GIDANMUNOVELS

GIDANMU 1 & 2 COMPLETE

GIDANMU HAUSA 1 & 2 COMPLETE

Shakira..
3/26/22, 22:59 – Ummi Tandama😇: GMB2🅿ï¸?22

Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488

After 1 week

Bayan Sati Daya da Tsaida Lokacin Bikin Tarewar Inteesar da Imran ta kowani bangare Shirye shirye yana ta Gudana,Domin Baffa Kabiru yace Umma Zatayi Taron Bikinta a Kaduna ne,Yayinda Inteesar zata koma Wajenta Angawaye zasu Dauko Tawagan Amarya zuwa kano Gidan Abba inda Suma zasu shirya nasu Taron Bikin.
Imran Dayaji haka mamaki ya kamashi yace shi kuwa ba zai je kaduna ba,Wannan ai Wahala ce Abba yace sai dai kada yaje ammh Tabbas Inteesar zata koma gaban Iyayenta achan zasu yi Taron Bikinsu,Shuru kawai yayi ammh acikin Ransa yace ba Inda zai je kafar Daya kaita sai ya Daukota ya Dawo da ita.
Baffa Kabiru shi ya karbi Ragaman komai gabadaya Tsarin komai sshi ya Tsara shi da Daddy sun zo har Kano sun ga Sabon Office din Abba sun saka albarka suka kwana Daya suka koma a kuma zuwan ne Baffa Kabiru bai Duba Girma da Shekarunsa ba ya nemi Gafaran Imu saboda yasan yaKullace shi kuma shima yasan bai kyauta ba.
Imran bai isa yace bazai yafe ma Baffa Kabiru ba Tunda ya gano kuskuransa,Daman kuma Mami Asma”u duk ita ke kara sakashi aikata Wasu abubuwan,Yanzu kuma bata nan Yusuf ya kyankyasamai Rabuwar Baffa Kabirun da Mami Asma”u Dalilin Zuwan Abba Kaduna suka Tafi Tare da Daddy a Abuja har acikin Ransa Dadi yaji kuma acikin Ransa yana addu”an Allah yasa Kada su Daidaita sai Daga baya ya Fahimci itace kan Macijin Shi kuma Baffa Kabiru ne gangar jiki kuma kai Shike Sarrafa Dukan jiki.
Inteesar Amarya kuma ba Lokaci Saboda suna ta Test da sun gama kuma Zasu Fara Jarabawa da suka Lissafa zata tare Ranar Lahadi,Ranar Monday da Safe zasu Fara jarabawa basu da Lokaci Zamansu kadan ne shima na Karatu ne ga kuma Shirye Shirye.
Basu cika Haduwa da Imran ba Saboda Sanda zasu Tafi makaranta Shi ya Tsufa a wajen aiki in suka Dawo kuma wani Lokacin suna Gidan Mama,In kuma suna gidan Abba Shi kuma yana ciki yana aiki Bisa System dinsa.
Sai dai kamar yadda Munari ta bata Shawara bata yar ba Tana Turamai Sako Kullum da Safe na Gud Mrning da kuma na Gud Night Tana Kiransa bayan kwana Biyu Taji Lafiyarsa,Kuma hakan yana ma Imran Dadi sosai yayi mata Uzuri Domin yasan Karatu ne yayi Zafi ga Test kuma yasan sun kusa Fara Jarabawa abakin Sagir yaji Tunda shi Sagir din suna ma Jarabawar ne ta shiga aji Hudu Shiyasa basu cika Haduwa ba Dukkansu basa Zama.
Akallah dai yana jin Dadin ta basa Girmansa kuma ta Daraja Mtsayin Miji Dayake awajenta shima in yajita Shuru yana Kiranta yaji Lafiyarta Bai isa ya karyanta yana son Inteeaar ba Domin Duka Motsinsa Tana cikin Ransa ne Ko wajen aiki yaje itace makale acikin Ransa,Tayi kane kane Zaman da bazata iya Fita da karfi da yaji ba Domin ta shiga a Hankali ne Batare Daya sani ba.
Batare da Sanin Imran ba Sagir Ya Dauki Lambar Khalil a Wayarsa ya Kirasa ya Fadamai Halin da ake Ciki Saboda Imran yaki yarda ya basu Halin kai ga su Munari sun Dage sai sunyi Shagali a taron Bikin nan.
Khalil bai yi mamaki ba Domin Lokacin yaji labarin Auran Imran din ammh a bakin Abbansu Dr.Isa Ali Argungu shima Abba ya Fadamai ammh Shi da Imran bai Fadamai ba,kuma alokacin Auran Sajida ne so bai san an samu wani Sauyi ba kuma shima Sagir din bai Tsaya mai Bayani ba.
Khalil yace kada ya Damu,ya bada Lambarsa a sakasa cikin Group din sai su Tattauna,Daya fadamai abunda Imran yace bamai mai Bidi’a abikinsa khalil yace wannan mganar Banza ce sai anyi Bidia ko yana so ko baya so Ai ba Jiransa zasu yi ba su zasu Shirya komai.
Haka kuwa akayi Sagir ya baama Munari Lambarsa ta saka cikin IMSAR Together,Sun ji Dadin Tattaunawa da Khalil She is Very Friendly,Duk da shima yana da Miskilanci Sai dai bai kai Imran ba,Dashi da Sagir kadai ne abokan ango Su kuma suka Dauki Ragamar Tsara komai,Sum bama su Munari Damar su Rubuto Abunda Zasu Shirya na Event su kuma su Duba su ga abunda zai yuyu din
Munari da Tasleem da Hafsah Da Nasara suka Zauna suka Tsara abubuwan da zasu yi,Sunce zasu yi Bridal Shower sai kuma Lonching,Da suka Fada musu Khalil yace su kuma Zasu Shirya Dinner da Walima mata Ranar Lahadi in an kawo Amarya da kuma addu”an Bude Sabon Gida da wannan Shawaran suka Tsaya Kuma duk wannan Tsara Tsaran Imran bai san anayin su ba Daga Sagir din Har Khalil din ballatana Inteesar da sai sun Tattauna Take jin mganar a bakin su Munari.
Umma ta shirya ma wannan Bikin na Autarta ita da Daddy shima ya Sakarmata kudi sosai,Inna Maimunatu ita ta fito da ankon yinin Biki,Less ne Rantsattse mai kyau Daga Bangaran Umma Tunda ita Zatayi Tarinta Ranar Jumma”a ne asabar da Safe Zata taho da Inteesar Kano Akuma Ranar ne Anty Safiya Zata Gudanar da Taronta itama Wanda ya Yusuf da Abba suka bata goyon baya Itama ta Fidda ankon Material Mai kyau mai yarari na yinin Bikinta Shiri suke sosai Domin Yusuf yace suma Harda Taron Bikin da basu yi ba nasu Zasu Hada suyi Tare zasu gayyaci Mutane Dabam Dabam domin suzo su tayasu Murna.
Baffa Kabiru Inna Maimunatu ya bama Kwangila Hada kayan Lefen Inteesar Kudi kawai ya Tura mata Lokaci Daya sai dai ta Kira Intee ta Tambayeta Size din abubuwan amfaninnta,Ita da ya”yanta suke Hada kayan Zainab da karima Tsadaddun kaya na gani na Fada sai Wanda ya gani ba Ha”inci ba zamba cikin Aminci.
Mganar kayan Gida kuwa sun gama mgana da Kamfanin Marhaba Kudi kawai suke jira ya Tura musu zasu zo su Kawata gidan sai wanda ya gani Dagachan bangaran Umma kuma Tana Siyayyan yan abunda ba”a rasa ba,Mama taje ma tayi Sati a Wajenta suka gama Shawara bayan ta dawo ta Dawo da kayan wanka na Lalle da su margaya ta jikama Inteesar aka Zuba Ruwan Turaruka Kala kala Inteesar tana wanka Dashi Safe da Rana sannan ga mgungunan Infection na Gargajiya shima Maman ta Dake ma Inteesar din tana amfani Dashi.
Yan”uwa kowa yana ta zumudin Bikin banda Inna Bintalo da abun bai Dadata da kasa ba Dataji Labarin Abun Alherin Baffa Kabiru cewa Tayi bai da zuciya Tunda har za”ayi ma yarsa wannan Sakin Wulakanci kuma yazo yana Rawan jiki,Ba wanda yasan Tanayi bama abi ta kanta ba Itace ta Fara Kiran Mami Asma”u ta Labartamata komai,Jikinta yayi Sanyi ta kuma kara Tabbatar ma kanta Kabiru dai da gaske yake ya Rabu da ita Tunda gashi ya Shareta har yau bai nemeta ba kuma gashi ya Daidaita da yan”uwansa Har yaje yana Kashe kashen Dukiya saboda wanda ya Lalatama yarsa Rayuwa ya maidata Bazawara duk da Taji mganar Tarewar abakin Umaima bata Zata Lokaci kadan aka Saka ba Mami Asma”u da Inna Bintalo kadai take waya a Dangin Baffa Kabiru kowa ya kamasa kansa da ita da yawa ma basu san abunda ya Faru ba itama Inna Bintalo Ta Kira Mamin ne tana mata Tsegumin da Saninta Baffa Kabiru ke Kashe kudi haka Sai kuma taji Labari mara Dadi ita kuma ta Fadama Inna Maimunatu wacce ta Tabe baki afili ta Furta Ya kabiru yayi min Daidai Wlh..Allah ya kara mganinta kenan!
Ganin Bata samu Fuskar da Zata kawo Wata mgana ba yasa ta kama kanta Musamman ta Shirya taje Dukku Tana yima Daada mganar ita azatonta bata Sani ba Daada ta nuna mata Babba babba ne bata nuna mata ba Taji ba Sai ta Nuna mata abakinta ma take ji ballatana ta Fadamata yadda sukayi da ya”yanta nata taja bakinta ta Tsuke sanin Halin Bintalo akwai Daukan mgana sannan suna Dasawa da Mami Asma”u tana kuma da Tabbacin Mamin Asma”un ne ta gayamata yadda akayi ammh tasan Kabiru Ko Mustapha ko Malami ba wanda Zai kira Binta Domin ya Fadamata wata mgama shiyasa tayi mata abun nan da ake cewa ta yaro kyau take bata Karfo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button