GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVEL

Kuka yakeyi sosai kamar qaramin yaro yana girgiza dannasa Kaka itama tana kuka tace “Shikenan ai kun kashesu kun huta saura yar itama gatanan Adamu kasa wuqa ka yankata sai ayi jana’izarsu gabadaya su ukun kukuma ku rayuwa a duniyar ku dawwama babu jarabawar ubangiji amma inaso ka sani nidai bazan yafe maka haqqi yarannan ba kuma Allah bazai yafe maka ba saboda shugabanci ba hauka bane Allah ma daya haliccemu munayi masa laifi ya yafe mana balle kai abin halitta Mai tarin dauda da zunubi”
Tana gama fadin hakan Hameed yaja wani dogon numfashi komai na jikinsa ya daina motsawa, wani ihu Daddy ya saki yace.
“Shikenan na kasheshi da kaina Innanillahi wa innah ilaihir raji’un Hameed….” Abubakar ne ya matso ya daga hanun Hameed din ya matse wata jijiya ya zubawa yatsun qafarsa ido babban yatsansa yada ya motsa yayi ajiyar zuciya yace “bai mutu ba akwai sauran numfashi a jikinsa ayi saurin kaishi asibiti”
Ai kafin Abubakar ya ida rufe bakinsa Daddy ya hada qarfinsa ya dago Hameed din Abubakar ya taimaka masa suka sashi a mota tun a hanya ya kira likitansa ya sanar dasu abinda ke faruwa.
Suna zuwa aka rufar masa aka fara jorner masa na’urori.
Ita kuwa Umaimah tunda aka kaita asibitin batasan waye a kanta ba daqyar likitocin sukayi nasarar tsayar da jinin dake zuba ta qasanta na hancinta da bakinta kam basusha wahalar tsayar dashi ba saboda kawai buguwa ce, saida aka farke dinkin da akayi mata aka kankare aka sakeyi mata sabo sannan aka daura mata drip Hajiya tana zaune a kusa da ita ta zuba mata ido tausayinta yana qara narkar Mata da zuciya Kaka ta shigo dauke da Shurafah a hanunta.
Da sauri Hajiya ta tareta ta karbi yarinyar da tayi kukanta harta gaji ta koma bacci tanajan zuciya tayi hamdala tace.
“Hankalina yana gurin yarinyar nan Kaka ina Hameed din?” zama Kaka tayi tace “yana emergency section kunsan matsalar danku kunma fini sani tunda kune kuka haifeshi saboda haka idan kun kasheshi hankalinku zaifi kwanciya”
Da sauri Hajiya ta tare Kaka da cewa “wai kina nufin ciwonsa ne ya tashi?” girgiza kai Kaka tayi tace “abubuwa da yawa daya dade yana binnewa a zuciyarsa sune suka hadu da wannan abun da kukeyi masa akan qaddarar da baku isa ku canzata da bacin ranku ba na tabbata da ace ana dawowa da mutum book din predestinations dinsa da Hameed yana cikin mutane na gaba² da zasuyi gaggawar sauya tasu qaddarar amma kun kasa fahimtarsa kun kasa yi masa adalci da uzuri a cikin rayuwarsa komai fa da kuka gani yana faruwa ne cikin sahalewa da buwayar ubangiji wlh na tabbata idan yaron nan ya rasa rayuwarsa ta wannan hanyar kema kina da kamasho kuma kece umul aba’isin faruwar komai Zulaiha kinada kaso me tsoka cikin abinda ya faru tsakanin Baby da Hameed saboda haka kiyi gaggawar tuba kema don basu kadaine suke cikin fushin ubangiji ba harda ku da kuka kasa sama musu mafita me kyau”
Sosai kalaman kaka suka daki zuciyar Hajiya kuma sukayi mugun sanyaya mata jiki qafafunta taji suna neman gaza daukarta ta sulale ta zauna a qasa kan tiles tana kuka me tsima zuciya tana qara shigar Shurafah jikinta tace “Allah na tuba astangafurullah ya Rabbil samawati wal ardi kaicona dana kasance me yanke hukunci cikin fushi kaicona dana zamo me gyara barna da barna kaicona dana zamo silar zuwanki duniya bata hanyar aureba Zulaihat me zan fada miki ranar da kikaji labarin nice silar zuwanki duniya ta wannan qazamar hanyar wayyoh Allah dama ka karbi rayuwata kafin wannan lkcn na zamo uwa mara amfani uwa me qoqarin rusa farin cikin yayanta da furucinta na tabbata da banyi furucin tsinuwa ga Hameed ba da babu abinda zaisa ya saki matarsa…..”
Ta qarasa mgnr cikin wani irin kuka me ban tausayi sun jima a haka kafin ta samu qwarin gwiwar miqewa ta fita ta nufi pharmacy din asibitin ta siyo madarar da zaa iya bama yarinyar ta dawo ta jorner kettle ta dafa ruwan zafi ta hadama yarinyar ta sanya a cikin feeder ta sanya cikin ruwan sanyi kafin Shurafah din ta tashi.
Sunanan zaune zaman jiran tsammani Daddy ya budo qofar ya shigo dukkansu suka zuba masa ido guri ya samu ya zauna ya hada uban tagumi yana share hawaye, Hajiya ce ta sake fashewa da kuka tace “Nikam naga ta kaina ni Zulaihatu ya mutu ko Alh shikenan Hameed ya mutu….” Dakatar da ita yayi ta hanyar girgiza mata kai yace “bai mutu ba amma yana tsakanin mutuwa da rayuwa Zulaiha Hameed yana fama da heart attack wanda zai iya zamowa sanadin salwantar rayuwarsa yanzu haka ya shiga commar wanda ko babu heart attack zaiyi wahala mutum ya shiga commer ya tashi yaci gaba da rayuwa….”
Ya qarashe mgnr cikin kuka tare da tashi ya bude fuskar Umaimah da taketa baccin wahala yayi ajiyar zuciya sannan ya koma ya dauki Shurafah da tunda aka haifeta sai yanzu ya dauketa ya zuba mata ido yanajin son yarinyar na ratsa jinin jikinsa ya rungumeta a jikinsa yana ajiyar zuciya.
UMMUH HAIRAN CE…????
[1/21, 7:02 PM] UMMUH HAIRAN CE…????: GIDAN UNCLE
Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:
PAGE FOURTY
Sun dade a zaune jugum² kafin Daddy ya tashi ya miqawa Hajiya Shurafah ya fita daga dakin sai dare Umaimah ta farka shassheqar kukanta ne yasa Hajiya fahimtar ta farka ta tashi da sauri ta qarasa gabanta ta ruqo hanunta tayi ta bude idanunta ta zubasu a kan Hajiya qwallar naci gaba da kwarara a idonta mgn takeson yi amma ta kasa sai jujjuya ido takeyi yarta kawai takeson gani ganin babu alamar yarinyar yasata qara sautin kukanta da sauri Hajiya ta juya gadon da aka kwantar da yarinyar tanata bacci ta daukota ta kwantar Mata da ita a gabanta.
Dagowa tayi ta kalleta kawai batasan sanda wani smiling ya qwace mata ba itama Hajiyan murmushin yaqe tayi mata ta koma ta zauna tana kallonta yanda idonta yake juyawa akan yarinyar duk da babu bakin mgn amma da ganin kallon da takewa yarinyar kasan nasone da farin ciki hadi kuma da tarin tausayi na da da mahaifi lumshe idonta tayi tare da daukan hanunta ta tallafo bayan yarinyar ta hadata da qirjinta wani bacci ya dauketa itama yarinyar numfashinta saida ya canza saboda jin dumin uwarta data yini tana kukan nema ko madara taqisha saidai zamzam da ake bata.
Alhmdllh jikin Umaimah yana sauqi sosai amma fah shi Hameed abun baa cewa komai saboda ko motsa hanunsa baya iyawa komai saidai ayi masa da na’ura ga wani qarin tashin hankali penis dinsa data miqe tun ranar da abin ya faru bata kwanta ba tun Daddy yana ganin kamar sauqi zaizo har ya sallamawa ubangiji komai saboda baya hangen wani sauqi a ciwon Hameed.
Kwanaki bakwai din a asibiti sukayita saboda dinkin Umaimah daya rikice sosai saida aka tsaya a kanta kana aka samu ya koma normal suka koma gda ranar da suka koma akayima yarinyar hakika raguna uku Daddy ya yanka mawa amaryarsa Shurafah da Sa yasa akayi sadaka duka a maqota ana fada musu haihuwar babu wanda yasan abinda ake ciki aikuwa a ranar akayita tururuwar zuwa tayasu murna saboda kowa sanin da yayi Umaimah matar Hameed ce saboda haka babu wanda yasan matsayin yarinya Shurafah sai su isu.
Kayan da Daddy yayima Umaimah da Shurafah ya bawa kowa mamaki saboda babu wanda yayi tunanin yanda ya dauki zafin nan zai siyawa maijego da jaririyar ko pant, sai dare da mutane suka lafa Daddy yasa aka kira masa Umaimah gata ga Hajiya ga Aunty Zarah ga Aunty Jameelah ga Kaka duk a gurin Shurafah tana tsakaninsu sai yawo take tsakanin dangin uwa da uba Allah Sarki shima shege me asali dan gata ne gadone kawai bashi dashi yanda ake lelen yarinyar har kuka yakesa Umaimah tana nadama da danasanin abinda suka aikata da Uncle din nata musamman idan ta tuna halin da yanzu haka Hameed din yake ciki na rayuwa ko mutuwa.