GIDANMUNOVELS

GIDANMU 1 & 2 COMPLETE

GIDANMU HAUSA 1 & 2 COMPLETE

Kuyi Hakuri Don Allah yau nayi Fama Da rashin Chaji ne,Bamu da wuta nakai wayata Chaji ban karbo akan Lokaci ba afuwan..

Shakira
3/22/22, 23:14 – Ummi Tandama😇: GMB2🅿ï¸?5

Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488

Mamakin Mami Asma”u ya kama Ilahiran wadanda ke cikin Falon,Barin ma Abba da Daddy da suka ga yadda Mami Asma”u take nuna Hannu tana so taja da mganar Daada wanda ko su basu isa su ja da Umarninta ba.
Imran manyan Idanuwansa ya Zubamata da suka Fara Chanza Launi Saboda bacin rai bai ce komai ba sai dai ya kara Ware idanuwansa kan Yarinyar da Daada takira da Sajida Duk da bai san ko itace ba a mganar Mami Asma”u ya tabbatar da Zarginsa sai akaci sa”a itama Sajidan shi take kallo da dukkan Tunaninta Shima sai Lokacin yake kare mata kallo Cikin kaskanci da bacin rai Billahil Azim Ko Dauramai wannan yarinyar akayi a Kafarsa sai ya kwance ko mata sun kare a Duniya babu abunda zai yi da ita ballatana Har Uwarta ta Nemi gayamai mganar Banza Daada kamar Tayi kuskure ne Wajen Fadan suna.
Sagir kuwa Tsabar mamaki ya kasa mgana Shi da Yuauf Imran kadai suke kallo suna Fatan kada wani Hargitsi ya Faru a wannan zaman sun sansa sun san Halinsa bayason ka Shiga Harkansa ka batamai rai yanzu zaku samu mtsala.
Khamis kuwa bai ce komai ba Ammh Shi kansa Hadin ai bai yi ba ina Sajida ina wannan Muradadden Mutumin wanda baisan yan”uwansa ba sai dai yana da Tarbiya bai saka baki cikin mganar da ba nasa ba.
Inteesar gabadaya Jikinta taji yana Rawa Zuciyarta na Bugawa Fat!Fat.Kamar wacce tayi Gudun Fanfalaki Kanta ya Fara wani Sarawa da Karfi Har Jikinta na kasa Daukanta Daga inda take Zaune Hannun Munari ta Damke Lokaci Daya tana Runtse Idanuwanta ta sauke kan Imran wanda ya Kauda kansa Daga kallon Sajida yana maidawa wani barayin yana Kokuwa da bacin Ransa ne bayaso Ransa ya baci ya Hargitsa wajen Wanda kuma ya Tabbata bazai ma kowa Dadi ba.
Munari da Hafsah cike da mamaki suke Bin Inteesar da kallo wacce ke Hada Uban gumi duk da Sanyin Fanka da A.c dake cikin Falon ammh bai isheta ba Lokaci daya Jikinta sai karkawa yake yi Har suna jin haka a Hannuwansu data Damke cikin nata.
Cikin Firgicin da suke ciki Munari tace”Intee meya faru..?Ciwon kan ne ya tashi..?
Haka suka Shiga Jera mata Tambaya Ita da Hafsah sai dai ita kanta Baxata iya Fasaara Halin data Shiga ba Tun Lokacin da Taji Daada tana Fadin Umarninta ne Imran ya auri Sajida Taji komai nata ya Tsaya Cak ta kasa gane gaba ballatana baya.
Cikin wannan Halin ne Muryan Inna Maimunatu ya Karade falon Inda ta Mike Cikin bacin rai Tana Fadin”Haba Asma”u ai banzata Tsaurin Idanuwanki yakai Har Daada tayi mgana ko gama Sauke Numfashi batayi ba ki mike kice bazai sabu ba..In kin manta bari na Tuna Miki Daada Uwa take ga Yaya Kabiru kuma Kaka take wajen Sajida kamar yadda kike da Iko da ita muma muna dashi..kuma Dangin Uba sune Kan gaba Wajen zaba ma ya”yansu Mazajen da suka Dace dasu ba ke ba..!
Ta Karishe Fada Cikin bayyana bacin Ranta da yadda Daman take Cike da Mami Asma”u da Raininta.
Mami Asma”u da idanuwanta suka Rufe ta Fara Tafa Hannu Tana Fadin”Eyye Ahhye..Wato saboda ba yarki bace shiyasa kikacewa haka..?in adalci ne meyasa sai yata..! Ba yar Muatpaha ba yar wajenki..Ko ba yar Wajen Binta Dole sai yata.?oh saboda kowannenku anan yasan Zafin nashi kuma Ko Mahaukaci nasan abu mai kyau da Nagarta,Shiyasa ba wacce Zataso a Dauki yarta a Hadata da Mai Shaye Shaye kuma Dan iska..!
Daddy ne yaji abun ya isheshi yana Daga Zaune ya Daka ma Mami Asma”u yana Fadin”Ya isa haka Asma”u..!
Jin haka yasa ta tasomai Tana Fadin”Ba zan yi shrun ba..?Saboda kada na Fadi gaskiya ko..?To wlh ba wanda ya isa ya Dinkemin baki sai nayi mgana In adalci ne ka Dauki Inteesar ka basa mana Sai ka Shiga maganar in kana so na Rufe bakina nasan kuma adalci ne za”ayi anan Wajen ba son kai ba..!
Tafada Tana kallon Daada Datake kallonta batayi mamaki ba Sai dai Tana kara Nazarin Wasu Hallayar Asma”u da ta dade da karantarsu,sai dai bata taba Nuna mata agabanta ba sai yau.
Kowa mamakinta ya cikasa da mamakin yadda take Fadar mgana son Ranta Baffa Kabiru ya kasa Dakatar da ita Daddy ya kallesa Cikin Takaichin ganin yayi Shuru ko Uffan baice ba Ballatana ya Dakatar da ita Cikin bacin rai ya Maida kallonsa kan Mami Asma”u yana Fadin”Wlh Tallahi ba Domin Umarnin Daada bane da yau na Nuna Miki iyakarki Asma”u Da yau na Nuna Miki Da Imran da Inteesar duka Dayane awajena anan Wajen ba sai gobe ba zan Biyamai Sadaki a daura musu aure..sai ki jika Taki yar kisha..Domin ba ita kadai bace ya”a ki duba Fadin Falon nan Cike yake da ya”ya da jikoki Saboda ya”yanki kadai Daada bazata ji Tayi wani Maraicin Rasa Jika ba..!
Yafada cikin Bayyana Bacin Ransa Imran kuwa jin Abunda Daddy yace ne yasa dago kansa ya Kalli Barayin da Inteesar take zaune karaf kuwa suka Hada ido Itama kallonsa take Cikin zuciyarta Tana jin Wani Rauni na shigarta,Hawayenta Datake ta Tarewa suka samu nasaran Zubomata Sharr saman Kuncinta shi kuma Imran sai yaji Ransa na Suya ganin tana kuka Wato itama saboda taji ance Zata aureshi ne take kuka..? Har haka ya zama abun kyama bai sani ba..? Shi fa Imran shine Inteesar take kuka Saboda mganar Daddy..! Tuni zuciyarsa ta bayyana Rauninsa Wanda ya Dade bai bayyana ba Abun yamai Ciwo kwarai shi bai damu ba don Mami Asma”u tayi wasu mgangu akansa Daman bata ishesa kallo ba ammh Yafi jin zafin ganin Inteesar na Hawaye bai sani ba Baisan yadda Inteesar take ji bane da bai yarda ya Zargeta kan Halin da ita kanta bata san Dalilin Shigarta ba.
Mami Asma”u da kalaman Daddy suka bata Dariya ta Murmusa tana Fadin”In ka Burgeni ka Daura mai Daure da Inteesar yanzu Mustpaha..!
Daddy ya yunkura zai mike Abba ya Rikeshi ya Dago yana kallonsa sai ya Girgiza mai kai shiyasa ya koma ya Zauna yana Huci Umma Kuwa na gefe Ranta duk ya gama baci tana ganin Sakacin Barrister sai yau ta Kara Tabbatar ma kanta ya Dade da Zama Mijin tace sai abunda Asma”u ta yanke.
Inna Bintalo ne ta Tabe baki Tana Fadin”Mganar gaskiya aduba mganar Asma”u..Ko yayane..Gwara abu mai kyau da Lalala..!
Mami Asma”u na jin haka Ta ce”Yauwa Binta daman nasan ko kowa bai Fahimceni ba ke zaki Fahimceni..Ki fa Duba Sajida fa kalleta ace Rana Daya za”a Illata Rayuwarta a aura mata Mashayi Rayuwarta ta Dauwama cikin kunci da bakinciki na Har Abada..Ina bazan bari a Cuceki ba Sajida bar kuka..!
Tafada Tana kallon Sajida dake kuka Wanda ita atunaninta kukan Mganar Daada take nan kuwa bata sani ba Sajida tana kukan yadda Lokaci Daya Zuciyarta ta kamu da son Imran sai dai Tana Hango wani al’amari nan gaba.
Daada da sai yanzu Tayi mgana Baffa Kabiru ta kalla cikin Takaichi kafin tace”To sallammmane ka Dakatar da Matarka hakanan tayi iya abunda zamu iya dauka ya kuma isa haka..Ko Tayi shuru ta koma ta zauna ko ta Ficemin daga Falo bana son ganinta!
Daada ta Fada Cikin bayyana bacin Ranta Mami Asma”u ta saki baki Tana kallonta ta Bude baki Zatayi mgana Khamis ya mike yana Fadin”Mami plz..!
Yace mata yana Riko hannunta Dole ta koma ta zauna kana ya koma Wajen zamansa Baffa Kabiru kuma bai ce komai ba,Kansa ma yamaida kasa,kamar bashi a falon saboda Yasan bazai iya Dakatar da Asma”u ba Yasan tabbas tana kan gaskiyanta ne sho kanshi bai yarda da mganar Daada ba banda Rikicin Tsufa Ina Sajida ina Imran ai Tazaran akwai Nisa kamar Tazaran sama da kasa ne.
Daada ta kada kai tana Fadin”Nayi matukar mamakin yadda na bada Umarni wanda ko ya”yana basu isa suce A”a ba sai ke Asma”u kika Mike agaban ya”yana kika ce ban isa ba kuma nayi son kai banda adalci..!
Ta karishe Fada Tana Kallon Mami Asma”u datake cika tana Batsewa.
Kafin ta Cigaba da fadin”Kuma agabanka Kabiru baka iya cewa komai ba saboda abunda tayi a wajenka Daidai ne ko..?
Dagowa yayu yana Shirin mgana ta Dagamai Hannu Tana Fadin”Ba sai kace komai ba na Riga nagama Fahimtarka..Ka nuna ban isa dakai ba Matarka ita keda iko dakai..Sai dai ina so ka sani Sajida bata fi karfin Imran ba sai ma shine yafi karfinta ba Domin Rayuwa ba ita bata isa ta taka Inda ya taka ba duk takamarta kuwa..Imran yafi karfinta da Duk Abunda Uwarta take takama dashi..!
Ta karishe Fada Tana bayyana Bacin Ranta.
Mami Asma”u tasan da ita Daada take wannan mganar Khamis sai girgizamata kai yake mganar Daada tayi ma Daddy da Inna Maimunatu Da da Munari da Safiya da Yusuf da Sagir Dadi Domin Ransu kuna yake data ke jifan Imran da kalmar dan Shaye Shaye Umma ma taji Dadi sai sakin Mirmishi take yi,Inteesar kuwa Ranta kuna yake ga Cin Fuskar Mami Asma”u ga Imu ga kuma mganar Daada.
Baffa Kabiru dayaji kunya ganin Daada ta ganosa ya muskuta yana Fadin”Ba haka bane Daada..!
Da sauri Tace”In ba Haka bane meyasa kayi shuru..?in kana so na yarda Matarka ba ita keda iko dakai ba..Ka Amince da wannan Hadin nawa..Sannan ina son a Daura auran nan Kafin kowannen ku ya koma Bakin aikinsa Gobe kenan in Allah ya kaimu..!
Gabadaya aka Zurama Daada ido Gaban Baffa Kabiru ya yanke ya Fadi ya Dago yana kallon Daada ta Hade rai ba Fara”a,kansa ya maida Wajen Mami Asma”u wacce ta Girgizmai kai da Sauri Rauninta ya bayyana bazata Jure ganin an Ruguzamata Rayuwar yarta ba.
Imran kuwa kansa na kasa bai Dago ba,yana Tunanin shi yaro ne da za”ayi mai irin wannan auran..? Me Daada take daukesa ne..?mara amfani ko wanda baisan inda kasan ke mai Ciwo bane?Kamar shi Imran ba wanda ya isa ya Wulakanta shi ko yakaskastan dashi bai nunamai kuakuransa ba Karyansa zai nuna ma Mami Asma”u tayi kuakure bazai taba Auran yarta ba Har Abada.
Baffa Kabiru bai da wata Manufa bai isa ya Bijerema Umarnin Daada ba Sai da ya Sadda kasa kafin yace”Shikenan Daada..Na Amince Allah ya kaimu goben lafiya..!
Da sauri Daada ta Saki Mirmishin Farinciki Tana Fadin’Masha Allah.Kai fa Malami me kace kan mganata..?
Abba bai da tacewa kansa ya Gyada yana Fadin”Duk yadda kikayi daidai ne ni da Imran masu Bin Umarnin ki ne..!
Mami Asma”u ta Mike Cikin Hargagi tace”To wlh in shi ya amince..Ni ban Amince ba..In dai ina Numfashi bamai Aura ma Ya”ta Dan iska Dan Shaye wanda baida Sana”ar fari ballatana na baki sai shaye shaye..!
Tafada da karfi Tana Zaro idanuwanta Waje.
Imran daya gama jin iya Abunda zai ji yakai wani limit din da Bazai iya Jurewa ba ya Mike da Sauri jikinsa na Rawa Cikin Dakakkiyar Muryansa mai Cike Amo da Zati yace”Kada ki kara Kirana Dan”iska..Ko Da’n Shaye..Shaye..Don”t Try it again..Don”t Ever Try it…!
Ya karishe Fada Jijiyoyin kansa sun Mike Radau har ana ganinsu Naman Kirjinsa na sama da kasa Lokaci Daya yan Sakin Huci mai Zafi tare da Zafin Zuciya kamar yayi Bindiga haka yake jin kansa,Hannunsa Manuniya ya Daga yana nuna Mami Asma”u dashi Cikin Alamun gargadi.
Gabadaya kowa sai ya koma kallon Imran cikin Mamaki,Umma aranta tace ai gwara yayi mganinta Haka ma Inna maimunatu taji acikin Ranta.
Mami Asma”u da Ta tsaya tana kallonsa Cikin dan shakarsa Tace”In na kara fa? Me zaka iya Mara kunya Fitsararre..?
Tafada Cikin Ingili tana Jifansa da Harara,Imran dayaji ya Fara rasa Duka Controling dinsa ya Fara Takawa zuwa gaban Mami Asma”u Cikin Dakakkiyar Muryansa yace”Sai na nuna miki Halin Dan Shaye shaye..Na kuma gwada miki Halin Yan iskan da kike Fada..!
Yafada yana kallonta Ido Cikin ido babu Wani tsoro ko Shakkarta.
Taji Tsoro saboda ganin yanayinsa sai dai kasawa ba nata bane Cikin Dari dari tace”An ce maka Dan shaye shaye..? Karya akayi ba Dan Shaye Shayen bane..?
Tafada Cikin Nuna iya gaskiyarta ai batama gama Sauke Numfashi ba taji Hucin Imran gabda Fuskarta kamar Walkiya ya kariso gabanta Idanuwansa Sun Rufe baima gani Dakyau Zuciyarsa ta gama Rufewa da wani Duhu har yana Hango kansa yayi Ball da Mami Asma”u da sai ta Gamu da Bango kanta ya shafe ya Tabbata bazata taba manta dashi ba.
Sai dai ya Daga hannunsa da Niyar Tureta Abba ya Mike da Sauri Cikin Abunda bai fi kiftawan ido ba ya Dakamai Tsawa”Imran…kada ka Fara..!
Yafada cikin Tsawa da Hargagi wanda ya Firgita kowa,Mami Asma”u tayi bayan Baffa Kabiru da suka Mimmikewa Cikin mamakin Imran,Imran kuwa Cak ya Tsaya yana Sakin Huci mai Zafi idanuwansa sun Juye kamar yana cikin maye,Inteesar da Munari suka kamkame juna suka Fashe da kuka Su Sadam kuwa suma Mimmikewa sukayi cikin mamaki.
Abba cikin Sauri yace”Yusuf da Sagir ku Rukemin shi..!
Yafada a Taushashe Daada Dake Zaune bata Motsa ba Illah dan Mirmishi Data saki In Asma”u ta tabata Kabiru yayi shuru ta tabbata In tayi ma Imran bazai kyaleta ba yaron Zamani ne mai ji da kuruciya Shine Daidai da ita.
Da sauri Yusuf da Sagir suka Karisa suka Rikesa daman suna Ta tsoron kada ya balle musu,Kokarin Fizge kansa yake yi suka mai Riko sosai Yusuf ya Kallesa yana Fadin”Imu..Imran kalleni..!natsu Nace maka..!
Yafada Cikin Daga Murya,kallon Yusuf din yayi yana Budemai idanuwansa Cikin Muryansa mai cike da amo yace”Na natsu fa kace..?Kake fadamin na Natsu..? To bazan natsun ba..ka sakeni nayi mganin matar nan..Nace bana son ana batamin rai Bana so…BANA SO..!
Tunda nazo na shiga Harkan wani..? Ina kebe kaina ne saboda ina Girmama yanayina..Bana so na bata ma wani rai nima bana son wani ya batamin Tayi ta mganganu akaina Cikin son ranta..Waya Dakatar da ita..?ko wayace mata ta bari bai kamata ba? Sai ni domin nagaji nayi mgana..? Wlh billahill Azim bata san Waye Imran ba yau bazan ji mganar kowa ba indai matar nan ta kara Bude baki ta Fadi wata mganar banza akaina sai na Nuna mata Kalata sai na Nuna mata ita din ba kowan kowa bace a Wajena..!
Ya karishe Fada Cikin Tabbatar da mganarsa Khamis ne ya Isa gaban Inran Cikin Fushi daman Tun dazu yana Tsaye so yake yaga Karshen Rashin kunyar Imran din in zai iya Dukan Maminsu..? Lalle da yau yagane Shayi Ruwa ne..!
Kikam ya Tsaya gaban Imran yana Fadin”Yanzu kai in aka barka sai ka Daketa..?kasan wacece ita agareni.?mahaifiya kasan kuwa mtsayin uwa a wajen D’anta..!?da zai iya zama ya Jure Cin Zarafinta Daga wani bangara..?
Yafada Lokaci Daya yana Dukan Kirjin Imran wanda ya tsaya Kikam Shima yana kallon Khamis Cikin wani Kallo na Takaichi Karamin Tsaki yaja kafin ya kwace hannunsa a wajensu Yusuf ya Saka Hannunsa ya bambare Hannun Khamis akan kirjinsa yayi irin Wurgi da Hannunsa da Zafi sai da Yayi baya kamar zai fadi kana ya Tsaya da Kafafunsa.
Cikin Nuna sa da yatsa Imran yace”Kai yaro kauce badai kai zan yi ba..Ita din wacece..?ni ba kowa bace a wajena..Ko Baffa Kabiru dake mtsayin Yayan Mahafina bai isa ya tsaya yana gayamin mganar da wanchan matan take Fadamin ba ballatama ita ba kowan kowa ba..In kai kasan Darajan Mahaifiyarka ni kuma da bani da uwa ai nasan Darajan kaina…Kauce kabani Wuri kafin ranka ya baci..!
Ya Karishe fada Lokaci daya ya bangaje Khamis dake tsaye sai da yayi gefe kamar Zai Fadi Sagir ya Rikosa gaban Sajida dake makale jikin Umaimah ya Karisa Cikin kallon Kaskanci Tare da kare mata kallo Daga sama Har kasa kafin ya Nunata da Yatsa yana Fadin”Wannan abar ne kike Rigima akanta..? Ai ni ban ga mace anan wajen ba..Na Rantse ga Allah ni Imran Abubakar Malami Wannan yar taki a cikin yanmatan da zan iya maneji dasu bata aciki ko acikin Tsakiyan Shinkafa ta shiga zan saka Hannu na Tsinceta na Wurgar..Nafi Karfin yarki da Duk Abunda ta mallaka..!
Yafada yana karkato da kansa Wajen Daada kana cikkn Kaushin murya yace”Daada ki janye mganarki..Ni ban amince da wannan Hadin naki ba Ko matan Duniya zasu kare Bazan iya Auran Diyar masu som kai da son zuciya ba. infact ma batamin ba..Bana sonta bazan taba sonta ba..!
Yafada kai Tsaye Zaro ido Kowa yayi yana kallonsa Mami Asma”‘u taji Tsoro yasa ta kasa wani Motsi tana Bayan Baffa Kabiru da shima ya kasa Cewa kala ballatana Fadan datafi karfinka sai ka maidashi wasa.
Ballatana Khamis da Mamakin karfin Imran ya kamasa Sagir dake rike dashi ganin yana Kokarin kwacewa yasa ya Girgizamai kai yana Fadin”Kada ka shiga wannan Fadan..Abba ne kadai ya isa ya Dakatar da Imu ammh wlh kai bazaka iya ba..!
Zallar gaskiya ya gani acikin Idanuwan Sagir yasa ya kasa Motsi.
Sajida kuwa Kukanta ne ya Karu jin Abunda Imran yace ita kuma alokacin ji take Imran yayi mata Dari Bisa Dari.
Inna Bintalo ce ta Saka Salati tana Fadib”La”ila Ha’illahu Ni Bintalo yau ina ganin Abun mamaki kai Imran Matar yayan Mahaifinka ka Daga hannu Zaka Daka..? Ashe baka da kunya da Tarbiya bansani ba..?
Kai Tsaye Imu ya kalleta Ido Cikin ido kafin yace”Eh..Ai ba uwata bace..?ko Ita din U..!!!
Bai kai Karshen mganarsa ba Yaji Abba ya Sauke mai kyakyawan mari Guda Biyu Dama da Hagu da sai da Kansa ya koma gefe yana jin Wani Radadi daga kasan Ransa Idanuwansa ya Runtse ko Dagowa bai yi ba.
Abba ya Nunasa da Yatsa Cikin Takaochi da Bacin rai yace”In ka kara cewa Tak anan wajen..Ni ba Mahaifinka bane..!
Da sauri ya Bude idanuwansa Jajir ya Sauke kan Abba zai yi mgana Abba ya Dagamai Hannu yana Fadin”Kace Tak zan ci maka Mutumci Imran..Kaji ma na Fadamaka..!.dole Imran yayi shuru Ya koma yana kokuwa da Bacin Ransa ji yake kamar ya Naushi kansa saboda Bakinciki da tozarci.
Abba ya sauke Hannunsa Cikin bacin rai yana Fadin”Ni kaina ban isa na take mganar Daada ba ballatana kai..To bari kaji na Fadamaka ba wanda ya isa ya Tada Umarninta Za”a Daura wannan auran agobe da yardan Allah kamar yadda tace sai dai in zaka Rataye kanka ne ko kuma ka sha Fiya Fiya ka Mutu karewar rashin So kenan..!
Yafada cikin Tabbatar da mganarsa kafin ya cigaba da Fadin”Kuma na Rantse in ka kara cewa wani abu kan wannan mganar sai naci maka Mutumci..Duka ka bama Asma”u da Yaya Kabiru Hakuri kafin na Saba maka..!
Yafada cikin bada Umarni Imran ya Dago ido yana kallon Abba,kai lalle uba ma wani abu ne Da ace yau ba Abba bane waya isa..?
Ganin ya tsaya kallonsa ne da Jajayen Idanuwansa yasa ya Dakamai Tsawa Har Jikinsa na rawa yace”Ko bazaka Duka bane ni na Duka da kaina na basu Hakurin Rashin kunyarka..?
Yafada yana Nunasa da Yatsa,Yusuf ganin yadda Abba ke rawan jiki yasa ya Isa kusa dashi ya Riko sa yana Fadin”Abba koma ka zauna zai yi Abunda kace..!
Yafada yana Rikosa,Yusuf ya kallah kafin yace”Kyaleni kawai Yusuf..!
Yafada cikin Tabbatarwa da nuna Bacin Ransa jin haka yasa ya Kyalesa ya Karisa Wajen Imran ya Dafa Kafadansa yana Fadin”Kayi Abunda Abba yace Imu..Plz..!
Bai yi gaddama ba ya saka Gwiwiyinsa a kasa Kirjinsa na kuna Cikin Dashashewar Murya yace”Ku…yi hakuri..!
Lokaci Daya yana Sadda kai Cikin Takaichi yanajin kansa kamar ma yayi Bindiga saboda Zuciya.
Mami Asma”u ganin an bata Hakuri yasa Ta fito daga bayan Baffa Kabiru Tana wanu tabe baki ganin haka Yasa Abba ya juya yana Fadin”Ina kara baku hakuri a madadinsa..Yaya Kabiru dake Asma”u ku yi hakuri ku yafe masa..!
Yafada yana Hada Hannuwansa alamun Roko Baffa Kabiru ne ya Jinjina kai Lokaci Daya yana Sauke ajiyar Zuciya Kafin yace”Is ok..!
Da haka bai kara cewa komai ba,Mami Asma”u baki ta tabe kafin tace”Uhm..Shikenan..!
Abba ya gyada kai yana Fadin”Nagode..!
Lokaci daya ya juya wajen Imran yana Fadin”Tashi ka koma Wajen zamanka..Kuma ba cewa nayi ka Fita ba..!
Yafada kafin ya kalli Sagir yana Fadin”Sagir kamasa kuje..!
Sagir na jin haka ya Rikosa yana Fadin”Tashi Imu..!
Bai yi gaddama ba ya Mike ammh Idanuwansa ma basa ganin gabansa Saboda bacin rai nan idanuwansa yakai kan Inteesar dake kuka Sai Yakara Rikicewa Kujeran dake Kusa dasu ya saka Kafa ya Daketa sai da tayi baya ta Wuntsula suka tashi a Firgece su uku ita da Hafsah da Munari suna Makyarkyata da kallo Kowa ya Bisa Abba kai ya Girgiza Shi da Yusuf.
Sagir yayi ya zauna yaki a Tsaye ya tsaya ya Harde duka Hannuwansa saman Kirjinsa ya Lamkwashe kafafunsa yana Girgizawa.
Daddy ne yace kowa ya koma ya Zauna kana Falon ya natsu bayan kowa ya Zauna Abba zai yi mgana da Daada ta Dakatar dashi da Fadin”Ba sai kace komai ba Malami..Abunda kayi daidai ne ka nuna mana Rauninka baisa ka Daina bama ya”yanka Tarbiya ba,Duk da itama Asma”u bata kyauta ba ta shiga mganar da ba nata ba sai dai Duk inda karami da babba ke Fada to Karamin ne za”a Hukunta ko da shi keda gaskiya naji Dadin Hukuncinka..!
Ta karishe fada Cikin Dattako kafin ta Dora da fadin”Dalilina na Hada wannan auran don Dinken wannan Barakan dana Hanga Tuntuni ne..Za”ayi wannan auran gobe insha Aallahu kamar yadda nace..Ke Asma”u Allah yasa kiyi Hankali..Yanzu Imran suruki yake wajenki in baki Daukesa Danki ba..Kai ma Imranu Asma”u Suruka take gareka in baka Dauketa Uwa ba..Ku koyi girmama juna saboda haka..Dare yayi kowa yaje ya kwanta ya”yana kuma zamu kara Tattaunawa acikin Daki..Allah yayi muku albarka Gabadayanku..!
Wasu ne suka samu amsa ma Daada da Ameen Mikewa tayi Daddy da Abba da suka mike tsaye suka Taimaka mata zuwa Dakinta,Inna Maimunatu da Inna Bintalo da Baffa Kabiru suka mara musu baya.
Imran kuwa shi ya Fara Fita Waje Haraban gidan kansa sarawa yake yana jin kamar ma yayi Bindiga saboda Bacin rai wato sun Dage sai anyi ko..? Lalle zasuv samu karamar bazawara kamar yadda suka Dauramai bada son ransa ba Wlh Tallahi sai ya aikata abunda bazai ma kowa Dadi ba.
Yafada Lokaci Daya yana Zaro karan Sigarinsa ya kunnata ya Haye saman Motan Yusuf ya shiga busa Hayaki ta Hanci ta baki itace kadai zata saka yaji Bacin ransa ya Ragu in ba Haka yau ba zaman lafiyaa
Achan Falo kuwa kowa ya Watse Munari ta kama Inteesar suka Shige tana Waigen Inda Imran yabi ya Fita Mami kuwa ya”yanta ta Rumgume tana jin wani Radadi acikin Ranta Yayinda Khamis yazo yana bata Hakurin ganin Harda kukanta.
Su Anty Safiya Daki suka shige Kowa zuciya ba Dadi Umma ma Dakin ta Shige Domin barci ne a idonta itafa bata ji wani damuwa ba mganin mai Son kansa kenan
Su Yusuf kowa wajen kwanciya suka Nema kowa ba Fara”a ammh kai tsaye Sadam yace yaji Dadin abunda Imran yayi ma Mami Asma”u kila ta Daina abunda takeyi.
Badai wanda yace komai Yusuf da Sagir Tunaninsu na wajen Imu basu san Halin Dayake ciki ba sai dai Dole su kyalesa sun san ko giyan Wake suka sha Karyansu suje wajensa ahalin Dayake ciki Kadaicinsa Shine mafita da wani yaje ya Damesa sai dai suna Fatan Allah ya Huci zuciyar Mazaje…!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button