GIDANMUNOVELS

GIDANMU 1 & 2 COMPLETE

GIDANMU HAUSA 1 & 2 COMPLETE

Janafty..
3/22/22, 23:13 – Ummi Tandama😇: GMB2🅿ï¸?4

Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488

Ta kasa dauke idanuwanta akansa Haka kurum bata san Dalili ba Zuciyarta ta fara Bugawa Fat!Fat!yanayinsa da komai ya tafi da Tunaninta wanda ya Haifarmata da kuramai ido ta kasa Dauke idanunta akansa.
Shi kuwa Tunda ga wannan kallon bai karama kallon Inda take ba ammh yanaji ajikinsa Tana kallonsa Tattare Naman goshinsa yayi waje daya cikin Takaichi ammh yaki yarda ya Kara kallon barayinta Akallon Farko yaji Kwata kwata yarinyar batamai ba Daga yanayinta da komai Tun kafin yasa itadin wacece Tunda shi dai Tunda yazo bai taba ganinta ba sai yau.
Ita kuwa kallonsa take Tana so Tayi Tunanin waye shi..?Domin bata taba ganinsa ba ko yana daga cikin Ya”yan Baffa Malamin ne bata sani ba..?koma waye ajinsa da yanayinsa sun mata a irin yadda take son ganin cikakken Namiji mai cikar Zati da Haiba.
Basheer ne ya Daga ido ya kalli Imran Daya ke Tsaye kikam aransa yana mamakinsa Shi ko gajiya ma bayayi Gyaran Murya yayi yana Fadin”Imran zo ka zauna mana..Kana ta Tsayuwa..!
Yafada yana kallonsa Shi kuma dan yamutsa Fuska yayi kamar yace A”a sai yaji bazai iya Ture alfarmansa ba Haka kurum Sagir kuwa yana Shirin cema Basheer ya kyalesa bazai zauna ba sai gashi ya bashi kunya ya Fara Takawa Cikin Takunsa na isa da Sassarfa ya isa kusa da Basheer din ya Zauna Lokaci Daya yana Harde Hannayensa saman kirjinsa yana Jingina da Jikin kujera Bai saki Fuskarsa ba sai ma kara wani Hade rai da yayi,su Sadam suna gefe suna kallon komai Mirmishi kawai sukayi akallah dai ya Fara shiga Cikinsu.
Dago idon da Imran zai yi suka kara Hada Ido da Sajida dan Waro manyan Idanuwansa yayi akanta irin Lafiya..?sai lokacim ta sunne kanta A kafadan Mami Asma”u dake gefenta sai alokacin Taji kunya ta kamata Imran kuwa Dama ya Fahimci Sajida ita waye karamin Tsaki yaja Har sai da su Basheer suka Juyo suna kallonsa bai basu daman mgana ba ya Kirne Ran nan ya Kauda kansa Lokaci Daya yana wani Dakuna Fuska.
Khamis ne Dake kusa da Sa”id ya taso yazo ya zauna Kusa da Mami Asma”u suka sakata a Tsakiya kenan Kallonsa Tayi Tana Fadin”My son ya wajen aikin naka..? Hop ba wata mtsala ko..?
Tafada Cikin Kulawa da Annurinta na son ya”yanta.
Kansa ya Dora saman Kafadanta yana Fadin”Komai Normal Mami na..I miss u..,!
Sumar kansa ta shafa tana Fadin”Muma muna kewarka Our Son..!
Sajida dake gefe ta Tura baki Tana Fadin”Wai Mamina..? Sai kace Maminka ne kai kadai..?
Kallonta yayi kafin ya Dago kansa yana Fadin”Yarinyar nan baki da kunya kin Rainani ko..?Shegen son jiko kamar mage ga Umai ce ta Shiga Cikin yan”uwa ke kuma kina nan Wajen Mami kina Sakale da ita Kamar Zaki koma ciki..!
Yafada Cikin jin Haushinta Sajida ta kara Nanikema Mami Asma”u Tana Fadin”Mami kin gansa ko..?
Mami Asma”u tace”Zaka fara ko..? Kaifa babba ne..Namiji kuma Ita kuma Macece ko aure tayi a wajenmu She is a kid..!
Bai ce komai ba Sanin wacece Mami Asma”u kai kawai ya Rausayar Daidai Lokacin da idanuwansa yakai kan Imran wanda shima yake kallonsu Duk da ba suna Kusa bane sosai sai dai Yana jin duk Abunda suke Fada Haushi duk ya kamasa Matar nan yar Renin Hankali ne daga ita Har ya”yanta da Mijinta They are all Selfish.
Bawai fa bai gane Khamis bane ya gane sa Sarai domin ya tuna gabda Rasuwar su Anni da Abba ya matsamai suka zo suka kwana Biyu Khamis din ma yazo Tare da Baffa Kabiru kawai dai Shi bai son mu”amala da Khamis ne,Haka nan yaji yaron bai mai ba yana ganinsa Kamar Mahaifinsa ne,kuma shi baya Doguwar Mu”amala da wanda Ra”ayinsa da Zuciyarsa bai kwanta Dashi ba,Bakinsa ya Mele Lokaci Daya yana wani Yamutsa Fuska kamar yaga Kashi ya wani Dauke kansa Khamis shima ya kallesa a Saukaken kafin shima ya Kauda kansa Mikewa yayi ya koma cikin su Sa”id da Yusuf Sajida kuwa Tana jikin Mami ammh gabadaya Hankalinta da Tunaninta na kan Imran wanda bai ma kara Kallon Barayinta ba Sajida ko Wayar nata bata kara Dannawa ba Saboda Kallon Imran gabadaya ya Dauke mata Hankali.
Waige waige ya farayi acikin Falon ko zai ganta saboda yaga ga su Munari na Taya Baba Asabe jera abinci ammh bai ganta ba sai yaji ya Damu,Falon Dayake isu isu ne kadai su Abba suna Dakin Daada,Kamar ya share sai kuma ya kasa Kuma bayason ya Tambayi Munari ta Rainashi sai kawai ya Fito da karamar Wayarsa Ya Shiga Wajen Tura sako.

“Kina ina..? Ban gan ki ba..?

Haka kawai ya Rubuta mata ya Tura mata Sai dai Har tsawon wani Lokaci yana Duba wayarsa bai ji sakonta ya Shigo ba alhalin yana da Tabbacin Inda Lafiya da Tuni ta bashi amsa sake Turamata yayi.

“Ki amsani mana..!

Sai dai shima Shuru sai ya kasa Natsuwa zuciyarsa ta fara Bugawa baisan Dalili ba,Ganin ya kasa Daurewa ne yasa ya Mike kawai zai Fice Daga Falon da Sauri Yusuf Dake gefe yace”Imu ina zaka..!?
Yana Tsoron Kada Zarginsa ya Tabbata Sigari zai fita yasha Ya tsaya ammh bai juyo ba yace”Zan yi kiran Waya ne..,!
Ya fada Cikin jin Haushin Tambayar da Yusuf din yayimai ajiyar Zuciya ya Sauke jin abunda yace Saboda ya Tabbata da ita zai sha sai ya Fadamai gabadaya kowa hankalinsa ya koma kan Imran Daman Tun Lokacin da Yusuf yayi mgana kowa Hankalinsa ya koma kan Imran din Har ya Fice Daga Falon.
Sajida acikin Ranta ta maimata sunansa”IMRAN..! Nice Name..!
Take Fada tana dan Mirmishi Shi kuwa Sagir mamaki ya Kasheshi Dawa Imran zai yi waya..,? Wanda ya sani Dagashi sai ya yusuf yake da Lambarsu sai munari kuma Duka gasu tare,Mamakin hakan ya kamashi Sai dai bai isa ya karyata shi ba Sanin Halinsa Kaifi Daya baya karya Duk Abunda kaji ya fada to iya gaaskiyansa kenan bai mtsama kansa da Tunanin dawa Imran zai yi waya ba ya watsar da komai suka Cigaba da Hirarsu Sama sama da Basheer.
Imran kuwa yana Fita Haraban Gidan Jikin Motar Yusuf ya Jingina yayi Shuru yana wani Tunani gabadaya yaji bai da Natsuwa In kuma bata da Lafiya fa..?
Tuna haka yasa da Sauri ya Lalubo lambarta ya Kirata sai dai Har ta gama Ringing bata Daga ba Ransa sai ya Fara baci ga Zuciyarsa na masa Zafi ya kara Danna mata kira Gbda zata katse Inteesar dake kwance ta Daga Kiran cikin Kasala da Sanyin Murya tace”Hello..!
Muryan ta Dakesa sosai har sai da yaji Hakan acikin Ransa sai dai Cikin Dakewarsa yace”Meyasa nayi miki Sako baki bani amsata ba..?
Sai da yayi mgana ta Zabura ta Mike Cikin Kasala Lokaci Daya Tana Dafe kanta Dake saramata ta kara Bin wayar ta da kallo Ta kara Tabbatar da mai Kiran nata Tunda Cikin dan Barcin Dayafara Daukanta Taji kiran Wayar Idanuwanta sun mata Nauyi bata Tsaya ma Duba mai kira ba ta Daga.
Jin tayi Shuru yasa yace mata”Kina jina ina mgana Shine kike banza Dani..?kinsanni kuwa..? Bana mgana ayi banza Dani kuma bana Tambaya aki bani amsata ya zama Dole duk Abunda nake son sani na Sani din..!
Yafada mata Cikin Zafinsa bai Tsaya Jiranta ba ya Datse kiran yana Jin kansa kawai yana Daukan Zafi haka Kurum baisan Dalili ba.
Inteesar Daga chan bangaran kanta ta Dafe Cikin yanayin dan Jin jiki kamar wasa suna Kitchen suna Taya Baba Asabe aiki suda su Munari,Kanta ya Fara saramata shine ta dawo Daki ta Kwanta Dakyar tayi sallar mangariba Taje ta Fadama Umma,ita ta bata panadol tasha tadan kwanta Shine taji Kiran Wayarta da Imran yayi mata.
Bin bayan Kiran nashi tayi kamar bazai Dauka ba sai daga chan ya Dauka bai yi mgana ba yana cin mgani.
Cikin muryanta Sanyi Sanyi tace”Am sorry Ya Imu..Bani da lafiya ne..!
Sai datace haka yaji ya kara Shiga Damuwa Cikin Dakewarsa yace”meke Damunki..? Meyasa baki Fadamin ba..?
Kara Lafewa Tayi kan gado Tana Fadin”Ciwon kai ne..nasha mgani..!
Kara gyara Tsayuwa yayi yana Fadin”Kinci Abinci..?
Kamar tana ganinsa ta Girgizamai kai Kafin tace”Ban ci ba..!
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace”Ki fito kici wani abu kada ki zauna da yunwa..Ok..!
Da sauri tace”Tom..!
Daga bangaransa yace”Ki rike wayarki a kusa dake kada na Kiraki baki Dauka ba..!
Da tom ta kara amsamai Kafin ya Datse Kiran asaman lebenta tayi dan Mirmishi,Ko minti Daya bai ba da Katse Kiran Ya sake Kiranta Da Sauri ta Daga Tun Kafin tayi mgana Taji yace”Ki duba Sako na ki bani amsa..!
Yafada Cikin Kaushin Murya Cikin Shagwaba tace”Ya imu to ba munyi mgana ba..!
Cikin dan waro ido kamar tana ganinsa kafin yace”Ki bani amsata..ni ne kadai nake da ikon kimin sako naki baki amsarki ammh ni ya zama Dole ki kulani kuma ki bani amsata Lokacin da nake Bukata..!
Abun nasa ma sai ya bata Yar Dariya Har sai da yajita da Sauri yace”Au dariya ma kike yi ko..? Ashe kina son Duka kenan ko..?
Da Sauri tace”Ban fa da lafiya..!
Tafada Cikin Shagwaba Har sai da yaji Hakan acikin Ransa Mirmishin Saman Lebe yayi kafin yace”Do as i say..!
Yes sir..! Tacemai tana yar Dariya shima Dariyan yaso yi sai dai bai bari taji ba ya Datse wayan ya koma ya Jingina jikin Motar Wani Nishadi na kara Shigarsa baisan Dalili ba In yana mgana da yarinyar yana jinsa kamar bashi ba Ya kasa Fassara hakan sai dai ya barsa ne a karfin jinin yan”uwantaka atare dasu,Shiyasa yanan nan Tsaye yaji Shigowar Sakonta,Da sauri ya Duba.
“Ban je ko”ina ba Ya imu..Ina Daki ina kwance ban lahiya..!
Sai kuma Dayan”Ehyyee..Ya imu ya Damu dani..!
Haka ta Rubutomai Dariya yayi afili ya Furta”Shagwabbiyar yarinya kawai..!
Yafada sanda Sagir ya kariso wajen yana Fadin”Kai kuma kai da Waye kake Dariya kai kadai..?
Dagowa yayi yana kallonsa Lokaci Daya ya maida Wayarsa aljihu yana Fadin”Ina Ruwanka banza Dan saka Ido kawai..!
Sagir yayi dariya daidai Lokacin da Sauran mazan suka Fito Harda su Abba domin zuwa masallaci an Kira Sallah da Sagir yama Imran mgana su Tafi cemai yayi shi Yaron sane da sai ya Tasa agaba…?
Yaje yasan Hanya zai zo Daga baya Sagir bai damu ba ya wuce,haka ma su Yusuf suka Fice abunsu sanin Halinsa kamai gwaninta ya Dizgaka
Ganin su Abba ne yasa ya wuce da Sauri bayaso ya gaida Baffa Kabiru shiyasa yayi saurin wucewa Abba yana kallonsa kuma ya Fahimcesa Sarai Mirmishi kadai yayi suma suka Rufa Musu baya zuwa Masallacin Dake kusa da gidan
Bayan an gama Sallah gabadaya suka Dungumo suka Dawo Gidan Imran ne abaya Shi kadai yaki ma yarda ya Jera da Kowa ko Sagir daya so ya Jirasa Cemai yayi yayi gaba basai ya Jirasa ba.
Bai damu ba ya Taka ya bi su Basheer ya kyaleshi yana Tafiya kamar bazai taka kasa ba.
Gabadayansu afalon suka yada Zango Domin cin Abinci Har da su Abba Daada ma ta Fito nan falon Imran yaso ya gudu ya koma Daki Daada ta Hanashi ta Kirasa tace yazo ya Zauna Kusa da ita bai da yarda zai yi Dole yaje kusa da ita ya Zauna,Yana cim mgani Irin su Mami Asma”u sai cika take tana batsewa,Ya”yanta na Gefenta Sajida da Umai,Sajida sai Satan kallon Imran take yi shi baima san Tanayi ba.
Tuwon Semo ne da Miyar kubewa Danya Dataji Naman Rago da Manshanu,sai Ci suke suna Sakin Santin su Anty Safeya dasu Aneesa suna Gefe suma cin na su suna Hira haka suma Mazajen nasu suna Waje Dayane,Haka ma su Abba suna Zaune dasu Daddy waje daya duka dai duk suna kan Katuwar Dardumam da Baba Asabe ta shimfidamusu ne.
Daada ne ta kalli Umma Dake gefen Inna Maimuna tana Fadin”Salaha ina Maryama..? Banganta ba..!
Tafada tana kallonta kafin Umma tace wani abu da Sauri Munari tace”Tana Daki batajin Dadi Daada..!
Daada ta jinjina kai kafin tace”Ayya..Meke damunta..? Taci abinci?tasha mgani..?
Tayi Tambayar Duka Lokaci Daya,Munari tace”Eh Daada tasha Tea dazu kafin na Fito..!
Daddy ya ijiye Spoon yana Fadin”Tun yaushe ne bata da lafiyar..!
Umma tayi Saurin Taresa Tana Fadin”Yanzu da yamman ne fa Abban Intee..Ni na bata mgani kasanta Raguwa ce gajiyan Hanya ne..,!
Kai ya kada bai ce komai ba Saboda Yasan meyasa Umma ta katsesa.
Khamis kuwa Hankalinsa ya tashi jin Inteesar bata da Lafiya Daman Tunda yazo ita yake songani Cikin nuna Alhini ya kalli Munari yana Fadin”Mai sunan Goggo jikin Inteesar din da Sauki ko..?
Kai ta gyadamai kafin tace”Eh Kamar ta samu barci ne..!
Kai ya jinjina duk ya Damu yama kasa Cigaba da cin Abinci,Mami Asma”u na Lura dashi Ranta ya baci ta kallesa Tana Fadin”Kacigaba da cin Abincika Tuwo ne fa nasan kuma Kan sonsa sosai..!
Dan Mirmishi yayi ya cigaba da cin Abinsa Imran kuma Cokali Daya yayi bai kara ba,wayarsa ya Fiddo ya Turama Inteesar sako.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button