GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVEL

Miqewa tayi ta shige jikinsa ya rungumeta sosai ta saki wani marayan kuka tace “Daddy na tabbatar da bloody bayason Salma Daddy bayason auran Salma kuyi masa sauqi wlh qaddararmu ce Salma ni dashi Daddy ya sanar dani komai ya fadamin yanajin tsanar Salma a cikin jininsa amma kuma yakasa bijiirewa auran ta baya tunata idan baya tare da ita sai ta kirashi kota nemeshi kuma idan ta kirashi baya iya bijirewa umarninta Daddy ba fushi zakuyi da Bloody ba addu’arku yake buqata wlh Daddy baya cikin hayyacinsa kagafa yanzu kawai mgnrta nayi masa ciwonsa ya tashi wannan wacce irin masifa ce Daddy me Salma take nufi damu? Meyasa ta nace sai ta shigo cikinmu ta rusa mana farin cikinmu?”

Ajiyar Daddy yayi me qarfi ya sanya hanunsa ya dagota ya fara share Mata hawayenta yace “akwai manufar wannan shedaniyar yarinyar akansa koma dai menene yau dai an daura aure Umaimah tun lkcn da Hameed yayi min mgnr auran yarinyar nan na nuna rashin amincewata amma naga ya dage nasan tabbas akwai matsala so nayi qoqarin tursasashi amma yaqi Umaimah an tsaface mini da an sanya masa ya daina jin tsorona dagani har mahaifiyarku yama daina zuwa inda muke saboda zamu fada masa gsky Hajiya tace jiya ta kirashi tace ya sakeki saboda bazaki zauna da muguwar yarinyar nan ba da Sunanta yayi tambari ta fitar da mace a gdanta kota hanyar saki kota haukata kota kashe abune me sauqi a gurinta amma yaqi yace tayi masa uzuri ku hakan bazai faru daku ba saboda kun fahimci juna kuma kin bashi hadin kai shine ta kumayi masa rantsuwa akan saiya sauwaqe miki bazai kasheki da baqin cikinsa a banza ba Umaimah bayan qiyayyar Salma da ciwon auranta dakecin zuciyarsa harda wadannan kalaman na Hajiyanku addu’a kawai ya kamata muyiwa Hameed saboda kansa na cikin tukunya baya cikin hayyacinsa nasa ma da sauqi saboda qarfin kariyar farko da kuka samu daga kakanku musamman ke da kike mace da abin sai yaci uban haka ki qara hqr Umaimah mijinki yana sonki da izinin Allah komai zaizo qarshe bada dadewa ba”

Da wadannan kalaman ya rinqa kwantar Mata da hankali har yasamu yaga ta nutsu sannan ya zaunar da ita ya shiga ciki yaji dadin ganin jikin Hameed din bai tsananta sosai ba har yadan dawo hayyacinsa yana shiga ya zuba masa ido saida ya qarasa gabansa ya kamo hanunsa yace “sannu babana kuma ango Allah ya sanya alkhairi” kallon Daddy yayi da sauri yace “an daura ne?” Murmushin takaici Daddy yayi yace “to me zaa jira tunda kabada komai Allah dai ya tayaka ruqo ya baka ikon kwatanta adalci babu wata nasiha da zanyi maka tunda kai ba baqon riqe mace biyu bane amma wannan takun yana da bambamci da takun zaman Sadiya da Umaimah dole ka sanya ido a gidanka tunda ka nace hadasu zakayi Hameed kada naji kada na gani wlh har idan kakai hqrn Umaimah qarshe wlh babu ruwana zan cire hanuna daga lamarinka da ita gabadaya na zuba muku ido saboda itama yace kuma tanada yanci”

Numfashi ya sauke me wahala yace “ina take Daddy cikine da ita ko?” Kawar dakai yayi yace “tana waje bansani ba saboda bamu samu ganawa da likitan ba amma dai bata cikin nutsuwarta akwai damuwa sosai a tattare da ita Hameed ina qara jaddada maka girman amanar dake hannunka ba iya mata kawai take a gurinka ba qanwa ce kuma yace sannan amanar Allah ce” yana gama mgnr ya juya ya fita tana ganinsa ta miqe tayi gurinsa tace “ya tashi Daddy?” Murmushi yayi yana jinjina girman qaunar dake tsakanin yayan nasa yama rasa tsakaninsu waye yafi qaunar wani.
Jinjina mata kai yayi ta nufi dakin da sauri tana shiga ta nufi gadon baiji shigowarta ba saboda duniyar tunanin daya lula saida yaji ta rungumeshi ta karkatar da kanta daidai fuskarsa gabanta ya fadi sosai ganin hawaye a idonsa tasa harshenta ta lashe tace “nayiwa mijina kuma dan’uwana alqawarin zan bashi matsala ta kowanne bangare ba” matsata yayi s jikinsa yace “na gde bloody I love you so much” shigowar Dr Saleem da Daddy ne yasata miqewa a kunyace ta koma gefe ta zauna sukayi murmushi dukkansu Dr Saleem ya dubesu yace.

“Ya kamata ku cirewa kanku damuwa ku karbi duk abinda ya fado rayuwarku a matsayin qaddara Hameed rayuwarka tana cikin barazanar katsewa indai bazaka daina sanya muguwar damuwa a zuciyarka ba kasan matsalarka yakama komai ka rinqa maidashi abin wasa sannan matarka tana buqatar kulawa saboda nagani blood pressure dinta ya hau sosai sannan ga jaririn ciki komai zai iya faruwa saboda haka kuyi taka tsantsan dukkanku kunada matsalar da batason damuwa” hakanan sukayi sallama dashi suka tafi bayan ya dorashi akan magungunan da yakesha idan irin wannan matsalar ta taso.

Itace take driving din yana zaune a gefe Daddy kuwa gda ya wucce suna tafe kamar kurame babu wanda ya iya cewa da wani komai suna shiga get din gdan gaban yayi wata muguwar faduwa saboda ganin dayan bangaren cike da mutane ana shiga da kaya da qarfi taci wani uban birki ta juyo ta kalleshi shima ita din ya kalla da sauri yace “ Innanillahi wa innah ilaihir raji’un bloody kinga har sun kawo kayanta wayyoh nikam na shiga ukuna wannan wacce irin qaddara ce” wani matsiyacin kallo ta watsa masa ta bude motar da sauri zata fita yayi saurin riqo hanunta yace “kiyi cooling mind dinki bloody kada su gane rauninki suje su fada mata don Allah na fada mata cewa matata halin nana Fadimatu (R.A) ne da ita inasonki kema kinasona kuma kinason farin cikina kina tayani son duk abinda na kawo Umaimah dole ne kishi kuma halal ne nima bazanso ace baki kishina ba amma kiyi qoqarin danneshi ki barshi iyakar ni kada mubada qofar da zaa samu a shigo mana da baraka cikin gdanmu don Allah wlh nafiki kishin kaina Umaimah ji nake kamar na kashe kaina jinake dama na mutu na dawo duniya a wani bani ba mai tarin qaddarori marasa dadi Umaimah dama mu mutu kowa ya huta tunda mun kasa samun farin ciki a duniya qila mu samu a lahira……

UMMUH HAIRAN CE…✍????

[1/28, 2:03 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍????: G.U

Kuka ta saka masa ta qanqameshi shima hawayen yake yana buga bayanta alamun rarrashi daqyar suka iya saita kansu ya sanya harshensa ya share mata hawayen ya bude motar ya riqota a jikinsa bai damu da yawan mutanen dake gdan ba kuma bai amsa gaisuwar da dangin Salma suketa yi masa ba yaja matarsa suka shige part dinta yana shiga yayi turus ganin Hajiya a zaune a parlourn da Aunty Jameelah da Zarah ga qawayen nata guda uku qanqameta yayi a jikinsa cikin rawar murya yace “shi… shikenan Hajiya tazo ta rabani da rayuwata Hajiya Umaimah rayuwa tace kada kice zaki rabamu wlh alhakin kisana zai rataya a wuyanki saboda inason matata Hajiya cikine da ita kada ki rabamu ki tausayawa yayan mu wlh mutuwa zanyi idan babu Umaimah a cikin gdana”

Miqewa Hajiya tayi tana zagaya parlourn tace “Zarah shiga ki hado mata kayanta ai ba wannan ne karon farko da mace take haihuwa a gda ba wlh Hameed bazan bar yar qanwata ta salwanta saboda kai ba kaidai na sallama ka tunda kai ka daukowa kanka kara da kiyashi dama ai hausawa sun fada jaye-jaye ke sanya jidali wlh baka fara kuka ba Hameed indai Salma ce gakanan gata ko kasheka zatayi babu abinda ya shafi Zulaiha amma Umaimah kam saika barta ko itace ke busa maka numfashi….”

Fuzgo hannun Umaimah tayi da qarfi shi kuma ya riqeta qam a qirjinsa yace “wlh Hajiya ko zaki tsinemin bazan rabu da matata ba saidai ki kasheni” tsayawa tayi sororo tana kallonsa yayi qasa da gwiwarsa ya durqushe yana wani irin kuka me ban tausayi jikinsa yana rawa yace “meyasa kullum tausayinki ya qare akan Umaimah Hajiya ni bakya tausayina meyasa bakwa yiwa rayuwata uzuri bayan bani na tsarota haka ba kuma ban isa na canzata ba meyasa kullum burinki nayi miki biyayya ni na cutu Hajiya ya kikeso nayi ya kikeso na kasance gwauro babu Umaimah ina Hajiya bazai yuwu ba bazan iya biyayyar dazan cutar da kaina ba…”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button