GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVEL

Yamutsa fuska tayi ta hadiye wani yawu me daci tace “na gde” daga haka bata kuma cemasa komai ba ta juya zata tafi ya sake ruqo hanunta yace “kamar kina sauri Babyn Uncle wai bakyason gani nane kome?” da sauri ta daga masa kai tace “eh hakane Abu Shurafah wlh banason ganinka jinake kamar na kashek….” da sauri ya hade bakinsu ya matseta a jikinsa sosai qirjinsa yana bugawa da sauri².
Sosai take kiciniyar qwacewa amma yawi qyaleta yaqi sakin mata baki saida yasha iya shansa sannan ya saki wasu hawaye masu zafi suka zubo masa yace “wannan kalmar ita Hajiya ta fadamin yanzun nan kema kuma kika sake maimaita min Umaimah nima wlh bansan meyasa nakeson auran nan ba nasani babu wata mace da nakeso da sha’awar kasancewa da ita a duk fadin duniya data wucceki ki yarda dani Umaimah aure na qaddara ce kuma kece kika jayo nasani badan kin gujeni ba da qila bazan hadu da Salma ba balle naji inason aurent…..”

Daga masa hanu tayi tace “ya isa haka Abu Shurafah nasani kuma naji auranka qaddara ce kona yarda ko kar na yarda ba fasawa zakayi ba saboda haka yardata batada wani amfani amma nidai nidai nasan auranka ba qaddara bace son zuciyarka ne duk da haka inayi maka fatan alkhairi ka matsamin na wucce inada abinda yafi wannan surutun muhimmanci” tana gamawa ta fincike hanunta ta haura saman da gudu²nta bin bayanta yayi da kallo yana hadiyar yawu mace iyakar mace.

Daga murya yayi ya kira sunanta amma Ina ta shige dakinta ta datse yaja wani gwauron numfashi ya sauke ya koma gurin abincin ya rinqa turawa daqyar danma yanajin yunwa ne kawai Umaimah ta riga ta rikita masa lissafi ba dafaffan abinci yakeso ba danye yakeso kuma na jikinta, da wannan tunanin ya gama ya tashi ya shige dakinsa yayi wanka ya dauki remote control din qofar dakin nata ya fita ya nufi dakin ya bude ya shiga a saman sallaya ya sameta tayi sujjada tana kuka tana roqon Allah cikin larabcinsu na shuwa kuka takeyi sosai tana roqon Allah ya kawo mata dauki ya rabata da qaddararren auransa.
Miqewa yayi da sauri ya dagota zuciyarsa na tafasa baisan meyasa kowa ya juya masa baya akan auran Salma ne koda yake dama yasan haka zata faru amma baitaba tunanin zafin kishin Umaimah yakai haka ba baitaba tunanin zata nemi rabuwa dashi akan wannan qaramin dalilin ba……….

UMMUH HAIRAN CE…✍????
[1/27, 9:02 AM] UMMUH HAIRAN CE…✍????: G.U

Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan;09031307566:

Hadata ya fara qoqarin yi da jikinsa amma taqi yarda ta rinqa tureshi tana dukansa ta ko Ina tana mgn cikin yarensu tana fadin “ka sakeni Hameed ka sakeni na gaji da zalincinka Hameed nagaji dayi maka biyayya kana cutar dani Hameed ka sawwaqemin wannan masifaffen auren naka na tsaneka Hameed bazan iya cigaba da rayuwa dakai ba cikin wannan rayuwar da komai nayi maka ban iyaba baka yabawa bare na burgeka wlh Hameed nagaji da zama dakai ko ka sakeni ko kada ka sakeni sai nabar maka gdanka bazan yarda hqrna da kawaicina da kuma rashin gatana yasa ka debomin masifa ka kawomin ba Ina baka isa ba Hameed koda kuwa kai kadai ka saura namiji a duniya wlh yau saika sakeni idan ba hakaba zan baka mamaki mamakin da bazaka samu damar yinsa a duniya ba”

Sassauta murya tayi tayi qasa ta zame ta zauna tare da riqe qafafun sa ta dago ta kalli cikin idonsa daya kada yayi jajur saboda zafi da radadin kalamanta tace “Abdulhameed pls daivoce me” qwace qafarsa yayi ya juya zai fita zuciyarsa tana tafasa ta miqe a mugun guje ta datse qofar tare da zare mukullin tayi saurin danna mata sabon password juyo kamar zautacciya tayi jifa da hijjabin jikinta tayo kansa ta shaqeshi ta jijjigashi da qarfin dabai taba sanin tanada shi ba tace.

“Billahil lazi La’ilaha illah huwa fitar daga dakin nan baka bani cikakkiyar amsar da nake so daga gareka ba daidai yake da yankewar numfashi a jikinka dan wlh saina zama ajalinka a gdannan Abdulhameed da hanuna zan kasheka na kashe banza jahili mara amfani a duniya ta kuma butulu da baya taba hangen tarin alkhairaina a gareshi kullum burinsa ya cutar dani Hameed baka isa ka kasheni da baqin cikin kaba wlh qarya kake azzalu….”

Bai iya barinta ta qarasa tsauraran kalamanta gareshi ba ya sauke mata wasu kyawawan maruka guda uku a fuskarta tayi baya a gigice tare da dafe kumatun ta tace “kutmar uba nika mara Hameed?” Kafin ya ankara yaji saukar wani abu qwal ga goshinsa ya dafe gurin da sauri ta kuma jefoshi da kwalbar turare itama ta sameshi a goshin nasa ta qara jefoshi da wata ya goce da sauri tare da dafe gurin da jinin yake zuba yama rasa meya ya kamata yayi mata saboda ya lura da gaske take kasheshi zatayi a yau din shikuma yayiwa zuciyarsa alqawarin duk rintsi bazai saketa ba sake nufoshi tayi cikin bushewar zuciya dauki wani dan qaramin table din glass zata buga masa ya riqe da sauri tare da hada hannuwanta a cikin nasa yace.

“Kee Umaimah baki da hankali ne meye yake damunki….” ta katseshi da sauri da cewa “duk ma me zakace ka fada a yau dai baka isa ka rintsaba idan bakayimin abinda nakeso ba na tsaneka! na tsaneka!! na tsaneka Hameed ka sakeni kawai ka huta nima na huta aure ne na gamashi dakai dama ka fadamin nayi gangancin dawowa rayuwarka Hameed…” daqyar ya samu nasarar hadata da jikinsa zuciyarsa tana bugawa da qarfi ko lkcn da ya auri Umaimah haukan Sadiya baikai na Umaimah Umaimah ba a lura da gaske Umaimah takeyi kasheshi zatayi.

Qanqameta yayi a jikinsa yanajin sabon sonta da tausayinta na kwarara a zuciyarsa ya rasa meyasa ya dage akan auran Salma har yana fito na fito da iyayensa akanta ya rasa meye yake damunsa shidai Allah ya sani ma baitabajin son Salma a ransa ba amma yanajin I bai rayu da itaba zai iya hallaka yana masifar son yaga ya aureta.
Wasu hawayen tausayin kansa ne suka zubo masa shidai kullum cikin laifi yake da zunubi bashida wata hanya da zaibi ya samu sauqi a gurin parents dinsa da matarsa daya tilo da yakewa so na mutuwa da rayuwa tabbas dada yanda zaiyi ya dojewa auran Salma da yayi badan farin cikin kowa ba saidon farin cikin Umaimah tunda ta yarda taji ta gani zata iya dauke lalurar rayuwarsa ita daya yasan yanzun ma duk shine yaja take gudunsa tunda a baya batayi masa hakaba amma tabbas da aiki ba qanqani ba a gabansa saboda itama Salman ya fahimci ta tsani yayi mata mgnr Umaimah wanda shi a duniyarsa hira idan bata shafi Umaimah ba bayajin dadinta ko kadan”

Cikin sarqewar harshe yace “ya isa haka kiyi cooling mind dinki pure heart wlh ki rubuta ki ajiye Hameed nakine ke kadai zuciyarsa tsarkakakken so take miki baso irin na sha’awa ba Umaimah kece cikon farin cikina kece rayuwata ruhina yana qirjinki idan kika kumayin nisa dani wlh azeem rayuwata ta qare don na tabbata koda ban mutu ba to zanyi rayuwa mara yanci kuma mara amfani Umaimah ki daina daukata me son kai nafi sonki fiye da kaina zan iya hqr da komai saboda ke wlh da zan iya da tuni na hqr da auren Salma amma na kasa idan ta kirani jikina har rawa yake wajen amsa kiranta idan na ganta sai naji zuciyata tana muradinta amma idan muka rabu sai naji ta fita a raina banason komai ya sake hadamu to yazanyi Umaimah ke kika ja kinsanni fiye da kowacce mace a duniya babu macen da zatayimin sanin da kikayi min wlh Umaimah Sadiya matatace ta sunnah a baya amma bantaba wanka tare da ita ba bantaba yin sex da ita da rana ba kuma bantaba saduwa da ita a cikin haske ba amma ke wanne ne bana miki har yanzu da kika canjamin kike azabtar da zuciyata ban fasa nemanki ba bana iya zuciya da duk abinda ya shafeki Umaimah danke kadai aka halicceni kamar yanda aka halicceki saboda ni kadai nasani kuma naji a jikina duk wacce ta shigo rayuwata dake kuma tace zata rabamu to ganganci tayi saboda babu yanda zaayi zuciya tayi aiki babu jini toni jininki ne ke yawo a tawa zuciyar kada ki barni Umaimah kada kibada qofar da zaa qara rabamu wlh wannan karon bazan kai lbr ba Umaimah…..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button