
Tammat bihamdullahi Godiyata Ta tabbata ga Allah Subanahu wata”ala daya bani ikon Fara wannan Littafin Lafiya na kuma gamashi yau Lafiya Allah ne abun godiya Tsira da aminci su kara Tabbata kan Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu Salallahu Alaihi wasallam,Tare da Iyalansa da Sahabansa gabadaya Ameen summah Ameen..
Bazan Rufe wannan Littafin ba sai na Mika Dukkan Godiyata da jinjina kan Masoyana masu son cigabana Masoyana da suka Taru suka nuna min kauna Wajen siyan wannan Labarin Da kuma yadda suka yi jimarin Bin Rubutuna Tun daga kashi na Farko Har gashi yau mun kamallah kashi na Biyu Wato GMB2BANDGROUP Hakika naji Dadi kwarai Allah ya saka Muku da alheri Allah ya Biyaku Allah ya bar Zumunci Allah ya kara Hada Fuskokinmu da alheri,Sannan ina Neman afuwarku Kusan Dukkan Dan Adam Tara yake bai cika goma ba Allah ne Kadai Dari Bisa Dari ni Mutum ce kuma yar adam ce mai Rauni mai Kuskure in har a wannan Rubutun na bata ma wani ko wata don Allah ku yafemin kila akwai inda na Kuskure muku ko inda baku so haka ba to kuyi hakuri Ajizanci ne na Dan Adam ni ban isa nayi shi Dari bisa Dari ba Ina Fatan Sakon da kuka karanta zaku amfani da Darasin Dake Ciki akasinsa kuma ku Watsar Dashi Allah ya yafemana Kurakuran da mukayi Cikin wannan Rubutun ya bamu Ladan Dake Cikinsa Nagode kwarai da gaske sai Allah ya kaimu bayan Sallah da Rai da lafiya akwai Alkawarin Goron Sallah da nayi muku Da yardan Allah zan cikashi Zamu Fada Labarin SUNAIMA da MIJIN KANWARTA daya zama kaddaranta Shin wata irin kaddara ce..?kada ku Damu zamu fara wannan Tafiyar in muka gama azumi Lafiya Allah ya bamu Dacewa da Yantuwa acikin wannan Watan Allah ya Sa muna Cikin Salihan Bayi Ameen ya Allah Tanque all…
Janaftyshakira
31/03/2022
Intelligent writer”s ass
GMB2ONELOVE