GIDANMUNOVELS

GIDANMU 1 & 2 COMPLETE

GIDANMU HAUSA 1 & 2 COMPLETE

Cikin Lokaci sai gasu sun iso,layin Ashe su Anty Aneesa suna Farko Farko ne,Tun da suka taso ta Fito bakin Get din Tana jiransu Suna ma Cikin Tafiya Inteesar ta Hangeta Ita da Waleeda sabe a Kafadanta tace ma mai adaidaita ya Tsaya sun kawo.
Sai dai ta gansu kawai agabanta suka Fito Daga Cikin adaidaita Cikin murna sika Rumgume juna ita da Inteesar suna Murna ganin juna ta Karbi Waleeda Dake hannunta ita kuma ta Karisa ta bama adadaita kudinsa,ta nufosu Inteesar tana musu maraba tayi musu Jagora zuwa Cikin Gidan sai alokacin ta Lura da Munari sai da gabanta ya Fadi ta Kuramata ido Tana kallonta wannan tayi kama da na Hoton nan da Daada ta nuna musu a Dukku karamar ciki ammh in hakane meyasa Inteesar bata ganeta ba Ammh Tabbas wannan tayi kama da ita..
Tana ta kallon Munari,Har Munarin ta Tsargu ganin haka yasa sai ta Waske,gidan dan madaidaici mai kyau da tsari sai gasu acikin Falon gidan Anty Aneesa tace su Zazzauna Tatafi Kicthen ta kawo musu Ruwa da Abun shq kana ta Zauna suna Kara gaisawa.
Anty Aneesa ta Kalli Inteesar Tana Fadin”Itace kawar naki da kikamin zaku zo tare..?
Tafada tana kara Kallon Fuskar Munati wacce ke wasa da Waleda dake hannunta.
Inteesar tace”Eh itace sunanta Maimunat..Munari ga Anty Aneesa matar Ya sadam yaron autansu Daddy ne.inna Maimunatu. !
Munari ta Dago tana Fadin”Allah Sarki..Ina yini..?
Anty Aneesa ta amsa tana kara kallonta sai dai tana yi da taku kada Munarin taga kamar tana ta kallonta.
Inteesar tace”ina su waleed hala..?
Aneesa tace tana Mikewa”Ya bi Abbansa Asibiti..ai nasan in ya Shiga asibitin nan sai Allah Shiyasa nace ku Taho kawai..!
Inteesar tace”Gaskiya kam..gwara da muka Taho ba gashi mun zo ba..!
Aneesan tace”Wlh kuwa..Allah sa dai ya dawo kafin ku tafi..!
Inteesar tace Amin daganan ta koma Kitchen ta barsu nan Tana Hada musu Brekfast Tana ta Tunanin Munari itama in bata manta ba Kamar Fuskar ne tagani a Hoton nan sai dai hoton yana Wayar Baban Waleed ne Daya nan ne data Dauka ta Kara Dubawa ba kodai ba ita bace..?in da itace da Tabbas Inteesar zata fara sani kafin ita ammh in ko hakane kamar har ta baci.
Ferfesun kayan ciki ta kawo musu da Waina da Miya datayi da Safe,sai kunun Aya,da Soyayyan Naman kaza,Tazo ta zauna suna ta Hira da Inteesar ta rika jan Munari da Hira har itama ta Saki jikinta suka Zauna sukaci Wainan sosai da Ferfesun nan,suka kara komawa saman kujeru suna Hira sai da aka kira azahar kana suka Tashi zuwa Sallah Dakinta takai su tace suyi sallah ita kuma ta shiga Dakin Baban Waleed,waleeda Tana Manne dasu musamman ma Munari kamar ta santa.
Bayan ta idar da Sallah Kitchen ta Shiga ta Dora musu Dambun Cuscus na Zogala Cikin Lokaci ta gama shi suna Cikin Dakin suna Hira sai dai tazo tace su Fito suci suna ta mamaki.
Dambun yayi Dadi sukaci suna ta Santi,Sukace basu iya ba zasu dawo ta Koya musu Tace sai sun zo.
Bayan sun gama cin Abinci ne suka Dora da Zobon mai Dadi Data Hadamusu cikin su ya cika ammh Dadin Zobon yasa sai da sukaji ba Wajen Shiga kana suka Hakura.
Inteesar ta kunna Wayarta ta Kira Daddy tana Fadamai gata gidan Ya Sadam sai dai baya Gida sai Anty Aneesa Har ta bata suka gaisa Harda Umma,Daganan Ita Anty Aneesan ta Kira Anty Hauwa suka yi mgana da Inteesar ashe suna waya sosai Zumunci ya kullu Masha Allah.
Sai da sukayi Sallar La”asar kana sukayi Shirin Tafiya Tunda Ya Sadam shuru bai dawo ba,Aneesa nata Kiransa yace mata cikin wadanda suka ma aikin ido ne ya samu mtsala sai da suka kara komawa dashi su jiransa nan da Minti Talatin.
Sai dai har Ta wuce bai Dawo ba sai Inteesar tace bari su tafi Ranar Dayake gida Zata dawo ba yadda Aneesa ta iya sai dai taso yazo yaga Munari kila shima yaga abunda tagani ganin zasu tafi yasa tace su Tsaya suyi Hoto in ya Dawo Zata Nunamai haka kuwa akayi sukayi ta Daukan Hoto ta Daukesu Munari da Inteesar da yawa ta Dauka na Munari ita kadai itama Aneesan Inteesar ta Daukesu itada Munarin da Waleeda..
Kana ta Rakasu bakin Hanya suka Hau adaidaita zuwa gida ta basu 2k tace su biya mai adaidaita suka karba suna ta Godiya.
Gidan Mama suka yada Zango da suka Dawo sun gaji gashi Cikin su ya cika sun kasa Tafiya Munari bata koma Gida ba sai da Cikinta ya Sarara kana Inteesar ta rakata Gida,Koda suka je Abba ne kadai agidan Ya Yusuf da Anty Safiya basa nan Bata da Lafiya ashe Tun Safe take amai ya tafi ya kaita asibiti.
Jin haka yasa Inteesar ta zauna Har sai gabda mangariba suka Dawo Jikin nata da Sauki sai da Labari mai Dadi Tana Dauke da juna Biyu na kimanin Wata Uku Ba kunya Yusuf sai murna yake da bakinsa kuma ya Fada ma Abba.
Ana cikin Murnan sai ga Imran ya Fito Daga Dakinsa Da Sauri Yusuf ya Rumgumesa yana fadamai ya kusa Zama Baba sai alokacin Inteesar ta ga yayi Dariya Harwasu Daga Cikin Hakoransa sun Bayyana waje ya Bubbuga bayansa alamun Farincikin.
Su suka Rike Anty Safiya zuwa Shashenta suna mata Sannu Abunda yasa Inteesar ta manta da Abunda ya Faru da ita Jiya har ta kaiwa Bayan Mangariba.
Sai da su Abba suka dawo masallaci ta Tsorata ta tashi tace zata tafi Gida,Yana Dakinsa yaji Tana ma Abba Sallama Daman itace aransa yana Tunanin ta koma gida ko bata koma ba…?.sai yaji mganarta agogon Fatan Dake hannunsa ya kallah 7pm tayi Duhu ya fara Shiga Ransa ya baci ya Fito Lokacin har ta Fice Daga Falon Munari taso ta rakota tace mata ta Zauna Wajen Anty Safiya yau ma ba wayar nata agida ta barta.
Ta fito Gabanta sai fadi take tana ta Waige waige,Taji Tafiya a bayanta da Sauri ta Juya suka Hada ido dashi Sai taji wani Sanyi kamar an yi mata Gafara Tsayawa tayi tana Kallonsa yana Sanye da Riga da wando Baki da Fari,Ta lura blck and White kalansa ne Domin yawancin kayansa kalansu kenan sanan bata taba ganinsa da Manyan kaya ba Tunda ta Fara ganinsa bayan Jallabiya.
Ganin ta Shagala da kallonsa ne yasa ya Tsaya Hannayensa Cikin Aljihunsa yace”In kin gama Kallon nawa sai muje na Rakaki tunda ke baki jin mgana..!
Daga sama taji mganar sa Sai taji kunya ta Sadda kanta kasa Tana Fadin”Bansan Dare yayi bane..!
Da sauri yace”Oya muje..Bana son wata mgana kafin ki fashemin da kuka Shagwabbiya kawai..!
Yafada yana Kauda kansa dan Dariya Tayi kafin ta wuce yabi bayanta Sahu Sahu kafa kafa kamar wani mai tsa ranta Har Kofar gidan su Sagir Ita kuwa Gabadaya ta saka gane yanayinta jinta take kamar tana yawo Saman gajimare sai da suka iso kana yaja ya Tsaya ita kuma ta Waigo Tana kallonsa,Shima ya kallentan sai da ya Dauke kansa Mirmishi tayimai kafin tace”Nagode..!
Dahaka ta juya ta shiga Gida,dan Bakinsa yadan Cija kafin ya Juya zuwa Gida Aransa yana Fadin”Batajin mgana yanzu ba ban rakota ba wani abu ya Kara faruwa fa..? Da sauri ya Kauda wannan Tunanin jin har Zuciyarsa ta fara rawa.
Tana Shiga gida tama Mama sannu da gida ta Shiga Tiolet ta Dauro alwala tazo Tayi sallah bayan ta Idar ne ta Duba wayarta Taga Kiran Ya Sadam da Anty Aneesa,Da Mayen nan Khamis karamin Tsaki taja kaawai Ya Sadam ta Fara Kira ya dauka bayan sun gaisa ya Fara bata Hakurin rashin Dawowarsa tace bakomai kana ya bama Anty Aneesa ta yi mata ban gajiya Tana Tambayan Munari tace Yanzu ta Dawo daga Rakata Daga haka suka yanke kiran bayan Ya Sadam din yayi ma Inteesar Alkawarin sunan nan zuwa.
Aneesa Tayi ma Sadam mganar Munari tace”Honey ni kuwa naso ka Dawo dazu kaga wani abun mamaki..?
Yana kai Lomar abinci bakinsa ya Dakata yana Fadin”Mamakin me..?
Gyara Zama Inteesae tayi Tana Fadin”Kawar Inteesar da suka zo Tare take min kama da karamar yarinyar nan ta Hoton nan da Daada ta nuna mana adukku..!
Kallomta yayi kur kafin yace”Kina Nufin Hoton iyalan Kawu Malami..?
Aneesa ta Daga mai kai sai taga yayi Dariya yana Fadin”Daga ganin..Hoto sai kiga yarinyar mutane kice itace..?Ai da itane da Inteesar din ta Fara sanin hakan..!
Aneesa tace”To in ba itabace kamar har ta baci Wlh..Saboda haka nace muyi Hoto bari ka ganta..!
Cikin Halin ko in kula yace”Yauwa muga Hoton..!
Ta Lalubo Hoton Munarin kenan zata mikamai Waleeda Dake jikinta ta kwabe hannunta Wayar ta Fadi kasa ta Watse Ran Aneesa ya baci ta Maketa Ya sadam ya fara fada yana Fadin”Saboda Wayar banza zaki Daki yarinya..!
Cikin Kufulawa tace”in ta Lalatamin fa..? Banza yayi da ita ya Dauketa yana Lallashi ita kuma Aneesa ta Duka Tana Tattara Wayarta bayan ta Hadata Tayi tayi ta ki kawowa sai Ranta ya baci ta Shige Dakinta ta Jefa Wayar Cikin Wardrope shikenan ganin Hoto bai samu ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button