GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVEL
“Waye wanda kuka jera dashi dazu kuka shiga ciki dashi” batare da damuwar komai ba tace “abokin mijina ne” ya kalleta da sauri yace “abokin mijinki ince dai ba mijin naki bane?” Tabe baki tayi tace “ba abin mamaki bane idan kaji cewa ya zama mijin nawa ma…” wani uban birki daya taka shine yasata saurin dagowa tayi baya tayi gaba kawai saita fada jikinsa ya sauke wata ajiyar zuciya me qarfi yasa hanunsa ya maqaleta daga ita har shi sunajin wani irin yanayi a jikinsu janyewa tayi da sauri ta koma ta zauna ya sauke numfashi ya bude idanunsa akanta yace.
“Don Allah kiyi hqr da wasannan da kikeso muyi wahala zansha ki bani dama ta qarshe bloody idan har nayi wasa da ita kiyimin duk hukuncin da kikaga ya dace kada ki tausayamin amma yanzu ni abin tausayi ne a gurinki saboda zuciyata takasa hqr dake nayi iyakar qoqarina naga na cireki a raina amma na kasa nayiwa Daddy mgnr aurena dake tun jiya yace bazai miki dole ba sai abinda kikeso zaiyi miki har yana gargadina kada na takura miki”
Kallonsa tayi da wani irin salo na baka da wayo tace “aure kuma” dagowa yayi yace “Eh haka nace” dariya tayi sosai tace “tab kana ruwa iya wuya kuwa” daga haka bata kuma cewa komai ba shima baice ba yaja motar suka tafi gdan gonarsa yakaita yayi horn megadin ya bude ya shiga gurin ya girma sosai ya qawatu bangaren kaji daban na kifaye daban na gigs daban na shanun madara daban da bangaren tsuntsaye irinsu talo² dawisu da jimina abun dai baa cewa komai.
Wata qofa ya bude ya shiga ya tsaya yana jiranta amma sai yaga ta cake a waje ta tsuke fuska sosai ta yanda saida yaji gabansa ya fadi ta motsa dan qaramin bakinta tace “bance da Hajiya zan biyoka muzo nan ba saboda haka kazo ka mayar dani gda ko na fita na nemi abin hawa”
Murmushi yayi ya fito ya janyo qofar ya rufe ya qarasa kusa da ita yace “kina tsoron kada nayi miki fyade ko? Hmn” itadai batace komai ba suka koma suka shiga motar suka tafi gda suna zuwa ta bude zata fita ya ruqo hanunta ta juyo idonsu ya hadu tayi saurin janye nata yace “ki daina jamin aji Umaimah ni ba wanda zaki jawa aji bane ko yau kika amince min gobe zaa daura aurenmu so nakema naje nayi miki VISA saboda nagaji da zaman kadaici wlh kuma duk saboda kene bloody bazan iya zama da wata mace ba bayan ke idan har na rasaki to na hqr da aure har abada balle ma bazan rasaki ba wannan karon wancan ma qaddara ce ta rabamu” kalaman nasa mugun qonanta zuciya sukeyi saboda haka ta fizge hanunta ta shiga cikin gdan a fusace………
UMMUH HAIRAN CE… ✍????
[2/4, 9:05 AM] UMMUH HAIRAN CE…✍????: GU
Yanda Hajiya taga ta shigo gdanne yasata zuba mata ido sannu kawai tace mata ta bude qofar ta shiga daidai lkcn dashi kuma ya shigo gdan shima baiyiwa Hajiyan mgn ba ya shige dakinsa ya kwanta ya lura wahala zaisha sosai da Umaimah tunda ya fahimci babu digon tausayinsa a qwayar idonta amma duk da haka zai jure zai gwada tasa baiwar har ya cimma gaci.
Wayarsa ya dauka yayi short write ya tura mata tana zaune a bakin gado tana feeling din yayanta tana kallonsu saqon nasa ya shigo ta dauka ta bude
Tunda na rasaki Umaimah mace ta fita a raina ki daina jin tsorona wlh ba Hameed din da bane nasamu lfy ki bani dama bloody banason komawa California batare dake ba banajin dadin rayuwa ni kadai bloody inason mu rayu tare yaranmu su rayu a cikin kulawar mu inason twins dina amana tace babansu ya bani su tun kafin a dora masa ajalinsa yayimin kyautarsu tun kafin suzo duniya ki aminci su rayu qarqashin kulawata
Jikinta ba qaramin sanyi yayi da kalamansa ba wata kalma daya da D.S yayi mata ranar data haifi twince ta fado mata “nayi farin ciki da haihuwar nan Sweet duk da inaji a jikina bazan rayu dasu ba amma banajin komai saboda Hameed yana raye”
To dama kalamansa abinda suke nufi kenan ajiyar numfashi tayi cikin sanyin jiki da sallamawa rayuwa farin ciki wata kalmar da yake yawan maimata mata ta dawo mata.
“Umaimatu ina kishinki bana fatan ko Nazir qanina ya riqe hanunki mutum daya tak nake burin bayan bana numfashi ya zama replacing dina Sweet Hameed nake nufi da ace zan iya dana halatta masa ke ina raye amma bazan iyaba course inasonki sonda idan na rayu babuke zan galabaita sweet zansha wahala fiye da wadda Hameed yakeyi saboda ke dalili ni qaramar zuciya ce dani bantaba shiga tashin hankali makamancin wannan ba kiyi hqr kada ki qullaceshi wlh ba laifinsa bane sharrin qaddara ce yanzun wacce ta zama sanadin rabakun tana ina? Tana asibitin mahaukata idan ba saaba ita da hankali har abada itama ki yafe mata duk da nasani Hameed bazai yafe mata ba saboda ta cutar dashi ita duniya qaramin gurine da zaka zo ka taka rawarka ka kauce wani ya taka Umaimah ki yarda da hakan watarana _muma zamu kauce mu rabu rabuwa ta har abada rabuwar da bazaki sake ganina ba”
Wannan kalamai suna dukan zuciyarta dole tayi biyayya ga kalamansa wannan kamar wasiyya ce adali aqili managarcin mijinta ya bata miqewa tayi a sanyaye ta zaunar da yaran ta nufi bathroom taci kukanta me zuciya ta jima kafin ta daure ta miqe ta fito a zaune ta tarar dashi yana yiwa twince wasa ya dauki madara yana basu yana mitar anbar masa yara da yunwa bata kulashi ba ta fice daga dakin ta shiga kitchen ta zubo abinci ta zauna a dinning din tana juya cokalin Hajiya tana ankare dasu amma batace musu qalaba tanajin lkcn da Hameed din ya shiga dakin taso yi masa mgn amma ta lura duk a zauce yake wani abun ma baisan yanayi ba tarasa wanne irin so yakewa Umaimah kamar wanda tabawa ruwan nono yasha indai yana ganinta baya iya control mind dinsa har tausayinsa takeyi musamman wannan karon data lura kwata² baya gaban Umaimah.
Zama Hajiya tayi a parlourn tana zaune yazo ya wucceta hankalinsa nakan Umaimah yaje ya zauna a kujerar kusa da ita ya ajiye twince suka tafi harkarsu yasa hannunsa ya dago fuskarta yaga yanda hawaye kebin kuncinta gabansa ya fadi sosai ya sanya hanunsa ya fara share mata hawayen yana girgiza mata kai idanunsa nakanta yace “don Allah kiyi hqr wlh ban turo miki text din da nufin bata ranki ba bloody bani na dorawa kaina sonki ba Allah ne ya jarabceni da qaunarki tun bakisan kanki ba wlh bazan iya rayuwa da wata mace ba da zan iya kema shaida ce a yanda nake da tuni nayi aure amma na hqr na zabi na rinqa azumi akan na hadaki da wata Umaimah ke dayace matata bazan qara hadaki da wata mace ba….”
Daga masa hanu tayi tace “ya isheni haka Hameed ka matsamin wlh banason ganinka banason tuna baya shiyasa bana fatan sake rayuwa dakai Hameed me zaka fadamin na qara yarda dakai wacce kalma ta rage maka da zaka fadamin tayi tasiri a zuciyata ina cikin halin mutuwa ko rayuwa ina tsananin buqatarka da buqatar taimakonka lkcn da kowacce mace take samun soyayyar mijinta da tausayinsa lkcn da ya kamata kaji qaina ka tausaya min lkcn ne ka yanke shawarar rabuwa dani rabuwa ta qasqanci da wulaqanci Hameed saki biyu a lkcn da nake naquda ba lallai ne na tashi naci gaba da rayuwa ba ma nayi maka Hameed me kake tunanin zakayimin na manta da wannan abun a rayuwata Hameed wannan abun bazan taba mantawa dashi ba a rayuwata Hameed banyi rayuwar farin ciki ta shekara guda dakai ba tunda na fara rayuwa dakai cikin damuwa nake daga wannan matsalar sai wannan amma qoqarin dannewa nakeyi saboda so da tausayinka daka cusawa zuciyata Hameed bansan dadin aure a gdanka ba sai a gdan D.S wlh Hameed abubuwa da yawa idan na tuna badan arzikin zumunci ba dako gaisawa bazamu keyi dakai ba Hameed na tsani zaman aure dakai bana fatan sake shi idan ma kuma qaddara tasa na amince da sake rayuwa dakai to kasa a ranka Umaimatun daka sani da me sadaukar da farin cikinta akan na wani me qoqarin tursasa zucciyarta tayi biyayya ko bataso Umaimah shashasha da batasan ciwon kanta ba bata da choice a rayuwa sai naka Hmn Hameed wlh babu kaffara a kaina yanzu bada ita kake zaune ba na shaqi iskar yanci wata qaddarar gata ce rabuwata da qaddarren aurenka ta sanya idona budewar da bazan taba zabar farin cikin wani fiye da nawa ba”