GIDANMUNOVELS

GIDANMU 1 & 2 COMPLETE

GIDANMU HAUSA 1 & 2 COMPLETE

Masu cewa wai auran Safiya da Yusuf kamar yar tsana..? In kun bibiya labarin zaku iya Fahimtar Dalilin da yasa Auran ya faru cikin Lokaci Alhaji Alhassan yana matukar Daraja Mutumcinsa akan mutumcinsa kada ya zube zai iya yin komai,Kuma yarda yaga Imu ya tabbata zai iya bangala Sirrinsa yayi Tirere dashi acikin Farantin ya gama yawo dashi kowa yagani kuma ya saani bazai mai Wahala ba Shiyasa ya Daura auran ya yarda Kwallon mangwaro ya Huta da guda..🤣

Shakira..
3/22/22, 23:03 – Ummi Tandama😇: GIDAN MU..!
(Our House)
Book 1

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

DEDICATED TO:
Aisha alto(Sisinah)
Chubado muhammad(Uwar dakina)
Yahanasu Soupnass(Qawalli1)
Kausar salis(My jika)
Rahma Ladingo(Dota)

Ina godiya masoyan GIDANMU Allah ya saka da alheri Allahu ya bar zumunci Ameen,Musamman yan gidan Gidanmu comments Section 1&2,Janaf Novella,Zauren Janafty Shakira da sauransu Tanque so much

     *🅿�10*

“Lokacin da kiran Sagir ya Shigo wayar Imran yana kwance akan gado acikin Dakinsa ya gama Busa Sigarinsa har yagaji ya koma ya kwanta.
Gidan nasu ba kowa Yusuf ya tafi wajen aiki,Munari kuma Ta tafi makaranta shi kadai ne agidan,Daya tashi Dakin Abba ya leka ya sameshi yana zaune shuru Shi kadai shi ya taimakamai yayi wanka ya sauyamai kaya ya Hadamai Tea mai kauri da Soyayyan Dankalin da Munari ta soya kafin ta fita bayan ya bashi yaci ya koshi ya Doramai da mgungunansa,wanda ko Minti Goma bai yi ba ya Sulale yana Barci,wannan watan Chanjin mgungunan da Likita yayi mai kamar sun fi yimai amfani,Saboda ya na samu Ishashen Barci Kwakwalwarsa tana samun Hutu sosai Fiye da baya kuma suna ganin Chanji Sosai.
Bayan yayi barcin ne ya Fito Falo nan kan Dinnig ya Hada Tea yasha da Soyayyan Buredi,yaci ya koma Daki ya Dora da Busa Hayaki bayan ya gama ne ya koma ya kwanta sai ga kiran Sagir ya shigo wayarsa karama Kirar Nokia ce Rakani inda Zani Domin Imran bai tabaa Damuwa da sai ya mallaki Babban waya,Shi dai a kira ya Daga kawai kuma Mutanen dayake kira Daga Sagir sai Yusuf ko Munari yana da lambarta ammh ba sosai yake kiranta ba.
Cikin kasala ya Zura hannu ya Dauko wayar,ganin sunan mai kiran yasa yadan saki karamin Tsaki ya Daga kiran yana Fadin”Ya akayi ne Banzan Abokina..?
Dagachan bangaran Sagir dake kallon Baba Manu yace”Kana ina ne..? Ga Baba Manu na gidanmu yana jiranka..!
Imran ya lumshe idanuwansa kafin ya Bude su yace”Kaga mallam gajarta Zencen..Meya faru?
Domin duk da yasan mganar Neman auran yusuf haka kurum yaji ajikinsa da wani abu.
Baba manu ne yayi ma Sagir alamun Daya Fadamai Shi kuwa ya karkace kai yace”Kazo fa Domin Baban yarinyar nan Ya Daura auran Kuma ya Hado su Baba Manu da ita!
Imran bai wani ji mamaki ba sai ma wani Mirmishi Daya saki Kafin yace”Dakyau..Yanzu ta na ina..?
Sagir da mamaki ya cikasa yace”Tana Dakim Mama..!
Imran ya mike Zaune yana Fadin”Gani nan zuwa..!
Daga haka ya katse kiran,Cikin Sassarfa Ya Sauko Daga kan gadon afili yake wani Mirmishi kamar na mugunta aransa yace ya Rage ma kansa aiki..Shifa baisan komai akan Alhaji Alhassan ba Daga farko sai da ya Shiga Gonarsa kudi kalilan ya bada aka Zayyanemai Labarinsa bai sanshi bane shi kanshi a baya baisanhaka yake ba,Sai yanzu yake kara jin Tsoron kansa Sosai in yayi wani abun
Wanka ya shiga a gurguje,ya fito ko Mai bai shafa ba ya Bude Wardrope dinsa Dake cike da kayansa ya Zari Riga da wando Ruwan madara da da bakin wando ya saka,bayan ya saka karamin Cum ya taje kansa ya Dauki Wayarsa bayan ya saka wani Budadden Takalminsa baki na Fatar Damisa.
Dakin Abba ya leka ya iske har Lokacin bai tashi ba yana ta Barci yasa ya juya ya fice bai Nemi Hawa Mashin dinsa ba ya Taka da kafarsa ya Fice zuwa gidansu Sagir a kafarsa duk da dan Nisa bai damu ba,Kafin ya isa Gidan su Sagir ya Biya wani Shago ya siya kwalin Sigari da Lether ya manto nasu agida kuma yau yadda yake jin Nishadi ya kamata ya Busa Hayaki sosai.
Acikin aljihun wandonsa ya saka kafin ya isa kofar gidansu Sagir.
Waya ya Dauko ya kirashi yaceya Fito yana waje yana jiransa,Kafin Sagir ya Fito ya kira Yusuf sau Biyu bai Daga kiransa ba sai ya kyaleshi tunanin kila yana wani aikin ne
Ba dadewa sai ga Sagir ya Fito Hannu ya bashi sukayi Musabaha kafin Sagir yace”Meyasa ka tsaya Daga waje baka Shigo ba..?
Imran ya Dakuna Fuska yana Fadin”Kawai sai na kama Shiga Gidan Mutane kai na Tsaye..? Bar gani na D’an iska D’an iska nasan Abunda nake yi ina da Hankali..!
Sagir ya kusa sakin Dariya sai dai ya kanne kafin yace”Aifa ga Hankalin nan nagani..!
Kansa Imran ya Daka ya Duke yana Dariya kafin su Nufi Cikin Gidan.
Sagir ne agaba Imran a baya Da yayi sallama iya sallaman Lebensa Mama na Kitchen Baba Manu ne ke zaune yana Shan Ruwa Sagir ne ya zauna gefensa shi kuma Imran din Daga chan gefe ya Durkusa yana gaida Baba Manu ya amsa mai,Daidai Lokacin da Mama ta fito itama ya Gaisheta ta amsa Cikin Fara”a tana Tambayansu Mutanen gidan ya amsa mata da Lafiya
Baba Manu ya gyara Zama yana Fadin”kaji dai abunda ya faru ko..? Kamar yadda Sagir ya Fara gayamaka..Muna zuwa da niyyar Neman aure sai kawai aka Daura auran..Baisan me ya faru ba..Ammh naji ban ji Dadin Sanadiyar irin auran da yayi ma yarinyar ba haka ya Hadomu da ita ba Rakiyan kowa gwanin ban Tsausayi.!
Baba manu ya karishe Fada yana Bayyana Jimamin Abun.
Imran yayi Mirmishi kafin ya kada kai yana Fadin”Hakan yayi kyau..!
Dukkansu sai da suka kallesa yayi kamar bashi yayi mganar ba,Baba Manu yazaro Sauran Kudin Imran ya Mikamai yana Fadin”Dubu Dari ya karba Sadaki sai dubu Ashirin da aka kashe na Siyan Minti da Sauransu Ga Ragowar Dubu tamanin dinka nan..!
Kai kawai Imran ya Girzgiza kafin yace”Ka barshi kawai.!
Baba manu ya zaro ido yana kallonsa hakama Mama da Sagir Cikin mamakinsa Baba Manu yace”bangane ba? Ni don Allah nayi muku komai karbi kudinka yaro..!
Imran ya kara kada kai alamun bazai karba ba,Baba Manu yace”Ikon Allah..To in kabarmin wannan Zunzurutun kudin kai fa..?
Imran ya kauda kai kafin yace”Ni ina da kudi..!
Baba manu yace”Kana aiki ne.,? Ni a sanina Sagir ya Fadamin Yayanka kadai ke aiki..!
Wani kallon ya Sakarma Sagir kafin yace”Ina da Sauran kudin Albashina dana ke Tarawa.!
Gabadayansu mamaki ya Cikasu barin ma Sagir da bai taba jin Imran yayi mgana kan Abunda ya Shafeshi ba.
Cikin karin mamakinsa Baba Manu yace”A ina kayi aikin..?
Imran kamar bazai Tanka ba sai Chan yace”Ba anan bane..A lagos ne..!
Gabadayansu suka Zuba musu ido,ganin haka yasa yayi Saurin Basarwa,Da sauri Sagir yace”Wai daman ku yan Lagos ne..?
Da sauri Imran yace”A”a..
Daganan ya Tsuke bakinsa bai ce komai ba Sagir zai kara mgana Baba Manu ya Danne mai hannu ganin yadda Imran ya Hade kamar ya kuma matsa gefe kamar za”a ce wani abu ya tashi ya Fita.
Cikin Basarwa Baba Manu yace”yanzu ina shi yayan naka..? Ina bukatar ganinsa..!
Imran ya sauke ajiyar Zuciya kafin yace”Baya nan yana wajen aiki..!
Baba manu yace”To ka kirashi..!
Imran cikin kosawa yace”‘Na kirashi bai Daga ba..!
Baba manu ya jinjina kai kafin yace”Shikenam..Daman domin na Damkar amanar yarinyar nan ahannunshi..Duk da bamu hada komai daku ba naji ina kallon ku kamar kowa..Yanzu a ina zai ijiyeta..?
Imran ya wani kallesa a karkace kafin yace”Yana da inda yafi GIDANMU ne..!
Chan zai ijiyeta akwai Dakuna bazai gagaraba..!
Baba manu ya jinjina kai yana Fadin”Shikenan Allah ya basu Zaman lafiya..Gata nan Dakin Amina ni zan wuce saboda zan fita gareji nagode kwarai..!
Yafada Lokaci Daya yana Mikewa Dukkansu suka Mike Imran ya kalli Baba Manu kafin yace”Nagode..!
Kafadarsa ya Dafa kafin yace”Bakomai Kada ka Damu!
Lokaci Daya ya Turamai kudinsa Cikin Aljihu yana Fadin”Kada kace wani abu..Bazan iya karban ko Sisi Daga wajen ka ba..!
Dole Imran yayi shuru bai kara mgana ba Tare suka Fice Bayan Baba Manu yayi ma Mama Sallama Safiya na Daki tana jin mganganu sama sama,Tana Zaune afalon Mama bata fito ba.
Suna Fitowa Bayan Baba manu ya tafi Imran ya kalli Sagir yana Fadin”Zan je gida na Dawo..Na bar Abba shi kadai..!
Jinjina kai kawai Sagir yayi kafin yace”To ya za”ayi da amaryan ya Yusuf din?
Imran yace”Ya kuwa.? Bari naje gida zan kirashi muyi mgana in ya Dawo yazo ya Dauki matarsa yanzu dai ta zauna wajen Mama pls..!Sagir yace”Kada ka damu ai an zama Daya..!
Daga haka sukayi sallama,Sagir ya Dawo Cikin gida suna ta maida Zence da Mama.
Imran kuwa har ya koma Gida Abba bai tashi ba sai yayi Zamansa afalo yana auna wasu abubuwa,Alhaji Alhassan mahaifin Safiya yana Tsoron Tonon asirinsa wanda wannan Dalilin ne yasa yayi gaggawar Dauran auran,ya kawo yarsa a Wulakance kamar bata da gata Hallacin da Safiya tayi ma Yusuf dasu kansu Shi zai sa su riketa Riko na gaskiya da Watarana sai Mahaifinta yayi Nadamar Abunda ya aikata ya Dawo yana bata Hakuri kuma ko bajima sai asirinsa ya Tonu Domin Shi Sharri ai Dan aikeni Inda ka aikashi sai ya Dawo.
Sannan kuma Itace Mace ta Farko da Zata Shigo Gidansu a Lokacin da suka yanke tsammani da komai Ya Tabbata Yusuf ya Chanchanci yayi Farinciki Tun Bayan Afkuwar Kaddaran Data Fadamusu shi yake ta Wahala dasu ya Dauki Ragaman Abba Gabadaya akansa,Shiyasa zai Tsaya har sai ya ga ya samu abunda yake so koda shi zai rasa nashi Farincikin ne,Duk da daman Shi yariga yagama bamkwana da Farinciki.
Yana nan zaune sai ga kiran Yusuf sai ya Dauka bayan ya Daga sun gaisa yace mai suna Meeting ne shiyasa bai Daga kiran ba.
Nan Imran ya gajerce Mganar ya gayamai Abunda ke Faruwa Yusuf yana Zaune Cikin Officr dinsa sai da ya Mike Zaune Cikin mamaki da al”ajabi yace”An Daura auran kuma Imu..?
Imran yace”Eh…To miye aciki ya saukaka ma kansa ne..!
Yusuf na Sharan zufan Goshinsa yace”A”a Imran bamu shirya komai ba Infact ma ko Abba bamu Fadamawa ba..Ballatana Kanwarmu Munari ni bama wannan ba kai ina zan ijiye Safiya Imu..?
Imran bai wani bama mganar Muhimmanci ba yace”In ka dawo sai ka Fadamai Abba bashi da Mtsala hakan ba abun alfarinsa ba ne..Mganar inda zaka ijiyeta kuma ai ba wani abun Damuwa bane..Sai ta fara zama adakin ka kafin mu gyara mata Falon nan da 2 bedroom din nan dake korido din Dakin Munari..!
Yusuf yayi shuru kafin yace”Ok..Hakane Allah ya bani ikon Rike Safiya da Amana..!
Imran yace”Ameen ya yusuf Domin She Loves u.!
Yusuf ya saki Mirmishi kafin yace”I know..Zuciyata ta cika da Alherinta Imu..Ina ta kiranta Tun dazu bata daga ba yanzu tana gidan Maman Sagir din ne..?
Imran yace”Bakajin Hausa kenan..?
Yusuf yace”May be..!
Imran bai tsayama Sauraransa ba ya Datse kiran ganin Yusuf zai fara Zolayansa da bakwarcinsa shi kuma Baya cikin Mood din.
Dakinsa ya koma ya zauna kan kujera ya Shiga Busa Sigarinsa Hankalinsa kwance Sallar azahar ya tadashi yayi alwala yayi Sallah,sannan yazo ya adana Sauran kudin da Baba Manu ya maido masa,da niyyar zai bama Yusuf su ne yayi amfani dashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button