
Daga Kano Inna Maimunatu ta wuce Bauchi ya”yanta suma kowacce ta koma Gidanta Umma kuma bata Kwana ba ta koma kaduna Tunda Daddy da ya Basheer sun koma Shi da Anty Hauwa da Little Inteesar Anty Safiyama Da Imran karami Daya Fara Wayau duk sai sukaji Gidan Shiru ba Gilmawar Abba yana Barayinsa ba Munari sai su kadai Allah yasa ma ga Kirniyar imran karami.
Munari kuma Dagachan Abuja Inna Bintalo kwana Biyu tayi ta so tayi ta Koma Baffa Kabiru yace taa Tsaya ta Raka Munari Dakinta haka kuwa akayi kwanansu Uku a Abuja suka wuce Porthercourt da Rakiyan Inna Bintalo kwananta Biyu suka Hadota da sha Tara na arziki suka Sakota ajirgi sai Gombe Ta koma Gidanta Domin ta Sauke gajiyan bayan ta Kira Duka yan”uwanta tasanar dasu ta Dawo Lafiya ta Raka yarta Munari Dakinta.
Sai da suka Shafe wajen Sati Biyu suna Sauke Gajiya Domin fa an sha Zirga Zirga Munari suna waya da Inteesar da sauran yan”uwanta Inteesat tasha Korafin irin Wahalan da Abokan Mijinta suka gana ma kawayenta Harda Sajida ma suna mgana Ita tabama Imran Labari yayi ta Dariya To Daman Tunda suka auri wadanan Tazuran ai sun gama yawo sai Fatan Allah ya basu Zaaman lafiya ita kanta Inteesar din ai ta gayama aya Zaginta Domin kwanakin nan kaf sai da Imran ya Famshe ita Duk Sauke gajiyan da Kowa yayi bata samu wannan Damar ba.
Allah Sarki Inteesar ita kadai ta Cigaba da zuwa makaranta kafin Transfer din Hafsah ya samu ta dawo nan da Karatu Gidansu Imran ya kara Zama Gida Saboda Mama ta kama su Imran ta Rike gam kamar ya”yanta Abba kuma yahada kan Iyalansa Waje Daya Sagir Daya kasance Dan Gida ne bai da wata Mtsala Anty Safiya na jin Dadin Zama da Mama sosai Gabadaya Renon Imran karami ya koma Hannunta ashashenta yake wuni Ta Tabbatar ita da Abba zasu kwaceshi ne Ita kanta Anty Safiyan in ba Abba ko Ya yusuf ne ya dawo ba tana Wajen Maman.
Sagir ma shi da Hafsah suna Gidan kusan kullum sai da Abba yayi musu irin na Imran yace su zauna Gidansu kada su kara zuwa kana akaji Shiru Gabadaya Imran Dayaji Labari yana ta Dariya Harda gwalo.
Munari ta Bude musu Group isu isu Ita Hafsah,Inteesar, sajida Nasara da Tasleem Nasara itama an saka Ranarta anan Kaduna Zatayi aure wani ma”aikacin NNPC zata Aura Saura Tasleem da itama Zata Fara Karatu anan jami”ar Bayaron Inteesar nata Murnan ta samu yan uwa sunan Group din SISTER”S FOREVERâ¤ï¸,Chan suke Haduwa suna Baza Iskancin su son Ransu suna Tadin mazajensu da yarda zasu kara Zama Taurari a Wajensu da bama Juna Shawara Kowa Tana Fadin in Mijinta na kwararamata Ihun Dadi Inteesar taki cewa komai suna ta Tambayanta To ai in Ta Fada ta gama Tona asirin Ya Imu Daya Dade a Lullunbe bazata so kannensa su ji wannan mganar ba ganin Taki Fada suka Zageta suka Kyaleta ita sai dai Dariya kawai.
Ba Dadewa Hafsah ta samu Transfer ta Fara zuwa makaranta ba Depatment daya suke da Inteesar ba haka ma Tasleem data Fara zuwa sai dai kusan Kullum suna Haduwa Tasleem Direba ke zuwa Daukanta ita kuma Inteesar watarana Imran in yazo suna Tare da Hafsah ya Daukesu Dukkamsu in kuma sun tashi da Wuri kowacce Tayi gidanta Domin sun Fara Biya biyen Gidajen kansu ko na Abba Imran ya Tsawatar yace kowa ta Zauni Gidanta.
Sannu Sannu bata Hana zuwa sai dai a Dade ba”a je ba Gashi har Cikin Inteesar ya isa Haihuwa, Tana zuwa awo a wani asibitin kudi Ciki yayi Kato yayi Girman da bata iyama kanta Komai Allah yasa sun samu Hutun shiga aji Uku Daada Dataji Labarin Halin da Inteesar ke Ciki ta Kira Umma Tace tazo ta Dauke yarta ta Haihu agabanta Imran yaso ya Hana sai dai Abba yayi mai mgana Dole ya Kyaleta Daman ta Zama abun Tsausayi Ciki ya hana komai..
Umma tazo ta tafi da Inteesar ta Dawo gabanta ko kwana Goma batayi da dawowa ba ta Haihu a asibitin Barau Dukku Dake kaduna Yan Biyu ta Haifa mace da Namiji masu kama da Imran Murna Wajen Wannan Ahalin sai wanda ya gani Imran kamar ya Zuba ruwa akasa yasha a Kaduna akayi Shagalin suna Yara sukaci sunan Abba da Anni Wato Abubakar da Zuwaira kuma da Abba da Anni Za”a Rika Kiransu,Hafsace kadai tazo suna Sajida da Munari ba wacce tazo duk da sun so zuwa Munari Laulayi ne ya Hanata Sajida kuma Suna Jarabawa Domin ta Fara Karatunta Hafsah kuma Daman Tana da Karamin Cikinta..
Imran yayi bajinta sosai a Haihuwar Inteesar ya siyamata kyauta Mota karama 206na Murnan Haihuwan yan Biyu nan tayi jegonta Cikin Kulawar Umma da Daddy Kamar ya maidata Intee Ciki su Anni kuwa suna ganin gata Bayan Tayi arba”in bata koma Kano ba sai da ta Zaga Dangi sune har Abuja,Gidan Baffa Kabiru sai da suka Kwana Biyu suka Dawo Taje Bauchi Wajen Inna Maimunatu taje Gombe Daganan ta Karisa Dukku Burin Daada ya Cika ta Dauki Ya”yan imran da Inteesar jikokin Malami da Abubakar Sauran Jikokin Malami da Kabiru.
Har Dutse sai da Inteesar taje gidan ya Sa”id bayan dawowarta Daga Kadunna ammh shi ita da Imran sukaje suka kwana Daya suka Dawo Ta Dawo da Kwana ashirin ta koma Bikin Nasara sai a wannan karom Sajida da Munari suka zo murna ba”a mgana da suka Hadu sai Tashin Hira Gabadayansu suna da ciki banda Sajida Da suke mata Tsiyan ko Tana planing ne tace musu AllaH ne bai kawo ba Dukkansu da mazajensu suka zo bayan Biki kuma kowa ya tasa abarsa suka koma Amarya nasara ta tare agidan Mijinta Dake Malali kaduna.
Inteesar mai Taya Reno aka Daukan mata Wata yar yarinya saboda makaranta Mama ta samo mata nan kasansu take kwana wajen Inteesar din sai Weekend take zuwa Gida sunanta Hanne,Inteesar Tana Wahala sosai ga makaranta ga Renon yaran har Biyu ga Ubansu bai iya Komai ba sai fadan in anyi ba Daidai ba.
Sagir ya gama Karatunsa ya Cigaba da Dinkinsa Tunda aikin bai Samu ba suna dai Cigaba da nema.
Ashekaran suka je Lagos ita da Imran da yaran su an Turasu Seminar Gidan Abba suka sauka ba Hotel ba,Tunda Matan Lurwani maigadi suna kula da gidan ko”ina Tsab,Sati Daya sukayi kafin su gama Seminar,Su Inteesar taje Gidan Sajida suma sun zo musu Har Gidan Dr Ali argungun sunje,Bayan sun dawo Sukaje Parthecourt,Harda Sagir da Hafsah suka gano Munari suka Dawo.
MURFI…!!!
AFTER 7 YERARS BACK…
Bayan Shudewar wasu Shekaru Bakwai da suka gabata Ahalin Marigayi Alkali Dukku ayau ya Zama abun kwantance Baffa Kabiru girma ya kara kamasa Tun bayan Rasuwar Daada Shekaru Biyar da suka gabata ammu bata bar Gidan Duniya ba sai da Ta Dauki Jikokin Malami da Kabiru ta kuma Hada kan Zuru”arta Waje daya kafin ta bar Duniya.
Rashinta ya Girgiza ya”yanta sun yi kuka sosai sai dai kuma sun Dauki Girma da Ragamar komai akansu.
Ashekarun da suka gabata an samu Cigaba sosai ta bangaran Haiyayyafa da Karin Girma ayyukan wasu.
Imran ya samu karin Girma daga Assistan Manaja zuwa Manajan Gt brach Dake Lagos inda ya Taba aiki basu da Mtsalan gida ga Gidansu nan suka gyara ya Kwashi Matarsa da ya”yansu suka koma chan da Zama Sajida tafi kowa murna sun dawo kusa da juna duk da shima Khalil din ya samu karin girma, Shekaru Biyu da suka gabata Tunda Inteesar Ta gama makarantar ta,Su da kano sai in sunzo ganin gida ga gidansu suna da Wajen sauka in sunzo garin.
Bayan Haihuwar su Anni haihuwanta Biyar acikin Shekara bakwai Saboda Gwarne Takeyi Data yaye shikenan sai wani Cikin taso ta fara tsarin Ilyali Imu yace sai ya gani Allah ya Taimaketa Hanne na Tare da ita tana kara Taimaakamata.
Daga su Abba karami tazo Tayi mai sunan ya Yusuf suna Kiransa Boy,Sai mai sunan Daddy Mustapha,sai mai sunan Baffa Kabiru,Sai Sagir da Imran yayi mai Takwara yana Kiransa Friend sai Karamarsu mai sunan Daada kuma mai sunan Inteesar suna Kiranta Afiya.
Ya yusuf ya samu karin Girma shima iyalai sun cika Gida,Abba tuni ya gida wani Gaton gida a sharadi phase 1 sun koma da Mama tare da Imran karami da Khadija diyarsu da suka kwace musu, an kara gyara wannan Gidan Sagir ya dawo suna zaune Tare,gidansu kuma sun bama Baba Manu ya dawo nan da Zama Sagir ya samu aiki sai dai har yau har gobe bai bar Dinkin ba domin kome ya Zama Dinkin ne Sila shida Imran suka Hada Hannu suka kara Fadada harka yanzu Manyan Shaguna sun fi goma Cike da kekekuna da ma”ikata yara sai dai Sagir ya Daina Dinkin sai dai yaransa shi kuma Oga sama oga kasa.
Shima sun tara ya”ya shima yayi ma Imran,takwara sai mai sunan Mama Amina da mai sunan Babansa Tasiu.
Munari ma ya”yanta Hudu itama Tayi ma Anni da Abba duka Takwara da Mami Asma”u da Baffa Kabiru Sajida kuma ya”yanta uku ita kuma sai Tayi ma su Inna Maimunatu kara da Inna Bintalo Daada kuwa mai sunanta Kusan kowa nada Daada agidansa.
Nasara ma da ya”yanta Biyu su ya Basheer dasu Sadam duk sun zama magidanta Girma ya kamasu Tasleem ma Tayi aure sai dai kafin haka sai da Kaddara ta Fadamata wani Lecture ya Ribace ya Lalata mata Rayuwa.
Sai daga baya ya aureta bayan ta Tsarkaka Alhaji Alhassan yayi ta kuka Saboda yasan Ishara ne Allah ya Nuna mai Koda ya Tuba.
Gabadayansu Mazan sun Hade kansu Matan ma haka Imran ya Daina shan Taba Kwata Kwata saboda Shekara Uku da suka wuce ya Kusa Mutuwa Hayakin Dayayi ta bankama Cikinsa ya Taba Huhunsa sai da Abba ya Fita Dashi Kasar Amurka Ya kusan Wata Shida akayi mai aiki kana ya warke ya Dawo Gida Inteesar har ta Fara kukan rasa Namijun Duniya sai gashi ya Warke sai dai Tundaga Lokacin ko Warin Taba bayaso shi da ita har Abada.
Su Inna Maimunatu kam sun Zama Goggon gaske Yanzu Baba Asabe suka kama Suka Rike itace makwafin Daada Gidansu na Dukku na nan da Ransa bai Mutu ba Baba asabe na Cikinsa Tare da yan aiki masu Taimaka mata Suna zuwa yin Hutu ko Sallah Duk shekara gabdaya kwansu da kwarkwatansu Baba asabe me Zata ga Iyaalan Daada..?illah dai Fatan su gama da Duniya Lafiya da Fatan Allah ya Jikan Daada da Alkali Hamisu Ameen.
Umaima tayi aure anan Kaduna Wani Dan kasuwa take aure mai kudi sosai har da Danta Daya.