
Washegari Abba ya wuce Kaduna Motar Haya yabi,Ba”a riga an samomai Direban da zai rika Tukasa ba Tunda shi Tuki yanzu ai sai dai su Yusuf,Ya”yan nashi basu so ya hau Motar Haya ba yace ba komai Bai kuma yadda ya Fadamusu zasu je Abuja ba Yusif Daya tambayesa yace Zai je Wajen Baffa Mustpaha ne Imran kuma bayanan sun dai yi sallama da Abba Kafin ya wuce wajen aiki.
Yusuf da su Munari suka kai Abba Tasha sai da Motarsu ta tashi Daganan ya Biya ya kaisu makaranta Shikuma ya wuce wajen aiki.
Wajen karfe 11am na Safe Abba ya isa Daddy yazo ya Dauke anan Tashar kawo Daman yasan da zuwansa.
Suna zuwa gida Umma ta gabatar musu da Breakfast suka karya already daman Basheer ya siya musu tiket din Jirgi gobe karfe 6am na Safe zasu Wuce Abuja Gidan Baffa Kabiru..
Bayan sun gama karyawan Daddy yaja Abba suka Fice yakaisa Shagunansa ya gani ya saka albarka Har gidan su Umma sai da sukaje suka gaida Inno da Mallam Babba.
Sai La”aar suka Dawo gida sun iske Anty Hauwa tazo ta kawo musu Dambun Shinkafa Dayaji Zogala da gyada sukayi ta ci suna Saka mata albarka,Ga Lafiyayyan Zobon Data Hade musu dashi da Sanyayyan kayan Marmari,Tunda Basheer ya Fadamata Abba yazo shine tazo gaisheshi ita dasu Abidin.
Bayan sun gama suka baje afalo suna hira kan Abunda ya shafesu har kan mganar Tarewar Inteesar Da Abba yayi mgana Daddy yace Mgana tana Wurin Imran ko gobe yace Inteesar ta Tare bai da Damuwa Abba yace to in ya koma zai kirasa yaji saboda kada su Dauki Lokaci Daada tace sun yi Watsai da mganarta.
Nan Abba ya kwana shida Dan”uwansa Daki Daya suka kusa Raba Dare suna Hira irin tasu ta yan”uwa gari na Waye suka shiga Jirgin kasa sai Abuja Karfe 9am na Safe suka sauka Daganan suka Nemi Tashar Taxi sai gidan Baffa Kabiru Dake Maitama Abuja.
Shakira..
3/26/22, 22:59 – Ummi Tandama😇: GMB2🅿ï¸?21
Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488
Gida ba kowa sai yan aiki Mami Asma”u Tana gidansu tun Ranar Umaima ta tafi makaranta Baffa Kabiru kuma ya tafi Office.
Dayake yan aikin sun sansu gama kama nan,Kuma Daddy na yawan suwa Abba ne ya Dade bai zo ba Tun kafin barinsu gida yasa nan da nan suka shiga dasu babban Falon gidan Kafin kace kwabo sun cika gabansu da kayan Ciye Ciye da Shaye shaye.
Daddy ne ya Kira Baffa Kabiru a waya ya sanar dashi gasu acikin Gidansa yayi matukar mamaki sai dai bai Tsaya bata Lokaci ba ya Hado ina inasa ya taho gida.
Lokacin Daya shigo Falon Yaga yan”uwansa Zaune suna Jiransa bai kawo cewa sun ji Labarin Rabuwarsu da Asma”u ba ya zata sun jisa Shuru ne suka Biyo Sahunsa da kuma Tattauna abunda ya Faru a Dukku.
Kunya ta Hana Baffa Kabiru iya kallon Cikin Idanuwansu sanda ya kariso Gabansu ya basu hannu Dukkansu suka Sarke Musabaha.
Sai ga Baffa Kabiru ya Duka gaban yan”uwansa yana Hawaye yana Sharan kwallah yana Rokonsu Gafara yana Fadin”Ku yafemin yan”uwana..Ku yafemin Duk da nasan Ni din mai Tarin Laifi ne..Bai chanchanta ku yafemin ba na Zama babban Banza wanda bai rike yan”uwansa da Amana ba,ku yafemin Wlh kunya da Nadama ne suka Hanani nemanku ammh na yanke Shawaran ko baku zo ba gobe na Shirya Tafiya Dukku na Duka na Roki Daada gafara kan Laifin dana aikata mata ko ta yafemin Allah ya Duba Lamarina..!
Yafada yana Goge kwallah Abba da Daddy jikinsu yayi Sanyi sosai suka Mike atare suka Rikosa Suka Hadu suka Rumgume shi suma Kamar su yi Kwallar Saboda Tsausayinsa Jini jini ne duk inda naka yake komai Lalacewarsa naka ne.
Daddy ke fadin”Haba ya kabiru ka Daina kuka..Bai kamata ba..Wlh mu bamu Taba Rikon ka ba..Daada ma bata Rike ka ba Fushi ne na Dan Lokaci kuma Zata sauko da yardan Allah..Muma kafarka kafarmu zuwa Dukku Bazamu samu Salama ba sai Dan”uwanmu ya Daidaita da Mahaifiyarmu ko ba Haka ba Ya Malami..?
Abba ya gyada kai yana Fadin”Tabbas hakane..Duk da akwai Dalilin daya kawomu ammh shima wannan yana daga Cikin Babban Dalilin zuwan mu..!
Baffa Kabiru ya Dago yana kallonsu kafin yace”Nagode muku sosai..Malami musammann kai ka yafemin nafi kowa sabamaka..Ammh Insha Allahu na gane inda na Kuskure Da yardan Allah zan gyara ZAmu je gaban Daada Zan Roketa gafara na kuma mata alkawarin ko Bayan Ranta Bazan bari Zumuncin mu ya Rabe ba mun Zama Tsintsiya Daya madaurinta Daya..!
Yafada cikin son Tabbatar da mganarsa,Daddy da Abba suka Rike Hannunsa Cikin Jin Dadi suka Hada baki Wajen Fadin”Insha Allahu..!
Daganan suka koma suka Zazzauna,Daganan suka yi Breakfast Harda Baffa Kabiru domin shima bai karyan ba ya Fita duk ya zama wani iri kamar bashi ba Daurewa kawai yake ammh Tabbas Rabuwa da Asma”un ya Tabasa.
Sai da suka Natsa kana Daddy ya gyara Zama yana kallon Baffa Kabiru lokaci Daya yana Fadin”Wani Labari mukaji mara dadin ji Ya kabiru..?
Ya kallesa Cikin mamaki kafin yace”Wani Labari kuma Kuka ji Mustapha..?
Daddy yace”Shekaranjiya Da Daddare Yar Wajenka Umaima ta Kirani a waya Tana kuka Take fadin kun yi yar Hatsaniya da Asma”u Karshe dai Har da Saki..!
Baffa Kabiru ya sauke ajiyar Zuciya yace”Eh..Ashe ta Kiraka..!
Daddy yace”Eh Data kirani Gaskiya Hankalina ya tashi..Sai na Kira ya Malami mukayi mgana,muka Tsaida mgana kan cewa yau zamu zo mu ji Ta yaya haka ya Faru..? Mu kuma baka Hakuri komai ya Faru ya wuce Zuciya bata da kashi kayi Hakuri ka maidata Dakinta Ko Domin Darajan ya”yanku bazasu ji Dadin hakan ta Faru a Tsakaninku ba..!
Abba ya karbe da cewa”Kuma in Rai ya baci ai Hankali ke Nemosa Mustapha..Duk in akayi Hakuri sai komai ya wuce Watarana sai Labari..Kuma ku ba yara bane kun Girma bai kamata hakan na Shiga Tsakanimku ba ya kabiru..!
Baffa Kabiru na jinsu kansa na kasa Sai da suka gama kana ya Dago Kansa yana Fadin”Duk naji bayanan ku..Buh kuyi Hakuri Zama Tsakanina da Asma”u ya kare in har bata gyara Halinta ta gane tayi ba Daidai ba..!
Daddy yace”Ai ya Kabiru hakuri zakayi a Hankali kana nuna mata Har Ta gane..!
Baffa Kabiru yace”Kayya ai bazata taba ganewa ba..Da kuke cewa na maidata kunsan abunda ta aikata..?bayan cin Zarafin Datayi ma Daada a Dukku a gaban i…!
Daddy ya Dakatar Dashi Da Fadin”Kayi Shuru Kawai Ya Kabiru ba sai ka Fadamana abunda ya Faru ba wannan Sirrinka ne Tsakaninka da matarka kuma Sulhu muka zo nema ba Tada mgana ba Don Allah kayi hakuri ka maidata ita kanta Daada in taji haka bazataji Dadi ba ga ya”yanku Taya zasu Fuskanci wannan Raunin..?kuma an riga an zama Daya Ku da zaku yi ma wasu Fada Yaya..! Bai kamata ba don Allah kayi Hakuri ka Maida komai ba komai ba ka Maidata Dakinta ko Saboda Darajan Daada da ya”yanku da alfarman da mu yan”uwanka muka Nema don Allah..!
Abba ya jinjina kai yana Fadin”Kuma zama ba Mata haka ai bai Dace ba..Ko ni Saboda Mutuwa ce da kuma Rashin Kwanciyar Hankali ammh ai cikar Namiji Shine Matarsa don Allah kabar Tuna baya ka yi Hakuri ka maidata Dakinta..!
Baffa Kabiru ya Sauke Numfashi kafin yace”Zan maidata ne saboda Darajan Daada da kuma Kimarku da kuka baro Ayyukanku kuka zo har Gida Domin nuna Damuwarku akaina..Nagode kwarai Allah ya bar Zumunci..!
Suka amsa da Ameen Cikin Jin Dadi Daddy yace”To baka ce ka maidata ba..?
Baffa Kabiru yace”Ni kabiru na maida Matata Asma”u na janye Sakin Dake Tsakaninmu.Ba Shikenan ba..!
Abba da Daddy suka yi Dariya suna Fadin”Alhamdulillah..!
Baffa Kabiru ya ce”Na maidata ammh da Sharadin bazan Gayamata na maidata ba Har sai ita da kanta tayi Nadaman abunda ta aikata na Nemi mu Daidaita sai na Fadamata na Maidata ammh ko nan da shekara nawa ne in bata yi Nadama ba ni kuma bazan nemeta ba..!
Suka jinjuna kai atare kafin Daddy yace”Insha Allahu ba Matsala ai Barrister ta barrister ne Zaku nemi juna in kuka Huce..!
Ya karishe Fada yana Dariya Abba na Tayashi Baffa Kabiru Mirmishi kadai yayi bai ce komai ba.
Abba ne yace”Ina Sajida take ne..?munyi mgana da Daada tace min ta Dawo Daga Dukku..?
Baffa Kabiru ya Muskusta yana Fadin”Daga Dukkun bata dawo gida ba Makaranta ta wuce Direct,ba kowa agidan nan Asma’u Tun Ranar da abun ya Faru Mahaifinta Juctice Tafida ya aiko da Direba aka Tafi da ita Khamis ma Ranar Monday yabi Jirgi ya koma bakin aikinsa..!
Cikin Tsausayawa suke Kallonsa Abubuwa sun Taru sun yimai yawa sosai.
Daddy ne ya fara baki bshi Tare da Lallashi Abba dai ya kasa mgana Sabida yana jin kunyar abunda Imran ya aikata na Sakin Sajida sai dai bawa bai isa ya ja da Hukuncin Allah ba.
Daddy ya kada kai yana Fadin”Nadade ina jin Labarin Rikewar Boko Da akidan Banzan Justice Tafida ban kara yarda ba sai yau Sabani ya Shiga Tsakanin Yarka da Mijinta ammh bai Kira yaji Neman ba”asi ba kawai ya Turo Direba an Dauketa me hakan ke Nufi..?
Baffa Kabiru yace”Ai bazai Taba kirana ba..Shi a kidansa bazai Turasasani na maidata kan Ra”ayina ba itama bazai mtsa mata kan hakan ba acewarsa sanda muka Hadu muka Kulla Soyayya muka Aminta da juna bai Sani ba kuma muka yadda da Ra”ayin auran junanmu yanzu kuma da Hakan ta Faru Ra”ayinmu ne Justice Tafida yana da akidan Bin Ra”ayin Kowa baya kutse Cikin Ra”ayin Wani ko da Ya”yansa ne na Cikin shine suna da wannan Right din..!
Daddy da Abba suka jinjina kai,ba su ce komai ba Domin abun ya wuce suyi mgana Aran Abba yana Fadin Dole Asma”u Ta zama yar gaban kanta ta Hadu da Uban mai Bin Ra”ayin kowa da Ra”ayi mai kyau da mara kyau Daddy kuwa Tir da Tarin Ilimi yake Ilimin da bazai amfani Mutum ba.
Nan fa suka Bude Hira Kala Kala su tabo Chan su Tabo chan,Har mganar Samun aikin Abba sai da sukayi Baffa Kabiru yana nuna jin Dadinsa sosai Sallar Azahar ya tadasu bayan sun je sun Dawo su ka kara zaman Hira yaushe gamo suna ta Tabo Labarin baya Tun Lokacin Gwarzon Mahaifinsu nada rai suna Tuna abubuwan da suka Faru alokacin Tuni Baffa Kabiru ya saki Jiki Cikin yan”uwansa Kamar bai da wata Damuwa.
Sai da Umaima ta Dawo makaranta Daga su Abba taji Dadi sosai ta Dinga Murnan Mami Zata dawo.
Allah Sarki Mami Asma”u tana chan Cikin Damuwa da abun kunya Domin Gotai gotai da ita Sakin aure a gareta abun kunya ne in wani yaji Labari zai zama abun Dariya a gareta.
Koda yan”uwanta suka zo gidan suka ganta bata yarda ta Furta Kalmar Sakinta akayi ba nuna musu tayi Tazo ta Huta ne ba wanda ya yarda da ita Taya ya Zata baro Gidan Mijinta Tace Tazo Gida Hutu da wani dai mgana,Hajiya Turai ma taki ce musu komai ballatana Justice da ba Ruwansa da Shiga abunda ba”a Saka sa ba,Indai ba Asma”u ta Fada ba shi baza”aji komai Daga Bakinsa ba.
Batare da Shawara da kowa ba Hajiya Turai tace ma Asma”u ta Dakatar da Shigar da karan nan Saboda ceton Auranta ita kanta Barazanace ammh Asma”u fa ba yarinya bace akwai Tarin Kalubale ta Zauna gabanta Tana Zawarci ba gaddama ba Musu Mami ta Kira Brr.Zailani tace a Dakatar da komai Shi kuma bai kawo abun har takai ga Rabuwa ba ya Zata Brr Kabiru yayi ma abun Tufkan Hanci ne bai san ya bama Mami Red card ne wanda ya Girgixata da Girmanta an Saketa abunda Tun Lokaci Tana da kuruciya bai Faru da ita ba,Ta tsinema Daada acikin Ranta yafi a Kirga Domin har lokacin bata Fahimci bata kyauta ba gani Take Duk Daada ce ta ja komai kuma itace silan Mutuwar auranta,Ego dinta da son kanta yasa ta kasa Zama ta Fahimci matsalan Daga Wajenta yake,Sakin ya Dameta gani take kamar Abun kunya Aji kamarta ace Mijinta ya Saketa ko kawayenta sai sun Rainata
Sajidan ma Datake Fada akanta ta Gujeta ta Zabi Dangin Ubanta akanta bayan Sakin Wulakancin da Kabiru yayi mata tayi ta Kiran Sajidan bata Dauki Wayanta ba daga Karshe ma Sai ta Ratayeta kwata kwata ma ta Daina Samunta Khamis ma bata samunsa Kwata kwata a waya Umaima ce kadai take Kiranta Umaima kuma yarinya ce bata san komai ba,gabadaya taji kamar ta Rasa komai ya”yanta da bata da kamarsu batasa tare da ita Ta kara jin Ta Tsani Daada tana ganin Duk itace Silan komai.
Sai da Umaima ta Fadamata Sajida na School kana Hankalinta ya kwanta,Sannan ta Gudura aranta Bazata nemeta ba ai ita Uwa take gareta komai lalacewarta Tana nan a Mtsayinta na Uwa Zata Tsaya tagani Shin Sajidan ta Sauya wata Uwar ce Bayan ita..
Umaiman duk sanda sukayi Waya ta Dinga Fadin Plz Mami Come Back itama Sai tace ba Laifina bane Umaima a kunnenki kikaji Ubanku ya Sakeni yace nabarmai Gida,Har Fadama Daddy da Umaima Tayi ta Sanar da Mami Asma”u aranta tace Dole yazo ya bani Hakuri Haka Umaima na Dawo makaranta ta gansu ta Kira Mamin ta Fadamata kanta ya Fashe ta Fadama Hajiya Turai wacce tace”Ai daman na sani Kabiru baazai iya Rayuwa baki ba..Allah yasa su kwaso Kafafuwansu nan gida sai nayi musu Fata fata kafin na yarda ki koma mu Zaimaida Kananun mutane..!
Ita kuma Mami Sai Mirmishin Mugunta take yi Tana Tunanin yadda Mustapaha da Malami da shi kanshi Kabirun zasu Duka suna bata Hakurin ta koma ma Dan”uwansu sai Ta Rama Wulakanci da Tozarcin da suka mata Musamman ma Mustapha Daya Dauki yarsa ya aurama Imran bai ma Tsaya Jimamin Sakin kaskascin da akayi ma yarta ba Da Umma data bata mamaki Wlh ita taga Kalar kowa a wannan Dangin Bata taba Tsammanin Umma Zata yarda a bama Imran auran yarta ba ta Dauka saboda ita da Sajida ita ta mike tace A”a in ta kama sai dai Imran din ya Maida Sajidan ko kuma ya Fita Waje ya auri wata badai acikin Dangi ba.
Sai dai tayi ta Zaman Jiran gawan Shanu Har Washegari Shuru bata ga Kowa ba ta ta kiran Umaima bata Samu ba Tatafi makaranta Sai da ta Dawo Dataga Kiran Mamin Dayawa Bayan ta Kirata take Tambayanta ina Baffaninta..?
Umaima ta Tabbatar mata tun da Safe suka kama Hanyar Dukku Harda Dad dinsu Mami Asma”u sai taji jikinta sanyi Jin Tunaninta bai zama Daidai ba Ko Hajiya Turai dataji sun Tafi Dukku Jikinta yayi sanyi ada ta Hango Daidatawar Komai,Taso ne itama ta Wulakanta Kabiru kamar yadda ya Tozarta mata y’a sai dai hakan bai samu ba ba Baffa Kabiru ba su Abba sai Mami Asma”u ta koma Tana neman ma kanta Mafita ammh Har Lokacin batayi nadama ba Tana ganin koma meya faru ita aka Cuta..!