GIDANMUNOVELS

GIDANMU 1 & 2 COMPLETE

GIDANMU HAUSA 1 & 2 COMPLETE


Washegari
Kano.
10:00am

Hajiya Mero ce da Alhaji Ahasaan da Tasleem zaune kan Dining din Dake Falon gidan,Suna Breakfast kowa na cin Abincinsa bakajin karar komai sai Cokali da bugawar Filet da Kofuna.
Hajiya Mero bata wani ci da yawa ba ta Share bakinta da Tissue tana kallon Tasleem tace”Tasleem tashi ki Daukomin wayata acikin Bedroom dina..!
Alhaji Alhassan dake Zaune yana Tura Dankali soyayye Cikin bakinsa,Cikin muryan Abu na Cikin bakin mutum yace”Haba Mero kina gani fa Breakfast take yi ai kya bari ta gama ko kuma ke tunda kin gama ki tashi ki Dauko Da kanki..!
Wani kallo tamai batace komai ba Tasleem ta mike tana fadin”Bakomai Abbu bari na Dauko mata..!
Shima bai yi mgana ba ya cigaba da Tusa dankalinsa yana Hadawa da Kurban Ruwan tea a wani karamin mug mai kyau da yarari.
Ba jimawa sai ga Tasleem ta Dawo da Wayar Hajiya Mero a hannunta sai da ta Zauna ta mikamata Tana fadin”Gashi Mommy..!
Karba Tayi tana Yar dariya da sai da suka Kalleta gabadayansu Lambar Safiya ta Lalubo ta doka mata Kira ta saka Wayar a Speaker ta ijiyeta nan kusa da Hajiya Alhassan saman Tebir din.
Kira Daya biyu uku Safiya Daga Chan bangaran da suke Kitchen suna aikin Abincin da su Abba sukace ayi mai yawa Saboda bayan Salar azahar in in aka gama Daura auran za”a Fito da Abincin arabama Mutane.
Gefe ta koma kafin ta Dauki Wayar Tunda gabadayansu suke Kitchen din Har da Inna Maimunatu dasu Zainab dasu Aneesa da su Munari Inteesar na Cikin Daki bata Fito ba tace kanta na Sara mata.
Sallama ta Ragada kafin tace”Mommy ina kwana..!
Momny ta amsa Tana Fadin”Lafiya lau Daugher ya kuke..? Ya Dukkun..?
Tafada tana kallon Alhaji Alhassan Daya ijiye cin abinsa yana Sauraransu Da mamakin jin ta ambaci Dukku.
Safiya Dagachan bangaran tace”Lafiya lau Mommy gamu cikin sha”anin biki kin ji Hayaniya ko..?
Mommy tace”Eh fa bikin waye..?
Safiya tace”Mommy Imran za”a Daura ma aure yau da yar”uwansa Diyar wanda Abba kebi Baffa Kabiru Barrister Dake Zaune A Abuja..,!
Mommy ta Rike baki tana Fadin”Ikon Allah kice Tuwon a maina Za”ayi..Ammh abu cikin gaggawa haka..?
Safiya tace”Daurin auran kadai za”ayi Mommy Tarewa inaga sai daga Baya..Daada ta hada abun saboda kara Hada kansu Waje Daya..Mommy kinga Danginsu gabadayansu kowa yazo da ya”yansu gidansu Babban Gida ne Mommy a Dukku su din Dangin Manyan Mutane ne Duk garin Dukku ba wanda baisan Iyalan Gidan Marigayi Alkali Hamisu Dukku ba..!
Mommy Dake sakin Dariya Tana kallon Alhaji Alhassan ta gfen ido kafin tace”Masha Allah..Naji Dadi sosai Safiya..Allah bai barin Zalunci Daman Nagodema Allah yadda wani yaso ki tozarta Allah bai bari haka ya Faru ba gaki yanzu cikin Ahalin mijinki Cikin nasaba da Karamcin da Tushe da asali in arzikin ne suma sun Taka Allah ma godemaka da kika Tsallaken Siradin Tozarci sai dai Mutum ya Tozarta..!
Ta Karishe Fada da karfi kuma da gayyah ba Alhaji Alhassan ba Hatta Tasleem da Safiya susan da wanda suke.
Safiya tace”Plz Mommy..!
Tafada Cikin shagwaba Hajiya Mero Tace”Ki gaidamin da Yusuf sai kun dawo zamu zo da Saratu da Tasleem Insha Allahu..!
Safiya tace”Tom Mommy ki gaida Abu da Tasleem sai na Kiraki..!
Daga haka ta katse kiran Mommy ta Mike Dauke da wayar tana yar waka Lokaci Daya tana Fadin”Allah ba azzalumin bawa bane..Allah kana gani..!
Haka take fada Cikin Salon waka ta wuce zuwa Falon tana Hararan Alhaji Alhassan Ta gefen ido samin baida gaskiya ko Dagowa ma bai yi ba kansa na kasa gabadaya Jikinsa ya gamayin Sanyi Tsoro ya Shigesa yana Tsoron kada Hakkin Safiya ya kamasa a sirinsa ya Tonu,Domin bai fa Daina Dabi”arsa ba sai dai kalaman Hajiya Mero sun bashi Tsoro,Ashe yaron nan Yusuf dan asali ne,Lalle ne kada ka shiga Hurumin Ubangiji gabadaya ya kasa Tashi ma Har Tasleem ta gama tabi bayan Hajiya Mero zuwa Falo kunya ya hanasa wani Motsi.


Imran cika kawai yake yana batsewa kamar yayi Bindiga sai kunkuni yake Fuskar nan ba Fara”a ya Hade ran nan kamar bai taba Dariya ba.
Zaune yake gefen gadon dakin da suka sauka,Sagir da Yusuf na Tsaye kansa,Wasu Fararan kayane Riga da wando na Wata Shadda mai kyau da yarari,kayan Yusuf ne Abba yace ya bama Imran ya saka saboda Daurin aure,Da farko so yayi ma ya Gudu ya bar anguwa sai Abba ya Ritsashi yace mai in yasake ya Fita sai ya sabamai baida yarda zai yi Dole ya koma yayi lakwas,Sha biyu ta wuce sun fara Haraman Daurin auran tunda Har sun Daddy ya baama su Basheer kudi sun siyo goro da Minti Umarnin Daada ne Gida kuma ana ta Girki Kayattace,Mami Asma”u na Cikin Daki ta kasa Zama sai kiran Baffa Kabiru take tana so su kebe bai bata Dama ba Saboda baisan me zai ce mata bai isa yabi mgnarta ba yabar Umarnin Daada ba
Shiyasa yaki yarda su Hadu hankalinta ya shi sosai,Khamis ma ta kirasa tana Fadamai yaje ya gayama Baffa Kabiru kada ya yarda a Daura wannan auran bata amince ba Da ya fita bai Dawo ba bayason Mami Tana irin wannan sai abu yazo ya Lalace Daga baya.
Sajida kuwa Daada ta saka Inna Maimunatu da Da Inna Bintalo suka Daukota nan Dakinta Mami Asma”u tana ji tana gani bata da tacewa,Ta Kira Chan gidansu ta Fadama Tsohon Alkalin Alkalai Justice Tafida tana kuka bai biye mata ba yace Baffa Kabiru nada Hurumi da iko kan yarsa ganin ba Sa”a yasa ta Kira Hajiyarsu Hajiya Turai itacre ta Dauki ZAfi ta Kira Baffa Kabiru,bayan sun yi mgana ya nuna mata Umarnin Daada ne shi kuma bai isa ya kauce ma Umarninta ba Dole tayi Shuru ta kira Mami tana bata Hakuri Mami Asma”u ta Cika kamar ta Fashe ga ya”yanta basa Goyon bayanta Umaima ta shige cikin Danginta Ita da khamis suna ta Shirin Daurin auran

Sagir ne ya kalli Yusuf yana Fadin”Ya Yusuf inaga fa sai mun Dannesa mun sakamai kayan nan zai saka su..!
Ya yusuf yace”Naga alama..Imu tashi ka saka kayan nan kafin mu danne ka mu Maka Sintir mu shiryaka..!
Bai ko kallesu ba yana Daga Zaunen yace”Ni ba kayan da zan saka..Kayan Jikina sun isheni..Kuma infact ma ni manyn kaya ba Kayan sawa na bane zan iya kirga sakasu ma da nayi a Duniya..!
Yafada Cikin Dakuna Fuska yanajin an gama Kashe Rayuwarsa wlh.
Ya yusuf yace”zaka sa ko kuwa sai mun Danneka..,,?
Kallon irin lallene ma yayi musu kafin ya Tabe baki yace,”Uban Daya Fasa..!
Zaro ido sukayi dukkansu suna kallon Imran din wanda ya kara Hade ransa Sanye yake cikin Shigar riga da wando 3Quater,duka bakake ya gyara Gashin kansa Daadan nasa ya kara Fitowa tas dashi ahaka zai je Daurin auran domin ya gama Tsarinsa bamai sakashi Sauyawa.
Ya yusuf ya kada kai yana Fadin”Bari na Kira Abba na gayamai kace Uban da ya fasa..!
Yafada yana Fito da wayarsa ya Farra Dannawa Imran na jin haka ya Mike Cikin kunkuni yana Wani Dakuna Fuska yana Fadin”Tsakani ga Allah an Takuramin..An Takuramin an gama dani ni dai an cuceni Wlh..,!
Haka yake fada kamar yayi kuka Dukkansu dariyansu suka kanne Yusuf yace”Abba ya gode..Tunda ya Cuceka Imu..!
Yana Daukan kayan yace”Ni ban ce ba..kuma afita abani waje ko agabanku zan Tube na saka kayan masu gadi..?
Yafada Cikin bacin rai da Takaichi Dariya suka saka Imran ya Saka Kafa ya Shuru Sagir Yana Fadin”Munafuki..Shidai gefe ya matsa yana Dariya Yusuf yajasa suka fice suka Rufomai kofa abakin kofan suka Tsaya suna gadinsa sanin Halinsa zai iya Fitowa ya kara gaba.
Sun bashi Minti Talatin suka koma Dakin Wow mssha Allah haka suka Hada Baki wajen fada.
Sagir ya Kalli Imran da yayi wani irin kyau cikin mayan kayan,Ya yusuf ya azamai Hula zanna Bukar Dake hannunsa,mai zanen bakin zaren aikin Dake jikin shaddan yana Fadin”Rufe wannan Tozom gashin naka..Kada ango ya zama abun nunawa..!
Imran ya yamutssa Fuska yana Fadin”Asan Mutum dai asan cinikinsa Shine Rayuwa ba Karya da munafunci ba..Ni ban damu ba ko Duniya zata nunani am Remain Who i am..!
Ba su tankasa ba sanin yana neman Hanya ne,Sagir kuwa Hoto kawai yake Daukan Imran yana Fadin”Da kasan yadda manya kaya ke maka kyau da daga yau baka kara saka kananun kaya ba..,!
Wata uwar Harara Imran ya Aunamai yasa ya kama bakinsa yana Dariya suna cikin haka sai ga su Sadam sun shigo da Sa”id da Basheer suna ganin Imran suka Fara ihu suna yaba kyansa Suka Firfito da wayoyinsu suna ta Hotuna dashi,Suma kowanne yaci kayansa sabi duk da abun ba Shiri ammh sun shirya ba Laifi.
Duk Hoton da akayi Imran bai saki Fuska ba Sa”id ne ya Daki Kafadansa yana Fadin”Haba Angon Sajida Smile..!
Daya fadi haka Sai da Imran yaji kamar ya yarfamai mari Saboda sunan Daya ambata daga saman lebensa yace”Har Abada bazn taba zaman angonta ba ko na zama na yan a wanni ne a suna..!
Dakyar yadan saki ransa aka gama Hotunan kamar wani Rakumi da akala haka Sagir da ya yusuf suka Riko Hannunsa zuwa Falo,Sai da wayar sagir yaji ana kira ne kana ya sakesa Mama ce ke kira Domin Umma ta Kirata ta shaida mata komai tace ace ma Imran tanamai murna.
Su Aneesa da su Abida kefadin ga Ango ya Fito Inna Maimunatu ta Fito tana Guda,Gudan Daya Fadar ma da Mutane guda uku gaba na Farko Inteesar dake kwance cikin Daki na Biyu Mami Asma”u na uku Sajida dake Dakin Daada Inna Bintalo ta gama Shirya ita da ya”yanta Hamdiya ta mata kwaliya Saukakkiya suka Dauko Cikin kayan data zo dashi wani less suka sakamata bayan sun azamata Daurin Zahra Buhari sai gashi ta Fito duka Daada ta bada Umarnin hakan.
Inteesar na jin haka ta sauko Daga kan gado ta Leko Falo karaf kuwa ta Hangosa duka Mazan dake falon shi Zatinsa na musamman ne Manyan kayan Dake jikinsa sun kara Bayyana kyakyawan Zatinsa da Haibasan yayimata kyau din da bai taba mata ba.
Idanuwa shima yake Wulgawa Yana nemanta bai ganta ba kamar ance ya Kalli Kofar dakin suka hada ido wanda da Sauri tayi baya batasan ya ganta ba Wani Dum yaji acikin Ransa yana jinsa kamar bashi ba.
Daada har Falon ta Fito bakinta yaki Rufuwa Dafasa tayi tana Fadin”Allah yayi maka albrka Imrana kamar yadda Ka Bi Umarnina Allah ya baka y”yan da zasu bika kaima!
Su yusuf ne suka amsa da Ameen banda Imran da acikin Ransa yace”Ba Ameen ba kar allah ya bani da’n da zan Tursasamai yin abu yayi ba don son ransa ba..kuma ki daina Saurin jin Dadi Bacin rai zai gauraye wannan Dariyar taki.keba Uwata ba kin Rikitomin bala”i cikin Rayuwata..,!
Yana Tunanin yana wani Dakuna Fuska Daidai Lokacin da Mami Asma”u ta Fito suka Hada ido kallon kallon suke ma juna ganin yadda duk ta ZAbge ne tayi wani wuri wuri yasa Imran yaji Dadi harda Dan Taune lebensa na kasa kafin ya Daga mata Babban yatsanshi yayi kasa dashi alamun kin Fado.
Takaichi da bakinciki suka kamata bata iya yin komai ba Har suka Tarkasa suka fice Daga Falon,Sagir da Yusuf na Rike dashi kamar zai gudu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button