GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVEL
“Saboda zanyi aure Umaimah sai akace idan mijinki zai qara aure ki qaurace masa ki daina kulawa dashi ki daina sauraron kukansa da buqatarsa hakan shine zaisa yasoki ya fasa abinda Allah ya hukunta masa kada ki mayar da kanki jahila bayan nasani bakin gwargwado iyayenmu sun bamu ilimi kada ki biyewa son zuciya ki cutar damu Umaimah inasonki kina sona kada mu zalumci kanmu qarin aure bashine yake rusa zaman lfy da farin cikin gda ba rashin fahimtar junane ki yarda dani inasonki” yana fadin haka ya janyota jikinsa yaci gaba da famfata da kalamansa masu saurin canza mata tunani duk da haka kuka takeyi hakanan ya rinqa sarrafata tana kukanta tana komai ya rabata da komai na jikinta ya kwantar da ita ya rinqa aika mata da saqonsa yana tsotseta hakanan badon tanajin dadi ba yayi abinda zaiyi ya dagata yaje yayi wanka yana fitowa wayarsa tayi ring ya dauka da sauri jikinsa har rawa yakeyi ya kara a kunnensa yace “hello my love ganinan fitowa” kalmar ba qaramin girgiza nutsuwa da lfyr jikin Umaimah tayi ba ta zuba masa ido yanda yake ta sauri yanasa kayansa baiko bi takanta ba yayi ficewarsa ta miqe daqyar ta leqa ta window taga yanda yake wani gudu² ya shiga motarsa ya fice tana tsaye jikin windown wani malolo ya taso mata a zuciyarta yanzu duk wannan saurin da yakeyi saboda wata mace yakeyi yana ganin halin da take amma ya tsallake ya barta saboda buqatarsa ta biya.
Da wannan tunanin tayi wanka ta fito ta shiga kitchen ta dora tea ta dawo parlour ta zauna tana zama tajiyo kukan Shurafah ta miqe ta haura ta daukota ta dawo ta zauna har lkcn idonta bai daina zubar da ruwa ba daidai lkcn wayarta tayi Ring ta daga da sauri ganin number Aunty Jameelah tace “he… helo aunty yaushe zakizo?” yanda taji muryar yar uwar tata tasan ba lafiya ba tace “yadai meye ya faru Umaimah naji Daddy yace mijinki aure zaiyi saura kwana uku daurin auren hakane?” Ajiyar zuciya tayi tace “hakane Aunty Salman gdan Alh Musa zai aura….” katseta tayi da sauri tace “kutumar ubancan wannan tsinanniyar gantalalliyar yarinyar zai auro miki Umaimah kayyy Innanillahi wa innah ilaihir raji’un wannan wacce irin masifa ce ne Umaimah me kikayi masa haka?”
Cikin kukan da batasan yaushe ta fara ba tace “bansani ba Aunty wlh iyakar sanina banyiwa Abdulhameed komai ba Aunty meyasa rayuwa na zama karfa ne wacce batada rabon farin ciki meyasa kowacce masifa take fadowa kaina ne? Aunty meyasa su mama da Abba suka mutu suka barni Allah da nasan wannan muguwar rayuwar zan riska bayan mutuwarsu dana bisu mun tafi tare”……..
UMMUH HAIRAN CE…✍????
[1/26, 8:07 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍????: G.U
Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:
Daqyar Jameelah ta iya rarrashin Umaimah saboda yanda take kukan bilhaqqi da gsky tace “babu komai Umaimah ki kwantar da hankalinki kici gaba dayi masa biyayya kima kiyi hqr da duk abinda zakiji ko ki gani Umaimah da hqr da rashinsa taqinsu kadanne idan kuma kikayi hqr zaayi dake kuma shi zalinci baya tabbata indai Hameed yayi aurene ne saboda ya zalinceki da sannu zakiga sakayya batare da kinje ko inaba yauwa kuma nasan kinsan komai game da gdansu kishiyarki basu zama da kishiya balle ke da duk inda Hameed ya zauna bashi da zance sai naki bashida hira sai taki sannan ko badon wannan ba saboda kyawunki da quruciyarki Salma zata zafafa kishinta akanki to ke kiyi qasa da naki duk da kowa ma ya sani namu na gadone bama iya control dinsa idan ya motsa amma ki rinqa daurewa kina dagewa kina basarwa kada ki yarda mijinki da kishiyarki su gane raunin ki ta wajen kishi musamman kishiya Umaimah kada kiyi kuskuren nuna Mata ke raguwa ce sannan ki riqe Allah ki cire kasala ki rinqa tashin tsakar dare kina fadawa Allah damuwarki lkcn da kowa yake bacci da sannu Allah zai kawo miki mafita Umaimah wlh daga Daddy har Hajiya babu wanda yayi ammanna da auren nan kawai dai don babu yanda zasuyi dashi ne kinsan mijinki da murdadden hali akan raayinsa saboda haka ko kadan kada kiga laifinsu kuma kada kiga laifinsa shima ina zargin bayin kansa bane saboda nasan tarihin soyayyarsu da Salma tun zamanin quruciya ma baisota ba balle yanzu data zama abinda ta zama”
Kukanta take qoqarin tsayarwa tace “amma Aunty haka zanci gaba da zama dashi banida wani amfani a gurinsa sai lkcn biyan buqatarsa idan naqi ya gwadamin qarfi babu ruwansa da halin da zan shiga kawai shidai buqatarsa ta biya anya Hameed yana sona kuwa Aunty kamar yanda kike tunani?” Ajiyar numfashi Jameelah tayi tace “karki damu da wannan Umaimah nidai alfarma daya zan nema a gurinki duk rintsi kada ki yarda karatunki ya salwanta ki tsaya kaida fata wajen ganin kin gama karatunki ki fitar dashi daga zuciyarki Umaimah inada tabbacin duk ma inda yaje zai dawo gareki saboda kedin is naturally kinada qualities din da baduk mace ba”
Da wadannan kalaman ta rinqa rarrashin qanwar tata harta tursasa ta akan taje tayi masa girki batayi musu ba tana ajiye wayar ta tashi ta shiga kitchen ta fara shirya masa dinner tare da kunna karatun qur’ani saboda ragewa kanta quncin zuciyar da take ciki bayan ta gama ta shiga wani daki a qasan abin yaso bata dariya dakin guda kayan wasan Shurafah ne ajiyeta tayi a ciki ta nufi sama tayi wankanta tayi kwalliyarta me kyau tsari ta dawo parlourn ta zauna tare da daukowa Shurafah motar wasanta taci gaba da zagayawa a parlourn tanata debewa uwarta kewa sunata dariyarsu saidai idan lkcn sallah yayi ta tashi tayi ta dawo ta zauna haka har lkc yaja ta tashi ta shiga dakinta ta sake shiryawa cikin kayan baccinta tana tsaka da fesa turare ya shigo gdan yaga yanda ta gyara ko ina sai abin ya burgeshi Umaimah akwai tsafta komai nata kaf-kaf cikin tsari yunwa yakeji sosai saboda shi iya wuya bai yarda yaci abinci a waje ba indai ba qasar ya bari ba.
Dinning table ya nufa ya zauna yana bude abincin qamshi ya dakeshi ya lumshe idonsa ya bude tare da fara zuba abincin daidai lkcn ita kuma ta gama lallaba Shurafah ta sauko da gudu²n ta domin daukar wayarta tun tana saman ya qura mata ido yanajin wata muguwar faduwar gaba yarinyar komai nata daukar hankalinsa yake towai shi mene ma yaja raayinsa ga Salma har yake sha’awar aurenta ita ba kyau na azo a gani ba ita ba diri ba nagarta ba ita ba komai ba amma yanajin kamar zai zauce akanta amma dai ya sani koma me yakeji akan Salma baikai wanda yakeji akan Umaimah ba saboda duk inda yake a fadin duniya indai a cikin hayyacinsa yake to ita kadai yake tunawa.
Baiji qarasowarta ba saida yaji sautin sassanyar muryarta tace “sannu da zuwa” firgigit ya dawo hayyacinsa ya sakar mata murmushin sa me tsada ya lumshe idonsa tare da budewa daidai lkcn data bar gurin ta matsa kusada center table din ta dauki wayarta ta juya zata wucce ta tsinkayo muryarsa yana fadin “Hearty” tsayawa tayi cak ya taso a hankali ya sanya hanunsa ya tallafo faffadan hips dinta daya baje cikin blue din rigar baccin jikinta iya gwiwa yaja numfashi me qarfi yace “bazaki tambayeni meyasa naje nakai dare ban dawo ba” wani mugun yawu me zafi ta hadiye tare da kada kai tayi gaba zata tafi saboda batajin zata iya furta masa kalma daya me dadi a yanda takejin zuciyarta na tafasa idan ta ganshi sake ruqota yayi yace “naje gurin Salma ne akan tsare²n yanda bikin zai kasance so abin yazo unexpected babu wani shiri bazan samu damar yimata lefe ba shine tace na bata million daya da rabi tasai kayan fitar biki so naje na cira na bata shine nakeson kema ki fadamin abinda kikeso nayi miki?”