GIDANMUNOVELS

GIDANMU 1 & 2 COMPLETE

GIDANMU HAUSA 1 & 2 COMPLETE

Shakira
3/22/22, 23:06 – Ummi Tandama😇: GIDAN MU..!
(Our House)
Book 1

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

       *🅿�24*

Duk abunda ya faru Imran bai sani ba Kowani Dakika da kuma Wayewar gari Inteesar na cikin ransa yana kuma Kirga kwanaki da Ranar da Hutunsu zai kare,Domin tun yana Daukan Lamarin wasa har ya fara ganinsa da gaske ne,Domin baisan wani yanayi yake ciki ba ammh Tabbas da Tunaninta yake kwana dashi yake tashi yana jinsa kamar ba Daidai ba in bai ganta ba yana jinsa kamar ya rasa wani kuzarinsa ne da Tatafi.
ya zauna yayi Tunanin meye Hadinsa da ita da Har Tunaninta yake Hanashi Sukunu ya kasa gano bakin Zaren yanzu ya daina Tunanin Tayi mai asiri sai dai yafi Tunanin kila shine Aljanun suka shigeshi Shiyasa ya kasa Gane kansa Kwata kwana.
Afarke yake ko cikin Barcinsa Inteesar ce take giftamai abum kamar almara Ko yana zaune ne yana Kallon wani Waje Fuskarta yake gani Mganarta kuma namai amsa kuwwa acikin kunnuwansa Saboda ita yanzu ya Rage shan Sigari koda ya Daukota zai kunnata sai ya Tuna da mganarta yaji kawai bazai iya Saba mganarta ba Duk da bai mata alkawari ba sai da yaji yana son ya Daraja mganarta akalla ko bata Dawo ta gansa ya Daina sha ba ta Gansa ya Rage shanta Fiye da baya ba kuma domin yana Tsoron kada Tamai Lahani ga Lafiyarsa ba wannan baya gabansa Ya sani Shi Tuni Lafiyarsa ta Samu Tawaya.
Ko alama baisan bata da Lafiya ba Saboda ko Sagir bai taba mai Zencenta ba kuma Saboda ita yake zuwa Shagon akai akai Koda Hirarta ne yaji Sagir din yayi mganarta shi kuma ko Sau daya bai taba mai ba Shi kuma Ego dinsa bazai taba barinsa ya Tambayeshi ba.
Ko agida bai taba jin Mganarta ba Saboda baya zama cikin su Munari ce Ke da Labarinta kuma baya Sakarmata Fuska ba,ballatana yaji wani Zencenta kuma bashi da Lambarta ballatana ya Kirata Ko da ma yana Dashi bazai iya Kiranta ba Saboda yana ganin ai bashi da wata alaqa da ita Abun na Dauremai kai Ko Lokacin dayake amsa sunansa na Imran Wata mace bata taba Burgesa ba Ballatana yanzu Daya Juyama Rayuwar jin Dadi baya,Abun kunya ne babba agareahi wani ya Fahimci Halin Dayake ciki Dalilin haka yasa ya Rage yawan Walwalwarsa Fuskarsa kullum tana Hade ba Fara”a koda bai da yawan mgana ballatana Yawan Dariya Ya yusuf da Abba sun Fahimci wani abu na Damunsa sai dai sun sani koda sun Tambayesa bazai taba Fada Musu ba Imran yana da Ego gayama wani abunda ke Damunsa koda Damuwar abun zai kasheshi ne ya Gwammace ya bar abun shi kadai baya son yadda Ransa ya baci kan al”amarin ya Raba Bacin ran da wani nashi.
Shiyasa yake ta Kokarin yakice abun acikin ransa,Bayason Tunanin Inteesar din tarabi Tunaninshi Sai dai ya kasa Controlling kansa da Tunaninsa Kowani Tunaninsa da Motsinsa Tana makale acikin Ransa da Zuciyarsa Kamanninta da mganganunta sun kasa bacemai acikin Idanuwansa da Kwakwalwarsa.


Sunday.
10:03am na safiyar Ranar Lahadi.

Abba ne da Ya yusuf sai Anty Safiya da Munari zaune kan Dining suna Breakfast,tunda yau din Lahadin karshen mako ne,Ya yusuf na Gida cin abinci Sukeyi batare da kowa yayi mgana ba bakajin komai sai karam Cokula da karan Mug din Tea.
Ya yusuf ne ya Kurbi Tea kafin ya maida Mug ya ijiye yana kallon Abba Dayake cin Soyayyan kwai ahankali ammh Rabinsa Hankalinsa baya kan abunda yake yi ya tafi wani Tunanin nadabam.
Ya yusuf ya gyara Zama yana Fadin”Abba badai Tunanin zaka Dawo dashi ba..?
Yafada yana kallonsa Abba Daya Sauke ajiyar Zuciya ya ijiye Fork din Hannunsa yana Fadin”Kunyi mgana da Dr..?
Yusuf yace”Eh jiya na kirashi yace…!
“Wannan watan da kaina zan je asibitin..Kuma ina Fatan ya zama na Karshe Tunda alhamdulillah na Warke da yardan Allah..!
Abba ya katesshi yana fadin hakan Yusuf ya kalli Safiya itama ta Kalleshi Kafin ya maida kallonsa kan Abba yana Fadin”Alhamdulillah Abba haka nake son ji..Allah ya kara Lafiya Gobe Kafin na wuce wajen aiki sai muje Tare In Allah ya kaimu..!
Abba ya gyada kai bai yi mgana ba Munari Dake gefe ta Tusa Dankali da kwai bakinta tace”Abba Am so Happy..!
Kamta ya shafa yana Fadin”Ki daina mgana hakan kada ki kware Munarin Abbanta..!
Kada kai tayi tana Kokarin Daukan Mug din Ruwan tea din Dake gabanta ta kurba ko abunta ta saka abakinta yawuce mata.
Abba ya Dauki Tissue yana Share Bakinsa Lokaci Daya yana Fadin”Yanzu ai nafi kowa sanin Illar Damuwa da Tunani Tunda Sanadinta yasa nayi nesa da komai nawa Ciki Harda yan”uwana da Mahaifiyata..Nasan Zafin Rashin naka sosai na kuma san Zafin Mutuwa Wanda cikin Zafinta nake har yau har gobe..Sai dai na Dauki kaddaranta nasan Mutuwa ta Allah ce kuma Kaddara Musulmi takaci..Mu kanmu Watarana zamu mutu duka munbar Duniyar muje mu Tarar dasu..Ni yanzu Addu”ata garesu Allah ya jikansu da Rahma Allah yasa sun Huta..!
Gabadayansu suka amsa da Ameen Cikin wani yanayi Abba na Shirin mikewa Yusuf yace”Abba Daman Ina son mgana Dakai..Kan Imu ne..!
Abba ya koma ya zauna yana Fadin”Meya samu shi Imran din..?
Yusuf yace”Abba kafi kowa sanin Imran na Bukatar Taimakon mu sosai..bazamu zura ido Rayuwarsa ta tafi a banza a Shan Taba ba Abba We hv to do Something..!
Abba yayi Shuru yana wani Tunani kafin ya kada kai yana Fadin”Kamar wani mataki kake ganin zamu iya Dauka kan Hana Imran Shan Sigari Yusuf…?
Kafin ya bashi Amsa Safiya ta Mike Zata bar wajen Abba ya Kirata ta Dawo Cikin Dattakonsa yace”Koma ki Zauna ina zaki..?
Cikin Ladabi tace”Abba zan koma Daki ne..Naga kuna mgana ne..!
Abba yace”A”a koma ki Zauna..Meye baki sani ba..?wannan gidan kema Kamar Gidanku ne zauna mganar Dukkanmu ta Shafemu..!
Bazata iya ma Abba gaddama ba, yasa ta Koma ta Zauna tana gyara Zaman Vail din Data yane kanta dashi.
Abba ne ya maida Hankalinsa kan Yusuf yana fadin”Umh ina jinka Wata Hanya kake ganin zata Bullemana..?
Bayan Nasihan Dakemai nima kuma inamai ita bai Daina ba..?
Yusuf yace”Eh to kamar mu nema mai Taimako wajen Malaman addini na addu”a Abba..Ko da bana shan sigari ba..Na bakar zuciyar nan Abba da rashin son zama cikin Mutane..!
Abba ya kalli Yusuf sosai Kafin ya dan Murmusa Cikin Dattakkonsa yace”Ba wani Taimakon da zamu nema mai Yusuf..Kafi kowa sanin Imran kamar yadda nasanshi bazai bamu hadin kai ba..Taimako Dayane kawai ya Ragemin agareshi zan koma cikin Ahalina Ina da Mahaifiya Hakkin Daada yana kai na matukar ina da rai da Lafiyata In na koma gareta Cikin yan”uwana zan basu dama su Zartar da Hukunci kan Rayuwarsa na Tabbata bazasu barsa haka ba..!
Yusuf ya kada kai kafin yace”Abba Inran din zai yarda wani bakai ba ya Zartar da wani abu akan Rayuwarsa..?bama haka ba Abba Bana jin Imran zai yarda ya koma cikin Yan”uwanmu Domin kullum ikirarinsa kenan..!
Abba yace”Shi ne zai bani Umarni ko nine zan basa..?
Ya yusuf ya kada kai kafin yace”Kai ne zaka bashi Abba..!
Abba ya Cije baki kafin yace”To bai isa na bashi Umarni ya Tsallake ba..Koda kaga ina Dagamai kafa na Dan Lokaci ne..Zamu koma Cikin yan”uwana Lokaci kadan da yardan Allah In yaga Zai iya Binmu ya kyauta ma kansa in kuma Taurin kansa ya Hanashi sai yayi Ta zama ni baruwana dashi..!
Yana gama Fadin haka ya Mike Da sauri Munari tace”Abba Lagos zamu koma ko Dukku..?
Ya waigo yana Kallonta kafin yace”A”a ba inda zamu ai nam din shine GIDANMU munari..Lagos kuma Zaman achan ya kare bazan iya Zaman garin ba..Dukku kuma Zamu jene ganin Daada da Sauran yan”uwana In Allah ya yarda..!
Munari tace”Abba kenan nan zamu Cigaba da Zama har Abada..!?
Gyada mai kai kafin yace”Da yardan Allah..Shine gidanmu..!
Washe baki tayi tana Murna kanta Abba ya Dafe kafin ya wuce bai Tsaya afalo ba ya shige Daki Daga gani mganar Imran ta Dameshi Sosai.
Yusuf ya Sauke Numfashi batare da yayi mgana ba ya Mike shima ya Wuce Shashensu Itama Safiya ta Mike tabi bayansa bayan ta bar ma munari Sallahun in ta gama ta Kwashe komai takai Kitchen tace mata Toh
Chan taje ta bama Yusuf baki Domin Taga Shima duk ya Damu,Abunda ta Dade Tana Nusar dashi kenan kan Neman Danginsu sai gashi yau Abba ya Furta da kansa sai mganar Imran shi kuma Wata mganace ta Dabam baka isa fa ka Chanxa Abunda Allah ya Hallicesa ahaka ba sai dai kayi iya Bakin kokarinka ka barshi yadda yake.
Sai dai kila Mace zata iya Sauyashi Watarana Indai yana sonta.
Haka Safiya ta Fadama Yusuf mganar Dariya ta bashi sai da ya Murmusa kafin ya Kalleta yana Fadin”Wata Macen ne zata juya Imu..?ban jin akwai wannan macen Baby..!
Bata iyamai gaddama ba Tunda ko ta Fada bazai yarda ba su suna ganin bamai iya Lamkwasa sa ita kuwa Tana Hange Imu Wani Lokaci anan gaba da Mace zata Zama tanajan Ragamar Rayuwarsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button