GIDANMUNOVELS

GIDANMU 1 & 2 COMPLETE

GIDANMU HAUSA 1 & 2 COMPLETE

Sa’id ina kyautata Zaton Farincikin Daada zai dawo..Gamu aharaban gidan naga ma karin wani Shedan na Mutum daya sai dai ba Yusuf bane na manta sunansa..kada ka kirani sai na kiraka.

Daga haka ya Turamai kafin ya Dago Imran ya koma ya Cigaba da abunda yake yi.
Ganin haka yasa ya Nufi cikin gidan yana Waigen Imran wanda ke Hangensa ta Jikin Mashin dinsa Haka kurum jikinsa ya basa wannan Dan”uwane duk yadda akayi.
Sadam na shigewa Motar Yusuf na Shigowa Haraban gidan shima yayi matukar mamakin ganin bakuwar Mota Imran dake Tsaye ya rasa abun cewa da Yusuf ya Tambayesa Kallonsa yayi bai cemai komai ba bai Damu ba ya Dauki ledan Yalon daya siyoma Safiya zuwa Cikin Gida ya bar Imran na Tunanin kila yau komai zai Zama Tarihi.
Sadam na shiga Falon ya iske su Aneesa da Inteesar zaune a Bisa kujerun falon da su waleed.
Kallon Aneesa yayi kafin yayi mgna Aneesa ta Rigasa da cewa”Munari taje kiran Abbanta mu gaisa..!
Jin haka yasa ya ja ya Tsaya yama kasa Zama Daidai Lokacin da Yusuf ya sawo kansa Falon da Sallama abakinsa.
Sadam na Facing din kofar Shigowa ya Zurama Yusuf ido shima yana Shigowa Idanuwansa ya fada kansa.
Atare suka Zaro ido Lokaci Daya kowa na nuna kowa cikin mamaki da al”ajabi suka ambaci sunan juna..!
“Yusuf…!
“Sadamm..!
Suka Fada atare adaidai Lokacin Munari ta Fito Daga dakin Data shiga Bayanta Abba ne yana gyara Hulan kansa jin Munari tacemai yan”uwan Inteesar suka zo su gaisheshi.
Sai dai ya Dakata da gyaran Hulan nashi Sanda Idanuwan Sadam suka kusa Fadowa akansa Saboda mamaki Aneesa ma ta Mike Tana kama baki Inteesar ma haka Kanta ya Kulle ita da Munari suna kallon kallon.
Cikin Rawan baki Sadam ke nuna Abba yana Fadin”K…ka..kawuu..!
Yafada cikin Rawan Murya dana baki Abba yayi jagale yana Bin Sadam da kallo Hawaye sun cikamai kwarmin ido kamar yadda na Yusuf suka cikamai Cikin wani yanayi Yusuf yace”Abba ka ganeshi..? Sadam ne Dan Wajen Inna Maimunatu..!
Yafadi haka Daidai a kunnin Imran Daya bayyana afalon bayan kasa Natsuwan da yayi a Haraban gidan.

Janafty
3/22/22, 23:07 – Ummi Tandama😇: GIDAN MU..!
(Our House)
Book1

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

Bazan Rufe wannan Shafin Batare dana ambaceki ba,Godiya ta tayi kad’an na Furta miki Sisina Aisha alto da Hidimar da kikeyi dani da Rubutuna kin yi jimarin Posting din wannan Littafin Daga farko har zuwa yau din nan da muka kawo karshen littafi na Farko Nagode kwarai Allah ya saka miki da gidan Aljannah Firdausi Ameen

       🅿�30

Abba da jikinsa ke rawa idanuwansa sun cika da kwallah suna shirin zubowa Lokaci Daya ya fara takowa Tsakiyar falon duka Idanuwansa suna Kafe kan Sadam kamar wanda ya warke makanta..
Cikin wata irin Murya kewa da Farinciki da kuka Abba ya kalli Sadam yana Fadin”Sadam…!
Ya kira sunansa cikin wani yanayi Sadam da Hawayensa suka gangaro saman Fuskarsa yace”Na”am kawu malami..!
Yafada yana wani kada kai Abba Hannayensa ya Budemai yana Fadin”Taho nan Sadam Taho naji Dumin ka..Taho na ji dumin wani Daga Cikin Ahalina yau..!
Da gudu kamar karamin yaro ya Karisa ga Abba suka Rumgume juna Lokaci Daya yana Fadin”Kawu ina ka shiga muna ta neman ka..? Kowa ya shiga damuwa saboda kai..Daada kowa yaushe kuka take yi yau lafiya gobe babu duk saboda Rashinka..!
Abba yaji Hawayen dayake ta Tarewa sun zobomai yayi Saurin Sharewa Lokaci Daya ya dago Sadam yana Fadin”Ban je ko”ina ba ina nan a kasata..Nayi nesa da gida ne saboda Wasu Dalilai ko bamu hadu ba daman Lokacin da Zan koma cikin Dangina yayi ba saboda kowa ba ko Saboda Daada da nike kwana ina tashi da ita..!
Kada kai Sadam yayi Lokaci Daya yana Dauke kwallarsa Dagowa yayi suka Hada ido da Yusuf dayake sharan Kwallah Wajensa ya nufa yana Fadin”Dan”uwa Yusuf..!
Lokaci Daya suna Rumgume juna Inran na gefe yana Binsu da kallo Fuskarsa bata bayyana Wani Hali yakeciki ba na Farinciki ne ko na bakinciki.
Inteesar da Munari gabadaya sun Shiga Rudani sai bin kowa da kallo sukeyi ita dai Munari ta Fahimci Yau boye boyensu ya kare ne Dangin sun san inda suke ita kuma Inteesar ta Shiga Rudanin kada dai ace Munari yar”uwanta ce..?Abba shine Baffa Malamin da su Daddy ke wahalan nema Daada na Rashin Lafiya Saboda shi ammh take zaune dasu tsawon Lokaci bata taba Sani ba.
Aneesa na gefe farinciki ya cikata Harta su Waleed sun natsu ganin yadda Abbansu ke kuka yana Rumgume da Yusuf,sun dau tsawon Lokaci kafin su saki juna Sadam ya Bubbuga kafadarsa yana Fadin”Shekaru uku ba kwana bane..Duk ka Sauya Yusuf..!
Yusuf na Dariya yace”Kaima haka duk ka Sauya..!
Dariya suka saka gabadayansu Abba na Gefe yana kallonsu Lokaci Daya yana karama Allah godiya daya sa Daada bata bar gidan Duniya ba Tana da Rayuwarta zai koma mata..
Sadam ne ya juya yana kallon Imran Lokaci Daya ya Karisa gabansa yana Fadin”Imran ko .?
Yusuf ne ya bashi amsa ammh Imran Sai ya wani basar Kallon ma wani barayin yayi kamar ba dashi yake ba ganin haka yasa sadam bai Rumgumesa ba illah ya Dafa kafadarsa yana Fadin”Dan”uwa kai bamu san ka sosai ba..Ko a da chan Yusuf ya fika son zumunci .!
Kamar yana mgana da gunki haka Imran yayi mai Abba ya Kalleshi yana Fadin”Imran sadam ne dan Wajen Goggon ku Maimunatu ta Bauchi..!
Dakyar ya iya bude baki yace”Na ganshi..!.
Daga haka ya dauke kansa Sama Sadam bai damu ba ya jinjina kai aransa yana ayyana abubuwa Dadama kan Imran din .
Inteesar ne data gama Shiga Rudani ta Kalli ya Sadam Tana Fadin”Ya sadam…Abba..!.
Tafada Tana kallonsu dukkansu da Sauri Sadam ya Karisa gabanta ya Riko Hannunta yana Fadin”Inteesar baki gane su ba ko..? Baki ga Hoton da Daada tace a nuna ma kowa lokacin da mukaje dukku ba..?
Inteesar cikin kosawa tace”Bangani ba meya faru..?kamin bayani ka sani a duhu naji kana cema Abba Kawu..Kawu malami kardai kacemin Baffa Malami ne..!
Ta karishe fada cikin wani yanayi gabadaya sai kallo ya koma kansu harda Imran daya natsu yana so ya Fahimci wani Abu..
Abba ya Kallesu cikin mamaki yana fadin”Sadam..!
Lokaci daya yana nuna Inteesar da Hannunsa,Sadam ya kamo Inteesar zuwa gaban Abba yana fadin”Kawu baku gane juna ba..Abba Inteesar itama yarka ce..!
Cikin mamaki yace”Yata kuma..?
Imran ya waro ido yana so ya Fassara mganar hakama Yusuf Munari kuwa Hawaye take yi na Farinciki koda ba”a Fadi komai ba ita ta san kaunar dake Tsakaninta da Inteesar ta jini ce.
Sadam ya dauki hannun Inteesar ya saka cikin na Abba yana Fadin”Kawu Inteesar ce Diyar Kawu Mustpaha na kaduna..!
Abba yaji wani sanyi jiki ya kamashi Lokaci daya da Sauri ya damke hannunta yana Fadin”karamar yarinyarsa..Wacce taci sunan Daada..!
Sadam ya dagamai kai yana fadin”Itace kawu..Inteesar ce kana Tare da jininka ammh baka sani ba..!
Abba ya Ji hawayensa suna Kokarin kara Zubowa ya Rike Duka Hannuwan Inteesar yana fadin”bamu rike zumunci ba sosai ba…Ace yau na hadu da Diyar Mustpaha na wani Lokaci Tana Tare damu ban ganeta ba..Sai dai Wlh har ga Allah Tun ganin Farko da nayi mata naji wani abu acikin Raina ban taba mata kallon bare ba Daya na Dauketa ita da Munari Ashe Ashe itama Diyata ce..!
Yafada cikin Raunin Murya da Sauri Inteesar da itama ta fara Hawaye tace”Baffa….!
Tafada kafin ta fada jikin Abba tana fadin”Nima ina jin haka duk sadda na kanga sai naga kamar Daddy na..Yanayin mganarku da komai iri Dayace..In nazo gidan nan ji nake kamar ina Gidanmu in ina tare da Munari kamar ina Tare da yar”uwata uwa daya uba Daya..Ashe Gidanmu ne ku din Jinina ne Wayyo Dadi Abba..!
Take Fada tana kuka Shima Abba Hawayen yake yi Shi da Sadam da Yusuf Da Aneesa da Kukan Farinciki ya Kamasu Lokaci Daya,Imran ne kadai ke Tsaye idanuwansa ba alamun Fitar kwallah sai dai yadda abubuwan suka Juye ne suka sakashi Tsintar kansa a wani Hali Tabbas Jini yafi Ruwa kauri,ko shi yasa Yafi damu da Inteesar fiye da kowa..? Ashe ita din jininsa ce..!
Anty Safiya Dake gefe tana sharan kwallah Tun dazu ta fito ba wanda ya Lura da ita Hayaniya taji ta Fito tana Kwance afalo acikin Shashenta sai ta iske Abun Farincikin daya samu wannan Gidan ayau na cikon Abu Dayan da ya Rage gidan ya cika ya zama Gida irin kowani gida.
Yusuf ne ya hangota da sauri ya isa gareta ya Rumgomta yana fadin”Noor Boye boye ya kare..Danginmu sun same mu..!.
Tana rike dashi Tana Fadin”Alhamdulillah..Duka Burikana sun cika my dear..!.
Take fada cikin Farinciki.
Inteesar na kuka ta dago kanta tana Kallon Munari cikin kuka tace”Dilla ke baki zo muyi kukan tare ba. ?
Tafada Lokaci Daya Hawaye da Dariya da sauri Munari ta wani taho da Sauri ta Fada Jikin Abba dukkansu ya Hada ya Rumgume sai ga Hawayen Farinciki sharr.
Sadam Wayarsa ya zaro Tun dazu Sa”id ke kiransa bai dauka ba cikin Farinciki ya kirasa yana kiransa Ringing daya ya daga da Sauri yana Fadin”Sadam ya ake ciki..? An dace kuwa. !?
Sadam na kallon Abba yana fadin”Sa”id an dace gani ga Kawu Malami..Alhamdulillah gani cikin gidansu Zagaye da iyalansa..!
Sa”id ya mike da Sauri yana Fadin”Finally Alhamdulillah..!
Bai ma jira cewar Sadam ba ya Katse kiran Murta ta sa ya rasa nayi,Komawa yayi ya zauna yana Hamdala afili kafin kuma ya Fara Tattara kayansa yau komai Dare sai ya Shiga kano Sadam ya kara Kira yana Dauka yacemai kada ya bar gidan nan yanzu zai tashi daga Office yana zuwa Gida zai taho kano ayau din nan bai iya cemai kada ya Taho ba domin ya kamata yazo din.
Abba kuma yana Rike dasu Inteesar Hawayensa yaki tsayawa yana Kaicon wannan Zumuncin na wannan Zamanin da har yakai mu ga Lalacewar da jininka na tare dakai ammh baka sani ba.
Waje aka samu aka zazzauna Saman kujerun falon Abba ya fara Tambayan Sadam sauran yan”uwa yana Fadamai kowa Lafiya Imran na gefe bai Zauna ba ya Harde Hannayensa saman Kirjinsa yana jin duk abunda ake fada sai dai kalma Daya Tun bayan na Dazu bai kara Furtawa ba bama wanda ya Damu dashi sanin Hali Sadam ne ke yawan kallonsa Lokaci bayan Lokaci yana mamakin shi wannan Haka yake.?
Abba ne ya kalli Aneesa yana Fadin”Wannan mai Dakin ka ce..?
Sadam yace”Eh Abba..ga yara na nan Waleed da waleeda. !
Abba ya mikama su hannu yana Fadin”Ku taho nan wajen kakan ku da baku sansh ba..!
Basu da bakunta suka karisa Wajensa ya Daukesu asaman jikinsa.
Munari da Inteesar na gefe sun rike hannun juna baki yaki Rufuwa Safiya na Cikin su da Yusuf cikin Farincikin da bazasu misalta ba,Shiyasa tunda ya Fara ganin Inteesar wlh jininsa ya bashi Intadin kamar jininsu ce,bai taba mata Wani kallo ba ashe jini jini ba na waaasa ba.
Abba na kallon Waleed yace”Nasan sanda aka Haifi babban..Lokacin Maimunatu ta Kirani take fadamin Matarka ta Haihu wacce muka je cikin garin Azare muka karbo Auranta..!
Sadam na dariyan Farinciki yace”Anyi haka kawu tabbas baka manta ba..!
Abba na Mirmishi jin dadi yace”Ina Yayanka Sa”id da sauran kannen ku mata..? Kayya zumunci sai a hankali duk ban sansu ba..!
Sadam yace”Sa”id na Garin Dutse Abba chan yake aiki yana zaune da matarsa da ya”yansu uku..Karamar kanwarmu Hafsah tana Wajensa saboda Tana karatu nan Federal Univestiy dutse. !
Abba ya jinjina kai yana Fadin”Ku kiramin yan”uwana inaso na Hada dasu yau..Gobe ina so naje ni da duka Iyalaina naga Daada na Roketa gafara..!.
Imran na gefe ya kalli Abba irin Kallon nan nasan za”azo wajen bai dai ce komai ba Sadam ne yace”Kawu saboda Murna ban ma kira kowa ba Sa”id ne kadai shima yace yana Tafe yau din nan bari na fara Kiran Mommy na Fadamata..!
Inteesar dake gefe tace””Ni kuma bari na Kira Daddy na fadamai..!.
Dukkansu atare suka Kira wayar Sadam na Kira Mommy ta Daga Cikin Murna tana Fadin”Sadam yanzu nake shirin kiranka gama wayata kenan da Dan”uwanka yana gayamin wani Labari mai dadi kaga Yaya Malami da iyalansa..?
Tafada cikin wani Shauki Saukewa wayar yayi daga kunnensa ya saka Speaker yana Fadin”Wlh Mommy gani ga kawu ga yusuf ga Imran ga Inteesar Mommy ga Matar yusuf din dan wajen kawu malamin har yayi Aure .!
Inna maimunatu tana kwallah tace”Hadani da dan”uwana naji muryansa..!Sadam bai yi gaddama ba ya mikama Abba wayar ya Karba yana Fadin”Maimunatu Autan Daada..!
Tana jin muryansa sai kuka tana Fadin”Ya ya Malami ashe kana da Ranka..? Ka samu lafiya Allah abun godiya..!
Cikin wani yanayi yace mata”Na warke Maimunatu..Na samu Lafiya da ikon Allah..!.
Inna maimunatu tace”Allah mun gode maka da kakaddara Haduwa Tsakanin daada da Ya malami..Nima bazan iya zama ba bari Alhaji ya shigo na gayamai yau din zan taho kano..!
Da sauri Abba yace”A”a Maimunatu kada ma ki fara Dare yayi..Ki bari insha Allahu gobe bazan kara kwana agarin nan ba sai a dukku gaban Daadarmu sai mu hadu achan.!
Inna Maimunatu na sharan kwallah Tace”Shikenan Ya malami daman Sa”id yace min ya kira Kawunshi kabiru na Abuja yafadamai shima yace zai kamo Hanya in ya Samu jirgi shikenan in kuma bai samu ba zai yi Tafiyar Mota..!
Abba na Dauke Hawayensa bai so su kara zuba yace”Barrister..Yaya kabiru ashe baya Fushi dani..! Da Abba ya Fadi haka kamar Imran ya Mutu haka yake ji,baima san sadda Abba ya gama Wayar ba sai da ya tsinci Muryan Inteesar tana mgana da Daddynta.
Alhaji Mustpha shigowarsa Gida kenan Shida Basheer Inteesar ta Kirashi Kokari ma yake ya shiga gida yayi alwala ya samu Sallar mangariba Domin yaji ana ta Kira Basheer kuma ya Biyosa gida ne saboda akwai Lissafin da zasu yi yaji kiran Inteesar.
Suma shiga Falon ya Daga Kiran irin yadda yaji yanayinta cikin Murna yasa yace”Inteen Daddynta me ya Faru ne najiki cikin Annshuwa..?
Inteesar na kallon Abba tace”Daddy Albishirinka..!
Yana zama kan Daya daga cikin kujerun falon yana Fadin”komai Intee na take so shine goron albishir dinta..!
Yafada Daidai Lokacin da Umma ta iso Falon dauke da Ruwa da Kofuna Basheer na gefe zaune yana Latsa waya a Hannunsa..
Inteesar tace”Daddy gani ga..Baffa Malami gani kusa dashi..!
Daddy yaji mganar asama adaidai Lokacin kuma Ana ta Kiransa a waya Call Waiting,.
Cikin Dan daburcewa yace”Wane kikace Intee Daddy..!?
Da sauri ta kara Fadin”Baffa malami Daddy gashi ma kuyi mgana..!
Tafada tana mikama Abba wanda ya karbi Wayar yasa a kunni lokaci Daya yana Fadin”Mustapha Baban Basheer Mijin Salaha..!
Kamar a mafarki haka yaji muryansa da Sauri ya mike jikinsa ba inda baya rawa,har yana Ture Umma Dake duke gabansa Tana Tsiyayamai ruwa.
Suka Mike atare suna binsa da kallon mamaki.
Cikin In ina yace”Yaya Abbakar..? Kai ne da gaske..!
Abba na Mirmishin jin dadi yace”Nine Mustapha..Abun kunya Inteesar na tare damu na tsawon Lokaci ban gane yata bace..! ?
Yafada abun na karamai ciwo Daddy daya yi mutuwar Tsaye yace cikin son Tabbatarwa
“kai..kai ne Baban Munari kawarta..!?
Abba yace”Ni baban Mai sunan Daada ne..sai dai in kaine Baban Mai sunan Autan Daada..!
Sai ga Daddy na Hawayen Farinciki cikin murna yake kallonsu Umma yana Fadin”Wlh shine Salaha Basheer..Babanka ne ya Malami ne fa muke mgana dashi..Ya malami fa Alhamdulillah Alhamdullilah..!
Su Abba suna ji daga alamu ma ya manta yana waya ne ya Gama Rudewa Inteesar ta karbi wayarta ta kashe nan take ta Kira Mama tace ita da Sagir suzo gidansu Munari hankalin Mama ya tashi ta Zata wani abu ya samu Abba Sagir na Kofar gida Yana kokarin Daura alwala ya shiga Sallah Tunda an kira Mama ta Fito da Hijabi a Rude tana Fadamai Halin da ake ciki Sallar da bai shiga ba kenan ya Rufa mata baya zuwa gidansu Imran.
Su Umma mamaki ya cikasu da Daddy ke maida Zencen ya kasa Zama Umma tana ta maimaita Allah gagara Misali Daman Munari yar”uwan Inteesar ce..? Koda tace ramar data fara ganin Hotonsu tare sai da taga kamarsu Data fada kuma ba wanda yabi ta kanta.
Suna cikin haka Baffa Kabiru ya kira Daddy ashe shi yake ta Kiransa yana waya da Inteesar yana Dagawa Cikin Farinciki ya gayamai labari mai Dadi sai yaji yana Fadamai Cikin Farinciki Daddy yace”Wlh nima har mgana ma munyi da ya malami Barrister…Inteesar ta Hadani dashi Allah sarki Rayuwa..!
Baffa Kabiru Daga chan bangaran yace”Yanzu haka ina hanyane ban sanu jirgi ba Tafiyar mota ce ni da Ma”u ce,kaima kayi kokari ka Tashi yau din bana so mu kuskure ya sake bace mana kuma ka da ka kira Daada so nake mu bata mamaki har Bintalo na gayamawa yanzu muka gama mgana da ita..chan zamu kwana Gobe in Allah ya kaimu sai mu hadu da kowa da kowa a Dukku..!
Daddy yace”Yanzu kuwa zamu kamo Hanya..!
Daga haka suka yanke kiran Daddy na Kallon Umma yana Fadin”Salaha Shirya..Ko kuma ke Salaha ki bari gobe Direba ya taho daku keda Hauwa da yara mu a hadu a dukku..Kai Bashir kira matarka ka Fadamata bari na shiga ciki na fito yanzu zamu dauki Hanyat kano ba sai gobe ba..!
Baima Tsaya Sauraransu ba ya Shige ciki kamar zai kifa saboda Sauri.
Umma ta Kalli Basheer tana Fadin”Kai duk tare zamu tafi..Nima bazan iya Zama sai gobe ba kira matarka mu biya mu daukesu ayi tafiyar gabadaya..!
Basheer yace”Umma anya Zata iya..? Kunsan yanayinta ko zamu Kyaleta kawai mu muje..!
Umma ta kada kai tana Fadin”Kuma fa hakame..Shikenan kirata ka Fadamata sai muje din..!
Daga haka ta bi bayan Daddy shi kuma ya Dauko wayarsa Domin ya Kira Hauwa ya fadamata Halin da ake ciki.
Mami Asma”u ta kalli Baffa Kabiru bayan ya gama mgana da Daddy Tana Fadin”Yanzu daman duk wannan uban Wahalan neman da kuke ma wannan bawan Allah yana kano zaune abunshi bbu abunda ya Dameshi..!.
Take fada Lokaci Daya tana kara gyara zaman gilashin dake idonta suna Kishingide a bayan Motarsu Kirar prado Direba na gaba yana jansu.
Cikin wani yanayi ya kalleta yana Fadin”Bari kawai. Ni kaina naji abun haka..Ace yana nan kusa ammh ya kasa neman kowa..?
Kuma daga alamu he is Fine now..!
Mami Asma”u ta tabe baki Tana Fadin”This is Selfish yana chan yana Jin dadinsa ya manta da ku..Alhalin kuna nan baku huta ba wajen nemansa..!
Baffa Kabiru yace”Saboda Daada nake komai kuma kinga all the blemming akaina Daada ta maidashi so yanzu zan yi amfani da wannan damar na Daukesa na maida mata..!
Da sauri tace”Shikenan kuwa..Ammh sam bai kyauta muku ba..!
Shidai bai kara ce mata ba sai Dannan Wayarsa yake yi Khamis ya Tura ma Sako ya kira Wayarsa bai Dauka ba..
Umaima da Sajida suna gida suka barsu Umaima ce ma taso zuwa Uwar ta Hana Sajida kuma bata manuna Concern dinta ba she is telling cewa Test zasu fara karatu take bata da Lokaci.
Mami Asma”u ita da kanta tayi Ra”ayin zuwa saboda tana so taje taga komai kuma Komai za”ayi so take ayi shi agabanta bayan ikonta da izzanta na akwaita da son gulma da kure Mutane.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button