GIDANMUNOVELS

GIDANMU 1 & 2 COMPLETE

GIDANMU HAUSA 1 & 2 COMPLETE


Yusuf ne ke Tallafe da Abba yana Bashi Tea abaki Munari na Gefensa Tana mikamai Buredi mai yanka yanka yana Bama Abba Imran na Tsaye Daga Jikin Wardrope din Dake Dakin Abba yana Sanye da Farar Singelet da Wani Bakin wando 3quater,Hannunsa sanye Duka Cikin aljihun wandonsa Allah ya Taimaka yau ba”a Busa abun Ransa ya Hade Tamau kamar bai Taba Dariya ba yanayin yadda yake Tsayen kiris yaje jira atabashi ya Fashe.

Har Yusuf yagama Bama Abba Tea din ya bashi mgangunansa yana kokarin maidashi ya kwanta Imu Dake Tsaye yace”Ka barsa ma Ruwan zafi yabi Jikin nashi..”Yafada Cikin muryansa mai Cike da Amo da zati.
.bai yi gaddama ba Munari ta sakamai Karamin Filo a bayansa suka Jinginshi ya Dago yana kallonsu yana Fadin”Allah yayi muku albarka..”Yusuf yayi Mirmishi ya amsa da Ameen Abba Allah ya baka Lafiya Dukkansu suka amsa da Ameen kafin Yuauf ya Zarce da Fadin”Na Fara Tunanin ko mu Sauya ma Abba Likita ne..?
Imran Dake Duke da kansa yace”Saboda Mene..? Yusuf yace”Bana ganin wani Cigaba..Kullum Abba jiya iyau..Kamar ma Baya yafi akan yanzu..”
Imran ya shafa Gashin kansa Dayayi Uban Dada yace”Ai ba Laifin Likitan bane..”Yusuf ya Kalleshi yana Fadin”Kake gani..? Imran yace”Kaima ka sani ko..?
Yafada yana kallon Maimuna Dake kallonsa Cikin Hararanta yace”ke Lafiya kike kallona kamar Wata mayyah..? Da sauri ta kauda kanta karamin Tsaki yaja yana Fadin”Tashi ki Fita ma..Kinsan bana son yawan kallo ko..? Kwalkwal Tayi da ido kamar Zatayi kuka Zaburo mata yayi yana Fadin”Au bazaki tashi ba kin tsayane kina neman min kuka.? Fice anan kafin ki Tunzurani na Miki Dameji da Fuska..”Da Sauri tatashi Ta Fice Dauke da Mug din da Abba yasha Taa da Bread din.
Yusuf ya kalleshi yana Fadin”Wai waya bata maka rai ne..Kazo ka sauke kan Munari.?
Bai samu Zarafin mgana ba sukaji Muryan Abba yana Fadin”Kabi ahankali IMRAN…’Yafada ahankali Cikin Sanyin Murya duk sai Jikin Imran din yayi sanyi Kawai sai ya gyada kai yana Fadin'”Mubar Abba ya samu barci..Muje Dakina muyi mgana achan..!
Daga Haka ya Fice yana Takunsa na Daya Bayan Daya.
Sai da Yusuf ya ggyarama Abba kwanciya kana ya Baro Dakin Gidan Shuru kamar ko Yaushe Munari yassn ta kwanta Tunda Imu yayi mata jan ido.
Dakin Imran din ya Shiga Cikin mamakinsa ya samesa yana Busa abar tashi Girgiza kai yayi yana Fadin”Wai kai baka gajiya da Busa Hayaki ne..? Kada ta maka illah Fa Imran..!
Cikin Lumahe ido yace”Me yayi saura..? Ai ni Daman Tuni Illah ta gama illatani Hayakin Saura ya samu!
Jin haka yasa Jikin Yusuf yayi sanyi kawai sai ya zauna Gefensa yana Fadin”Hakane..Ammh akallah muyi kokarin ganin mu Rayu Cikin Farinciki ko Saboda Abba..”
Har ya Fidda rai da zai bashi amsa sai yaji yace”Ya mganar Tura mgabatanka gidansu yarinyar nan..?
Yusuf ya sauke ajiyar rai yana Fadin”Nima bansan ya za”ayi ba..Kuma Mahaifin nata niyake Sauraro..”
Imran ya Busar Tabarsa yace”Wazaka Tura..? Yusuf ya kalleshi yace”Bansani ba..Ammh nafara Tunanin kiran gida na Sanar dasu inda muke da kuma abunda ke Faruwa akallah koda bamu koma wajensu ba zasu zo sukaga inda muke kuma Duniya Zata shaida bamu kadai bane AGIDANMUÂ muma muna da Ahali..”

Kamar wani Kumurci haka ya Mike yana Fadin”Kar ma ka Fara Ya Yusuf Kada ma fara nace….! Yafada da karfi yana Nuna yusuf din da Yatsa Mikewa yayi shima yana Fadin”Nima ba yadda zanyi ne hakan shine mafita..Domin aure ai ba wasa bane..”Imran yace”Ko ka kirasu sunzo babu Abunda zai Sauya su bazasu Taba Fahintarmu ba muma bazamu Fahimcesu ba..Zasu zo ne su kara Daukan Hauka su Dora ma Abba..Su Rika Bleeming dinsa kan Abubuwan da suke Faruwa..Muma ai ba Laifinmu bane Kaddaran Allah ne da Jarabawansa Saboda haka kada ka sake ka kira wani Ballatana a Fahimci inda muke gwara mu Cigaba da Rayuwar ahakan Tafiye mana zama inda baza”a Taba Fahimtar mu ba ballatana abamu Uzuri..!
Ya karishe Fada Cikin kunar rai yana ji kamar alokacin ne abubuwa suke ta Faruwa.
Dafasa Yusuf yayi yana Fadin”Na Fahimce kayanzu ina Mafita…?
Kai Imran ya Shafa Lokaci Daya yana kai ma Gemunsa Wutan Taban Dake hannunsa da Sauri Yusuf ya Buge hannunsa Taban ta Fadi kasa Cikin Fada yace”miye haka..?Zaka yi ma kanka Lahani da kanka fa..!
Mirmishi Imran ya saki yana Fadin”Common Bro..It’s Normal fa..”Karamin Tsaki Yusuf Yaja yana yin baya Lokaci Daya yace”Kayi ma yi wanka yau kuwa..? Wlh duk warin Taban kake yi bakin ka kuwa kamar sokaye..”
Imran bai Damu ba sai ma Dariya daya saki yabi Yusuf din yana Busamai iskan bakinsa Yusuf kuma yana mtsawa bayana Fadin”Don”t Come close..Imu Bari..Allah zan yi Amai..”Cikin Dariyan keta yace”Aman nake son na gani..”Da gudu ya Bisa shi kuma ya kwasa Zuwa Tiolet dinsa ya Rufo yana sauke Numfashi Dariya ta kama Imran ya Dinga kyakyatawa Cikin mamaki Domin ayanayinsa sai kace bai Taba Dariya ba.
Kofar Tiolet din yaxo ya tsaya yana Fadin”Matsoraci Fito..Wasa ya kare..”.daga ciki Yusuf yace”naki wayon…!
Imran yace”Baka yarda dani ba..? Yusuf yace”Kace Wlh ka bari..!
Imran na Danne Dariyansa yace”I swear na bari..”Sai alokacin Yusuf ya Bude kofar ya Leko da Sauri Imran ya Turo Kofar ya Jawosa suna Dariya gabadayansu kan gadon Imran din suka Fada Yusuf ya Mirgina gefe yana Fadin”Imu kazami..Matarka zata sha waharka..!
Imran yace”Daman shi tazo yi..!.
Yusuf yace”Wahalar..? Imran ya Zakuda kafada yace”Ofcourse..!.
Tashi Zaune Yusuf yayi yana Fadib”To Allah ya shirye ka..!
Imran yace”Ameen Shirin Allah bata Jigidan mata ba..”
Yusuf dau sai dariya yake kafin yace”Tashi..What is d Solution..”
Imran na kwance Rigingine yace”Baban Sagir zamu je muyi na mgana Shi zai nemi mutane su Shige maka gaba..!
Yusuf yayi shuru kafin yace”Baba Manu..?
Imran ya gyadamai kai Da sauri yace”Kana ganin zai yarda..? Imran ya Mike yana wani Tangadi kamar wanda yasha Giya yace”Kada ma yarda..Yagani..!
Yafada daidai Lokacin Daya abude Kofar Tiolet dinsa Yusuf ya Kallesa yana Fadin”Naga kana layi..Anya Imu baka Fara Kora Giya ko Tabar wiwi ba..?
Yana jinsa yamasa banza sai da ya Shiga Tiolet din kana ya leko yana Fadin'”Ban fara ba ammh Sai da Kafada naga ya kamata na Fara Tanque for ur Advice Bro..! Lokaci daya ya maida Kofar ya Rufe Yusuf yayi Dariya ya Jinjina kai yace”Imu…Imran…Ta bakin Abba yace Imran..Imran Rigima..”Daga haka ya Fice Daga Dakin zuwa nashi yasan Kila Safiya nata kiran wayarsa Daya barta adaki.

Tanque Masoyana naji dadin yadda kuka karbi wannan Labarin I promise u bazan baku kunya ba..

Shakira…
3/22/22, 23:03 – Ummi Tandama😇: GIDANMU..!
(Our House)
Book1

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

DEDICATED TO:
Aisha alto(Sisinah)
Chubado muhammad(Uwar dakina)
Yahanasu Soupnass(Qawalli1)
Kausar salis(My jika)
Rahma Ladingo(Dota)

           *🅿�4*

“Ya fito Daga lacture din da suka shiga ta safe kenan yaji wayarsa Dake cikin Aljihun wandonsa na kara yana Fitowa da wayar yaga Sunan mai kiran nashi DAN ISKAN ABOKINA..!
Sai da yayi mirmishi Daya ga sunan mai kiran Saboda ya Tuna sanda Abun ya faru,Ranar suna zaune ashagonsa ne Sai Wayar Sagir din ta Fada cikin kayan Dinkin mutane Dake kasa akayi ta Nema ba”a gani ba sai ya karbi Wayar Imran din da Niyyar ya kira Wayarshi yana saka Lambarsa yaga Sunansa ya Fito da BANZAN ABOKINA..!
Galala yayi yana kallon Imran din Dayake kallon wani barayi Kamar ma baisan da Mutane a Shagon ba an ci Sa”a Ranar bai shigo yana zukan Taba nasa ba Daga dukkan alamu akwai abunda ke damunsa Ranar kuma bayaso Tattaunawa da kowa kuma baya son ya zauna agidan Shiyasa ya fito yazo shagon Sagir din ya zauna batare da ya Tankama Sagir din ba Duk da Tarin Tambayoyin daya rika Jefansa dashi.
Cikin Jin haushi Sagir yace”Nine ma Banzan ko..?
Batare da ya kalli Sagir din ba yace”Eh Ko kana da wani suna ne Bayan Banza..?
Sagir ya kada kai yana Fadin”Wlh nima sai na Rama..! Yafada daidai Lokacin da ya kira Wayar tasa yaji kaaranta nan cikin kayan ya Tafi ya Dauko Yana Fadin”Kaima sunan banzan daka sakamin zan saka maka..Me ma zan saka maka ne..?
Yafada da Sigar Tunani Batare da Sagir yayi aune ba Imran ya karbi Wayarsa Bayan ya taso Ya Goge sunansa da Sagir ya saka mai Ya maida masa da Da’n iskan Abokina kana ya mikamai yana Fadin”Gashi na Rama maka..!
Ya karba yana gani kafin yace”Kai..! Dan iska ne kenan da gaske..?
Imran ya Zakuda kafada Lokaci Daya yana Saka Duka Hannuwansa Cikin aljihun Wandonsa,ya Kama Hanyar Ficewa Daga Shagon yana Fadin”Eh ai Dan iska ne..!
Daga haka ya fice Daga Shagon bai Damu da kallon da Sagir ke Jifansa dashi ba,Bai yi mamaki ba Sanin Halin Imran kai fi Dayane shi Gashi bashi da Tsoro,baya karya domin ka so shi ko ka yabeshi baya jin Nauyin gayamaka Gaskiya komai Dacinta baida Boye Boye ko Kumbiya Kumbiya shi Mutum ne Street Forword baya Munafunci Ballatana gulma baya jin kunya yace yana aikata wani abu koda Zaka Tsireahi ne,Wannan Hallayar nashi suna matukar Birge Sagir dashi shi kanshi ya san Imran Jajirtattace ne kuma Jarumi ne sai dai abu Dayane ya kasa ganewa game dashi..Menene Takamemmen Abunda ya Faru dashi..? Domin in bai manta ba Imran din da kansa ya Fadamai abaya ya Tsani mai Shan Taba ko Warinsa Baya son ji ammh Saboda kaddaran Rayuwa yanzu yafi kowa jin Dadin Shanta aduniya.
Ko haduwarsu Allah ne ya Hadasu Tunda suka Dawo anguwarsu basu Taba Mu”amala da kowa ba sun kebe kansu iya su kadai Gidansu da suke zaune yanzu Babu Nisa da gidansu Sagir din gidaje kalilan ne Tsakani kuma ada asalin megidan Rasuwa yayi sai aka Siyar da gidan kila Lokacin ne su Imran suka mallaki gidan.
Tun Dawowarsu anguwan Sagir yake ganin Imran da safe in ya Fito Jogging,shi kuma lokacin bai Dade da Bude shagon sa Dake kofar gidansu ba alokacin bashi da wani yaro shi kadai ne yake Dinkinsa da keke guda Daya.
Akullum da safe yana ganin Imran Haka kuwa Allah ya Doramai kaunarsa Duk da basu Taba mgana ba ammh Shi kanshi Imran din in yazo wajen Shagon na Sagir sai ya tsaya sun ma juna kallo kallon kafin ya wuce.
Watarana ne Imran din ya zauna yana Shan Taba abakin Shagon Sagir din Abunda ya kara bama Sagir mamaki bai Dace ace kamar Imran nashan Taba ba Daga ganinsa bai rasa komai na Rayuwa ba a kallon Farko ya Fahimci Imran yana da ilimi da Wayewar sanin Rayuwa haka kurum yaji yana so ya samu kusanci da Imran din Dalilin haka yasa Washegari da Safe da Imran din ya Fito Jogging Shima ya Fito har ya samu nasaran suka Bangaji juna kalma ta Farko da Imran ya Fara gayamai bayan sun gama karema Juna kallo
“Kai baka ganina ina Tahowa ne..?
Sai Sagir ya Ballamai Harara yana fadin”In na ganka sai me..? Hanyar ai bata gidanku bace..!
Sai kalaman suka bama Imran Dariya Har sai da ya Murmusa ganin haka yasa Sagir ya bashi Hannu yana Fadin”Sunana Sagir kaifa abokina..?
Kamar bazai bashi Hannun ba Saboda baya Bukatar wata mu”amala da kowa ko afarkon Rayuwarsa bai yi Abota ba ballatana yanzu da abubuwa suka Sauya sai dai ya kasa Kin bama Sagir din hannu Kamar Zuciyarsa na Jansa..Kaunarsu da abotarsu Daga Allah ne Mikamai hannu yayi yana Fadin”Imran..!
Daga haka bai kara cewa komai ba Sagir ne ya Dingamai Zuba yana Nunamai gidansu,Har da gayamai wasu Tarihin Rayuwarsa na Rasuwar mahaifinsa da kuma Inda yakezaune shi da Mahaifiyarsa harda matakin karatunsa Shidai Imran Jinsa kawai yake yana mamakin Sagir daga Haduwa dashi sai ya fara gayamai wani abu a kansa..? Yana so yace ya kyaleshi ya Dameshi ammh ya kasa Haka kurum yaji bazai iya Wulakanta Sagir ba
Duk iya kokarin Imran na kada Shakuwa ta Shiga tsakaninsa da Sagir sai da ta shiga,Shi sagir mutum ne mai barkwanci Da kuma Raha gashi bai da Zuciya da Fushi kome Imran zai Fadamai baya Damuwa Haka zasu Rabu Baram baram ammh Gobe zasu nemi junansu,Duk iya Kokarin Imran na kada Sagir ya shiga Gidansu sai da ya Shiga,Yaya yusuf ya sansa haka ma Maimuna da Abba,Sai dai har gobe Sagir bai san Asalin Labarinsu Koda ya Tambayi Imran baya Fadamai,Labarin da Sagir ya Dinga Bama Inna Amina Na su Imran yasa taji tana son ganinsa Ta shirya Sagir yakai ta har Gidan,Shi kuma Imran din Sagir ne ke jansa Gidansu da karfin Tsiya,Akwai wani al”amarin, da Allah ne kadai ya sani Duk da Imran na Zillewa ammh Sagir da Mahaifiyarsa basu Nuna sun gane ba sun Daukesu Tamkar yan”uwa Duk da Zamewarsa yana zuwa gidansu Sagir din in yajasa,Su shiga ya gaida Mama su kuma ci Abinci in Sagir ya matasamai barin ma in Tayi Abunda yafi so na Danwake.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button