
Imran na Sawo kansa Cikin Falon suka Ci mummunar karo da Inteesar Da Sai da Kafadarsa ta Daki kanta Tunda ya Fita Tsawo,bata san dashi ba da Karfinta ta Jefa jikinta Munari na Binta zata Rakata Haraban gidan,Kafadarsa ba kadan bace kuma Shima da Sakin jikinsa ya Sawo kansa Falon baisan da ita ba Shiyasa ya Bangajeta Bangazan da ta kasa Tsayuwa da Kafafunta tatafi Luu zata Fadi ta Gefenta da Wani Zafin Nama ya Saka Lallausan Igarman Hannayensa ya Tarairayota ta Fado kan Kirjinsa da karfinsa Har Karan Hancinta da Kirjinta suna Dukan Faffadan Kirjinsa.
Munari Dake tsaye har ta Sadakar Inteesar ta gama shan kasa,sai kuma ta kame gefe Daya tana kallon Inteesar Rike hannun Ya Imran hannayensa Zagaye da Kugunta Yayi mata Riko sosai.
Inteesar abun ya Faru cikin Lokaci kadan ne shiyasa bazata iya Tantance komai ba,sai da taji wani Ingarman Namiji mai Zatin jarumta yayi Saurin Tareta kuma ya Tallafota zuwa jikinsa Maida Nunfashi take sama sama Inteesar akwai tsoro ta Tsorata da Fadin da Zatayi yasa ta Saka Hannayenta Guda Biyu ta Rike Rigar Imran dashi Idanuwanta a Lumshe Tana maida Numfashi.
Imran kuwa wani Sanyi yaji yana Shiga Jikinsa da Zuciyarsa wanda Tunda yazo Duniya bai taba jiba ba..Kirjinsa Duka kawai yake yana Fat..! Fat..! Da karfi kamar wanda yaga wani abu tsoro..
Fuskar Inteesar ya Kurama ido Wacce ke kan kirjinsa Tana Rirrike dashi Da karfi,Kallonta yake kamar yana son ya Haddacr komai na Fuskarta Kada ta bacemai,Yana jin kamar Rikonta wani Salama ne da Farinciki awajensa kamar in ya Saketa zai Tagayyara ko zai Lalace yana jinta acikin jikinsa kamar Wani gafara ne Daga Allah.
Abba ya Bude Kofar Dakinsa ya Fito Dauke da karamin Littafin azkar Jikinsa Sanye da Wata Farar shadda Dinkin Riga da wando har da Hula.
Ganin Imran da Inteesar a wannan yanayin sai da gabansa ya Fadi Cikin Azama ya Karisa Cikin Falon yana Fadin”Kai Imran Lafiyar kuwa ka Rike Diyar mutane..,?
Yafada da dan Karfi wanda ya Dawo dasu Dukkansu Cikin Hankalinsu.
Inteesar jin muryan Abba asama yasa ta Dago Tana kallon Fuskar wanda ke Rike da ita ai Tana ganin Imran taji wani Yam! acikin jikinta da Sauri ta Kwace Jikinta Ta mtsa baya tana Maida Numfashi
Shi kuwa Daman jikinsa ba Karfi ga Kasalan data Rufeshi shiyasa Inteesar ta iya kwace Jikinta..
Da Lumsassun idanuwansa ya Kalleta Kafin ya juya ya kalli Abba batare da yayi mgana ba ya Fara tafiya zai shiga Dakinsa,Abba ya Daga baki yace”Kai IMRAN ya ka nan ya ina maka mgana kana wucewa..?
Yafada cikin bacin rai baya Fatan ace Ya Doke yar Mutane ne Juyowa yayi yana jin mganar tamai nauyin ya Fada Munari ce tayi Saurin cewa”Abba Karo sukayi da Intee…Basu ga juna ba Shine zata Fado ya Rikota..!.
Ajiyar rai Abba ya Sauke Kafin ya Maida kallonsa kan Inteesar Dake Jin wani iri acikin jikinta yace”Sannu Baki dai ji ciwo ba ko..?
Inteesar Dakyar ta iya Bude baki tace”A”a Abba..Sai da safe..!
Tafada tana Juyawa,ta gefen ido Take kallon Imran yana Shiga Dakinsa Abba yanata ta gaida Mama,Ta fice Munari ta Bita abaya suna Fitowa Munari ta Riko Inteesar tana Fadin”Kai Besty kinga yadda kikayi ajikin Ya Imu..? Na Rantse har ga Allah kunmin kyau kamar a Indian Film din nan irin Jarumar zata Fadi Jarumin yayi AzAman rikota ta Fadomai..!
Ta Kariashe Fada tana Dariya Inteesar ta Harareta Lokaci Daya tana Tuno yanayin data Fada kan kirjinsa sai da jikinta ya amsa domin Bayan Muharramanta wani namiji bai Taba koda taba Hannunta ba sai yau wanda Komai ya Faru bisa Rashin sani.
Ganin taki mgana yasa Munari ta Cigaba da Fadin”Nayi mamakin Ya Imu yau..? Kun bala”in dacewa kamar ace ku din Couple ne..!
Da sauri Inteesar tace”Da wa..?Allah ya Tsareni baki man fatan kwarai ba..Indai na auran wannan Muradadden yayan naki ne..!
Munari zata kara mgana Inteesar ta Dakatar da ita da Fadin”Kinga ni kyaleni..Nagode Daya Taimakeni Daga Faduwa kawai..Sai da safe ki koma gida malama..!
Munari ta kada kai Tana Fadin”Daga waasa..? Allah baki Hakuri..!
Inteesar ko kulata batayi ba ta wuce Munari ta Bita da kallon Cikin Rashin jin Dadin yadda ta Bata mata rai ita Har ga Allah waasa take mata kada kai Tayi ta koma Cikin gida Tana Fadin gobe zata bama Inteesar hakuri banda Abunta Ya Imu ai ba Aure ma yake da Ra”ayin yi ba Ballatana wannan mganar ta Dameta.
Inteesar har takai gida ta rasa yanayinta Kowani Dakika abunda ya Faru ne yake Dawowa mata Kuryan Daki ta Shige ta Fada kan gado ko Hijabin Jikinta bata iya Cirewa ba,gabanta sai Fadi yake Data Runtse ido sai ta ganta Rike da Imran Kirjinta yana Saman kirjinsa Runtse ido Tayi a Fili ta Furta”Shikenan Mara Mutuncin nan ya gama dani..!
Take fada tana kara jin wani Takaici Da ta Tuna abun sai ta Saki Tsaki kuma abun yaki bace mata acikin Ranta da Zuciyarta Har Mama Sai da ta Tambayeta ko Lafiya jin yadda Lokaci Bayan Lokaci take sakin Tsaki Sai ta sanu kanta da Boye abunda ya Faru tace bakomai.
Bangaran Imran kuwa ya kasa Gane Yanayinsa In ya Runtse ido Sai yaji Fadowar Inteesar a Kirjinsa sai gabansa ya amsa Yana jin alokacin Yanayinsa ya sauya kamar bashi ba yana Tuna yadda ya Saka Hannayensa ya Zagaye kugunta dashi,yana kwance da Silasin Dare ya kasa barci Ya Busa Sigarin nasa Ammh duk a banza Yana kwance yana Tunani kafin ya Murmusa afili ya Furta”Kugun nata ma D’An karami ne kamar yadda take karama da ita..!
Yafada yana Bin hannuwansa Daya Daga da kallo.
Kafin ya kara Juyawa yana Yin Filo da Hannayensa yace”Sai Rashin kunya kuma..!
Yafada shi kadai kuma yayi Mirmishi kamar wanda ya zare,Rufe Manyan Idanuwansa yayi Yana Fatan barci ya Daukesa sai mai gabadaya Fuskar Inteesar ne take mai Hazo da Gilmawa acikin Rufewar idanuwansa,Sai Mirgina yake yi yakasa Barci in ya Bude Idanun nasa ba Fuskarta yake gani,Mikewa Zaune yayi Cikin Duhun Dakin Sai dan Hasken Dake shigowa ta Labulan Dakin Dayake Dagawa ta Window.
Kansa ya Dafe yana Fadin”meke Shirin Faruwa dani ne..?taya ya ko ina nake ganin Fuskarta..?
Kodai ba Mutum bace Aljanna ce..!?
Wata zuciya tace”Mutum ce ba Dazu kaga Kafarta ba..Bata da Kofato..!
Sai kuma ya Saki Mirmishi kafin ya koma ya kwanta Ringingine yana mai Dora kansa saman Hannayensa acikin Ransa yace”Koma aljannace…Ni Imran nafi karfinta..!
Daga haka barci ya kwasheshi Dakyar ammh Abun mamaki masu cike da mafarkin Inteesar
Washegari sai 10am suka shiga makaranta Shiyasa Ya Yusuf ya tafi ya barsu sai da suka fito Daga Lecture suna Hanya zasu masallaci Munari ta Kalli Inteesar data ganta Yau wanu iri bata da Kuzari kamar ko yaushe tace”Besty wai duk fushin ne… ? Am Sorry..Wlh am just kidding..!
Inteesar ta kalleta kawai batace komai ba Sai Munari Taji wani iri Riko Hannun Inteesar tayi yasa suka Dakata da Tafiya Munari ta kalleta Tana Fadin”Meke damun ki ne..?
Inteesar ta Saki Mirmishi kafin tace”Bafa komai..Kece wai kika bani mamaki kina wani ban hakuri..? To miye na ban hakuri..?
Munari tace”Ai naga jiya baki ji Dadin nganata bace kuma..!
Manta kawai..!
Inteesar ta Katseta Lokaci Daya tana jan Hannunta suka Cigaba da Tafiya Munari dai sai kallonta take tana Naxarinta ta Tabbata wani abu na Damun Inteesar Ta san ta Tana da Sakin jiki da wanda suka saba kuma Tana da Kuzari da kazar kazar ba kamar yau data ganta sai a Hankali ba
Ganin yadda Tayi ne yasa bata kara Tambayanta ba ammh Haka suka Wuni acikin makaranta Inteesar bata da Kuzari sai chan ne na ta Dan saki suka Fara Hira,
Abunda Munari bata gane bane Inteesar Tunanin Abunda ya Faru jiya yaki wucewa acikin Ranta,itama Har mafarkin abun ta Sake yi,wai gata Rumgume ajikin Imran sai abun ya Dameta sosai Tana ganin ya gama da ita ne Tunda ya Rumgumeta kuma abun da bata saba dashi ba Shiyaasa duk ya Sakarmata Jiki da kwarin zuciya.
Sai dai ta saka aranta bazata Kara yarda su hadu da Imran ba Domin ai Tunda ya Rungumeta yaji Tudun Nonuwanta ya gama da ita Har Abada.
Tun kuma Daga Ranar Inteesar ta Yanke duk wani Hanyar Haduwarta da Imran ta Rage shiga gidansu in zata Shiga kuma sai ta Tabbatar da Baya gida,In kuma ta Hangesa sai ta Boye kanta saboda Bata so ya ganta.
Imran daya Daina ganinta bai Damu ba Sai Daga baya sai ya fara jin ya Damu Saboda ya daina ganinta agidan kuma bazai tambayan Munari ba,Yana Tsoron kada ace ta Koma Gidansu ne,Ya ma rasa Dalilinsa na Wannan tsorom Ranar har kiran Sagir yayi yana Tambayansa Wannan yarinyar fa..?
Daman Sagir na jin Haushinsa a Gadarance yace mai”Wata yarinya kuma..!Rainin Wayau ne baya so Shiyasa ya Datse Kiran yana kara jin Haushin kansa me ye hadin da ita..! Da zai ji ya Damu Domin ya Daina ganinta da wannan Tunanin ya Watsar da komai shi kuma Sagir bai maida kai kan mganar Imran ba yana Tunanin wani Wulakancin nashi ne ya Tashi kan Inteesar shiyasa ya Nunamai bai ma Fahimcesa ba.
Sai dai mai Imran yaji Duk Duniya Fuskar Inteesar yake son gani Duk da ya gama Haddace Fuskarta Inda ya Iya zane zai iya Zama ya zana sai dai Haka nan yake son kara Kallon Fuskarta Kamar za”ayi mai gafara Dalilin haka ya koma Zuwa Shagon Sagir,wanda yaransa Har sun Fara Sakewa suna Murnan Takurarre ya Daina zuwa sai gashi Ranar kwatsam ya Dawo,Ai Ranar ba wani wanda yayi Wani Motsi mai Karfin Sanin Halinsa Mganarsa kamar yankan Takobi ne in yace Dole sai takai Sara ne.
Ba domin kowa ya dawo ba sai Domin Inteesar ya gama yanke ma kansa mganar Cewa Inteesar ba haka ta barsa ba indai ita ba Aljannah bace to Akwai wani abu akasa.
Taya ya haka kurum rana Tsaka Zai Dawo ba Wacce yake son gani sai ita a Baya yadda da ana cewa Ana ma Mutum asiri sai yanzu ya Fara Tunanin asiri tamai ya Zama Dole ya ganta ko yatambayeta Me yasa tamai asiri sai dai bai samu ganinta ba,Ko makaranta suka Dawo bata yarda ta Sauka ta Kofar Shagon Sagir sai takara Chan gaba in kuma a kafa suka Tako da Sauri take wuce wajen bata ma ko kallon Barayin Duk da tana ganin Imran din ammh shi baya ganinta,sai sau Daya kuma kafin ya yi wani yunkuri ta Shige shi kuma bazai iya Binta ba.
Ana cikin haka suka Fara Test basa Samun Lokaci domin suna gabda Fara Exams din Farkon Zangon Karatunsu.
Daddy yazo ya ganta Sau Daya shima amakaranta ya Bita bai gayamata zai zo ba,Kawai ya Kirata yace ta ina..?murna kamar Inteesar zata Shida aka kuma yi Rashin Sa”a Munari ta Shiga Masallacin yin Sallah ita kuma Inteesar sai bataje ba ta Zauna anan Department dinsu tana Duba littafanta Daddy ya kirata.
Ashe ma ya shigo Cikin makarantar yana Office din abokinsa Wani Daurin auran Yar abokin su da sukayi karatu Tare ya kawosa,chan taje ta samesa suka ga juna,bai wani Dade ba yace zai tafi Har Department dinsu suka Dawo Neman Munari bata ganta ba Ta Kira wayarta sai ta Tuna ai jakar na Munarin gata a Hannunta,Kuma har Masallacin taje akace mata ta Fito,Karshenta Dai Daddy tafiya yayi basu hadu da Munari ba sai bayan tafiyarsa ne ta ganta ashe itama Nemanta Takeyi kuma ba waya ballatana ta Kirata Cikin Rashin jin Dadin Inteesar ta Fadamata Zuwan Daddy da Tafiyarsa ta bata 5k din Dayace ta bata Ita kuma 15k ya bata 10k yace takai ma Mama Munari ta karba Tana ta Godiya Tare da Cizon Yatsan Rashin Ganin Daddy a Karo na Biyu.
Sati biyu da gama Test dinsu suka Fara Jarawabawarsu Cikin Kwarewa Dama Tuni sun shiryamata basu sha Wahalanta ba,Inteesar nata Murnan Zuwa Gida Kaduna yayinda Munari ke alhinin kewar Inteesar din.
Sai uku sukayi suna Jarabawa kafin su gama sun samu Hutun Sati uku kafin su Dawo su Dora a Karatun Zango na Biyun aji Daya
Aranar da suka gama Inteesar Kamar Zata Suma saboda Murna ta gama Hada kayanta Ya Basheer da Safe zai zo ya Tafi da ita.
Munari duk ta shiga Damuwa Saboda Tafiyan Inteesar din itama Tana jin Zatayi matukar kewar Munarin.
Bayan sun Rabu aranar Inteesar Tayi Tunamin ta bama Munari wani abun Da Zata Rika Tunawa da ita sai ta Dauki wani Dankunnen gold dinta mai Sarka da Zobe da awarwaro ta saka ajaka zata kaima Munari ba Domin bata dashi ba sai Domin Wani abun da Zata Rika Tunawa da ita in ta koma Kaduna itama Zataje Munarin ta bata wani abun da In ta koma Kaduna ta Kallah Zata rika ganinsa kamar Munarin.
Karfe 5pm tayi ma mama sallama ta Fito tana Sanye Cikin bakin Wando plazo da wata Riga Mai Dogon Hannu ammh Tana da dan Tsawo,sai ta Sanya Farin hijabinta mai Hannu wanda yakai mata Har Gwiwa.
Karamar Jakar data saka Dan kunnen aciki sai Kafarta Sanye cikin Takalmi Sahu Ciki Fari kalan na mata.
Tun fitowarta Gidan ya ganta Lokacin ya Fito Daga Shagon Sagir Karan Sigari rike a Hannunsa yana sha Gida Zai tafi Domin yagaji da Zaman sai ya ganta Tanufi Hanyar gidansu Gabansa sai da yya fadi,Tun bayan mganar Data Fadamai na ya Daina shan Taba Kowa yasan ya Rage shanta sai dai Yanayin Dayake ciki na bukatuwan son ganinta ya kara maidashi Ruwa..
Jikinsa har wani mazari yake Zuciyarsa na Ingizasa yabi bayanta Cikin Takunsa na Sasasarfa ya Taka mata Baya Kowani Dakika na Takunta Sai Zuciyarsa ta Buga,kawai ya gama Sakama Ransa yarinyar nan asiri tayimai kuma yau sai ya Shaketa ta gayamai inda ta Binne koma Menene taje ta Hakosa Imran yafi karfinta bama Itaba yafi karfin matan da suka Fita komai da komai da duk Abunda suke Takama.