
Shakira..
3/22/22, 23:05 – Ummi Tandama😇: GIDAN MU..!
(Our House)
Book 1
Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janaftyâ¤ï¸
      🅿�17
Monday
12:12pm
BUK
“Yau ta kama Monday ko”ina kabi Sai Hada Hada ke wakana Saboda Monday Tushen aiki ne,haka yake Gudana a Tsakiyar Jami”ar Bayero Dake kano.
Dagachan Bangaran Economics Department na Hango Dandazon Jama”a Mata da Maza yan kwalisa Suna ta Tururuwan Fitowa Daga wani aji Daga Dukkan alamu Sun gama Daukan Lecture ne suka Fito,wasu Cikin makaranta suka Shiga wasu kuma Hanyar Cafteria suka Nufa Wasu kuma Masallacin Cikin makaranta suka Nufa Wasu kuma wucewa sukayi Suka Zauna Saman Kujerun Dake Zagaye da Department Din,wanda an Tanadanesu Ne Domin Zama da Huta gajiya ko kuma Karatu Irin haka dai.
Acikin Masu Zaman Inteesar Tana Daga Cikinsu itama Waje ta Samu ita Kadai ta Zauna,Yau Datake kwana Goma da Fara Zuwa makarantar Bazatace ta Saba da komai ba Sai dai ta Fara Fahimtar abubuwa Dayawa Sai dai har yau batayi Wata kawa ba Ita Kadai Zakaa ganta Sai dai Tana Yada Sallama Duk inda Tajee ko Taga Gungun Jama”a Ita Haka take bata da Saurin Saki jiki da Mutane Ballatana Sabo.
Yan ajinsu Da Dama suna Lura da ita Sai dai ba wanda ya Damu Kansa Jami”a Gidan kazo nazo ne,Akwai irin su Da yawa amakarantar Wadanda Basa Bukatar Alaqa da kowa cikin Masu Lura da Inteesar Tun Shigowarta Makarantar Harda Munari Sakamakon Department Dinsu Dayane Tun Ranar da Inteesar ta Fara zuwa Take Hankalce da ita..Sai Taga Itama kamar irin tace bata Hulda Da kowa kamar yadda Take ita Kadai haka Itama Inteesar take komai nata ita kadai,Tana ta so Tayi mata Mgana ammh Sai ta kasa sai yau Bayan sun Fito Daga Lecture din 10 to 12,Zasu yi Sallah suci Abinci 2pm suna da Wani Karatun.
A idonta taganta ta Samu Waje ta Zauna ta Fito da Wani littafin Datayi Note game da abunda aka Koya musu Tana Dubawa Munari bata son Dalili ba kawai Taji Kafafunta najanta Zuwa Wajen da Inteesar Take Zaune,Sai da ta Kariso Gabanta kana ta yi mata Sallama.
Inteesar Dake Tsaka da Karatu Hankalinta yana kan Karatunta ta Dago Suka Hada Ido da Munari Sai dai Ita Inteesar ta Toshe Idanuwanta da Wani Siririn Farin glass mai kyau da yarari yau Shigar Riga da wando Tayi Wandon Ja ne plazo mai Budewa Ta kasa,Sai Wata Riga Blue mai dogon Hannu Ta kama mata Jiki sai ta Dora Wata bakar Riga mai kama da kimoni a Saman kayan ta Zarge igiyarta Daga Wajen Jikinta,Sai Red din Vail Data yane kanta Dashi hakama Taklmin kafarta red mai Tudu sai Wata Karamar Jakarta Red Colour.
Yayinda ita Munari take Sanye da Doguwar Riga Kirar Armani,Baka sai ta yane kanta da Gyalen Rigar Dayake Fara ce sai Fuskarta Tayi kyau itama Bakar Jakace ke Rataye a Kafadanta na Dama sai Wasu littafai Dake hannunta.
Lokacin da suka Kalli juna suma basu san Dalili ba sai da gabansu ya Fadi a Lokaci Daya Kuma suka kasa Dauke Ido a Kallon Juna Cikin Sanyim Murya Inteesar ta amsa ma Munari Sallamanta Lokaci Daya Tana kara Kallonta da Nazarinta.
Munari ta Murmusa kafin tace”Don Allah zan iya Zama..!?
Tafada Tana nuna Gefen Inteesar din da Sauri ta Kwashe Jakarta da Littafanta Data ijiye a Wajen Tana Fadin”Haba sai ma kin Rokeni..Zauna mana..!
Tafada Cikin Mirmishi itama Gefenta Munari ta Zauna tana Fadin”Nagode..!
Mirmishi Inteesar Tayi mata kafin Tace”U are Wlcm!
Daga haka ta maida kanta Kan Littafin Da Munari ta Sameta Tana karantawa.
Sun Dade Shuru kowa na Nazarim Kowa Ita Inteesar Bata zata iya Gane Munari a ajinsu ba Tunda suna da yawa,Ba kamar Munari Datake ankare da ita Tun Fara Zuwanta makarantar ba.
Cikin Son Takalo Mgana Munari ta Gyara Zama tana Fadin”Ammh baki Dade da Fara zuwa Makarantar nan ba ko..?
Inteesar ta Dago kanta Tana Fadin”Eh..yau kwana na Goma da Fara Zuwa kefa..? Wani Course kike yi..?
Munari tace”Course din mu Daya Economics nake karanta..!
Inteesar ta dan Saki Fuskarta Tana Fadin”Allah Sarki..Ashe ma Tare muke Kema Kwananan kika Fara zuwa kenan..?
Munari tace”Eh to ban 1 Month dana Fara zuwa..!
Inteesar tace”Kice kin Rigani Fara zuwa..Aini koda na Fara zuwa Duk anyimin Nisa da karatu..Wajen ma Class Rep ne nake karban Wasu Note din ina rubutawa..!
Munari tace”Ayyah..Ai baki da Shiga Mutane ne kamar ni da kin samu..!
Inteesar tace”Kema haka kike kamar ni..? Kwata kwata bana da Sakin jiki da Mutanen da ban sani ba Haka nake Nafi sabawa da Yan gidanmu Fiye da kowa..!
Munari tayi Mirmishi kafin Tace”Kamar Ni kenan..Ni kaina tunda nazo makarantar nan bani da wata kawa Ni kadai nake Rayuwata..sai yau Naji ina Sha”awar nayi miki mgana Duk da ina Lura Dake Duk Sanda kika Fara Zuwa Haka kurum naji kina Burgeni ina son nayi miki mgama mu gaisa..!
Inteesar ta Fadada Fara”arta Tana Fadin”Allah sarki..Ni kaima Da kika min mgana sai naji ina son na gaisa Dake Haka kurum Daga ganin ki yau bansan Dalili ba..!
Munari tace”Kila Allah ne ya Hada Jinimmu..Yana so mu yi kawance..!
Atare suka saka Dariya gabadayansu Cikin Nishadi Shuru yadan Biyo Baya Kafin Munari ta mika mata Hannu Tana Fadin”My Name is Maimunatu Abubakar Malami ammh Agida Abbana da Brodas dina suna Kirana Munari ne..!
Imata Inteesar din Hannu ta Mikamata suka Cafke Cikin Annuri Tace”Nice to Meet u Munari..ni kuma Sunana Maryam Mustpaha Dukku Nima Kamar ke Daddyna da kowa Agida Suna Kirana da Inteesar Saboda Sunan Mahaifiyar Daddy naci Daada..!
Gaban Munari ya Fadi jin Inteesar ta ambaci Dukku Cikin mamaki Take Fadin”Ke yar Dukku ce..?
Inteesar tace”No..Daddyna ne Dagachan.Ummata yar Kadunace..Nima a kaduna aka Haifeni Chan muke Zaune da Zama Karatu ne ya kawo ni kano ina Zaune Wajen Mama yayar Ummace..Kema Abban ku Dagachan yake…?
Da Sauri Munari ta Girgiza kai Tana Fadin”A”a..Kawai na Tambayane..Ganin Daman kina Kama da Fulani..!
Inteesar tace”Kema ai kina Kama Dasu ..Kalle ki fa Fara ni kuma Fatats mai Duhuwa ce..!
Munari Tace”Ni kuma Nafi son irin Fatarki Wlh..!
Inteesar tace”Kedai Fadi gaskiya..Farar mace alkyabban mata fa..Nima Ummata na Dauko Da Fatar Daddy ce kamar ke zan zama Saboda Farin Bafullatanin Dukkune Gaba da Baya..!
Munari ta amshe da Fadin”Ni kuma Daga Abba Har Anni Duka Fulani ne kuma Fatarsu mai Haske ne Shiyasa..!
Inteesar ta gyada kai kafin tace”Ke nan ke yar kano ce..?
Munari tace”Eh..Gidanmu na Gadon kaya..kefa ina kike Zaune..?
Inteesar tace Tana Dariya”Ikon Allah Nima ai Gidan Maman yana Gadon kayan ne..!
Munari ta cafke Cikin Murna Tana Fadin”Shikeman Daman na Fadamiki..Haduwarmu Daga Allah ne..!.Inteesar tace”Na yarda da Mganarki..!
Daganan ssi Hira ta Tsinke kamar sun Shekara da Sanin juna,Haka kowanensu ke jin wani Farincikin na yau Kadai da suka Hadu,karin Farincikin Inteesar ma Da suka Tabo bangaran Karatu ta Fahimci Munari Tasan Abunda take yi Sosai,nan tace zata ari Wasu Notes dinta ta Kwafa Daga baya sai Munarin ta Koyamata Inda Bata gane ba Sai gashi Tare sukaje masallaci sukayi Salla Daganan suka Shiga Shago Inteesar ta Siya musu Freshyo,tazo da Cake suka Koma Suka samu wani Waje suka Zauna suka ci suka kora da Madara,Kafin su Shiga Lacture suka Duba littafansu Munari na kara yima Inteesar Bayanin karatun da akayi musu a baya Inda bata gane ba,har Lokacin Shiga Lacture yayi suka Shiga Tare suka kuma Zauna Waje Daya yan ajinsu sai mamaki akeyi Wasu acikin Ransu sukace sun Dace da juna ganin dukkansu Daman basu da kowa acikin ajin.
Ranar har suka gama Lecture dinsu na Ranar Suna Tare da juna 6pm suka Tashi,Tare suka Fita Bakin get suka Samu adaidaitan Gadon kaya Gidansu Sagir ne Farko kafin gidansu Munari ana Zuwa Inteesar tace zata Sauka Sai Munari itama ta Leko Cikin mamaki tace”Wai nan gidan kike Zaune..?
Inteesar na Shirin Bama mai adaidaita Kudin ta juya tana Fadin”Eh kinsan Gidan ne..?
Munari ta Fito Itama Tana Fadin”Sosai ma..Gidan su yaya Sagir..Ai abokin Yayana ne Ya Imu..!
Inteesar ta Washe baki ta ba Munari Hannu suka Tafa Tana Fadin”Abun mu Chas Wlh..,!atare suka Saka Dariya Bayan Inteesar ta Hada duka ta Sallami mai adaidaitan suka Nufo Gidansu Sagir Munari na Fadin”Ai Ni gidamu yana gaba kadan ne..!
Inteesar tace”Ayya Dayake Tunda nazo ban Taba Fita waje ba Daga makaranta sai gida..Bari mu Shiga mu Fito sai na Taka miki naga gidan naku..!
Sun Kariso Kofar gidan kenan sai ga Sagir ya Fito Yana yarfe Ruwa Daga Fuskarsa Kamar a mafarki ya gansu Tare bai Daina mamaki ba Har suka Gaisheshi ya amsa yana Fadin”Inteesar ina kika Hadu kuma da Munari..?
Inteesar na Mirmishi ta Kalli Munari sukayi Dariya kafin ta Kalleshi Tana Fadin”Makaranta yau muka Hadu..Ashe Course din mu Daya kuma ajin mu Daya..Ashe ma muna kusa sai da mukazo take cemin ai tasan nan Gidan kai abokin Yayanta ne..!
Sagir yayi Mirmishi yana Fadin”Eh Wlh..Nasan itama ta Fara zuwa makaranta To ban yi Tunanin Abu Daya kuke karanta ba Abu yayi kyau kin ga ke Inteesar kin samu kawa kema Munari kin samu kawa,sai ku Dinga Taimakama juna amakaranta Tunda kuna kusa..!
Suka Hada baki Wajen Fadin insha Allahu Sagir ya wuce yana Fadin”Ke Munari kada ki Zauna fa ki Fito ki tafi Gida..Yanzu ma muka Rabu da Yayanki ya koma Gida su Taho Salla Tare da Abba..!
Inteesar ce Tayi Saurin Fadin'”Yanzu Zan Rakota Ya Sagir..!
Ya wuce yana Fadin”Kuyi Sauri kunji an Fara Kiran Sallar mangariba..!
Daga haka ya Shige Shagonsa su kuma suka Shiga Cikin Gidan suka Iske Mama a Tsakar gida Tana alwala ta Dago Tana amsa Sallamarsu itama Bakin ta Sake tana Kallonsu Daidai ta Idar da alwalan ta Mike Tana Fadin”Ikon Allah wa nake gani kamar Munari..?
Dariya tayi Tana kallon Inteesar Tace”Nice Mama..!
Mama ta Rike Haba Tana Fadin”Ikon Allah Maryam ina kika Samo ta..?
Inteesar tace”Makaranta Mama ashe ajinmu Daya bamu san muma kusa ba..!
Mama tace”Kaji wani ikon Allah..abu yayi Dadi ku shiga ciki ai nan kamar Gidane ga Munari gidansu na gaba Kadan,Imran yayanta ai Abokin Sagir ne na Sosai Ya kwana Biyu bai Shigo Gidan bane da kun Hadu..!
Suna gaba tana Bayansu Zuwa cikin Dakin,Sai da suka Zauna kana Suka gaisa da Munari Inteesar Tana ma Mama Bayanin Haduwarsu da Sagir akofar Gida da abunda yace Mama tace”Ya fadi gaskiya..Munari ga Kawa nayi miki Diyar kanwatace Salaha kema Inteesar ga Kawa nan munari Makota muke dasu..!
Suka Hada ido kafin su Hada baki Wajen Fadin insha Allahu Daganan Mama tatashi Bayan tacema Inteesar abincinta na Kitchen Itama kuma ta Shiga Ciki yin Sallah Inteesar Tayi ma Munari Tayin Cin Abinci sai ta Mike Tana Fadin”Nagode Kawas ki bari in na Sake Dawowa zanci..Yanzu Tafiya Zanyi in ya Imu yaga ban Dawo ba Wlh Zan ci kaniyata ne..!
Jin haka yasa Inteesar tamike tace suje ta Rakata,Kayan Hannunta Kadai ta ijiye suka Fice Tunda Mama ta Tada Sallah Tafiya kadan sukayi sai gasu Kofar Gidansu Munari ta Kalli Inteesar Tana Fadin”To kin ga GIDANMU..!
Inteesar ta Kalli Gidan Tana Fadin”Nagani Ai nasan Gidan yanzu..Da Zama ya Isheni in bamu Shiga Sch ba sai dai ki ganni..!
Munari tace”Shikenan sai na ganki..Bye sai gobe in mun Hadu..!
Inteesar tace”Gobe 10am muke da Lecture ki Biyomim mu Tafi tare..ko Kina da mai kai ki ne Kada na Takura Miki..?
Munari tace”Yayana ne Daman ke ijiyine in muna Karatun 8am Daganan ya Wuce Office in kuma ya Wuce Haka Dan Sahu nake hawa..Kada ki Damu Zan zo sai mu Tafi Tare..!
Inteesar tace”Yauwa..Kawo wayarki na Saka miki Lambata..!
Ba Musu Munari ta Daukota Daga Cikon Jaka ta Mikamata ta Saka mata Tana Fadin”Wani Suna Zan saka miki..?
Munari tace”Ki saka Besty Intee..!
Inteesar Tayi Dariya Tana Fadin”Au..Nima kuwa Da kin je gida ki kirani Zan saka Besty Munira..!
Dariya suka saka Gabadaya Daganan sukayi Sallama ganin Maza nata Haraman Zuwa Masallacin Inteesar ta Juya Zuwa Gida Tanajin Wani Farincikin in Tana Tare da Munari Sai take ji kamar Tana Tare da yar”uwanta na jini kamar Nasara,Dayake Daga Munari har Inteesar basu Taba gaanin juna ba Shiyasa bazasu Shaida juna ba sai dai Bond din Jini Dake Tsakaninsu ne yasa Sukejin kamar wani iri a Tsakaninsu hakama ta Bangaran Munari tana jin Intesar Sosai acikin Ranta.
Tana Shiga Haraban Gidan suka ci karo da Abba da Imran Harda Ya Yusuf ya Dawo Ganin ya Imu sai da gabanta ya Fadi tana gaishesu Abba ne kadai da Ya Yusuf ya amsa bandashi Daya wani Hade rai yana kallon Gefe.
Abba ne ya Kalleta yana Fadin’Munarin Abba ina kika Tsaya yau kin gota Lokacin Dawowarki..?
Kafin Tayi mgana Ya yusuf ya Rigata Da Fadin”Ni kaina na Damu yanzu Safiya ke Fadin Shuru bata Dawo ba Har 6:30pm ta wuce..?
Yafada Lokaci Daya yana Duba agogon Fata na kamfanin Rado Dake Daure a Tsitsiyan Hannunsa.
Da Sauri Munari tace”Ban samu Adaidaita ne da Wuri ba Ya yusuf Shiyasa..!
Jin haka yasa Dagashi Har Abba suka Kada kai Ya yusuf yace”Kawai Daga yanzu in na taso da Wuri Zan rika kiran ki naji in kun gama Sai na Biyo na Dauko ki..Kina mace bana so kina Yin Dare a waje..!
Kai ta gyada batare da tayi mgana ba ta Mike ta Wuce Sum sum ta wuce Ba Saboda kowa taki Fadan inda ta Tsaya sai Saboda Ya Imu ko kowa zai Fahimeta ban dashi ta Tabbata sai yayi kwallo Da ita bayan ya Fara Sauya mata kammin Dayake ikirarin Tun a Haraban gidan kafin su Shiga Ciki Shiyasa ta Rufama kanta asiri.
Cikin Gida ta Shiga su kuma suka Fice koda ta Shiga Safiya tana Shashnta Tana Sallah Domin ta Lekats sai kawai ta Wuce Dakinta Kafin ta Shiga wanka sai da ta Kira Inteesar sai taji bata Dauka ba sai ta Tura mata sako
Salam Besty nice..Munari..!
Daganan ta ijiye wayar ta Tube ta Shiga Tayi wanka,Ta Dauro alwala Tazo Tayi Sallah Ta idar kenan Tana Saka kaya Safiya ta Shigo Tana yi mata Sannu da zuwa Sai da Tagama Saka Kayan suka Fita babban Falo su Abba basu Dawo ba sai da sukayi Isha”i Lokacin Munari taci Abincinta Saboda yunwa Tea kadai ta Kara sha tayi musu Sallama ta Shige Dakinta ta Kwanta tagaji,Ta bar Abba da Ya yuauf da Safiya a Falo Abba da Ya yusuf Hira suke Safiya kuma Tana kallon Imu dai yana Dakinsa yau ko Tea din bai Sha ba Tun bayan Dawowarsu ya Shige Ciki,Sigari Ta Riga ta gama Cikamai Ciki in ji Abba Suna Dariya Shida Yusuf.