
Tafiyar Mama ya tashi Ana gobe Zata tafi Taje gidansu Munari da kanta Inteesar ta Rakata ta gaida Anty Safiya wacce ke fama da kasala,da Amai kana ta gayama Abba Zataje Biki Zata bar Inteesar Wajensu Abba yace bakomai bama sai tazo ta Taambaya ba,Inteesar kamar ya take a wajensa,Munari da Inteesar sun fi kowa Murnan hakan,Washegari Tun Safe Sagir ya Raka Mama tasha tahau Motan Kaduna,Inteesar kuma sun Tafi makaranta sai da suka Dawo Munari ts Tayata Debo kayan da Zatayi amfani Dashi kafin Mama ta Dawo,Sagir daman baya Zaman gida yana Shago Abinci kuma Siya zai rika yi Shima Ranar asabar zai tafi kadunan.
Imran baisan Inteesar ta Dawo Gidansu ba sai da Sassafe ya Fito zai Tafi jogging ya ganta Tana goge Dining Abun ya bashi mamaki har tsayawa yayi yana Kallonta baki sake Data gaisheshi Abun sai ya kusa saka Inteesar Dariya ta Rufe bakinta ta Shige Kitchen da gudu Munari Dake Feran Dankali ta bita da kallo.
Daman saboda ta gansa tace ma Munari bari ita ta gyara Falon ta Goge,Ita kuma ta Soya Dankali da kwai Kada su makara Karfe 8:30am suke da Karatu,Anty Safiya kuma Lafiyan sai Hankali bata Girki a asibiti ance ta Huta sosai kafin ta fara aiki.
Kuma ta gansa Taji sanyi acikin Ranta ita kanta akwanakin nan ta rasa meke Damunta jinta da ganinta Imran ne in bata gansa ba ta rika Shiga Damuwa kenan sai ta gansa take jin Sanyi,Sabida ta gansa tazo gidan ta Wuni bata tafiya sai duhu yayi Saboda ya Rakata tasan bazai taba barinta tabi Hanya ita kadai ba Kamar ma Dakonta yake yi Data Fito zata gansa yana Binta abaya koda bazai ce mata komai ba har sai ta Shiga gida zai koma ya Lura batajin mgana ga Tsoro ga Taurin kai bayason yayi mgana ta sakamai kuka ya Lura ta Fiye shagwaba Shiyasa Ya gwammace ya Rika gadinta Kullum in tazo takai yammah agidansu.
Har ya Dawo Daga Jogging yana Mamakinta Yana Shigowa Haraban Gidan ya gansu Yusuf ya daukesu zuwa makaranta Sai da ya Shiga Gidan ne ya Shiga wajen Abba yana so ya Tambayeshi ammh ya kasa sai ya bar Abun aranshi.
Sai dai ya samu amsar Tambayarsa Wajen Sagir Tunda ya fadamai Gobe Zai tafi kaduna Daurin aure Mama ma tana chan Tun jiya Shiyasa Inteesar ta koma Gidanku maimakon ada da bayason wani ya Rabesu,sai yaji Salama da wani Natsuwar da bai taba jiba.
Washegari Asabar da kanshi ya Raka Sagir tasha akan Mashin dinsa ya Daukesa Sagir yamai Tayin zuwa yace bazai jeba bai bar wajen ba sai da Motarsu tatashi kana ya koma Gida.
Kamar yadda suka saba kwana Biyun nan Suna Falo ita da Munari suna Kallo suna Hiramsu Anty Safiya na Barayinta ita da Ya Yusuf Abba ne Kuma yanzu yana cikin Dakinsa In suka gansa sai su Natsu suna Raba ido Da ya shiga Daki sai su Fara Dariya.
Hakaman yake jin Dadin ganinta a kusa Dashi koda bazai mata mgana bane baya ma son Mama ta Dawo ace ta koma Gida,Ranar asabar da yammh Tasleem tazo ita da Mommy da Anty Saratu suka zo Duba Safiyar basu jima ba Mommy da Anty Sarati suka tafi suka bar Tasleem Datace nan zata Kwana sai Monday Zata koma Taga su Inteesar.
Suka Hade su uku suna ta Bidrinsu Inteesar ne ke jansu zaman Falo Saboda Taga Giftawan Imran Munari kuwa bata so saboda Imran bayasom Hayaniya tafi son su zauna Shashen Anty Safiya yafi susha Hiransu kala kala bamai Takuta musu.
Adakin Munari suka Kwama Dukkansu Harda Tasleem Dataki kwana Shashen Anty Safiya.
Washegari Lahadi suka zage suka gyara Gidan
Inteesar ta matsa ma Munari su Zauna afalo su kunna Kallo,bayan sun Karya Abba na Samam Dining shi da Ya Yusuf suna Cin Abinci suna Hira su su kuma suna saman kujerin falom Sun kunna Arewa24,lokacin ana Maimaicin kwana Cha”asin suna ta Hayaniya Munari da Tasleem nata bama Inteesar Labarin Film din Tunda ita ba wani Kallo take sosai ba Daman Saboda Taga Imran ne yasa ta Mtsa musu su Zauna.
Yana cikin Dakinsa Hayaniyarsu duk ta Cikamai kunni Tun yana Sharewa Har Ransa ya baci ya tashi ya Fito a Fusace Jikinsa ko Riga babu Daga shi sai 3Quater,kamar Walkiya suka gansa gaban Kayan kallon ya Zare Soket din gabadaya ya yar a kasa ai kafin ya juyo Munari tayi ta kanta Tasleem ma ta mara mata baya Inteesar ne ta Tsaya tana Raba ido Hararanta yayi kafin yace”Bar nan Wajen..!
Da sauri ta Mike tana Kokarin Hana kanta Dariya yana kallonta aransa yace”Shikenan ta gama Rainani.!
Abba suna gefe suna kallobsu Abba ya Sa baki ya Kirashi ya Juyo yana kallonsa Cikin Mirmishi yace”kai da idon sani da bako Duk Dayane awajen ka ko Imran..?
Dakuna Fuska yayi kafin yace”Abba Hayaniya suke min akaina..!
Yusuf yace”Ai ba Dakinka suka shiga ba Ishasshe..!
Bata rai yayi ko mgana bai kara ba Ya shige daki har yana Bango Kofa Yusuf yayi Dariya yana Fadin”Na tabo Yaron Abba..!
Mirmishi kadai Abba yayi bai kara mgana ba.
Su kuwa Shashen Anty Safiya suka koma suna Sauke Numfashi Munari Ba bakin mgana Inteesar na Dariya ta Daka mata Duka tana fadin yau daya Daketa kanta zata rama ta kusa jamata masifarsa Ita dai Dariya kawai takeyi Burinta ya Cika Tunda ta gansa,sai da yanayin Data gansa ayau din ba Riga Gabadaya yasa ta jin wani iri Imran yana da Cikar Zatin da kowacce Lafiyayyiyar mace in ta gansa ahaka Taji wani iri hakan ne ya Faru da Inteesar wacce ta Wuni Tunaninsa bai bace mata ba.
Shakira
3/22/22, 23:07 – Ummi Tandama😇: GIDAN MU..!
(Our House)
Book 1
Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janaftyâ¤ï¸
       🅿�29
Har garin Allah ya waye Inteesar bata kara saka Imran a idonta ba duk da kuwa yadda taso ta kara ganinsa,Gashi yau din ta kama Monday ne suna Class da safe shiyasa suka Shirya da wuri Ya yusuf ya daukesu yakaisu kafin ya wuce wajen aiki basu kuma dawo ba sai yammah Tun suna makaranta Inteesar sukayi Mgana da Umma ta fadamata Su Mama sun kamo Hanya tun dazu shiyasa da suka dawo nan ta Tsaya tunda sun dawo gama Sagir nan a kofar Shagonsa shida Imran suna mgana.
Sun gaisheshi Sagir ya amsa cikin Fara”a yana Tambayansu karatu sukace Alhamdulillah,Inteesar na Tambayansa ya Kaduna yana Fadamata Hargidansu yaje Imran na Gefe ya Kauda kansa yau din ko sau Daya bai kalleta ba bayaso Zuciyarsa ta Saba da kallonta alhalin yau zata koma Wajen Mama,lokacin da Sagir ya Kirasa ya gayamai sun dawo bai ji dadi ba ko baya ganinta yana Samun Natsuwar Sanin Tabbas Numfashinta yana Kusa da nashi,yanzu din ma ita yake son gani yasa da Sagir ya kirasa yace sun dawo ya Fito suka Hadu Tunda yaga Munari bata dawo ba ya tabatar da suna makaranta in ma kuma sun dawo suna gidan su Sagir ya Tabbatar ma kansa zai ganta..
Har suka wuce cikin gida kansa na kallon wani waje,Duk da Satan kallonsa da Inteesar din Tayi tayi bata Samu Nasara Hada ido dashi ba.
Sagir na lura dasu acikin Ransa ya Dade yana mamakin wani abu Shi dai bazai ce soyayya suke yi aboye ba..?sai dai ya Fara Lura da wani abu ko Rakotan da Imran yake yi Sagir na ganinsu bai dai taba ma Imran din mgana bane sai shi kadai yayi ta mamaki yasan waye Imran ya Tabbata Baya abunda Ransa bai so ba Bamai sakashi yayi abu Dole duk abunda yayi ko ya aikata yayi Niyya ne kuma Ra”ayinsa ne Sai dai in ya Tuna Kaifin Imran sai yaga da kamar Wuya ace Soyayya suke shi da Inteesar sai dai yabar abun acikin Ranshi ya zura musu ido yana Bin Duka Takunsu itama ya Lura da kallon Data dinga bin Imram din dashi kallo ne na samun Salama da sukuni ya shiga Rudani shiyasa ya kasa Dora komai a inda ya dace ya bar Lokaci ya bayyana komai.