
Imran..!
Sai Hawaye sharr..Baffa Kabiru ya tashi Daga kujeran Dake gefen Sajida ya nunama Imran alamun ya zauna ba Musa yaja ya zauna Cikin bayyana Jimaminsa sai dai bai nuna afuska ba,inteesar na gefen Munari duk sai taji Kishi ya kamata kada fa ace Mijinta ya sake auran Sajida..?domin bazata iya zaman Kishi da ita ba..!
Sajida ce ta kara kiran sunan Imran yasa ya amsa mata Cikin Muryansa mai Cike da Zati tana kallomsa Tace”Imran nasan ka Tsane ni ko..?
Sai kuka wiwi sai tari mai Hade da Jini Imran yaji wani iri acikin Ransa Hannun Sajidan da ba”a sakama Drip ba ya Rike gam yana Fadin”Wlh ban Taba Tsanarki ba Sajida..!
Yafada yana jin Rauni da Taausayinta sai dai ba wai don yayi Nadaman Sakinta ba A”a baya sonta bazai aureta ya Cutar da ita ba.
Sajida tace cikin muryan kuka..”Meyasa ka sakeni..?meyasa baka sona..!
Imran ya Runtse ido kafin ya Bude yace”Na sakeki ne saboda bana sonki na aure ki in na Zauna Dake zan kwareki..Inteesar nake so..Kinga bai kamata na Zauna Dake ahalin ina son Wata ba..Kuma ni zuciyata Tana Girmama Ra”ayina mganar na Tsaneki bata taso ba..Ina sonki Soyayya irin ta yar”uwa da Dan”uwanta..!
kafesa Tayi da ido kafin tace”Kana sona Kamar kanwarka Munari.?ko haka na samu ma na gode..!
Take Fada Tana Hawaye Hannu ya saka yana Dauke mata Hawayen Lokaci Daya yana Fadin”Ki Daina kuka..Munari ta zama Old kece sabuwar kanwar tawa Tilo….!
Tana Dariyan DAuriya tace”Ko yau na Mutu naji Dadi..!
Imran yace”Ba mutuwa yanzu kamwata..Maza kitashi Aure ma zan yi miki da yardan Allah..!
Cikin Rinanun idanunta tace”Wazai aureni…?
Bai amsa mata ba ya Dago kansa yana kallon Khalil Dake kallonsa Shida Sagir Gabadaya ma Dakin Hankalunsu na kansu Banda Inteesar da Kishi ya Turnike tun sadda ya Rike hannun Sajida ta kauda kanta.
Tashi yayi Tsam yaje ya Riko Hannun Khalil wanda ya saki baki yana kallonsa Munari ma haka dasu Abba Har gaban Sajida ya Zaunar dashi inda ya tashi ya Dauki Hannunsa danata ya Hada yana kallonta yace”Ga Mijin dana Zaba miki kanwata ina Fatan bazaki bama yayanki kunya ba..!
Yafada yana kallomta kafesa Tayi da ido kafin tace”yana sona ne..?
Imran ya kalli Khalil dayayi sunan Zaune Kafin yace”Sosai ma..Tambayesa kiji..Wazai ki Zangadediyar yarinya kamarki Diyar Lauyoyi jikar Lauyoyi..!
Ya karishe Fada da Sigar Zolaya.
Sajida ta kada kai Tana dariya da Hawaye Lokaci Daya Tana kallon Khalil da jikinsa ya gamayin Sanyi ya Imran zai mai haka ya manta da Munri ne kamar yadda Itama Munarin ke Tambayan kanta haka suna kallon juna ita dasu Hafsah da inteesar.
Sajida na kallon Khalil tana Fadin”Kana sona da gaske..?
Tafada Cikin karyayyiyar murya Cikin Rauni da saka rai Imran ya Daki Kafadan Khalil bayan ya Dago ya kallesa Kallon ya zakamin haka.?
Bazai iya watsamai kasa a ido ba yasa ya Gyadamata kai yana Fadin”Indai kin amince ko gobe ne A Daura mana aure..!
Sajida Sai Farinciki ya kamata ko bata auri Imran ba ko bai sota ba ya Fadamata bai Tsaneta ba sannan itama Zatayi aure kamar kowa sannan Zata auri abokinsa Daman haka Rayuwa ta gada ba Lalle ne sai mun samu abunda muke so ba..
Ido ta Runtse sai Hawaye gabadaya Kowa sai jikinsa yayi sanyi Khalil ya Kasa Hada ido da Munari Lokacin Datake kallonsa na yaya Zakayi Dani..?
Imran ya isa gaban Baffa Kabiru yana Fadin”Baffa Khalil abokina ne..Zaka bashi Auran Sajida..?
Baffa bai san me zai ce ba iya Kafadan Imran Daya Dan Daka yana Fadin”Allah ya sanya alheri..!
Abun fa na Imran ba wasa bane kamar yadda wasu suka Dauka.
Gaban Mami ya isa kafin yace”Mami Zaki bama abokina Khalil yarki..Kin gansa ko Sigari Bai taba Shaba..Sai dai Ma”ikancin banki ne kamata babansa kuma Malamim Jami”a ne kamar Mahaifina ba Lauya bane kuma ba Jikan Lauyoyi bane..!
Yafada yana kallonta Mami kuka ya Kamata batasan Sadda ta Durkushe kasa ba Tana Fadin”Ku yafemin don Allah ku yafemin.!
Yadda Take kukan sai ta bama kowa Tsausayi Imran ya Saka Hannu ya Dagota yana Fadin”Haba Mami..Bai kamata ki Dukamin ba..Nima ya kamata na Duka miki nima ai nayi Miki Rashin kunya ki yafemin.?
Mami na Kuka Tana Fadin”Wlh bakamin komai ba Ni nayi muku..Maimunatu Malami da Mustapha ku yafemin Kabiru kaima ka yafemin da duka sauran wadanda na Batawamawa ku yafemin.!
Kuka take jiri neman gadata Imran ya Riketa da Sauri Khamis yazo ya Taimakamata Daddy yadauko mata Kujera ta Zauna Abba ya Miko Ruwa suka Bata ta karba tasha Tana Dauke kwallarta Tana Musu Godiya Abba da Daddy sukace su bata musu komai ba sun yafe mata.
Inna Maimunatu ma haka Inna Bintalo ma sai Hawaye ganin yadda Mami ke kuka itama ta Roki yan”uwanta gafaran Abunda Tayi ta yi na Gulma da Bin bayan karya sukace sun yafemata.
Munari dai ta kasa mgana kanta na kasa Khamis ya bama Imran hannu suka yi Musabaha bayan sun ma juna Sallama
Khamis ya Kalli Munari kafin ya kalli Imran yana Fadin”Babban yaya Tunda dai am min kafa awajen Inteesar sai ka bani Dayan kanwar Taka Tunda naga kana ta badasu ka manta Dani..!
Gabadaya sai da kowa ya Murmusa Har Sajida dake kwance.
Imran ya shafa kansa yana Fadin”Wacce Daga ciki..!?
Hafsah dai Na Riga na bama Abokina Sagir..Sai Autar Abba Daman ta ishemu na baka ita..!
Ya juya wajen Munari Dake Hawayen wannan Karfin Halin na an rabata da masoyinta za”a likamata wani.
Yace”Ke..Ga Khamis nan shine mijinki bana son gaddama..Saura ki rainasa yayanki ne kuma sojane kinsan sauran..kai kuma in tayi maka ba Daidaita ba ka sauya mata kammani ni na baka Umarni..!
Khamis ya Ramkwafa yana Fadin”An gama Babban yaya..!
Imran ya Dafa kansa yana Fadin”Yauwa dan abarka..Kafi sauran ladabi..!
Yafada yana Hararansu Khalil Gabadaya Wajen sai da aka Saka Dariya ganin yadda Imran yayi Harda Mami da Murna da kunya suka kamata Ita taki Imran saboda yana shan Taba yau ga Malami zai bama D’anta Yarsa wanda har da mata yayi mu”amala Mami ta ji kunya Nadama Ta kara shigarta.
Khamis gefen Munari ya koma yana mata mgana Sagir na gefen Hafsah Hakama Khalil yana gefen Sajida ya Duka yama mata mgana Domin Lamarin Tsarin Ubangiji ne matar Mutum kabirinsa.
Imran ma Wajen Inteesar ya koma ganinta Tana Tura baki Ido ya kanne mata yana Fadin”Sorry..!
Tura baki Tayi ta kauda kai yana Dariya ya rikota su Abba kam suna ta kara bama Baffa Kabiru baki kan ya saurari Mami Asma”u su yusuf kam komai yayi daidai suna ta mgana dasu Sadam Umma na Tare dasu Inna Maimatu kafin Lokaci kadan gabadaya an samu Fahimtar juna gaban kowa da kowa Mami ta Duka ta bama Mijinta Hakuri ya Dagota yace ya yafemata kuma yashaida mata ita din Matarsace tun sadda ya Saketa yan”uwansa suka saka ya maidata Mami ta karajin kunya ashe haka su Abba suke..?yadda taci ma Daada Zarafi basu Riketa aransu ba da sun Riketa da basu ceci auranta ba Hakan ba karamin Dadi yayi ma Khamis da Umaima ba suka Hadu suka Rumgume Mamin da Baffa Kabiru Sajida na kwance Tana Miko hannu suka Tafi gareta suka Rumgumeta Mami nata kuka tana share ma yarta Hawaye
Kowa sai Dauke kwallar Farnciki yake yi Munari ma Tuni ta Daina kuka suna ta mgana da Khamis Domin ta ma Cire Khalil Daga Lissafinta Lokaci Daya Taji Khamis din ya kwanta mata kamar yadda Shima anashi Barayin yaji Sajida tayi mai daidai dashi Duk tun a hanya sagir ya bashi Labarin abunda ya Faru da komai da komai.
Likita ne yazo ya Korasu waje suka Duba Sajida suka mata allura Barci Likita ya Fito da Murnan ganin Chanji Tare da tabbatar musu indai Sajida Zata kasance Cikin Farinciki Zata Samu kanta dayardan Allah
Sai da suka baro Dakin ne Imran ya Radama Yusuf wata mgana akunne shi kuma yaja Daddy da Baffa Kabiru ya Fada musu suna Dawowa suka kalli Abba Daya Tsargu Baffa Kabiru yace”Malami kaima aure zam maka nagaji da ganin ka ahaka..!
Abba ya Zaro ido gabadaya wajen aka Saka Dariya Daddy yace”Eh musan zaka ce baka da wacce ka Tsaida mu muma dashi..Imran da Yusuf sun ga Chanchantar Amina yayar Salaha..Maman Sagir Saboda haka ita muka Zaba maka itama musan bazataki ba..!
Abba zai yi mgana kenan Imran yayi Zaraf yace”Kuma saboda Daada..Allah ta kusa Mutuwa gwara dai ta Fara Daukan sauran ya”yanku kafin namu!
Abba ya kaimai Duka yana Hararansa ya Goce jikin Yusuf gabadaya aka saka Dariya Yusuf ya Daga hannu sama yana Fadin”Ba ruwana Abba Imran ne..!
Yadda yayin ne Zaka gane bai da gaskiya Dariya aka kara sakawa Sagir ma Farinciki ya Cikasa Abba ai Mutum kwarai ne kowacce mace Zata so ya Zama bangonta.
Inna Maimunatu ta Kira Daada ta Labarmata komai Daada nata Kukan Farinciki akabama su Abba Tayi ta saka musu albarka Tana jin hadin da Imran yayi da kuma mganar Abba Daada ta Roki alfarman Azo Dukku duka a Dauran auran da Shagalin Bikin Tana Bukatar ganin Ahalinta Waje Daya Cikin Farimcikin da bata Taba gani ba nan da man kuwa su Abba suka amince Umma kuwa har ta Kira Mama ta Tsegunta mata mama kunya ta kamata in ita ina kin Abba..?Umma ta fesa Labari har kaduna Wajensu kawu Bala sukace ai wannan Labarin ya gama yi musu Dadi ba Dukku ba ko”ina ne sun yarje sun bada Dama Ko Daddy ya isa ya zama Waliyin Mama
Gabadayansu Gidan Daddy suka kwana Harda Mami Data Kira Hajiya Turai ta gayamata Komai nan da nan Tayi hamdala da jin wannan Labarin Tana gayama Justice bakinta kamar ya Tsage shima ya jinjina kai afili ya Furta Alhamdulillah!
Sajida kadai suka baro a asibitin saboda basa Bukaatar masu jinya
An kwana cikin Farimciki matuka imran da Sagir da Khalil da Khamis sun Hade waje Daya suma su Inteesar suna Tare da Umaima