GIDANMUNOVELS

GIDANMU 1 & 2 COMPLETE

GIDANMU HAUSA 1 & 2 COMPLETE


Dukku local goverment
Area:Balikaje.

Kamar yadda take Ranar Lahadi a garin kano haka take Lahadin karshen Satin agarin na Dukku.
Yau gidan na Daada yana Cike da Mutane ne kama Daga ya”ya zuwa Jikoki,Tun jiya asabar Wasu suka sauka kamar su Inna Maimunatu da Inna Bintalo su da gayyar ya”yansu da marasa auran da masu auran duka suna Gidan Daada,Tun safe kuma Baffa Kabir ya sauka shima Tare da Mami Asma”u da ya”yansu duka Uku Wato Sajida da Umaima da Khamis wanda wannan karon Dolensa ya bar Aikinsa ya Taho Saboda Kiran Daada.
Baffa Mustpha ne karshen Zuwa Misalin karfe 11am na Safiya suka iso Bashir ne ke jan motar Umma da Inteesar da Hauwa suna Baya sai su Abiden Dake jikin Umma.
Inteeesar tun da suka Dauko Hanya bata iya cewa kala ba Bakinta kuwa ta gaji da Turasa ma ta Hakura ne bata so zuwa Dukku ba har ga Allah hakan baya Cikin Adanjanta Gobe ne suke Komawa Makaranta ta Fara Shirya kayanta Zata dawo ko Laraba ko alhamis Domin har mgana sunyi da Munari Zata dawo haka Kurum taji bata Kyauta ba in ta sabama Ya Imu alkwarinsa kuma ya gayamata Baya alkawari in yasan bazai cika ba kuma Shima bayaso ayimai in har baza”a cika ba..
Bata so ta karyamai Zuciya da Saba alkawarinta shiyasa ta Fadama Daddy zata koma Ranar Alhamis ko Laraba kuma ya amince mata har yayi mata alkawarin zai maidata kano da kansa Har Umma ta fara mata Shirin komawa Tunda har Mama ta kano sun yi mgana tace mata Intee na tafe Cikin Satin nan mai shiga kawai Rana Tsaka Ranar jumma”a Sai ga Kiran Baffa Kabir yana Fadama Daddy Daada Tana chan tana kuka Baba Asabe ta Kirashi ta gayamai shine yace abama Daada Wayar yana Tambayanta me ya faru nan take fadin Tana son ganinsu dukkansu kwansu da Kwarkwatansu Bata son ace mata wani baya nan ko yana makaranta ko yana Wajen aiki Dasu da duka ya”yansu take son gani kafin gobe a Dukku Domin Tana so ta Hada kansu ne kafin Ajali ya Risketa.
Ba Lallashin da bai mata ba ta Kafe kan mganarta Dole ya Kira Daddy ya Fadamai bayan ya Kira Su Inna Bintalo ya Shaida musu Halin da ake ciki Shine nan fa Kowa ya Tarkato Iyakansa ya Yada Zango adukku Gidan Tsohon Marigayi Alkalin Alkalai Hamisu Dukku.
Baffa Kabir Daman Khamis yazo Gida a Ranar zai yi kwana Biyu ya koma sai ga Kiran Daada Sajida kuma suna Hutu Tana gida Umaimace Take makaranta ba Halin adauje ma Tafiyar Duk yadda ko suke Girmama Karatun ya”yansu wannan karon basu da Tacewa Dole suka Tarkato har su sai sun Rasa aikinsu Gobe Monday Tun ba lalle bane su koma aranar sai takai su Gobe Tunda basu san Dalilin Taruwar da Daada ta Hada Lokaci Daya ba
Tun suna Hanya Mami ke ta Fada Tana Fadama Baffa Kabir Tana san bai wuce kan malami ba,tasa sukabar Komai nasu suka taho Mutumin Daya Gujeta da kansa kuma Miye abun Damun kai,Shidai yana Jinta bai ce komai ba sai Korafi take zata Rasa aikinta Gobe kadai Sajida ma Ranta bace saboda bata son Wahala ballatana Hayaniya gidan Daada kuwa komai da kanka Zakayi ba yan aikin da zaka saka suyi maka Khamis kuwa Da Umaima Ransu Fes Suna Farincikin zasu mahaifarsu suga Daada Daman Shima yana da Niyyar Zuwa sai ya bari sai wata watan in ya samu Huti bazai ma je Abuja ba Direct Dukku zai wuce yayi Hutunsa na Karshen Wata awajen Daada tunda Har ta gama Shan jinya bai Zo ba sai da ya Tura mata sako kuma Sunyi mganata ta waya..

Aharaban Gidan Basheer Ya faka Motar kusa da Tsala tsalan Motocin Ya”yan na Daada,Sai da kowa ya Fito Daga Motar kana Inteesar ta Fito Tana Tura baki Fuskarta ba Fara”a ko kadan Sanye da wani Riga da wando,Rigar Top ce Baka mai Dogon Hannu sai Wandon nata ja ne mai Tsuke ta kasa ya kamata ba sosai ba Sai kafarta Cikin Red Talkami Sawu Ciki Ta sanya After Dreess Baka Ta Saka Red din Vail din Mayafi ta yane kanta dashi haka kuma karamar Jakar Bayanta,Mai ratsin ja ce itama wacce ta ke goye abayanta kayanta ne ke Ciki Kala Daya da sauran kayan amfaninta.
Inteesar Tana bala”in son Best clour dinta Shiyasa yawancin kayanta Red ne.
Daddy ne akan gaba Sai Ya Basheer Dake Dauke da Abiden sai Umma Dake bayansu Dauke da Abida,Anty Hauwa ce ke baya Tana Tafiya a Hankali Saboda bata jin Dadin jikinta sosai,Laulayi Inteesar na bayanta kamar Tana Kirga takunta Gabda zasu Shiga Falon gidan ne Umma ta Waigo Tana kallon Hauwa Dake tafiya Sannu sannu ga Jaka ahannunta Inteesar na Bayanta bata karban mata Jakar ba.
Dakatawa tayi su Daddy suka Shige Shi da Basheer sai da Hauwa ta Kariso kana Umma tace”Hauwa basai ki bama Wannan Sangartattaciyar Rikon Jakar naki ba?
Kina tafiya Dakyar Dakyar Dauke da Kayan Nauyi kuma ga yanayinki..!
Anty Hauwa ta Murmusa tana Fadin”Bakomai Umma zan iya..!
Tafada Tana Sadda kanta kasa Domin ita akwai kunya.
Umma ta kalli Inteesar Data ke Tafiya kamar kwai ya fashemata acikin Ciki ta Aikatamata da Harara kafin tace”Abun da kika iya kenan..Kina ganin ta tana Tafiya Dakyar bazaki karban mata Jakan hannunta ba..?
Inteesar ta Tura baki Tana Fadin”Nima fa Umma ina Fama da tawa Jakar ba wanda ya karban mun..!
Umma ta aikamata da Dakuwa Tana Fadin”kin ga naki nan mara Mutumci..Ni ko Ubanki ko yayanki ne Zamu karban miki jakan..?
Kinga Inteesar ki kama jikinki ina gayamiki nan dai Dukku ne ba Kaduna ba..ki kama Jikinki Dangi sun Hadu kada atafi Dake a baki..!
Daga haka ta mikama Hauwa Hannu Tana Fadin”Bani jakar ni na Rike Miki Hauwa..!
Anty Hauwa ta Girgiza kai Tana Fadin”Umma don Allah ki barshi Zan iya..Kina fa Dauke da Abida nauyin zai Miki yawa..!
Umma ta Mika hannu ta karba jakar Tana Fadin”Bakomai bani ai ni bana Dauke da Lalurar dakike Dauke da ita..!
Dole ta sakarmata Jakar ta Dauka Daman ta kayansu Abiden ne da Madaransu sai ruwa jakar nasu kayan Tana Booth din Mota tare da nasu Umma..
Ko bi ta kanta Umma batayi ba ta Wuce zuwa Kofar da Zata Sadaka da Babbam Falon na Tsohuwa Daada.
Anty Hauwa ce ta Juya tana Kallon Inteesar data kusa Sakin kuka Saboda Haushi ta Murmusa kafin tace”Intee Daddy kawo jakar taki na Rike miki..!
Kunya ta kama Inteeaar sai ta sunne kai Tana Dariya Anty Hauwa ta kamo Hannunta Tana Fadin”Ai sai na Daukan Miki yar kanwata..!
Inteesar tace”A”a barmin abata kafin Umma ta ganki ta kusa tsireni gaban yan Uba..!
Dariya suka saka gabadayansu kafin su fara taku zuwa Cikin falon Anty Hauwa ce agaba ita kuma tana Binta abaya Tun daga Wajen kake jin Hayaniya nata tashi da kananun kukan yara yamutsa Fuska Inteesar Tayi aranta tana jin Zata Takura Tsakani ga Allah bata son Hayaniya wani Lokaci.
Ta Saka kanta Cikin Falon kenan Shima ya Sako kansa zai Fito wayace a makale a kunnensa yana mgana Basu san Da junansu ba yasa Inteesar ta Bige hannunsa Wayar dake hannunsa ta fadi kasa ta Watse Da Sauri gabadaya Jama”ar Dake Falon na Daada suka Dago kansu zuwa Bakin Kofar Falon.
Inteesar Dake Tsaye ta Dago Dara Daram Idanuwanta ta Sauke su kan na Dan”uwanta Khamis Kabir Hamisu Dukku Dogon Namiji kakkarfa mai Cikar ZAti da kamala Fari ne ba sosai ba yana da Duhu akallon Farko in kayi mai kamar Baffa Kabir yayi kaki ne ya Tofar saboda yadda suke kama kwata Kwata kamar ba Mami ta Haifesa ba ko alama baya kama da ita kamaminsa ta asalin Fulanin Dukku ne.
Yana sanye da Rigar Fara sai Wandon Sojiji Dake jikinsa,Kamar yadda Take karemai kallo itama haka yake kallonta sama da kasa wani irin Kallo wanda lokaci Daya Inteesar taji kallon bai mata ba da Sauri ta kauda kanta bata sanahi ba sai dai tana ganinsa bata Bukatar karin bayani Dan Baffa Kabir ne.
Kauda kanta Tayi kafin ta Duka kasa ta Fara Tattaramai wayarsa da Sauri ta Dago tana mikamai Cikin Sanyin Muryanta tace”Sorry..!
Tafada Lokaci Daya tana Mikamai Sake baki yayi yana kallonta da Duka Tunaninsa Inteesar taji Haushi ya kamata kamar ta kara Wurgi da Wayar nashi a kasa,wannan kallon har ina..? Sam bai dace ba yanayin yadda yake kallonta.
Kamar Daga sama wata Murya Daga Cikin Falon ta ratsosu Tana Fadin”Khamis karbi phone dinka mana..!
Kamar an Dawo dashi Daga Duniyar daya shiga ya saka Hannu ya karba Tare da Shafa Gefen hannun Inteesar din wacce tayi saurin janye hannunta Tana kallomta Lokaci Daya ta ballamai Harara asaman lebenta tace”Allah ya isana Dan iska..!
Shi yaji Sauttin Allah ya isan sai dai bai ji karshen ba ta kauceshi Zuwa Cikin Falon yabi bayanta da kallo Cikin mamakinta.
Kafin ya kada kai yafice Wayarsa Dauke a Hannunsa
Sawu cikin kafarta ta Cire kafin ta Fara Taka Lallausan cafet din Falon da Kyawawan kafafunta Gabadaya a Tsarge take ganin yadda kowa ya Zubo mata ido gabadaya Falon yana Cike Dakyar ta iya Daga ido ta Hango Inna Bintalo kusa da ita Inna Maimunatu ne suna Zagaye da yara da alamu jikokinsu ne Tuna Huduban Umma Tun kafin su Fito yasa bata Tsaya ba ta karisa gabansu ta durkusa Tana Gaishesu Inna Maimunatu ta Dafa kanta Cikin Fara”a Tana fadin”Allah mai iko..Mai sunan Daada ce ta koma haka Ya Mustapha?
Yana Daga chan gefen Kan Daya Daga Cikin kujerun falon. Kusa da Baffa Kabir ya Dagamata kai yana Fadin”Ga tan fa MAimunatu..!
Masha Allah take ta Fada Inna Bintalo ce ta tabe baki Tana Fadin”Basu son zumunci Salaha bata nuna mata Darajan mu ba..har gwarama Basheer yasan Hanyan gidajenmu..Ammh ita kam bata sani ba ni Rabo na da ita ma Tun batakai haka ba Wlh.!
Yarta Hamida Dake aure a Katsina Dake gefe tace”Mama ko mu ta ganmu ahanya bazata gane mu ba..Bata kuma je gidanki ba ina ga mu namu gidajen..?
Yar”uwanta Siyama Dake gefe Tana Shayar da Jaririyanta ta Karbe da cewa”Gaskiya akwai mtsala..Nifa sai wannan Haduwar ne ma nake ganin wasu..Har gwarama Ya”yan Barrister Baffa kabiru ana ganinsu..!.
Kamar an tsokane su haka suke ta Tofa albarkacin bakinsu Inteesar Haushi kamar ya Kasheta Umma Dake Kusa da Mami Asma”u ta kada baki tace”Kayya Bintalo bai ko kamata ki ga Laifina ba..Intee ai taku ce Dukku Tun Tana karama take zuwanta In Babanta zai taho Data Girma ne saboda Karatu ta Dauke kafarta..!
Inna Bintalo baki ta tabe batayi mgana Domin ita daman in ta Raina Kurarka akwai Wulakanci basu yima Mami saboda bata Raga musu sun santa Sarai kan ya”yanta sai ajita Dakai Shiyasa tana Zaune ko Tankasu batayi ba Farin gilashi ne a idonta Tana Kallon Wayarta bama ta Lura da Abunda ke Faruwa ba,Tun bayan Shigowar Inteesar da Karon da sukayi da Babban Dan”ta Taga irin mayen kallon Dayake Binta tayimai mgana Domin Ita bazata taba bari Wani abu ya Shiga kansa ba yarinyar sam ba ajinsa bace.
Sajida ce zaune gefenta Ta Dota kanta Saman kafadarta Idanuwanta suna Lumshe kamar mai barci Alhalin Idonta Biyu ta gaji ne kwanciya Take so yi bata son Damu da Takura.
Inteesar dai Dataga Cin Mutumcin bazai kare ba sai ta mike Fuskarta ba Fara”a ko kadan ta Wuce Inna Bintalo ta Bita da kallo kafin ta Rike baki Tana Fadin”Ikon Allah..ji yadda take Kumburi Yi hakuri yar nan kada ki Dakemu don munyi mgana..!
Baffa Kabiru ne ya Dakatar da mganar yana Fadin”Binta kibar mganar nan hakanan..Taruwarmu anan Saboda Daada ne bawai zaman kace nace ba..mu bari Daada tatashi Daga Barci muji Dalilin Dayasa tayi mana wannan Kiran gaggawan..!
Inna Maimuna ta kada kai Tana Fadin”Baban Sajida..Ai itama Uwace ko bata zo ba ita ai sai taje ko..? Ammh itama Shekarar ta nawa Rabonta da gidan Ya Mustpha..? Bafa yaranmu nee keda mtsala ba abun Daga Wajen mu ya Samo asali bama Ziyartar junanmu sai dai in Mun hadu anan Wajen Daada imu imu fa to ta yaya ya”yanmu zasu san muhimmancin nasu Tunda basa ganinmu muna Ziyartasu lokaci Bayan Lokaci..!
Kowa falon sai da ya Natsu da mganarta.
Sa”id Dake gefen Basheer zaune ya jinjina kai yana Fadin”True Talk Mommy..Kin fadi gaskiya ni kaina naji Dadin wannan Kiran na Daada ina so nima na fadi wanna mtsalan su Kawu su Duba su gani ataru a gyara Shiyasa nazo da Iyalaina suma suga yan”uwana..!
Sadam Dake gefensa yace”Nikaina Kana kirana ka gayamin na Tattaro Anisa muka taho dasu Waleed Domin sau Daya muka taba zuwa Dukku dasu..!
Ya”yan Inna Maimunatu kenan suke mgana Mazan na ta fari Tuni sun Girma sun zama magidanta Sadam din likitan Ido ne a kano yake Zaune anan asibitin Makka yake aiki yana Zaune da Matar Anisa da ya”yansu Waleed da Waleeda shi kuma Sa”id yana Zaune ne a garin Dutse yana aiki da Hukunar Wutar lantarki ta Jahar gabadaya,Ammh basu san suje gidan kowa ba sai Bauchi,sai kuwa in sun Leko Dukku shima yana da Mata da Ya”ya uku sunan Matarsa Fareesatu suna zaune da kanwarsu Wacce batayi aure ba Hafsatu,Karima da Zainabu sun yi aure anan cikin garin Bauchi kuma suma sun samu zuwa..
Kowa yaji mgangansu kuma yasan kan gaskiya ne,Baffa Mustpaha yayi Shuru yana Tunani yayinda Baffa Kabir bai ma Damu da mganarsu ba Mgana suke kasa kasa Shi da Diyarsa Umaima Dake gefensa.
Ganin haka yasa Itama Inteesar ta Nufi Wajen Dadynta ganin Anty Hauwa tana Tare da Matan su Sa”id Umma kuma na kusa da Mami ita kuma bata ma kaunar kallon barayin Jikin Daddynta ta Raba tana gaida Baffa Kabir ya amsa mata hankalinsa nakan wayarsa kafin ta maida kanta kan Daddy tana Fadin”Daddy am so tired..Ina Daadan take ne..?
Kanta ya Shafa ya Mike yana Fadin”Tana barci tasha mgungunanta sai tatashi Inteen Daddy..Ko zaki je ki kwanta ne..? Bata samu Zarafin mgana suka Hada ido da Umaimai sai Tayi mata Mirmishi itama Tayi mata Daidai Lokacin da Baba asabe ta Fito Daga wani Daki Dauke da Manyan Dardume Tana ta Maraba kafin ta Shimfade su nan Tsakar Falon ta koma Kitchen tana Jido wasu manyan Flaks da Kayan tea da Sauran Kololi Inna Maimunatu ce ta Kalli Autarta Hafsatu tana Fadin”Sannu da aiko Baba Asabe..Ke Hafsa tashi ki Taya Baba asabe jigilan kayan nan ai da yawa gayyar..!
Tsam ta Mike bayan ta Sauke Yarinyar Hamida Abul Dake ke Jikinta Tun Dazu itama kamar sa”ar Inteesar ce,Umma na jin haka ta Kallo Inteesar Tana Fadin”ai bama ita kadai ba Maimuna Ga sauran yan”uwanta nan tashi..Intee kema ki kama mata..!
Inteesar batayi gaddama ba ta Mike tana Ciro jakarta ta baya ta Mikama Daddy Baba Asabe tace”Da kun kyalesu ai na gama komai..Nasan kun sha Hanya ku samu ku karya ku watsake kafin Daada ta tashi..ga Dakunan fa Hajiya Mami da Umman kaduna Tunda ko zuwan yau ne ku shiga ku samu Hutu..!
Umma ce kadai tace”Kada ki Damu Baba asabe..Gasu nan su Tayaki miye amfaninsu..!
Ganin haka yasa Umaimai ta Mike Tana Fadin”Nima zan tayaki Baba asabe..!
Mirmishi Tayi tana Fadin”To yar gidan Baba asabe..!
Daidai Lokacin da Khamis ya Dawo Falon bayansu kawai ya gani sun shiga Kitchen Mami ya kalla yana Fadin”Mami wadanchan fa ina zasu..?
Yafada yana Zama gefen Sajida Lokaci Daya yana kallonta Mami Tace cikin ko in kula”Zasu taya Baba Asabe Dauko Breakfast ne..!
Kamis ya kalli Sajida yana Fadin”And ita kima wannan Zaman me take yi..!?
Mami tayi kamar bata jisa ba Cikin Bada Umarni ya Zungureta da Kafada yana Fadin”Oya Comon Mike kema kije yayi aikin Dake mai shegen son jikin Tsiya..!
Sajida ta Fara Kokarin kuka Tana kara Lafewa Jikin Mami tana Fadin”Mami kingansa ko..?
Mami ta Dago ranta bace Tana Fadin”Khamis zan fa bata maka Rai..Meyasa kakeson Takuramata ne..?ko agida kaga ina sakata aiki ne ballatana ka mtsa mata sai tayi aiki anan..?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button