GIDANMUNOVELS

GIDANMU 1 & 2 COMPLETE

GIDANMU HAUSA 1 & 2 COMPLETE

Ranar data Damesa Sai yaTura mata Sakon cewa
“Kin gama Fushin ne..?

Da sauri tace

“Eh nagaji na tuba nabi Allah na bika Ya imu..!

Mirmishi yayi kafin yace mata

“In kin Gama ni yanzi zan fara nawa..!

Aikuwa ya fara nashi Domin Dif ya Dauke mata ya Rataye ta bata ma ganinsa tun 7:30am na safe yake Fita sai 6pm na yamma yake dawowa in kuma ya dawo yana Daki yana aiki Tunda ya siya karamar Laptop Apple Saboda aiknsa kudin nan ne lokacin Bikin Yusuf da Baba Manu ya dawo mai Dasu,Yusuf bai karba ba ya cika ya siya Computer,Sannan Abba yasa Yusuf ya basa kudi ya siya kaya da Takalma tunda har lokacin Akwai kudi a Bankin Nura sannan akwai kudin da suka saida Motocinsu da su ya kara ya siya Suit masu yawa da Takalma da agoguna Saboda yanayin aikinsa.
Mganar aikin Imran har Daada sai da taji Daddy ya Kirata ya Fadamata Tayi ta Saka albarka,Da sukayi ma waya da Abba Tayi ta addu”a Imran din basu samu mgana ba Tunda baya barin Wayarsa a Bude sai ya dawo gida.
Sati Daya da Fara aikinsa Bankin Gt ta mallakamai Gida Mai 2bedroom madaidaicin Falt,da Sabuwar Motar hawa Kirar 4matics kyauta Halak malak,saboda Sadaukarwarsa da da jajircewarsa Sulaiman Ishaq ne ya shigar da Korafin a Chan Sama Board of Directors kuma sanin Waye Imran Abubakar malami yasa akayi approving din mganar aka kuma Tabbatar.

Shakira
3/22/22, 23:15 – Ummi Tandama😇: GMB2🅿ï¸?14

Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488

Da wannan Labarin Farincikin Imran ya dawo gida Ranar Cikin Sabuwar Motarsa baka 4matic da makullin gidan da suka mallakamai Sulaiman ya kaisa yaga gidan dake Anguwar Alu Venue.
Abba Hamdala kawai yake ma Sarki gagara Misali Sai da yayi hawayen Farinciki,haka ya yusuf daya dawo yaga Sabuwar Mota aharaban gidan shi kam ya kasa Boye murnansa sai Faman cema Imran yake Congratulation u deserve everthing Brother,Safiya ma ta tayashi Murna su Munari suna makaranta sai da suka dawo sukaji abun arziki,Ba kamar Inteesar a Farinciki duk da gogan nata yana Fushi da ita Sagir yazo yaga Mota ya shiga ya zauna baki yaki Rufuwa ashe ashe akaai Ranar da zai ga Imu zaune cikin Mota yana Driving ba shakka Rayuwa ta gaji haka kada kuma Kaga Mutum a wani yanayi ka Raina masa Domin bakasan Baiwar da Allah yayi mai ba kuma Dan Hakin daka Raina Watarana shi zai Tsole maka ido.
Imran ya Fadama Khalil wannan kyautar Girma shima ya tayashi Murna matuka da kansa ya Kira Mr Tunde ya Fadamai Duk ya sani shima ya Tayasa murna tare da karin wasu Shawarwari.
Duk wanda ke tare da Imran sai da ya tayashi Murna saboda ya Chanchanta Inteesar ta Test messages ta Turamai Sakonta kuma yagani ammh bai nuna mata ya gani ba wannan Shariyan nasa tana matukar Damunta har ta fara rama barci kuwa sai ta kusa Raba Dare ya kasa Daukanta ammh gogan nata baisan tanayi ba komawarsa aiki yasa ya kara zama Rashin Tabbas Fiye da baya.
Ko sati ba”a Rufe ba Sai ga sunan Abba Jami”ar BUK ta Zana a mtsayin DEEN na Department din Daya fi kwarewa Akai wato Psychology Proffesor ne suka zauna da Daktoci da Deen na Faculty da Deens na Department da shuganni masu rike da madakin ikon Jami”ar Turanci ne kawai akayi ta Zabgawa kamar ba a kasar Nageria ba,ilimi ne da manya Kwalaye yayi aiki,Abba ma sun gayyaceshi yaje sun zauna Cikin manya manyan Proffesor,bai Razana ba ko kadan Tuni tsohon Dr.Abubakar Malami Dukku ya dawo,Tattaunawa Data kwashi awanni goma kafin agamata washegarin Ranar ne aka Fadi sunan Abba A mtsayin Deen na Departarment din Psychology.
Wannan abun wani Budi ne da Ni”ima Daga Ubangijin mai Rahma mai jinkai In wata Kaddara ta sameka ka Dogara ga Allah shi din Yana mganin kowani Tsanani da Sauki In ka Yi hakuri Zaka ga sakamakon ka a wajen Allah to hakan ne ta Faru da wannan ahalin da sukayi hakuri suka Dauki Kaddaransu Hannu Bibbiyu sai gashi Allah yana Dawo musu da Ninkin ba Ninkin Abunda suka Rasa.
Wannan Nasaran da Abba ya samu Daddy ne kan Tsani Duk da ba aikin Gwamnati yake yi ba yasan manya sosai acikin gwammati masu manya Mukamai da Taimakon su da Chachantar Abba ne ya kaisa wannan Mtsayin.
Tsayawa Fadar irin Farincikin wannan Gidan ma bata Lokaci ne sun yi Murna kuma sun godema Allah Duk da bazasu iya dawo da Ran Yan”uwansu da suka rasu ba akallah dai Zasu iya Dawo da Fiye da Farincikin da suka rasa abaya Dr.Abubakar Malami ya kara Tabbatar ma kansa mai Hakuri Shine keda riba wata Rana kuma Komai Tsanani mganinsa na Wajen Allah in kaddaran sa ta Faru dakai to akasin Farinciki da samu zasu Faru dakai in kayi Hakuri abaya ya riga ya Gama Fitar da rai da Rayuwa ballatana Har ya Cigaba da amfana da Iliminsa sai dai shi Allah mai kyauta kuma mai kari ne.
Wannan Sabon mukamin na Abba ba wanda bai jisa ba yan”uwa Sai kira suke suna Tayashi Murna Daddy da Umma Takanas ta Kaduna sukazo kano Taya Abba Murna Suka kwana Daya suka koma Tare da Mama suka Dawo Tunda Jikin Inno yayi Sauki ta Warware,Inna Bintalo da ya”yanta duk sun kira Abba haka Inna Maimunatu Sadam kuwa kullum Shida Aneesa in yau basu zo ba gobe suna gidan,Hatta Mutanen Ikko Dr.Ali isa Argugun ya Kira Abba yace a Jarida ya gani a Big Congratulation ya Chanchanta da wannan mukamin.
Banda Baffa Kabiru shi kam sai da kowa ya Kira kusan shine na Karshe ya Kira ya Tayashi Murna Abba Mutum ne bamai Riko ba sannan yana yima wadanda yake Tare dasu Uzuri ballatana Baffa Kabiru da shi ya Fita Dabam acikinsu.
Bai nuna mai wani abu ba ballatana yaga alamun ya Fahimci bai kyauta ba Shima Sai yayi amfani da kalmominsu na Lauyoyi ya Irin nuna ma Abba Hidimomi ne suka sha kansa shima Abba sai yayi amfani da Iliminsa na Sanin Hallayar dan adam ya nuna bakomai ya Tabbata daya samu Lokaci Har gida zai zo mai murna da Haka suka Rabu Labarin da Har Cikin Family Group din su sai da Sadam ya Sanar kowa ya gani Hatta Sajida wacce Take chan makaranta Bakinciki da soyayyar Mijinta sun kusa illatata Tana da Labarin samun aikinsa Ta Kirasa sai dai har Lokacin bai Sauketa Daga Sagale tan da yayi ba,Ta Riga ta gama Sarewa ta Tabbata da Mami Tayi mata mummaan Ramin da kafin ta iya Cikesa sai ta sha Wahala Tana son Imran kuma zata tabbatar da hakan bazata jura rasashi ba,shiyasa ta yanke shawaran Dukku Zata tafi wajen Daada ko kuma taje Gidan Baffa Malamin Imran din in ya ganta Dole zai karbeta tunda dai ita Matarsa ce,Sai dai kafin nan Zataje Dukku ta Fadama Daada tana son ta Tare a Dakinta Mijinta ta Tabbata in ta Cigaba da yin shuru Mami Zata kashe mata aure in kuma hakan ta Faru ta gama shiga uku ba wanda take ji take gani a farke ko acikin Mafarki irin Imran Rayuwa babu shi bata san yaya zata kasance ba ta bari ne su gama Covering semester su sai ta Shirya zuwa Dukkun koda makaranta ne batare da Mami Asma”u ko Dad sun sani ba ta Tabbata Sukaji Labari bazasu taba barinta ba.
Khamis ma yana Cikin Damuwa ganin Yadda Inteesar taki bashi Dama aiki ne yayi mai yawa bai samu Lokaci ba ammh ya Kuduri niyyar karshen Wata Zai je Har kanon zai kira Baffa Mustapha ya bashi Full Addrres din inda Zai sameta Zai je domin neman yardanta Bai ma Fahimci haka sonta yamamaye mai Ransa da Zuciyarsa ba sai da ya koma Anambara Tunaninsa duk itace tayi Daidai da Zabinsa da irin kalan matan dayake so.
Khamis bai Taba Zina ba Sai dai Bazawarin Kan Titi ne ya Fige mata da yawa asha baki yayi Romancing na Fitar Hayyaci aji Dadi da juna ammh bai Taba Tsallake iyaka ba ko kuma ya Tsallake Gonar da bata tasa ba ya riga yayi ma kansa alkawrin bazai tsallke Gonar kowa ba sai tasa.
Mami Asma”u Dataji Labari mamaki ya kamata ta Dinga maimaita lamarin a Fili,Tasani kuma ta kara Sanin Malami da iyalansa sun musu nisa ita kuma abunda da bata kauna kenan wani ya Fita ko ya fi mijinta da ya”yanta tana da Labarin samun aikin Imran Harda kyautar da aka bashi da Mota da Gida Zuciyarta tayi Sauki kan Auransa da Sajida sai dai kafin ta bashi yarta sai ta Gindaya wasu Sharruda kuma sai ya tako gidan nan ta Wulakantasa son ranta.
Ko awaya bata Kira Abba ba kuma a group da ake ta Fatan Alheri Tana gani batace komai ba Kuma Baffa Kabiru bai iya gayamata abunda ya kamata ba abunda taga Dama shi take yi shi bai isa yace wani abu Saboda Tun Farko haka suka Gina Rayuwar Zaman auran nasu.
Safiya ta Kira Hajiya Mero ta Fadamata Abun Alherin Daya samu Abba bakinta yaki Rufuwa daman wannan Ranar take jira da gayya Taje tana Fadama Alhaji Alhasan wanda Ya Razana kuma yaji mamaki Daman Sabon Deen da Jami”ar Bayero ta Fitar da sunansa Mahaifin Yusuf ne,Bai taba Tsamnani ba kuma bai Taba kawowa ba,Hajiya Mero tace ya Shirya yau Har dashi zasu tafi Gidan Taya su Murna ya Fara Kifta Ido,Wanne shi ake kira Inda ka Raina in da zaka na Ran maka ya Raina Yusuf ya Ci Zarafin gidansu sai gashi In bai yi hankali ba Kunya da Nadama zasu kamasa Lokacin hakan bai yi ba.
Ya Tabbata yasan Labarin yadda ya Basu Safiya a wulakance da yadda ya Tozarta Yusuf din Tabbas bai zo so su Fara Haduwa Cikin wannan yanayin ba Duk yadda yaso ya Zillema Tafiyar bai Samu ba Domin Hajiya Mero ta Tsaya sai yaje ita da kanwarta Anty Saratu da ta zo su tafi Tare.
Bashi da Mafita illah ya shirya Da Daddare suka tafi dukkansu har da Tasleem
Masu Karatu zan so ku Hango Fuskar Alhaji Alhassan agaban Abba kamar yayi mai sujjada ya kaskastan da kansa baya iya Hada ido da Abba ballatana Yusuf har ita kanta yarsa tasa Safiya,Gani yakevkamar Abba ya na kallonsa da abunda ya aikata Cikin Rashin sani yo cikin Rashin Sani mana in da ya san Akwai irin wannan Ranar wlh da bai fara wannan Tozarcin ba.
Sai dai ta bangaran Abba ba haka bane ya ma manta da wannan mganar Tunda akace mai ga iyayen Safiya Har da Mahafinta sun zo mai Murna Farinciki ya Kamasa Alhaji Alhassan na neman ya Dukamai ya Tarosa yana bashi hannu Cikin Fara”a Lokaci daya da godiya Domin iyayen Safiya abun karramawarsu ne Safiya Haske a Gidansu itace Sanadiyar da suka kawo yau a wannan Rayuwar Dole ne ya Godema iyayenta da ahalinta.
Lokacin da Abba ke godiya kan Alhaji Alhassan na kasa ya kasa ma Dagowa bai Taba nadamar Hallayarsa ba sai yau Ji Abba dai Daga ganinsa kaga Tsabar Ilimi da Wayewa tare da shi Wanda ko saman kafarsa bai kama ba godiya yake yimai Saboda ya aura ma Da’nsa auran Safiya a kaskaace bai Tuna da Cin Zarafim da yayi ba to shi kuma a wa..? Tabbas a wannan Gidan yaci sunansa gidan karamcin Kunya da Nadama sunki barinsa ya Saki jikinsa Su Mommy tun bayan da suka gaisa da Abba suka Rankaya shashensu Safiya Tasleem kuma Tana Tare da su Munari.
Abba da Alhaji Alhassan Suna Falo Abba ne ke tamai Hira Cikin Faram Faram da wayewa shifa sai dai Zugum da gyada kai,a Hiran Abba ne yaji Labarin Abba yayi Koyarwa a Jami”ar Lagos kusan shekaru ashirin ya Hallaci kwasa kwasa ba adadi kan abunda ya Shafi karatunsa Dr ne shi a bangaran Ilimi Babansa Marigayi Hamisu Dukku har ya rasu alkalin alkalai ne na Kotun musulunci to shi Waye..? Alhassan ne fa wanda ubansa ba kowan kowa ba almajiranci yazo yi garin Kano Allah ya taimake sa Da Taimakon Mallam yayi karatu da kuma alfarmansa ne har yau yake kan wannam mtsayin shi ko Rabin Dr bai kai a iliminsa ba,Karamin alhaki ne in kazo matakin rayuwa a kan Abba da Zuru”arsa.
Yusuf ya Fita Haraban gidan yayi waya sai ga su Baba Manu da Matarsa Kaltume da Mama da Sagir sun kawosa daman Tuni yaji Labarin komai a bakin Mama Shiyasa Dayaji wannan abun Faricikin yace ta kawosa yayi musu murna da Yusuf suka Fara jin karo yaji Dadin ganin Baba Manu saboda bazai manta dashi ba,Yayi musu jagora zuwa Falon gidan su inda su Abba ke zaune bayan sun gaisa Daga Waje Abba ya mike Cikin girmamawa Sanda Yusuf ya sanar dashi Baba Manu ne baban Sagir wanda ya karbomai Auran Safiya Alhaji Alhassan dake Zaune yana ganin Manu aransa yace Shikenan na Mutu Daman yana zaune ne yana Allah Allah kada tsagerin yaron nan ya Shigo Kada ya yagemai Sauran Rigan Mutumcinsa Dayeta ita a wajen Abba.
Sun gaggaisa Cikin Aminci da Farinciki Abba yayi ta ba Baba Manu Hakuri Da baisamu zuwa yayi mai Godiya ba Baba Manu yace Haba ba komai Shi kanshi yasan Wani kaya fa sai Amale Yusuf sun wuce Raini da Wulakanci Tunda yaji ance Yaya yake Wajen mijin Salaha kanwar Amina yasan Babban goro sai magogin karfe.
Sai da aka Natsu yama Lura da Alhaji Alhassan nan take ya Kira sunansa ya basa Hannu yana Dukar da kai da Kifta ido ya amsa mai shi bai ma Lura dashi ba sai acikin Ransa yaji Dadin Da Alhaji Alhasan din ya gane cewa Safiya batayi ma kanta Zaben Tumin Dare ba ta shiga Ahali irin Ahalin da kowa Ke Burin nashi ya kasance.
Munari da Inteesar keta Hidiman kawo ma baki abun sha da kayan Motsa baki Sagir dai Dakin Imran ya shiga ya samesa zaune kan Tsakiyar gadonsa yana ta aiki Bisa karamar Laptop dinsa nan ya Zauna suna gaisawa jin cewa da Baba Manu suke Imu ya mike ya Zira Jallabiya ko bakomai yana ganin kimar Baban Sagur din ba Dan”uwa bane ba kowa ba ammh yayi musu Ranar da wani nasu bai musu ba.
Ai yana Fitowa Falon Alhaji Alhassan yaji kamar kasa ta Tsage ya Fice ga Sanyin AC ga komai ammh Sai zufa yake yi,Imran bai ma gansa ba da Baba Manu suka gaisa sai su Mama da suka Fito Daga Shashen Anty Safiya Zasu tafi ne ma,Kawai yaji Alhaji Alhasan na gaisheshi kowa awajen sai da yayi mamaki sai alokacin Imu ya gansa yako hade rai ya amsa lokaci Daya yana Bashi Hannu sukayi Musabaha yana jin Sadda Hannunsa ya Jike da Zufa sai rawa jikinsa yake yi Dariya ta kamasa aransa yace kowa ya Tuba don Wuya ba lada Saboda Safiya bazai so asirin Mahafinta ya Tonu a Bainar nasi ba sai dai zai so ace ya Tuba kuma Allah ya Shiryesa ya Dawo uba nagari kamar kowaa yasan dai shi Imran bai jin mgana ammh Wlh bazai iya Fallasa asirin da wani ya Rufe ba har ga Allah yana mai Fatan Shiriya.
Su Baba Manu suka Fara Tafiya sai gashi Har da Ya Imu a yan Rakiya,sun Tafi kenan Ba Dadewa suma su Alhaji Alhassan suka wuce bayan yayi ta Dokama Mommy kira ta fito su tafi kunya yakeji gani yake kamar Kowa yasan abunda yake aikatawa Abba Har Bakin Mota ya rakasu Mutum mai Saukin kai inji Mommy Anty Saratu tace Dagani ya Gado Dattako da Mutumci shidai yana jinsu Tak bai ce kunyar duk ta gama kamasa sai da suka isa gida ya iya Ssuke Numfashi Anty Saratu nan zata kwana sai Gobe Zata koma Gidanta nan suka baje afalo suna labarin Karamcin Gidansu Yusuf anan me yake jin Labarin Safiya nada Ciki sai yaji Dadi ko bakomai zai yi Farinciki in ya Hada zuru”a da Abba Shi kanshi ya sani Babban Goro ai sai magogin karfe.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button