GIDANMUNOVELS

GIDANMU 1 & 2 COMPLETE

GIDANMU HAUSA 1 & 2 COMPLETE

“Kin manta dani ko..?

Alhalin fa ko jiya ta Kirashi sun yi da Daddare data kirassa yaki Dauka Saboda suna Tare da Khalil sai da ya Turamata sakon.

“Oya ki kwanta ki barci..Bana son Damu..!

Shine ne wai yau ta manta dashi so yake yajata da Zence.
Bata kai ga Turomai amsa ba Kiran Sagir ya shigomai ya Dauka suna mgana yana Tambayansa yaushe Zasu dawo yace bai sani ba,basu wani dade suna mgana ba ya katse kiran Saboda Hankalinsa baya kansa yana Wajen Inteeaar ne.
Illah kuwa yaga Sakonta Cikin Shagwabarta Duk da baya ganinta tace.

“Laaaa…Kai ya Imu nice ma na manta Dakai kai da kaje Lagos ka manta Dani kaga yanmatan Birni..Au koda yake ai kana da Matar Abuja Sajida..”

Sai da ma yaga Sakonta ya Tuna da Wata Sajida Tsaki yaja jin tama batamai Mood dinsa Raini yagani Kirkiri Tsaakaninsa da Inteesar Wato Shine ma ya samu yanmata ko..?kiranta yayi kai tsaye tana Dauka ya Fara Fadin”Kin raina ni ko..?Wato nine ma na samu yanmata ko..?Ni sa”anki ne Intee..?
Yafada Cikin wani Salon daya gama Kashe mata Jiki Gabadaya sai ta Fara mganarta Cikin Shagwaba Tana kanunun kuka Maimakon ya Dakamata Tsaawa yace ta Daina sai ya kasa ya samu kansa da jin Dadin Duk Abunda tayimai shi kanshi baisan Yaushe ba yadai samu kansa yana Biye ma Duk wata Tabaranta Wai kukan Shagwaba take yi basu dawo ba alhalin yace mata kwana Daya Zasu yi sai ga Imran yana mata Rantsuwan Wlh ba Laifinsa bane Daga su Daddy ne.
Soyayya mai sauya Mutum ta Sauya Imran bai sani ba ko aikin Daya amince zai koma Saboda Inteesar ne,yasan Zataji Dadi sosai,Kamar ya gayamata sai ya fasa yafi so ya bata Mamaki ne suna cikin Wayar Khalil ya zo Inda yake yana ganin haka ya katse kiran,Sai gashi ta kara Kira Bai Dauka ba sai da ta katse ya Tura mata Sakon

“Kije kiyi karatu…We tok Later bana Gida ne..”

Haka ya Rubuta kafin yabi Khalil wani dan Cafe inda suka Siya Coffea da lemu Anan Imran ya siya Sigari Khalil yaji mamakin ganin Imran na shan Sigari har sai da ya Furtamai Bai ce komai ba amsa Daya ya basa da cewa Life kenan.
Imran yasha Sigarinsa sosai,Saboda Tunda sukazo bai shafa ba,Har da Guzurinta yayi Khalil sai mamaki yake da Tsausayin Domin ya Tabbata Rayuwace ta maidasa haka abaya ko Kusa da ita baya zuwa.
Da suka koma gida basu ma Kowa bayanin inda sukaje ba Suma ba wanda ya Tambaeyesu..
Sai gashi bakin da zasu yi kwana daya sai gashi sai da suka kwana Hudu Tunda sai da suka jira Lurwanu ya Dawo da Iyalansa,Matan sa Biyu da yaya Bakwai irin auran Wuri ne ayi ta Tara ya”ya suka shige BQuaters Matar Buba da ya”yansu suka Tayasu gyara Komai har Cikin Gidan ma suka share suka Goge suka gyara kayan wasa kuma nasu Imran dasu Anni duk afito dasu wadanda bazasu Mori ba aka Zubar masu kyan suka Dauka sauran kuma zasu Sadakar dsshi ga Mabukata ana Gobe zasu tafi acikin Gidan suka kwana Saboda an gyara komai,Daga Gidan Dr.Isa Ali Argungun ake kawo musu Abinci Washegari Tun Safe suka Dauki Hanya bayan Abba da Dr Isa sun karbi Lambar juna haka ma Khalil da Imran sun Rabu kan in an nemesa zai gayamsa Insha Allahu.
Sai Cikin Dare suka iso kaduna anan suka kara kwana Sai Ranar Alhamis suka Dawo Kano,abun da ya bama Abba Da Daddy mamaki Har sukayi wannan Tafiyar Baffa Kabiru bai kira yaji Ya akayi ba sai dai sune suka Kirasa Daada kuwa Hankalinta kwance Koda yaushe Tana Waya da Malami Jininta ya Daina Hawa sai Dai ma yana ta kara Sauka ne.
Abba ya wakilta Yusuf ya Turama Daddy duka CV sa na Takardunsa Shi kuma ya Tuttura ma abokansa na nan Jami”ar Buk suka kuma Tabbatar da za”a dace Daman ana neman Wadanda suka kware kan Abubda Malamin ya karanta ya jira Lokaci kawai za”a kirasa.
Intee tafi kowa Murnan Dawowarsu daman Rashin ganin Imu duk ya Ramar da ita da kuma Gidan ba Dadi basu Abba Mama bata nan Taje Kaduna Bayan Tafiyan su Daddy Lagos jikin Inno ya Motsa sai sukayi mgana da Umma Maman ta Shirya tatafi Wajen kwananta uku kenan Daman Tun kafin tatafi suka dawo nan Gabadaya Saboda Taya Anty Safiya Zama.
Har ya dawo basu Hadu sunyi dogowar mgana ba sai dai sukan Hadu su kalli juna tayi mai Dariya shi kuma ya Hde rai ya Harareta,Sun Dawo Alhamis Ranar asabar da Daddare bayan sun gama Dinner gabadayansu Imran daman ba Zaman Dinner yake yi ba Tea kadai yasha sai gashi ya Fito Daga Daki ya Duka gaban Abba yana Fadamai Gobe yana so yaje Dukku.
Sun ji mamakinsa sosai Abba cikin mamaki ya kallesa yana Fadin”Dukku..?.
Kai ya gyada batare da yayi mgana ba Ya Yusuf dake Zaune gefen Abba ya kada kai yana Fadin”Dukku..? kodai Abuja mallam gayamana gaskiya..Kana son ganin Sajida ka Fake da Dukku..,,!
Kamar ya watsamai Ruwan Zafi haka yaji kallon Ya Yusuf yake yana auna in ba Domin shi bane wlh sai ya Duramai Ashariya Saboda Haushin mganarsa.
Inteesar ya kallah Dake gefen Munari da Anty Safiya itama kallonsa take Gabadaya Sai taji Ranta ya baci da aka ambaci Sajida kenan da gaske wajenta Zai je.
Kauda kansa yayi bai ce komai ba Abba na Dariya yace”Ai kamar tana makaranta bata dawo ba..Barsa kila ganin Kakarsa ne ya tasomai in yaje ya Dawo sai ya shirya yaje yaga matar tashi Lokacin ta dawo gida Tunda Ya Kabirun yace min suna Test ne..!
Har Abba ya gama mgana bai Dago ba.
Abba ya kallesa yana Nazarinsa kafin yace”Kwana zakayi in ka tafi goben..?
Dakyar yace”In Dare yayimin sai jibi zan Dawo..!
Abba ya kada kai yana Fadin”Allah ya kaika Lafiya Daada nada manyan Baki..!
Imran yaji Dadi da Abba bai kara Cewa komai ba ballatana ya Tambayessa me zai je yi wajen Daada yana Haararan Yusuf Dake Dariya ya Shige Dakinsa da Haushin Inteesar ta Kauda kai taki yarda su hada ido wai itana nan taji Haushi ne ko..?
Karamin Tsaki yaja yana jin Takaichi ya Riga yagama Shirinsa gobe sai Dukku waya ya Dauka ya Turama Intee Sako.

“Yayi miki kyau Tunda nine kike Turama baki kina kauda kai baki san ganina..!

Ba Dadewa ta bashi amsa da Cewa

“Eh din..Gobe zakaje kaga Amaryanka ina Ruwanka dani..!

Sai da ya waro ido Daya ga mganarta Dariya ta kamsa Yarinyar nan ta gama Rainasa cikin gatse yace mta

“Kamar kin sami ta Abuja zan sauka ko kina da sako wajen Amaryan tawa..?

Ya tura mata Sakon yana ta Dariya Har yana jin Sautinta yasan ya gama Kunno yar shagwaban kamar ya sani Dataga sakonsa sai da Zuciyarta ta Buga Saboda Takaichi da Kishi Cikin Tura Haushi ta Turamai.

“Ka gaisheta..Ango mijin Amarya..In kaga Nawa Mijin ka isar mai da Sakon i Miss Him Khamis Kabir Dukku nake nufi..”

Ai sai nata yafi Zafi Daya sakon nan kamar yayi Bindiga kiranta yayi taki Dauka sai yaji kamar Zuciyarsa Zata Fito Saboda Kishi Wai Mijinta..? Lalle nema to ba sai ya zama mijin nata ya gani ba haka yake ta Fada yana Sakin Tsaki.
Itama chan bangaranta haka tayi ta jan Tsaki tana kunkuni ita kadai Daga Karshe ma barin Falon Tayi,Ta shige Ba wanda ya Lura da yanayinta sai Munari ga Dariya ga Tsausayi..
Tana shiga Daki Ta Fada kan gadi ta saka kuka ranta na kuna Afili ta Furta”To ni ina ruwana ya ma je su Tare tare achan babu Abunda ya Dameni..!
Take Fada Cikin tura Haushi Lokaci Daya ga Hawaye Munari shigowarta kenan taji Abunda Intee ke fada Ssi ta bata Tsausayi bata nuna mata taji ba ta Basar ammh Tana Lura da ita bata wani samu barci ba Bini bini ta juya ta saki Tsaki shi kanshi Imran din Rabi da Rabi ne barcin nasa kowa ya kwana da Takaicin kowa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button