GIDANMUNOVELS

GIDANMU 1 & 2 COMPLETE

GIDANMU HAUSA 1 & 2 COMPLETE

Sun tsaya a Gombe sunyi Sallar azahar wajen karfe Biyu na rana kana suka Dauki Hanyar Dukku ba Dadewa suka iso Cikin Haraban gidansu na Dukku Abba na kallon Haraban gidan yana ganin komai kamar baya babu abunda ya Sauya sai ma sauye Sauye da aka samu,Idanuwansa suka ciko da kwallah na kewar Gida da Ahalinsa gabadaya da Daada dayake matukar jin kunyar Hada ido da ita.
Sai da kowa ya fito daga Mota kana Imu ya fito yana cin mgani Sagir sai bin Gidan da kallo yake yi yana Auna wasu abubuwa acikin ransa,Da Inteesar suka Hada ido suna Shirin Shiga Cikin gidan gira ta Dagamai Kafin ta dagamai hannu kau ya kauda kai kamar bai ganta ba,nan kuwa sun yi ma juna sako ta waya Inteesar sai mai Tabara take wai ta gaji da Zaman Mota shi kuma yace ta ce a sauketa in ta gama Hutawa sai ta hayo wata Motar ta samesu achan tunda bayan Shagwaba da Rigima ita din Raguwa ce sai Dariya take dayacemata haka.
Daddy ya Riko Hannun Abba gaba gaba zuwa Babban Falon Daada.
Wanda tunda sukaji isowarsu suka Firfito falo Daada da kafarta ta Fito Tarban Abba su Inteesar suka Fara shigowa sai su Aneesa da su Umma Mazan suna Baya ya”yan Inna Mainunatu su zainab natayi musu maraba su kuma suna ta Neman inda zasu ga Dan”uwansu,sai gashi Sun shigo shi da Daddy Baffa Kabiru na Binsu ta baya,Su Basheer na takemai baya Imu da Sagir ne abaya shi yana Tafiyama kamar bazai taka kasa ba.
Inna Maimunatu ce ta fara isa wajen Abba ta Rikeshi da Murna tana kwallah ita da Inna Bintalo,Daada na Bayansu Baba Asabe na Riketa Cikin Mika Hannu take fadin”Ina Malami..Taho nan naji Duminka na Tabbatar da yau Allah ya amshi addu”ata..!
Tafada cikin murya Tsufa Dakyar ya saki Hannunyensu inna Bintalo ya Nufi Daada cikin karayan zuciya,Hannayenta ya Riko yana Fadin”Daada…Daada..ki yafemi…!
Sai Hawaye Daada ta Rumgumesa tana Shafa bayansa Lokaci Daya Tana Fadin”Har Abada banta rike ka acikin Raina ba Malami..Addu”q da Fatan alheri ne tsakanina dakai naji dadi nagodema Allah dana ganka ka dawo Cikin Koshin lafiyarka Abubakar..!
Daada ta fada Cikon muryan kuka Duka suna Tsaye cikin Tsasayawa da Fuskar farinciki.
Ta dagosa Tana kallonsa kafin ta Shafa kanshi Tana Fadin”Allah na gode maka..Zan hada kan iyalaina kafin nabar gidan Duniya..Ina yaran nan Yusuf da Maimunatu..!
Abba ya juya yana Kiran Yusuf ya Taho da Sauri Munari ma haka Abba yakira Safiya itama ta kariso zuwa gaban Daada.
Daada na Hawaye ta Rike yusuf Tana Fadin”Yanzu wannan Yusufa ne..?
Kamkame hannunta yayi yana Fadin”Nine Daada..!
Idonsa ya ciko da Hawaye Ta dafa kansa Tana fadin”Masha Allah naji Dadin ganinku cikin Koshin lafiya..!
Tafada kafin ta maida Dubanta kan Munari dake Hawaye Daada ta Dafa kanta Tana fadin”Mai sunan Auta ta zama Budurwa itama Maimunatu kin ganeni..? Nice karki Daada..!
Tafada cikin karaya da tsufa jin haka yasa Munari ta Rumgumeta Tana Fadin”Eh na ganeki mana Daada..Daadam Dukku..Daadan Anni..!
Jin haka yasa kukan Daada ya Karu ta Rike Maimunatu tana fadin”Allah ya jikan Zuwaira da gafara..Allah ya jikansu ita da ya”yanta da suka rigamu gidan gaskiya..!
Gabadaya aka amsa da Ameem jikin kowa a sanyaye.
Daada ta dago da Munari daga jikinta Tana fadin”Ina yar tselen uwar nan Maryama da akace kun hadu Tuntuni baku gane juna ba..?
Munari na Dariya ganin Inteesar ta Hade rai tana fadin”Kai Daada bama kiji Dadi ba sanadina kin hadu da Baffa ba..!
Daada na Dariya tace”Naji dadi kwarai sai dai abu dayane bai min dadi ba..Yadda kika hadu da yan”uwanki baki sani ba wannan Dalilin ya kara Zaburar dani gyara wanu Gibi dna barsa a Bude insha Allahu..!
Baffa Kabiru ne yace kowa ya zauna Kada Daada ta gaji da Tsayuwa kowa ya samu waje ya zauna,Munari ta makale kusa da Daada Abba kasa ya zauna saman Cafet kusa da kafufuwan Daada shi da Yusuf.
Daada Mirmishi yaki barin Fuskarta sai Hamdala take acikin Ranta haka Yusuf da Munari bakinsu yaki Rufuwa Safiya sai waige waige takeyi Tana kallon kowa aranta Tna fadin ina Abbu yazo yaga Asali da kyakyawan Ahalin irin ahalin su Yusuf wadanda suka fisu komai na Rayuwa.
Daada ce ta ganta bata santa ba ta Kalli Abba Tana fadin”Malami wacece wannan..! Badai aure ka kara ba bamu sani ba..?
Mirmishi yayi Safiya sai taji kunya ta Sadda kanta Abba yakalli Daada yana Fadin”Yaushe na Warken ne Daada da zan kara aure..? Matar Yusuf ce wattani Baya ya aureta..!
Daada ta washe baki Tana fadin”Masha Allah taho nan Yata bana Jikar dake ni..!
Safiya ta Rarrafa wajen Daada ta Shafa kanta tana tasaka albarka.
Daada ta fara Wurga wurga ido tana neman wanda take son gani Sai dai bata gansa ba yana ta bayanta Shi da Sagir suna Tsaye kamar wasu sojoji sagir na son zama Imran saboda Mugunta ya hanashi.
Cikin dan Rage fara”a Daada tace”Malami ina cikon Dayan..? Ina jikana Imrana..!
Abba ya dago shima yana Wurga Idanuwansa cikin Falon hakama kowa afalon ke wurgawa sai gashi an Tsintosa chan baya kamar wani bare Baba Asabe ne Dake gefe tace”Daada gashi nan a bayanki..!
Duk da bata wani sanshi ba ammh yanayinsa yasa tasanshine Imran din ballatana ai tana jin Labarinsa Wajen Daada.
Abba ya kalli Baba Asabe yana Fadin”Baba Asabe ya bayan rabuwa..?
Baba Asabe na Dariya tace”Sai alherin Malamin Daada Tunda gaka ka dawo Ciwon Daada ya Kare..!
Yana Mirmishi yace”Da yardan Allah.
!Daada kuwa Juyowa tayi Tana fadin”Ina imranan yake ne..?ko nima baya son ganin nawa ne kamar yadda yace baya son ganin Baffaninsa..!
Kowa sai ya fara mamakin ina Daada ta samu labarin abunda ya faru a Kano Mami Asma”u ce ta labartama Inna Bintalo yau da safe data Kirata ita kuma Tana zuwa ta Saukema Daada da ya”yanta.
Abba ya kalli Imran dayake Tsaye ko Motsi yana Fadin”Kai baka ji Daada na mgana bane..? taho mana..!
Ba yadda Imran ya iya Dole ya Jawo Hannun Sagir yana Tirjewa yana wani balle mai Harara Dole ya Biyosa suka Zagayo zuwa gaban Daada a Dofane Imran ya Durkusa kusa da Abba Sagir dai zama yayi domin Tsakani ga Allah ya gaji.
Kansa na kasa yake gaida Daada Mirmishi tayi kafin tace”Bazan amsa wannan gaisuwan ba Imrana..Matso kusa na jika kusa dani..!
Bayadda ya iya Abba ya mtsamai ya Karisa Kusa da Daada ya Durkusa kasan na kasa ta shafa kanshi Tana Fadin”Imrana..Har yau baka Sauya ba kana nan a yadda na sanka ko..!
Imran ya Dago yana kallon Daada Kafin yace”Asan ka da Hallayarka Shine Cikakken Mutum Tsohuwa Daada..!
Daada ta Murmusa Tana Fadin”ina nan ina ta ciwon rashin sanin inda kuke..Kai kuma Ahakan har kana cewa Babanka bazai zo inda nake ba ko Imrana..?
Kai Tsaye ya rike Hannunta Guda Daya yana fadin”Ban isa na Hana Abba zuwa ganinki ba Daada..Ban kai wannan mtsayin da zan raba Uwa da Danta ba ai nasan Radadin rashin Uwa Daada..Kuma ko ina ganin Laifin kowa bana ganin naki Daada Lokaci bayan Lokaci ina Tunaki har nayi miki addu”a acikin Raina..!
Daada taji Dadi ta Washe baki Tana fadin”Allah yayi muku albarka Naji Dadin ganinku haka..Kun kula da Mahaifinku da Kanwarku Allah ya saka albarka..!
Gabadaya aka amsa da Ameen Sagir ya gaisheta ta amsa cikin rashin Sanin Abba ne yayi mata bayani ta jinjina kai Tana fadin”Oh yaron wajen Amina kenan Yayar Salaha dake kano wanda Maryama ke wajenta ko..!
Abba yace mata Eh ai abokin Imran ne Daada tace”Masha Allah sannunku..Allah yayi muku albarka ina Maman naka take..? Kansa na kasa yace tana gaisheta tace tana amsawa..
Baffa Kabiru ya Duba agogon Azurfan Dake hannunsa yana Fadin”An kusa Kiran Sallar la”asar mu bari muyi salla sai muci abinci sai mu zauna ko ya kika gani Daada..?
Daada tace”bazamu zauna batare da kowa ya Hallara anan wajen ba..!
Kowa ya kalleta da Mamaki kai ta gyada Tana fadin”Binta ki kira su karima su iso suma kaima Kabiru ka Kira me sunan megidana Hamisu Da sauran yaranka Sajida da Umaima suma sai sun zo sannan zamu taru muyi wannan Zaman da yardan Allah.!
Bai da tacewa illah Shikenan Daada Mami Asma”u tamai kallon ya zakace haka kasan yaran na makaranta Shi kuma yayi mata kallon ba Mafita sai Bin Umarnin Daada.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button