
Shakira..
3/24/22, 14:21 – Ummi Tandama😇: GMB2🅿ï¸?17
Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488
Aranar dai ba”a samu Daura Auran Inteeasar da Imu ba kamar yadda Daada taso,saboda yanayin Motsawar Jikinta da yadda Zukata suke babu Dadi,Allah ya taimaka da Daada ta Farka taji Sauki sosai shi ya kwantar ma dasu Abba Hankali.
Ranar gidan na Daada kowa kadaha kadaham banda Imran Daya kusa Raba Dare yana aiki Saman Laptop dinsa ko irin agefen Kwalan Rigarsa.
Sajida kwana Tayi kuka kafin Safe Zazzabi ya Rufeta duk mai Tsausayi ya ganta sai ya Jimanta mata Umma da Inna Maimunatu ne ke ta kula da ita Ita Taje ta Fada ma su Abba Hankali Tashe suka Rankayo Dakin suka ga Halin Datake ciki,Sajida ai tasu ce koda Daada tace ta cire Hannunta akansu Bacin rai ne ammh Hanunka baya taba Rubewa ka yankeshi ka yar Daddy ne bai Damu ba gwara Da Daada Tayi ma Yaya kabirun haka ko ya dawo Cikin Hayyacinsa ammh har ga Allah yana Takaice da Mami Asma”u kuma da jin zafin yadda ta Ci ma Daada Mutumci bata gama ganin komai bama yanzu ta fara gani.
Abba kuwa Daman Dan Sanyi ne gabadaya ya shiga Damuwa bai so yayi ma Daada mgana ne ta Birkice mai ga kuma Dokar Likita Lura da hakan da Daddy yayi ne yace ya bar mganar kwana Biyu sai su dawo su samu Daadan su zauna su Lallasheta ta yafe ma Yaya Kabiru,Kada Fushinta ya Shafesa a mtsayinta na Uwa a garesa ammh awannan Lokacin sun fi Bukatar Natsuwar Daada da kwanciyar Hankalinta.
Da wannan mganar Abba yayi shuru bai ce ma Daada komai ba ammh Hakika Lamarin ya Tabasa yana ganin kamar shine Silan komai da Imran bai Saki Sajida ba da haka duk bata Faru ba sai dai abun nan da Hausawa kan ce Ka Haifi yaro ne baka Haifi Halinsa ba.
Da Dr.zubaida tazo duba Daada da Safe Daddy yace ta Duba Sajida ta Wahala Zazzabin ya narkemata Jiki ga Ciwon kai ga Nauyin kirji Allura Tayi mata ta Rubuta Drip da mganguna ABBA ya Umarci su yusuf da Basheer sukaje suka siyo suka kawo tayi mata amfani Dashi ta Dora mata Drip din bayan ta saka wasu Allurai aciki ba Dadewa Sajida ta samu Barci Duk ta jeme ta Lalace Fuskarta sai Sauran Bushewae Hawayen kukan Data kwana Tanayi dukkansu suna Dakin gwanin ban Tsausayin Halin da Mami Asma”u ta saka yarta.
Daada ta aiko kiran Abba da Daddy suna zuwa tace maza suje a Daura auram nan da Abba ya kawo mganar Rashin Lafiyar Sajida sai Daada ta Saka Musu kuka,kan cewa in suma baza su yi mata Biyayya bane Sai su gayamata jin haka yasa suka Fice Daman Allah yasa da suka je Sallar asuba Daddy ya sanar da Liman akwai Daurin aure karfe 11am na Safe.
Haraban gidan suka Fice Daddy ya Kira Basheer da Yusuf ya basu kudi sukaje suka siyo Goro da dabino,Sha Dayan bata cika bama suka isa masalllacin Imran na Gida bai zo ba da Sagir yamai mgana kallonsa yayi kai Tsaye kafin yace”Ko naje ko ban je Inteesar Zata Zama matata so plz ka kyaleni..!
Sagir ya kada kansa yana Fadin”Kai dai Wlh baka da Tsausayi nan fa nazo Dazu ina Fadamaka Halin da yarinyar nan take ciki ammh kana ta jin Dadi anya kana da Zuciya a kirjinka..?
Imran ya kara Murmusawa kafin yace”In baka yarda bane ko Zamu saka Wuka ka fasa Kirjin nawa sai ka Duba kagani ina da Zuciyar ko bani da ita..!
Tunda ya Fadamai haka bai kara bi ta kansa ba to duk kowa bai da Natsuwa haka aka Daura auran Inteesar da Imran kan Sadaki Dubu Dari Daddy shi yayi ma Imran Waliyi Abba kuma ya bada Auran Inteeaar Mutanen anguwan suna ta yabon Ahalin Alkali Dukku marigayi suna Fadim bayan Ransa basu ya da Zumunci ba,Suna ta Hada ya”yansu auratayya Cikin Aminci,Kuma Daurin auran yayi jama”a matuka Domin kaf Anguwan ba wanda bai shaida karamici irin na Marigayi Hamisu dukku ba.
Daada bata ji Zuciyarta ta kwanta ba sai da Abba da Daddy suka dawo suka zube mata sadakin Inteesar da Goro da Dabino suka Tabbatar da sun cika mata Wannan Umarnin.
Daada na Sharan Hawaye tana saka musu albarka Tana fadin kamar yadda suke bin Umarninta Insha Allahu bazasu taba samu ya”ya wadanda Zasu bijiremusu ba Daada ta Bala”in basu Tsausayi Rauninsu ya bayyana sukaji suma kamar suyi ta kukan nan suka Taru suna Lallashinta Kafin ta Daina kuka ta koma Fara”a Da Dariya Lokaci Daya Tana Saka musu albarka.
Lokacin da Sagir ya shigo Dakin da Imu yake yana fadin an Daura mai aure Shi da Inteesar sai da ya Tsaya da aikin da yake yi gabadaya Jikinsa ya Saki yaji Wani irin Feeling mai karfi yana Tasomai yanzu Intee Matarsa ce ita din mallakinsa ne.
Baisan Sadda ya Furta”Alhamdullillah..!
Afili har Sagir ya jisa ba sai dai bi bi ta kansa ba Ya gama batamai rai ya kuma bashi Haushi Dauke kansa yayi kamar bai gansa ba ya Fara Shirya jakarsa Tunda yau zasu koma Imran na Kallonsa aransa yace kayi ka gama.
Umma kuwa Daman Tun jiya ta Kira Chan su Inno ta gayamusu komai suka Saka albarka da Fatan alheri,dukka yayyinta ta Kira su su Kawu Bala da kawu Salisu ta Fada musu sukace ba Domin bata gayamusu tun da Rana ba da sun samu Daurin aure tace bakomai suyi Zamansu Tunda anan kaduna za”ayi Bikin Tariyan Inteesar din.
Mama kuwa Daman ita ta Fara Kira ta fadamata Mama ta Saki Guda a waya Tana Bayyana Murnanta ta Tuna da Sanda tace ma Intee zata aurama Imran ita a wasa ashe dai Allah ya Hada al”amarin sai fatan Allah yasa su zauna Lafiya,Gari na Waye ana kuma Daura aura ta Kirkkira su Kawu Salisu ta shaida musu Nasara Kawar Inteesar sai da taji Labari kamar Daga Sama wai an Daura ma Intee Aure ita ta Fara Kiranta a waya tana Fata kwakwazon bata gayamata ba Inteesar tasha mamaki bata Taba Zaaton Auran zai zama cikin gaggawa haka ba tama kasa mgana Jikinta ya Mutu duk da kwanan Farincikin Datayi Zata Zama matar Imran jinta a Mtsayin Matarsa bayan a wanni kadan yasa komai ya Tsaya mata tama kasa gane wani yanayi take ciki.
Munari ta bari da wayar Tana ma Nasara Bayani har ta Fahimta Tana jinsu Suna Tsara yadda zasu gwangwaje alokacin Tarewar Bikin su Intee na Jinsu aranta tace badai da ba Ya Imu na aura ba shine zamu gwangwaje ammh wannam Dan ka”idan Allah yasa ma ya bari ayi Bikin.
Koda Anty Safiya ta shigo ta Fada musu Abun Farinciki sai ta iske ma Munari na waya da Nasara suna mgana Itama Yanzu Yusuf ya Kirata Rumgume Inteesar Tayi Lokaci Daya Tana Rangada guda,Munari na ganin haka tayi Saurin katse wayar Nasara bayan tace Zata Kirata Daga baya suka Hadu da Anty Safiya suna tayima Inteesar guda Da Wakar.
“Ke Kikace kina so..da baki ce kina so ba da ba’a baki shi ba..!
“Ta zama ta zama ta zama Dauko Riga ta zama Dauko wando..Ta zama Dauko Kofi…Ta zama..Ta zama..!
Kawai sai Inteesar ta saka musu kuka Hawaye Shabe Shabe Anty Safiya ce taci Girma ta koma Tana aikin Lallashi Tana fadin”yi shuru abunki..Amarya guda da kuka..?matar Imu guda a”a bar kuka Kada yazo yaga nasaka matarsa kuka yace zai Sauyamin kammanni..!
Gabadaya suka saka Dariya Harda ita Tana Hawaye,nan suka zauna da Anty Safiya da Munari suna Tsara yadda komai Zai tafi harda kirga ankon da Zasu yi lokacin Bikin Tariyar domin zasu Famshe Bikin yaya yusuf da ba”ayi Taro ba zasu yi gayya na kece Raini Taro sunan Taro ita dai Tana gefe Tana kallonsu Gabadaya Hankalinta da Tunaninta na kan Imran yana ina..? Wani Hali yake ciki..?
Kafin kace kwabo Labarin Daurin Auran Inteesar da Imran ya Zaga kunnen kowa a Dangi Ya Basheer ya Hau Whatapps ya sanar a Group Cikin Fahari da Farinciki a Mtsayinsa na Dan”uwan Intee yasan ta Gama Dacen Miji irn Imran irin su ne ake kira One in Million,Matan kuma su Anty Hauwa su Aneesa duka mazajensu suka kirasu suka Sanar dasu Inna Maimunatu ma ta kira su Zainab ta Shaida musu kowa yaji Sai yayi Murna yana Fadin Wlh Imran sun Dace da Inteesar Hadin yayi matuka.
Hafsah ma Dataji Labari ta Daka Tsalle ta Rangada guda Tana juyi Tana Fadin kano akwai Shagali Fareesatu namata Dariya,Kiran wayar Inteesar Tayi munari ta Dauka suka Dinga mata ihu suna Tsokananta da Amarya Amarya,ita dai tana jinsu bata mgana yau aure ya kashe bakin Intee Hafsah Har tafi Munari Zumudi Tana Fadin Taga wani less ko shi Zasu yi Ranar Dinner..? Intee Dariya suke bata da Tsausayi Sun manta wai Waye Imran ne Ta Rantse har ga Allah sai yayi Ra”ayi Duk abunda bai yi Ra”ayi ba ba wanda ya isa.