GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sake jan jiki yayi kusa da Hajiya yace “Hajiya wlh aurena da Salma qaddara ce wlh tallahi billahillazi La’ilaha illah huwa Hajiya banajin ko digon soyayyar wata mace a raina bayan yar’uwata kuma matata Umaimah Hajiya na tsani ko tafiya ta tasomin wacce zata nisantani da kwanciya a jikin matata Umaimah Hajiya babu macen da nake samun nutsuwa da ita kuma nasa a raina zan samu bayan Umaimah Hajiya babu macen da zata iya dauke lalurar rayuwata bayan Umaimah saboda ita kadaice take sona domin Allah kuma ita kadaice take gamsar dani”

Yanda yake mgnr yana kuka muryarsa na daukewa ne yayi bala’in tsorata Umaimah ta fashe da kuka ta qanqameshi tace “Hajiya badon halinmu ba kiyi hqr wlh Hajiya inason mijina kuma baa kaina aka fara kishiya ba Hajiya shikenan idan kin rabani dashi haka zan rayu bazanyi wani auren ba idan har kin yarda zakita kallo na bazaki sake auradda ni ba to na amince ki rabamu idan kuwa kinsan zaki qara auraddani to kiyi hqr ki barni na rayu da dan’uwana Hajiya bansan waye zan aura ba meye halinsa matansa nawa idan bashida mata inada tabbacin wataran bazai min kishiya ba banida shi saboda haka Hajiya ki tayamu da addu’a Allah ya bamu ikon cinye jarabawarmu”

Ba qaramin sanyi kalamansu sukasa jikin Hajiya yayi ba ta dubesu a sanyaye ta tsugunna ta kama hanun Umaimah hawaye ya kwace mata tace “mar’atussaliha baki cancanci suna Umaimah ba duk da itama asalin mai sunan sahabiya ce kuma baiwar Allah amma naso ace sunanki Fadimatu saboda halayyarki tayi kama data Nana Fadima itace macen da har kullum take fifita farin cikin mijinta fiye da nata Umaimah da ace a zamanin annabi Muhammad (S.A.W) mukazo inada tabbacin kina cikin khulafa’ul rashidun ko kuma kina daya daga cikin matan da annabi ya dafa kawunansu yasa musu albarka kuma ya roqa musu albarkar ubangiji duniyarsu da lahirar su tabbas ina alfahari da samun ya a gareni kuma Ina alfahari da kasancewarki suruka a gareni Umaimah dama ace inada wani dan bayan Hameed wlh rayuwarki bata dace da azzalumin mutum irin Hameed ba da kullum baya sanin haqqin kowa sai nashi tabbas mgnrki gsky ce addu’a zan tayaki da ita Allah ya kareki da sharri da makirci irin na jinin Hajiya Talatu kishiya juji shidai daya debo da zafi ya qare a bakinsa”

Miqewa tayi ta taka zuwa tsakiyar parlourn ta tsaya ta sake share hawaye ta juyo tace “bazan maka mugun fata a cikin aurenka ba kuma zan tayaka da addu’a tunda kaima nawane ban isa na canza maka suna ba amma ka sani auranka da Salma babu wani alkhairi saboda haka bacci ba naku bane ku daure ku rinqa tashin tsakar dare kuna salatulduha sannan ku rinqa azumi da yawan karatun qur’ani hakan zai zame muku kariya daga sharrin shaidan da sihiri ko wanne iri ne duk da kaidai ka riga ka shiga hanu wlh na sani kuma na yarda auranka da Salma aikin sihiri ne”

Tana gama fadar haka ta fice daga parlourn suka kalli juna ita dashi taga yanda yake kwararar da hawaye masu dumi zuciyarsa tana wani fat² tayi saurin rungumeshi tace “ina tare dakai mijina a kowanne hali ina fatan kazama kaine mijina a jannatul-ma’awah” miqewa yayi ya dagata cak bai damu da yawan mutanen da suke gurin ba ya haura sama da gudunsa saboda bayason surutu.
Duk wanda ke gurin saida ya zubar musu da hawaye Saudat Alfah tayi ajiyar zuciya tace “bantaba ganin soyayya me ratsa zuciya daban tausayi irinta Umaimah da mijinta ba wlh ko soyayyar Aunty Murjanatun mu da Muhammad mijinta batakai wannan soyayyar dadin kallo da burgewa ba tabbas Umaimah yar aljannah ce kamar yanda Hajiya ta fada saboda dukkanmu na tabbata babu wadda zata iya yiwa mijinta wannan sadaukarwar qaunar akan kishiya kishiyar ma wacce take barazana ga rayuwarta da lafiyarta da mijin ma gaba daya dole mu jinjinawa Umaimah Umaimah na sallama miki kinyi nisan da bazamu tadda ke ba”

Sukuwa suna haurawa ya direta a gado ya fara romance dinta ta riqeshi da sauri tace “bloody muna da baqi fah a gdannan ka sani” lumshe idonsa yayi yaci gaba da matsata kamar lemon tsami yana cire mata kayan jikinta yana cewa wlh ko a gabansu zan iya turmusheki Hearty inajinki a duk wani bangare na jikina bloody soyayyar jini daban take da kowacce soyayya a duniya baayi kamarki a duniyata ba kuma ba zaayiba kece farko kece qarshe Umaimah ni da ke abu dayane zuciyarmu daya jininmu daya komai namu dayane Umaimah”

Da wadannan kalaman suka fara tsotse kansu suna shafe²nsu wanda Allah ya sani Umaimah badon dadi takeyi ba tanayi ne kawai donta faranta masa saboda ta lura yayi nisa sosai saida ta tabbatar ta gamsar dashi suka shiga sukayi wanka sukayi sallar azahar ya tayata ta shirya tsaf cikin wata atamfar Super Holland ja tayi kyau matuqa duk da ramar da tayi shima ya shirya cikin wani blue din yadi dake jikin atamfar tata da blue saiya zamana kamar anko sukayi nan fa suka bata lkc wajen yin hotuna sune har parlour ana suba selfie sudai su Aunty Jameelah da Aunty Zarah da Sa’ud da sauran mutane sai suka zama yan kallo a gdan suna sha’awar soyayyar ma’auratan.

Bayan sun gama haukan selfie dinsu suka zube a parlourn suna dariya dariyar tasu saida tasa kowa ma dariya harga Allah shidai ya manta da mutane a parlourn saida yaji sunyi dariya ya shafa kai cike da kunya yace “inajin yunwa bloody” miqewa tayi ta shiga kitchen ta zubo masa abincin da su Aunty Zarah suka girka ba kunya ya noqe kafada yace “muje na tayaki muyi namu ni duk abincin daba hanunki ne ya girka ba ba dadi yakeyi min ba”

UMMUH HAIRAN CE…✍????
[1/28, 8:26 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍????: G.U

Bata iya yimasa musu ba ta miqe suka shiga kitchen din basuyi wani abu me wahala ba jallop din taliya ce sukayi ta zuba masa takai masa sama ta hada masa lemukansa da komai takai masa ya zauna zaman cin abincin itakuma ta sace jikinta ta koma parlour sukaci gaba da hira da baqinta dauriya kawai takeyi tana yaqe saboda bataso tabada qofar da zaa fahimci rauninta amma zuciyarta cike take da fargaban zuwan Salma gdan yau hakanan dai suka yini har dare sannan duka suka watse suka tafi suka barta saida ta rakasu har inda suka aje motarsu sannan ta dawo ta kwanta a parlourn tana tunanin wadanna irin mutane ne dangin Salma da bazasu iya zuwa inda take ba saidai idan ta fito su rinqa binta da kallo kalma wata Mata ta tuna lkcn data rakasu Aunty Jameelan bayan sun tafi ta juyo zata dawo sukayi karo da ita ta fito daga bayan dakinta taja baya da sauri kawai sai taga matar tayi murmushi tace “Umaimah kike ko?”

Daga kai tayi da alamun mamaki tace “eh lfy?” Sake fadada fara’arta tayi tace “aa to lfyr kenan dangin kishiya kam ai bakya tambayi lfy a gurinsu ba koda yake meye ma na bata bakina abuda saura qiris” wannan kalamai sune sukeyi mata yawo a zuciyarta “saura qirin meyene to saura qiris din?” Tambaya ce da bata da amsa saboda haka tayi luf a kujerar tanata zuba hailala da salatin annabi har akayi sallar insha ta tashi ta shiga dakin qasa tayi sallah ta haura saman harta nufi dakinta sai kuma ta juya ta shiga dakinsa ta bude ta shiga yana kwance da Shurafah rungume a qirjinsa idanunsa a bude suke ya zubawa pop din dakin ido har ta qarasa kusa dashi ta zauna baiji ba saida ta tabashi sannan ya dawo hayyacinsa ya sauke idanunsa akanta tare da sauke ajiyar zuciya tayi murmushi tace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button