GIDANMUNOVELS

GIDANMU 1 & 2 COMPLETE

GIDANMU HAUSA 1 & 2 COMPLETE

Janafty
3/22/22, 23:14 – Ummi Tandama😇: GMB2🅿ï¸?9

Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488

After 1 week
Kimanin Sati Daya kenan da zuwansu Dukku,Imran har zuwa wannan Lokacin bai warware ba Ya daina ma kowa mgana Abba ne kadai daya zama Dolensa yake Fitowa ya gaishesa da Safe,duk da kowa ya sanshi da Rashin son shiga jama”a ammh wannan karon abun nashi ya Taba zuciyar wadanda ke tare dashi,ganin ko Masallaci ya daina zuwa na kusa da Gidan su Sagir sai ya koma zuwa wani karamin masallaci na chan gaban gidansu Tunda suka Dawo Daga Dukku ba wanda yaji kalma Daya Daga Bakinsa bayan gaisuwa.
Abun ya damu Yusuf har sai da yayi ma Abba mgana Domin har ga Allah shima yaga baiken Daada akan wannan Hadin a yadda Imran yake Gudanar da Rayuwarsa auran Hadi bai Dace dashi ba kuma bai Chanchanta dashi ba.
Kamata yayi ya samu wacce yake so tana sonsa ahakan Za”a samu Riba kan Riban abunda ake nema ammh a yanzu da kunci ya kara Dabaibaye Rayuwarsa zai iya koma Fiye ma Imran din da suka sani abaya,Shan Taba kila Har ya Fara kora wasu kayan Mayen in ya Damuwa tayimai yawa Har acikin Ransa bai da yadda Zai yi ne ammh Tabbas Hadin nan na Daada ko alama bai kwantamai ba Duk da Sajidan bata da wani aibu sai dai A kallo Daya da yayi mata yasan bazata iya Zama da Imran ba bata dace dashi ba.
Abba Dayaji bayanan Yusuf shi kanshi ya gamsu kuma Daman yana Cikin Damuwar haka din ne sai dai bai bari Yusuf din ya Fahimceshi ba Sai ya nunamai ya kyalesa babu Abunda zai faru dashi Fushi yake na wani Lokaci in Abun ya sakesa zai Wartsake,Ya nuna ma Yusuf kada ya sake ya Tari Imran da wata mgana Saboda bayaso kuma abubuwa su Dawo baya Yasan Halin Imran ciki da Waje shi ya Haifesa ya kuma Tabbata shine kadai weekness din Imran in ba shi ba bai ga wanda ya isa ya Rika Lamkwasasa yadda yaga Dama ba Shi kanshi yana jin Tsausayinsa sai dai Abun nan da Hausawa kan Fadi kaki naka Duniya tasoshi hakan da yake yi Shine Daidai in Imran ya gane yana Tsausayinshi to zai yi amfani da wannam Damar yayi abunda yake so Shi kuma bazai barsa ba Yana da Sanyin Hali yana son Mahaifiyarsa da ya kwashe Fin shekaru uku bai sata a ido ba karon Farko bayan sun Hadu ta bada Unarni kan Abunda ya Haifa bai isa ya Taka wannan Umarnin ba ko shi baya Taka Umarnin Daada ballatana Abunda ya Haifa Shiyasa Daga shi Har yusuf suka Zura Mai ido Bawanda yace mai kala kamar yadda Shima bai damu yace dasu wani abu ba..
Ammh acikin Ransu suna Fata damai addu”an Allah ya sassautamai koma Miye ke Damunsa acikin Zuciyarsa.
Bayan Abba da Ya yusuf Inteesar ma tana Cikin Damuwa wannan yanayin da Imran ke Ciki Tunda suka Dawo bai kara yarda sun hadu ba Tayi ta Turamai sako zai gani zai karanta bazai bata amsa ba,Datagaji sai ta Fara Kiransa nan ma sai ta gaji da Ringing bazai dauka ba Daga karshe sai ya Kashe wayarsa Inteesar ta shiga Damuwa sosai na Rashin Sanin Halin Dayake ciki ga Karatun makaranta yayi Zafi sai ta fara Rama atsaye gata Daman ba wani kauri ba,Duk yadda taso su hadu hakan bai samu ba Zasu kwana su Wuni acikin Gidan nan ko Gilmawarsa bata isa ta gani ba Tunda suna Raba Raba ne,Yau su kwana a nan gidan Gobe gidan Mama saboda ta Saba da Inteesar tafiyarta zai saka ta ji Kadaici ya Dameta shiyasa suke Raba Raba ita da Munari da suka kara Shakuwa kamar wasu yan Biyu Daya bai iya Boyema Daya abu sai dai Inteesar ta Boyena Munari Damuwarta kan Imran ko dataga Tana ta Ramewa Data mata mgana sai ta ce saboda Stress din Karatu ne.
Inteesar Zuciyarta Zafi take tana da Raunin Data kasa Daukan Lamarin Imran yana bata Wahala batare data san Dalili ba Zuciyarta na Zafi Wani Lokaci Jikinta ya Dauki Dumi Zata iya Jure komai banda Fushin Imran Dafi ne gareta Ta zauna Tayi ta kuka ita Kadai in abun ya Dameta sai kuma Daga baya tayi wani Tunanin Kila ya Daina kula tane saboda Sajida yayi auransa me zai yi da ita yanzu..? Inteesar batasan Soyayya ba Domin bata taba yi ba ballatana ta gane itace ta mata Mugun kamu sannan bata karance karance Social median ma Bata wani Dameta ba,shiyasa ta gaza Fahimtar wani Hali take Ciki kamar yadda Ego din Imran yaki bari ya Fahimci Inteesar ta gama Mamaye Zuciyarsa da gangan Jikinsa ta yadda bazai iya Gudanar da komai acikin wannan Rayuwar ba sai da ita.
Abunda Inteesar bata sani ba Imran yafi ta Shiga Damuwa ya fita Wahala akanta,Sai dai shi Namiji ne kuma Shi din bamai Rauni ne bane ko Rauninsa ya bayyana baya yadda wani na Kusa Dashi ya Fahimta.
Atsakanin nan yadda yake azabtuwa da Rashin ganin Inteesar ko Abunda Daada tayimai baya Damunsa Saboda yagama da wannan Shafin Tuni Ransa ne yake bace tun Dawowarsu Daga yaji bayason kowa kusa dashi yafi son ya zauna shi kadai Daga shi sai Busa Hayakinsa,Bai taba Tunanin Rashin ganin Inteesar zai zama Cuta garesa ba sai alokacin,Fushi yake da ita Fushi mai Tsanani Saboda In ya Runtse idonsa ganinta yake Khamis rike a Hannunta sannan kuma yana Tuna kalamansa na ita din tashi ce in ya Tuna Hakan sai yaji har ita bayason gani kwata kwata..
Yana ganin Sakonta kuma yana karantawa Domin sune suka Zamemai Tamkar Rigakafin Samun Saukin Wutar da Zuciyarsa ke ciki,In bata Turo ba Wuni zai yi yana Duba Wayarsa yana sakin Tsaki in bata Turo ba Haka zai ta maimata sakonta na Baya wani yayi Mirmishi wani yaji Haushi,in kuma ta Turo ya Dinga maimaitawa kenan kamar yadda yarinyar ta damu dashi matuka Sakonta Duka iri Daya ne.

“Ya imu kana lafiya ko..?

“Kaci abinci..? Don allah ka Rika cin Abinci bana so ka zauna da yunwa..”

“Fatana dai ba rashin Walwalarka Laifi nayi maka ba ko?

“Ya imu plz am sorry in wani Laifi nayi maka kada ka Hora kanka da Zaman kadaici..”

“Ok..Naji..Plz kada rika shan Sigari..bana son watarana na Rasaka I miss u..”

Iraren sakonta kenan sakon da sukasa Nishadi,Suke Debemai kewa Cikin Satin Dayan da yayi yana Boye mata kanshi,Ko Sagir bai kara yarda sun Hadu ba Tun bayan Dawowarsu ya Kirasa a waya yaki Dagaewa Kila Shima Fushi yayi bai kara Kiransa ba kuma bai nemesa ba Shima yafi son haka,Yafi so ya gama Da Kansa Tukunna kafim yazo kuma yaji da Damuwar wasu kuma.


Abuja

Labarin mutanen Abuja Hajiya Mami da ya”yanta wanda tunda suka koma bata barsu sun zauna Lafiya ba haka take ta fada Tana fadin Baffa Kabiru yayi Shuru Danginsa sun ci Zarafinta ita da ya”yanta tayi ikirarin wlh Sai ta Raba auran Sajida da Imran yarta bazata taba zama da Dan”iska ba.
Baffa Kabiru dai bai ce mata komai ba Khamis ne ke bata baki shima ta Hada dashi ta Balbale tare da Gargadi mai Girma kada ta karajin mganar Inteesar a bakinsa bata kaunar wannan Hadin kwata kwata,Ita ce nan Mahaifiyarsa ita Zata zabamai da matar Daya dace da shi.
Anan gabar kan Baffa Kabiru yayi mgana yace mata kada ta shiga Hurumin da banata ya yadda Imran bai Dace da Sajida ba,Ammh Inteesar bata da wani aibun da Zatace Khamis bazai aureta ba Kuma Diyar Mustapha ce suna da kyakyawan alaqan Jini da yan”uwanta da bazai ji Kyashin Hada Zuru”a dashi ba.
Mami Asma”u na jin haka ta Daka Tsalle tace bazai sabu ba bazata bari su hade mata kai shi da Danginsa ba,Sajida an mata auran kaskascin Auran da bazata iya Daga baki ta Fadeshi Cikin Dangi ba Ta tabbata masu mata Dariya suna da yawa sannan kuma shima Khamis din sai ya kara Zama nasu ta gama Wahala Dashi ya kawo yanzu sai ya zama Surikin Mustpaha da Salaha ita ta Zama yar kallo kenan bata yarda ba bata Amince ba kuma ba wai tace yarinyar nada Illah bane kawai Hadin ne bai mataba bata Ra”ayi kuma Tunda aka mata fim Karfi kan Sajida wannan karon bazata kara yarda ba.
Baffa Kabiru dai bai biye mata ba Sanin Halinta sai ya kyaleta,Sai ta koma kan Khamis tajamai kunne sosai na kada ya sake taji wata mgana kan Inteesar ta kara tashi Daliln Dayasa yaji Zaman Abujan ya isheshi kwana Biyu yayi ya koma Anambara Sai dai kafin Tafiyarsa sun yi mgana da Baffa Kabiru sosai ya bashi Daman Indai yana son Inteesar ya Nemi soyayya da yardanta yayi mai alkwarkn zai shigemai gaba sai ya aureta da wannan kwarin gwiwan ya koma Bakin aikinsa da yakinin zai samo kan Inteesar da yardanta Tunda Dad ya shigemai gaba Mami ba Damuwarsa bane in ta gama bambaminta shikenan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button