GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ke dan kutumar ubanki tashi wlh saikin fadamin ubanme kikayi min na kusanceki” dagata yayi yayi wani wurgi da ita kanta ya hadu da bango bai damu da jinin daya balle mata a kanta ba ya dauki rigarsa yasa a firgice ya nufi qofa ya bude da gudun tsiya wanda shi kansa baisan ya iyashi ba ya nufi bangaren Umaimah a bude yaga qofar hakan ya bashi mamaki amma bashi da lkcn wannan sama ya haura da gudu yana kiran “bloody kada ki zargeni don Allah tsaya kiji wlh bansan ya akayi naje dakin shegiy….” Mgnr ce ta maqale masa ganin dakin nata a bude ya danna kai ga mamakinsa babu kowa a ciki ya bude bandakin nan ma babu kowa fitowa yayi ya shiga dakinsa yanata doka mata kira fadi yake “Ummuh Shurafah kada kimin haka fito kiji banason irin wannan wasan wlh bada niyya nayi ba basan ya akai naje dakin ba kai anya ma kuwa nine?” Tsayawa yayi cak bayan ya gama karade gdan lungu da saqo bai ganta ba yana kiranta yana kiran sunan Shurafah yana cewa “na shiga ukuna Umaimah bake kadai bace kada kisawa kanki damuwa wlh yau zan saketa na tsaneta Umaimah kada ki wahalar da kanki da cikin jikinki”
Waje ya sake fita ya nufi gurin megadi yana fadin “Mal Ibrahim Ibrahim Ina Ummuh Shurafah take Ina kaga ta tafi?” Cikin in…Ina yace “ranka ya dade jiya misalin 12:30am Hajiya da Daddy sukazo suka dauketa da alamun batada lfy….” “What? Sukazo suka dauketa ina ina ni meyasa bata fadamin batada lfy ba Mal Ibrahim meye yake faruwa ne?” Juyawa yayi da sauri ya koma part din Umaiman ya fada wanka ya tsarkake jikinsa a gurguje yayi sallah ya dauki key din motarsa lkcn bakwai na safe ya fita a guje zuciyarsa tana bugawa da qarfi yama rasa tunanin da zaiyi yana zuwa gdan megadi yace masa yanzu suka shigo gda ya shiga yayi parking ko kashe motar baiyi ba ya shiga gdan a guje sukayi karo Daddy yana qoqarin fitowa daga dakin Hajiya da jariri a hanunsa matsawa yayi da sauri yace.
“Yawwa Daddy ina take ta haihu ne?” Kallonsa yayi batare da ya nuna masa wata damuwa ba yace “Eh Allah ya sauketa lfy Hameed bata mutu ba Allah bai cika maka burinka na kasheta da kayi niyyar yi ba banda abinka Hameed ai ko baka batta cikin halin ciwo ba takardar sakin daka batama shaida ce ta baka buqatar zama da ita to yau dai qurunqus dan kan barya Hameed aure babu tsakaninka da Umaimah kuma aure indai irin nakane to Umaimah ta barshi har abada wlh indai irin zaman da tayi a gdanka ne gara nasata a gaba nayita kallonta” duk cikin kalaman na Daddy babu abinda ya fahimta ya dago zaiyi mgn Hajiya dake fitowa ta daki bakinsa har saida ya fashe tace “sannu da zuwa tatacce dan’uwan koko ubanme kazo fada mana kazo ka jaddada mana ka saki Umaimah saki biyu ne ka cike mata ya zama uku?” Murmushi tayi me ciwo tace.
“Ai dama kayi zamanka gurin matarka abar qaunarka basai kazo ba saboda zuwan naka bashida wani amfani” dagowa yayi cikin tashin hankali da kidima yace “na roqeku badon halina ba ku taimakeni ku warwaremin qullin nan wlh fahimci me kukeso kuce ba” kallonsa Daddy yayi kallon tsaf yace “waye Abdulhameed Adam Hameed Shuwa ne?” Dagowa yayi yace “nine Daddy” ya kuma cewa “wace Umaimah ne?” Sake dagowa yayi yace “qanwata ce kuma matata ce Umaimah” murmushi Daddy yayi me ciwo yace “to tunda hakane karanta wannan takardar rubutun waye a jiki?” Miqa hanunsa yayi jikinsa na rawa ya karbi takardar daya rubuta da manyan kalmomi “NI ABDULHAMEED ADAM HAMEED SHUWA NA SAKI MATATA UMAIMAH SAKI BIYU BATARE DA WANI DALILI BA
Tashin hankali wanda baasa masa rana wata uwar zabura da yayi yayi cilli da takardar yana ja da baya yana girgiza kai yanason bude bakinsa amma ya kasa wani mugun jiri yakejin yana fuzgarsa kuma ya kasa tsayawa da tafiyar da yakeyi da baya da baya Daddy ne ya miqawa Hajiya Shuraif dake hanunsa ya tafi da gudu ya ruqoshi yana dafe da kansa dake sara masa yace “rur.. rubuta nane Daddy amma yaushe na saki matata ni da kaina na saketa Daddy aa wlh bani bane”……..
Kuyi hqr da wannan banida charge kuma inason muyi fira
UMMUH HAIRAN CE…✍????
[1/31, 8:55 AM] UMMUH HAIRAN CE…✍????: GU
Yana fadin haka yayi baya luuuuuu cikin fitar hayyaci ya dafe saitin zuciyarsa data daukar masa wani mugun zafi yaci gaba da cewa “ya yama zaayi kuce na saki matata me tayimin dazan saketa bayan itace rayuwata Daddy koda Umaimah yankar jikina takeyi tanaci wlh bazan iya rabuwa da ita ba Daddy ku duba lamarin nan kuyimin rai wlh Allah Daddy bansan sanda na rubuta mata takardar nan ba bansan meye ya faru dani daran jiya ba a dakin Bloody na kwanta amma dana tashi da safe saina ganni a dakin Salma wlh Daddy bansan komai akan takardar nan ba ku dabeni kuji qaina ku tausayamin kada ku rabani da matata”
Yana mgn muryarsa na kakkatsewa saboda tashin hankali kamashi Daddy yayi ya zaunar dashi a kujera ya dora masa Shuraif a cinyarsa yace “abinda ya faru ya riga ya faru ka saki Umaimah a daren jiya ta haihu a daren jiya ta tsarkaka daga iddarka ga danka nan kasa masa albarka dama rabonsa ne yasa ta koma gdanka nayi maka shisshigi nayi masa huduba da sunan marigayi babanku da fatan banyi laifi ba don kai yanzu hukuma ne sai lallashi”
Shigewa Daddy yayi daki ita kuma Hajiya taja qofar dakin da Umaimah take ciki ta datse da mukulli ta nufi kitchen tafi awa daya a kitchen din ta fito ta tarar dashi a zaune tayi mamakin ganin yanda ya rungume Ahmad Shuraif a qirjinsa numfashin sa yana sarqewa bata kobi takansu ba ta shige dakin hakan ya bashi damar miqewa yana hada hanya ya nufi cikin dakin ya tsaya a bakin qofar ya zubawa Umaimah manyan idanunsa da suka kada sukayi jawur tana kwance nannade da blanket amma yana jiyo shassheqar kukanta daqyar ya iya jan qafarsa ya matsa ya zauna a gefen gadon yana jiyo sautin muryarta tana maimata kalmar innanillahi wa Innah ilaihir raji’un hanu yasa ya janye bargon data rufa dashi ta dago da sauri suka hada ido tayi saurin kawar da nata yakai hanunsa zai ruqo nata tayi saurin make hanunsa tace “kada ka tabani Hameed na haramta gareka har abada insha Allahu sai Allah ya sakamin wannan baqin cikin daka qunsamin Hameed nayi danasanin saninka a rayuwata bantabajin tsanarka da tsanar zuri’ar dake tsakanina dakai ba sai dama ashe haka so yake meyasa ka cusamin sonka da tausayinka bayan kasan bazaka rayu dani ba Allah ya isa tsakanina dakai Hameed kuma wlh azeem idan baka daina bibiyar rayuwata ba zan gudu ku nemeni ku rasa kowa ma ya huta”
Fitowar Hajiya ne yasata tayi shiru da kukan da takeyi ganin a zaune yayi mugun qonawa Hajiya rai ta nunashi da hannu tace “tashi ka fita daga dakinnan” dagowa yayi yace “amma Hajiya ya kamata ku tsaya ku fahimceni waini meyasa kullum ni me laifine bakwa yimin uzuri Hajiya kada idonki ya rufe kema kamar yanda na bloody ya rufe take caccakamin maganganu masu ciwo son ranta kuyimin adalci kafin yanke hukunci naji ni me laifine amma ku tsaya kuyi tunani da hankalina zan saki Umaimah har saki biyu wlh Hajiya ko maqiyina yasan inayiwa bloody son da bazan taba yiwa wata mace ba a duniya bazan iya rabuwa da itaba itace rayuwata Hajiya itace farin cikina”
Wani murmushi Hajiya tayi me ciwo itafa ta fara tantamar hankalin dan nata saboda kalaman gaba daya babu hankali a cikinsu dauke yaron tayi daga jikinsa ta kama hanunsa tace “miqe ka tafi gdanka safiya ce yanzu matarka tanacan tana jiranka ka cika mata burinta tayi nasara ta rabaka da matarka me qaunarka domin Allah ga gidannan ku zauna ku kadai” tana fadin haka ta turashi waje ta rufe qofar.