata gashi can a ciki” shiga sukayi Hajiyan ta gasa mata jikinta sannan suka fito ta zaunar da ita a gefen gadon dagyar saboda ta dunku kamar qwarya sai a lkcn Hajiya ta samu damar daukar jikar tata da taketa wawuran abinci ta zuba mata ido kamarta da ubanta lkcn yana jariri har tayi yawa.

Hakanan suka yini a asibitin Hameed yana liqe dasu suna zuwa Hajiya dakinta takai Umaimah tana mata sannu har yanzu tana maqale da jikarta saida ta bawa Umaimah abinci da tea tasha sannan ta dora mata babyn a cinyarta tayi murmushi tace “yarinya kyakkyawa amma kun bata mata nasaba saboda son zuciyarku”

Hameed ne ya dago ya kalleta ya kalli Umaimah da kanta yake qasa yace “muma ba muso hakan ba Hajiya komai yana faruwa ne bisa buwaya da ikon ubangiji ku daina zargina wlh ba haka nakeba rabon wannan yarinyar zatazo a hakane yasa kika takura saina saki matata a halin inasonta tanasona kuma mun riga mun zama abu daya bazata iya rayuwa babu niba nima bazan iya rayuwa babu ita ba Hajiya ku taimaka ku dawomin da matata tunda ta haifemin abinda ke cikinta”

UMMUH HAIRAN CE…✍????
[1/20, 7:57 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍????: GIDAN UNCLE

Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:

PAGE THIRTY-EIGHT

Miqewa Hajiya tayi ta zugewa Umaimah rigar jikinta ta sanya hanunta ta ciro nononta ta dago yarinyar ta sanya mata a bakinta yarinyar ta kama tana tsotsa ya zubawa nonon nata ido yanajin wani shauqi da feeling na bijiro masa da sauri ya miqe ya fita daga dakin don ya fahimci zamansa zai iya haifae da matsala ko wanne lkc zai iya kai hanunsa ya cafki nonon ya taya yartasa sha.

Gidansa ya nufa yayi wanka sannan ya fara sanar da abokan arzikin sa anyi masa haihuwa matarsa ta haihu harda hotunan da yayi da bebyn ya dora a status dinsa na WhatsApp da Facebook aikuwa ya samu addu’a sosai zama yayi dirshen yana kallon bebyn da yayima huduba da sunan Hajiyansa Zulaiha yana kallon hoton yana hawaye yana Istigifari nadama yake da zuciya me tsarki tabbas ya aminta so masifa ne saboda sone umul aba’isin faruwar komai tsakaninsa da qanwar tasa amma meye ya sabbaba hakan? “Hajiya” ya fada a fili tare da cewa “itace taja mana komai amma yanzu laifina suke gani saboda nine mara gata”

Wayarsa ya dauka a karo na ba adadi ya kira layin Umaimah amma a kashe yasani koda a kunne take ba dagawa zatayi ba saboda ta dade da ajiyeshi da rayuwarsa a gefe gashi shikuma sai yanzune ma yake qara gasqata cewa soyayyarta itace take sarrafa rayuwarsa komawa yayi ya kwanta a kujera ya zubawa hotonsu ido lkcn farin cikinsu nanan bai gusheba shi abin ar mamaki yake bashi yanda yake hangen tsantsar qiyayyarsa a idon Umaimah Umaimah da a baya yake sarrafata da zuciyarta yanda yake so.

Da wadannan tunane² ya kwana da safe ya tashi ya shirya domin tafiya aiki saida ya fara zuwa yaga lfyr Umaimah da bebynsa daya laqabawa Shurafah sannan ya haura sama gurin Daddy daya dawo daga tafiya jiya da dare suka gaisa yayi masa barka kamar abin arziqi sannan yace.

“Alhmdllh babana Ina tayaka murnar samun qaruwar da kayi taya mace naji karar da kayiwa mahaifiyarku ka kyauta daka sanya sunanta wa baiwar Allan nan Shurafah so kamar yanda na fada maka lissafin da mukayi a baya zai canza ne bayan haihuwar Umaimah to alhmdllh ta sauka lfy saboda haka yanzu zabi biyu gareka kodai ka karbi yarka ka nemi wacce zata shayar maka da ita ko kuma ka rinqa biyan uwarta take shayar maka da ita”

Mamaki ne ya kusan kashe Hameed wannan fah shine tsugunu bata qareba ansai da biri ansai mage.
A sanyaye ya dago yace “amma Daddy na dauka cewa Umaimah koba itace ta haifi Shurafah ba ita me riqemin itace ta shayarmin da ita batare data nemi ko qwandala daga gurina ba….”

Daga masa hanu Daddy yayi yace “ai wai da take uwar tata shiyasa muka fada maka haka dama da ace ba ita ta haifaba ma aida mu da kanmu zamu bata ta shayar maka da ita saboda haka zabi ya rage naka idan ka yarda zaka rinqa biyane to wajibine duk wata ka kawo min 5 million na ciyarwa”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button