
Shakira…
3/22/22, 23:14 – Ummi Tandama😇: GMB2🅿ï¸?7
Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488
A haraban gidan suka iske su Abba Shida Daddy suna mgana suma sunci manya kayansu sun sha kyau sai Baffa Kabiru dake gefe yana amsa waya Khamis na kusa dashi shima wayar ce a Hannunsa yana ta Latsawa Suma sun yi Shiga mai kyau da Tsari.
Tunda suka Fito Hankalinsu Abba ya koma kansu Zaratan SAmarin ya”yan nasu Imran duk ya Cinyesu akomai Kallo Daya zakayi mai kaga Tsabar Zati Haiba da kamala Uwa uba Kwarjini da wani baiwar Kyau da Allah yayi mai.
Abba da Daddy baki suka Washe azuciyarsu suna Fadin Masha Allah ballatana Baffa Kabiru da Khamis da suka Saki baki suna kallon Imran Duk da bai saki Fuskarsa ba ko kadan ammh Kana kallonsa Zaka Tabbatar da wannan cikakken Namiji ne inda ake Kiran Maza masu sunan Maza.
In bace maka akayi yana Busa Sigari ba akallo Farko bazaka taba yarda ba Saboda yadda kyansa ya Fito da kyakyawan Zati sukansu sun shaida Karyansu suce Sajida tafi karfin Imran Sai dai shi yafi karfinta ma sai dai in Akayi duba da abunda suke Dubawa din ba Domin wani abu ba.
Har gaban Abba da Daddy Yusuf da Sagir suka Kaisa yana ta wani Fadin Rai Abba ya Dafa Kansa yana Sakn Mirmishin Farinciki Cikin Annushuwa yace”Allah Sarki Zuwaira Allah ya jikanki da Rahma ina ma Kina Raye yau kikazo kiga Imran din ki Zai zama Babban Mutum..!
Gabadaya sai jikin kowa yayi sanyi jin kalaman Abba da kuma yadda Hawaye suka ciko Idanuwansa yayi Saurin maida su yana Jijjiga Kafadan Imran Lokaci Daya yana Fadin”Allah yayi maka albarka..!
Daga saman Lebensa ya amsa da Ameen Hakama Daddy ya sakamai albarka ya amsa Kamar mai Ciwon baki.
Sai Lokacin Khamis ya Kariso wajen ya bama Duka su Basheer hannu sukayi musabaha Daya Miko ma Imran sai ya Karkace kansa gefe kamar bai gansa ba Khamis ya karajin ya muzanta Da Sauri ya maida Hannunsa Bayaso wani Cikin su yaga wannan Tozarci da Imran ke nuna mai duk sanda ya Nemi wani Huldar Arziki ta Shiga Tsakaninsu.
Koda Baffa Kabiru ya kariso Wajen Imran Saboda kada ya gaisheshi baya ya koma,kawai ya Saka Hannayensa Cikin Aljihun wandon Shaddar Dake jikinshi yana kallon kowa Daya bayan Daya yana jinsa yau din nan kamar bashi ba,Ga wadanan kayan Dake Jikinsa ba karamin Takuramai sukayi ba.
Ganin Lokacin Sallah ya kusa ya saka duk sukayi alwala anan Haraban Gidan,Inna Maimunatu ta Fito musu da Botoci sukayi amfani dasu kana suka Rankaya zuwa masallacin Dake kusa dasu,Basheer da Sadam na Dauke da Dabino da goron da za”a Raba Kafin Daurin auran Imran kuwa Yusuf da Sagir na rike dashi kamar wani mai Laifi ransa ya baci da hakan ya Kallesu yana Fadin”Wai meye haka kuke wani Rirrikeni kamar wani Barawo..?
Yafada yana kara Dakuna Fuska Sagir ne yace”Saboda munsan Halinka Za”a iya nemanka awajen Daurin auran nan a rasa..!
Wani Mirmishin Takaichi ya saki kafin yace”Rubbish..Dilla Malamai ku Sakeni na Rantse da Allah in nayi niyyar Tafiya ba wanda ya isa ya Hanani..Daman bazan je ko”ina Saboda Abba Shi kadai ne yake iya Takama Ra”ayi Burki..So please let me go.Nasan abunda nakeyi.!
Yafada Cikin bacin rai jin haka yasa Yusuf yace su sakeshi Tunda ya Fadi haka ba inda zashi sun sakeshi yana ta Hararansu kamar ya Dakesu haka yake ji ba karamin Cutar Rayuwarsa akayi ba wlh ayadda yake fama da kansa Din nan ace za”a kara Dauramai wani Nauyi..? Ina Wlh bazai Dauka ba su dai Daura auran ai Alhakin komai yana Hannunsa ne yaga ta yadda Zai zauna da wannan Shegiyar yarinyar mai kama da uwarta.
Sai da aka idar da Sallar azahar kana aka kara Sanar da Daurin auran Daman kuma Tun safe Daddy yazo ya sanar da limamin masallacin akwai Daurin auran Jikokin Marigayi Alkali Hamisu Dukku.
Mutane duk basu Tafi ba Daman masallacin ana cika sosai nan su Basheer suka tsshi suka Fara Rabon Dabino da Goro,suna gamawa aka Fara Gabatar da Neman aure Daddy shi ya Biya Sadakin Imran Naira Dubu Dari Cif,Baffa Kabiru ya Umarci Liman Daya bada auran Daddy shi ne Uban ango shi ya karbi Auran Sajida Kabir Hamisu Dukku Yayinda Daddy ya Karban ma D’ansa Imran Abubakar Malami auranta kan Sadaki Dubu Dari lagadan ba ajalan ba.
Lokacin da aka Tabbatar da Daurin Auran sai da Imran yaji kansa ya Saramai Bakinciki kamar yayi kuka Babban Ci bayane ma ace an Taba Daura mai aure da wannan Yarinyar Har Abada bazai manta da wannan Ranar a Sahun Ranakun bakincikinsa ba.
Bazai iya Zama acikin masallacin ba Shiyasa ya Fito ya saka Takalmi kenan sai ga Sagir ya Fito rikosa yayi ganin Mutane Tundaga Ciki suna ta gaisawa dasu Abba kowa na Wurga idon ganin Ango Yusuf ne ya Hangosu Daga Waje ya nunasa nan fa Mutane ke ta zuwa da sun zo suna kokarin mikama Imran Hannu sai ya Kara Hade rai ya Kauda kai Hannayensa na Goye a bayansa ko Fito dsu bai yi ba Sagir ya bari da karban Musaban yana kuma amsa Fatan Alherin dinsu.
Da kafarsa yake zungurin Imran Wanda ya wani Dauke kai kamar ma baisan me ya aikata ba Mutane sun zata ma Sagir ne ango Imran abokinsa wasu Da dama sun tafi da Fadin kai Abokin angon nan bai da Fara”a Ko kadan shi kuma ko ajikinsa Domin tsayuwarsa a wajen ma ba karamin Takura bane ga Rayuwarsa yau Darajan Abba kadai akaci da ko Sama da kasa zasu hade bai ga Uban Daya isa yayi mai abunda akayimai yau ba.
Gajiya da Zungurinsa da Sagir yake yayi ya Wurgamai Harara yana Fadin”Mallan Lafiya..? Kafa isheni ka mtsamin Kafin na Sauke bacin Raina akanka Wlh yanzu ka tsinci kanka cikin wannan Kwalbatin Dake gefenmu..!
Imran ya Fada yana Nunamai kwalbatin da baki Sagir ya juya yana kallon Kwalbatin cike da kwata da Sauri ya matsa Yabar Kusa da Imran din Saninsa Wlh zai iya aikata Abunda ya Fada Mirmishin Fatan baki Imran ya saki Kafin murya kasa kasa yace”Better for u..!
Hararansa Sagir yayi saboda yajisa Kafin yace”Kaifa baka da Mutumci Daman na sani..Kana ta wani cin mgani Gata Daada tayi maka ta aura maka wannan Santaleliyar Budurwa batare da ko sisinka ba ya kamata ma ka Gode mata ne ba wai kazo kana wani Daure Fuska kana wani yamutsa Fuska kamar kaga kashi ba..!
Imran ya kallesa galala irin kallon Are u Mad..? Karkace kai yayi yana Fadin”Nace tamin gatan ne..?Ko Daadan Uwata ce..?
Yafada yana Tsatsare Sagir da Mayun Idanuwansa Cikin mamaki Sagir yace”Ikon Allah Ita Daadan..?
Cikin Takaichi ya saki karamin Tsaki yana Fadin”Eh ita ai ba uwata bace..Bani ta Haifa ba bata da wani iko akaina..Abba ne Da’nta meyassa shi batayimai gatan ba..? Ai naga shima bai da mata dashi tama wannan gatan bani ba..Kuma Duk Cikin Tarin Jikokinta sai ni ta Zaba..!Wato nine Maraya Uwata ta mutu Dole a Dinga Walagigi da Rayuwata to ban Dauka ba Wlh..Koda nayi Rashin Uwa baisa na Rasa kimata ba nasan Darajan kaina da Mutumcina saboda Haka ni Daada batamin gata ba wlh sai ma Kokarin Takurama Rayuwata Datayi kada ka kara cewa wai Daada tamin gata ni ban gani ba kai koma gatan tamin ban gode ba domin ban ce ina Bukata ba..!
Ya Karishe Fada a Fusace kafin ya Tada Iska ya wuce Fuu kamar zai Bangaji Sagir yayi Saurin mtsawa yana Binsa da kallo kafin ya Girgiza kai yana Fadin”Kin auri aiki yarinya..Imram..Imran ba kanwar Lasa bane..!
Fitowa kawai su Abba sukayi basu ga Imran ba Sagir yace ya wuce gida suma Daganan gidan suka Wuce Tare da wasu Mutane saboda Walimar da sukace zasu suyi.
Suna zuwa Haraban gidan suka iske Imran na saman Motan Yusuf yana ta Busa Sigarinsa ya Cire Rigar jikinsa Daga shi sai Vest ya kwabe Hula wai ta Damesa,Sai da yaga Abba ne yaji kunyar Ya Saki Taban ta Fadi kasa ammh ko ganin Baffa Kabiru da Khamis ba sa ya Fasa Abunda yake yi ba,Baffa Kabiru da Khamis Takaichi Duk ya Cikasu na ganin irin Mijin da Sajida ta aura Mutum Har Mutum ammh ba kyan Hali haka Khamis ke Fada acikin Ranshi.
Abba ne ya mikama Imran din hannunsa yace ya bashi Kwalin Sigarin da makunninta kafin ya Sabamai Dole baida yarda zai yi ya saka Hannu acikin Aljihun wandon Dake Jikinsa ya Dauko Duka ya Mikama Abba ya karba yana nuna ma Daddy,Kai kawai suka Kada acikin Ransu suna Fatan Allah ya gyara Kayanshi Domin shiriya tana wajen Allah ne.
Ganin haka yasa Imran bai Tsaya ba ya Kwashi Rigarsa da Hulansa ya wuce Cikin Gida yana wannan Takun nasa na Sassarfa afalo yaci karo Dasu Basheer su Sagir gasu Inna Maimunatu suna ta Hayaniya jin an Daura auran Sadaf sadaf ya wuce kafin a gansa ya shige Dakin da suka Sauka shida Sagir ya Rufo kafa Gabadaya ya Kwabe wandon Jikinsa Da Vest din ya Rage dagashi sai Boxers ya haye gado ya kwanta bayan ya kunna Fanka Zafi duk ya ishesa Yana jin karkashin Zuciyarsa na wani kuna Bini Bini ya saki Tsaki kamar wani Tsaka.
Achan Falo kuwa Tunda Labarin Daurin auran yazo Cikin Gida Mami Asma”u ta shige Daki tana ta Rizgan kuka yanzu Shikenan Tsagerin yaron nan yayi nasara akanta ina bazai yuyu ba Tunda aka nuna mata iyakarta itama sai ta nunama kowa nata iyakar Sai a Dauki Sajidan akaimai Tagani Indai Tana Raye ba wanda ya isa.
Sai da taji kukanta ta gaji kana taje tayi wanka ta Shirya Fuskarnan duk ta Kumbura ba wanda yabi ta kanta su Umma duk suna Falo ana ta Hidima Bata ga ko Daya Daga Cikin ya”yanta ba,Sajida Tana Dakin Daada Umaima tana Tare dasu Munari Khamis kuma suna Haraban Gidan inda suke Walimar su nacin Abinci isu isu da sauran Mutane an Shimfida manyan Dardume suna zaune suna cin Abinci ga ababen sha nan Birjit sai wanda ka Zaba Imran ne kadai bashi a wajen kuma ba wanda ya Damu Dashi Sanin Halinsa.
Bangaran Amarya Sajida kuwa tana jin Gudan Inna Maimunatu Tana Fadin an Daura aure taji wani sukuni Tare da Salama ya Shigeta,abaya kafin Taga Imran tasha Mafarkin yadda Kayattacen Bikinta zai bar Tarihi a Nageria sai dai ganin Imran da Faruwar komai ya Sauya mata Duka Tunaninta Abunda ya Faru bai Dameta ba sai ma wani Salama Dataji na Zamo warta Mata ga Imran
Ya”yan Inna Bintalo ne suka zo suna ta Daukan Hoto da Sajida su Hamida,anan ciki aka kawo mata Abinci Tunda Daada ta hanata Fitowa Daga Dakin ballatana su Hadu da Mami Asma”u Alokacin ma ita kanta Sajidan bata kaunar ma taga Mamin Saboda tasan har yanzu da aka Daura bazata Daina adawa da wannan auran ba ita kuma ayadda Lokaci Daya Soyayyar Imran tayi mata kamun kazan kuku Tana Daidai da tayi Fito na Fito da wanda yace zai Rabata da Abunda take so..!
Bangaran Inteesar kuwa tun Safe tana Kwance gabadaya ayyukan da akayi da Ifacen ifacen da akayi ta yi acikin Gidan baisa ta Fito ba kanta Nauyi yayi mata Kirjinta na mata Zfi duk sanda ta Tuna da Imran zai auri Sajida ba yadda su Munari basu yi ba kam Tatashi Tayi wanka taci abinci tayi banza Dasu,gajiya sukayi suka kyaleta,su dai bayan sun gama aiki suka shaba wanka da kwalliya Har da Umaima Data shige Cikinsu suna ta Daukan Hotuna Munari ita ko ajikinta Domin ba wani Sanin Sajidan tayi ba,sai dai ta Tsausayamata Domin har ga Allah an bata aiki babba na Aura mata Ya Imu.
Inteesar tana daga kwancen Munari tazo tana Fadamata an Daura aure gasu Ya Basheer chan sun dawo Sai Inteeser taji kamar Zata Mutu sai Hawaye Sharr Hankalin Munari ya tashi ita taje ta Kira Umma Duk ta Rikice ta Rikita Umma itama ganin tana kuka yasa ta zata Jikin ne basusan Hakikamin me ke Damunta ba ita kanta bata sani ba Ballatana ta Fada musu sai dai Kirjinta nayi mata wani Zafi kukan datake yi shine kadai Salamanta.
Umma ce ta Lallabata tarakata Tiolet tace tayi wanka ta saka Munari ta Hado mata Tea saboda tasha Cikinta ya Warware,Inteesar na Shiga Tiolet din ta Zauna saman sit din Cikin Tiolet din ta Fashe da kuka yi take ba kakkautawa kamar wacce akace wani nata ya Mutu kanta yana Sara mata ga Nauyin Kirji,tana cikin kukan Wata Zuciya tace mata”To ke Inteesar kukan me kike yi..? Ina ruwanki Domin yayi auransa bai kamata kizo kina saka kanki acikin Damuwa ba Har kina kuka ba Tunda ba sonshi take ba..,!
Sai wata Zuciyar tace mata”Ko bana son shi ai dan”uwana ne bazan so mai abunda baida kyau ba..Sajida bata Dace dashi ba Shiyasa nake Damuwa..!
Tafada acikin Ranta tana jin yes wannan ne Dalilinta,Da wannan Tunanun ta Lallashin kanta ta yi wanka ta Dauro alwala ta Fito Umma da Munari na Jiranta,mai ta shafa kafin ta saka Doguwar Rigarta baka Kirar Armani,Munari ta mika mata Tea din tasha Umma ta balla mata mgani ta bata tasha ta Dora Tea din Daman tana jin yunwa Cikinta sai kuka yake,Tagama sha sai Zufa alamun dai ta Fara samuwa ganin haka yasa Umma ta Fita ta barsu,Munari ta Shimfida mata Darduma ta Fita ta barta Bayan ta Tada Sallah.
Tana Fitowa Falon Lokacin su Abba na Shigowa nan suka gaggaisa dasu Inna Maimunatu suna ma juna Fatan Alheri da Fatan an kulla alheri kafin su Dunguma Zuwa Dakin Daada dake Cikin Dakinta taci kwalliya bakinta Har kunne Casbaha na Hannunta tana ta Lazimi ranta Fes Koyau ta Mutu Burinta ya cika.
Ganin Shigowar ya”yanta nata yasa ta Kira Hamida tace tazo ta kai Sajida wajen Mahaifiyarta haka kuwa akayi ita ta rike Hannunta zuwa Dakin da Mami Asma”u wacce bakin ciki kamar ya kasheta.
Saboda Takaichi takasa ma cema Sajidan komai kallonta kawai take tana kyafci tana Girgiza jiki da kafa,Wayace a Hannunta tana ta Kiran Baffa Kabiru bai Dauka ba suna Gaban Daada,bazai iya Daukan Wayanta ba yasan Rigima ce kwance a wajen Mami Asma”u.
Inteesar Dole yasa ta Fito Falo Tunda Munari sun mtsa mata sai ta Fito,ita kuma Ranta baya mata Dadi,sannan bata son ta Hadu da Khamis yana ta Damunta da waya da Sako ko ta kansa batabi ba..
Koda ta Fito duka an hadu a falon Mazan da matan su inna maimunatu dai suna Dakin Daada su Aneesa ne dasu Anty Safiya kowacce tana Tare da mijinta sai su Munari dake Hotuna,Khamis na Dakin Mami yana bata baki har ya gama mgana kanzil batace ba,har yagaji ya Fito nan yayi Tozali da Inteesar ya kafeta da ido yana kallonta Yarinyar nan tana bashi Wahala sosai gabadaya soyayyarta ya gama kasarashi sai dai tanayin wani abu kamar bata gane ina ya Dosa ba..
Suna Hada ido ta Hada rai ta kauda kanta kamar bata ganshi ba ta Dauko wayarta tana Dannawa ba Domin tana wanu abu ba Imran take Tunani bata gansa ba wata Zuciya tace”Ina Ruwan ki kumi dashi..Yanzu ai baida Lokacinki Tunda yayi aure. !
Tuna haka yasa taji zaman Wajen ya gagareta tatashi tana Shirin Tafiya Zainab din Inna Maimunatu ta jawo tace suyi Hoto bata da yarda zatayi Dole ta tsaya Khamis kuma yana binta da kallon Sha”awa da kauna ya Nufi wajen su Basheer dake zaune suna Hira gefe kuma Matayensu Sa”id ne sun ci gayu suna ta Hira gwanin Sha”awa.
Suna ta Hotuna Kada Munari da Hafsah suji Labari,Munari ce uwar kankaba tace afito musu da Amarya suyi hoto Hafsah tasan Hali bata je ba Umaima ce taje ita dasu Hamida suka Fito da Sajidan Daga Wajen Mami Asma”u wacce ke cika tana batsewa kala bata kara Furtama kowa ba Bata so tayi mgana saboda in ta Bude baki tace wani abu zata iya Fashewa da kuka kuma Faruwar hakan kamar Imran yaci nasara akanta kenan Baffa Kabiru take jira shine Zata saukema gabadaya Bala”in Dake Cinta.
Sun Fito da Sajida nan Falo waje ya Kaure da Gudan ga Amarya su Sa”id na Dariya Yusuf da Sagir suna kallon Sajida sukace masha Allah tayi kyau matuka,Inda Imran mai Wayau ne basu ga aibun Sajida ba mace duk inda ake neman takai,Khamis yazo ya Rumgumeta ganin Inteesar a wajen Har dashi ya Dinga shiga Hoton Bakinciki ya cika Inteesar tana so ta gudu Munari ta Hanata,Ga Waleedan Anty Aneesa ta makalemata sai ta Dauketa Kallon Sajida take tana mamakin ganin ta ko Damuwa acikin Idanuwanta Fuskarta bayyana wani Damuwa ba,sun kalli juna ido Cikin ido kafin kowa ya Dauke kansa,Abunda ke bama su Inteesar da Hafsah mamaki ganin Sajida tana mgana da Munari har da mata Dariya Inteesar Ranta wani kuna yake yi wato Saboda ta auri Dan”uwanta Ita tasan Darajanta,Inda ma mutane zasu Lura Hawaye ya cika kwarmin idanuwanta Tayi saurin Sharewa kada wani ya gani.
Sun cigaba da yin Hotuna har Da su Sa”id da suka taso ana ta Family Picture,Khamis sai da yasan yadda yayi ya dawo kusa da Inteesar ya Riko Hannunta bata zata ba da Sauri ta Dago tana kallonsa Gira ya Dagamata Lokaci Daya yana marairaicemata kamar zai yi kuka kwace hannunta tayi tana Hararansa Haushi Rike mata Hannun da yayi taji Har Cikin zuciyarta.
Mtsawa tayi daga kusa dashi ta koma Kusa da Hafsah ganin munari na kusa da Sajida,wacce ke ta wurga ido tana Neman inda zata ga Imran bata gansa ba bata so kuma tayi mgana aga Zakewarta sai tayi shuru da bakinta.
Kiran Sallar La”asar da Fitowarsu Abba ya Dakatar da Hotunan suka ce mazan su fito su tafi masallaci matan kuma suma suyi sallar acikin gida.
Baffa Kabiru sai Lokacin ya Shiga Inda Mami Asma”u take tana ganin Shigowarsa Rauninta ya bayyana ta Mike ta isa gabansa Tana Fadin”Yanzu Kabir kana gani aka Daura ma yarka aure da wannan Dan iskan yaron.?Kana ji kana gani aka yi ma yarka auran kaskanci ammh ka kasa cewa komai ko Kabiru..?
Tafada tana Fashewa da kukan Takaichin Dake Cinta acikin Zuciyarta Saman kirjinsa ta fada Tana Dukansa Riketa yayi yana jin pain din Datake ji Cikin Lallashi yace”Ma”u ya zan yi..?Ni ban isa na Tsallake Umarnin Daada ba..Kada kuma ki manta Abubakar Dan”uwana ne Dana saki Nono ya kama Taya zan nuna ina gudin hada jininsa da nawa..?ya zai ji acikin Ransa..? Ammh wlh ni kaina Ma”u banso wannan Hadin ba Tunda kikaga ban yi mgana ba bani da Mafita ne acikim al”amarin..!
Ya karishe Fada yana riketa acikin jikinsa bata iya cewa komai ba sai kuka Bakimciki ya cika ta gani take Cika bakinta ya zama na banza Daada ta gama Cutar da ita cutar da bazata manta ba Har Abada.
Dakyar ya iya Lallashinta Tayi shuru da cewa bari yaje suyi salla su dawo zasu yi mgana kana ta yarda ta sakeshi ya Fice ta koma ta zauna tana Sharan kwallah jira take yazo suyi mgana Gobe goben nan bata kaunar ta kara Kwana agarin Dukku Har Daadan bata kaunar gani Zata Tarkata ya”yanta ta tafi dasu Sai taji kuma ta gani wanda ya isa yazo ya Dauki Sajidan Wlh sai dai ya gaji da auran ya Saketa tana Fatan Tsautsayi ya sa ya kwaso kafafunsa zuwa Abuja A nan ne Zata nuna mai ikon Barrister Asma”u..!
Imran sai bayan da kayi sallar La”asar kana ya Farka Daga Barcin Daya kwasheshi cikin kasala ya Mike ya Fada Tiolet ya Dauro alwala yazo ya saka Riga da wando baki da Fari,kana yayi Sallarsa acikin gida tunda an riga anyi Sallar,sai Lokacin ya Fito Daga Dakin Falon ba kowa duk suna Dakuna suna Sallah Hafsah kadai ya gani Data gaishesa Sai da ya juyo yana kallinta asaman Lebensa ya amsa kafin ya kada kai ya Fita Haraban gidan Inteesar yake son gani bai ganta ba Tun dazu din nan Daya hangota ta Boye kanta.
Yana Duba wayarsa su Basheer suka shigo gidan sun dawo Daga masaalaci
Ganin su yasa ya koma Chan gefe yayi kamar yana waya saboda bayason mgana da wani suna ba wanda yabi ta kansa Harta kuwa da Sagir suka Shiigewarsu cikin Gida sai da yaga Shigarsu kana ya Sauke Wayar Daga kunnensa ya Lalubo lambar Inteesar ya Tura mata sako.