
Sajida Tana makaranta bata san Abunda ke Faruwa ba saboda ta yanke alaqa da duk wani abunda zai Karamata Mikin Dake cikin Ranta Da Umaima kadai sai Dad take mgana ta Sauke Duka Kafar sada zumuntar Dake Wayarta sun gama Test suna gabda Fara Jarabawa ammh bazasan Hakikanin Abunda ta Rubuta ba,Gadai Tanan nan kaawai Ta Rame Duk ta lalace kamar ba Sajida yar gayu bai ji da kanta da Takama da komai ba.
Ita kanta sani Tana da Cuta acikin Zuciyarta Har ta koma ga Allah Bazata Daina son Imran ba ba ita ta Dora ma kamta ba Allah ne ya Dora mata kuma bata isa tace Zata yaye ma kanta ba,Sai dai ta Dauki alhakin komai ta Dorama Mami itace Silar komai Sannan Daya Daga Cikin Ayyukan Mamin ne ita ta Girban mata Sakamako ne take gani ta Dauki hakan a Mtsayin kaddaranta Tunda Duk Zuwan da Dad zai yi wajenta ko ya Kirata a waya Nasihar shi da ita kenan yana Shiga Damuwa in ya ganta Ta Rame duk ta saki Ta Zama wata iri kamar ba Sajida ba
Bata da kuzari kamar mara Ishashen jini ajikinta ko Ruwa bata Farinciki Koda yaushe Cikin kunci in Ta gaji da Boye abun acikin Ranta tayi ta kuka Karatun ma bata Fahimtar sa kawai yinsa Take yi ba wai tasan ina Take ba ko ina Zata ba..!Jenefer kamta da suke Zaune Daki Daya tasan Sajida Ta Sauya haka ma abokan Karatunta da kawayenta Kowa Sajida What Wring..?me zata ce..!nayi aure ban Tare ba Mijin ba ya Sakeni..?kuma Duka Uwata Data Haifeni ta Ja Faruwar haka?bata da karfin Gwiwan bada wannan labarin amsarta Dayane bakomai ba abunda ke Damunta alhalin ita kanta ta sani Tana da Cuta acikin Zuciyarta Cutar da Sanadinta Mami Asma”u indai ta Fara Bin Ra”ayinta Tun Farko da ta Tabbata abunda ya Faru bazai Taba Faruwa ba.
Abakin Umaima take jin mganar Tarewar Inteesar din da Imran alokacin Sauran kwana Goma Sha Biyar,Ta zo Dubata tayo mata abinci da Miya Direba ya kawota Ranar asabar,ita kanta Umaima tayi ta ma Sajidan Korafin Ramarta Sai tace mata Stress din Karatu ne anan nema Umaima ke Nuna mata ankon da Munari ta Turo mata Guda Uku Less,na Dinner sai Wani Material na Bridal Shower sai Atamfa na Yinin Biki shi kuma za”a saka aje Lonching ta Nuna ma Dad yace ta zo ta nuna mata In tana Bukata sai a Daukan mata Sajida tace Bata Bukata bazata samu zuwa taron Bikin ba Saboda Lokacin sun Fara jarabawa Umaima bata Mtsa mata ba nan ta wuni Tare da ita akallah dai ta Debe mata kewa Umaima ta Tambayeta ko suna mgana da Khamis tace mata basa mgana Tun Dawowarta makaranta Cikin Damuwa Take sanar da ita basa samunsa ta waya Harta kuwa da Baffa Kabiru baya samun Khamis din Waya Sajida ta ce kila yanayin aikinsa ne kamar yadda Umaima ta Tambayeta Baffa Kabiru ma ya Kirata ya Tambayeta tace basa mgana bata Duba ammh Tana da Tabbacin shima yana chan yana Fama da Zuciyarsa kamar yadda itama take Fama anya Mami ZAta gama da Duniya Lafiya kuwa..?Tabar ganin Tana da Mtsayin Uwa a wajensu kamar yadda Take da Hakki a kansu suma suna da Hakki a kanta Sai dai bata Duba wannan ba Daga ita Har Khamis batayi musu adalci ba.
Umaima Tazo asabar Mami Asma”u ta shigo Cikin makarantar Ranar Lahadi,Daga Office take taje Duba Wasu Takardu shine ta Biyo ta makarantar su Sajidan Tunda ta Rufe Duk Hanyar da Zata sameta suyi mgana Mami Asma”u ta yanke Shawaran ta zo ta samu Sajidan suyi mgana Taji menene Nufinta..?ta sauya taa ne a Mtsayinta na uwa ko yaya..?
Har Hostel din ta shigo Dakin da su Sajidan suke Sajida na kwance Tana Fama da Tunanin Data Saba a koda yaushe Karatu take yi ammh bata Fahimta Sai da ijiye ta koma Tana Tunani Zuciyarta na mata suya Hawaye suna Zubomata in ta Tuna da kalaman Imran akanta Son maso wani Take yi Domin a gabanta a gaban Kowa da kowa ya Tabbatar mata da baya sonta kuma bazai Taba Sonta ba Har Abada.
Duk Sadda Ta Tuna da Wadandan kalaman sai ta kwana kuka Kirjinta yayi mata Nauyi yana Suya yanzu din ma kukan take ita kadai acikin Daki Jenefer ta tafi gida Weekend bata nan Sai ga Mami Asma”u ta shigo.
Dukkansu sunyi Shock da ganin junansu Sajida tana kallon Mami yadda Ta koma duk ta wani Fige kamar ba ita ba,Idanuwa sun Zurma Daga gani bata Samun Cikakken Barci Ballatana Kwanciyar Hankali ita kuma Mami Asma”u ta Firgita sosai na ganin yadda Sajida ta Rame tayi baki ta koma kamar Wacce take cikin Wani Cuta.
Sajida ta gabatar ma da Mami Ruwa da Lemo Tunda suna da Fridge acikin Dakin,Mami bata iya ko shan ruwa ba Ta Fara Tambayan Sajida me ke Damunta..? bata da lafiya ne..?meya sameta..?
Sajida kallonta kawai take yi Lalle ne ma Mami Tambayanta ma take yi me ke Damunta..?ita bata sani bane..?
Ai tafi kowa sanin Damuwarta Tunda itace Silar Shigarta Cikin Wannan Halin batacemata komai ba illah Shuru Da tayi mata tana Binta da ido.
Ta Zata Sakin da Dad yayi mata zai saka ta Sauki ta gane kuskuranta Sai dai a kalaman Mamin Gabadaya ba Nadama Illah kara Kaucema Hanya.
Tunda tazo take Zagin Daada Tana Dora alhakin komai akanta
Sajida Tagumi Ta Zabga Tana kallon Mamin Sadda take Fadin”Sajida kema kin Gujeni ko..?kema Daada ta Rabani Dake kamar yadda ta Rabani da Babanku..Ga Yayanku shima Tunda ya Tafi ban kara Samunsa a waya ba..Sajida nasan kina jin Haushina ko.?miye Laifina na..?miye Laifina Domin na so ya”yana na Nuna ma Duniya kune Duniyata..? Sajida wannan yakin saboda ke nake yinshi Kalleki yadda kika koma da Kuruciyarki da komai an Bata Miki Rayuwa an maidake Bazawara da karfi Da yaji wannan wani irin Abun kunya ne..?in na Tuna wannan abun sai naji kamar na Kashe kaina Saboda Takaichi kuma na mike Zan kwatar Miki Yancinki Dad din ku ya Sakeni Sajida kuma kun juyamin baya,Nasan kan wannan yaron kike Rama Sajida ki Kwantar da Hankali kefa Diyar Asma”u ce da Kabiru Gangariyan Miji yana nan zuwa Miki wanda yafi wannan yaron komai da komai ki cireko aranki Domin bakya gabansa Bikin Tarewarsu ma da yar Wajen Salahan ya kusa Babanku na chan yana Kashe Kudi Kinga fa Bintalo ta gayamin Shi zai yima Mara Mutumcin yaron nan Kaayan Lefe Ita kuma Inteesar din shi zai yi mata kayan Gida Gabadaya shi bama ta ya”yansa yake ba yana chan yana Kashe kudin Inda aka ci Zarafinsa aka Sauke Darajan yarsa Sajida ina Cikin Damuwa bana iya barci Babanku bai Nemeni ba bai Nemeni ba Yana Nufin ya Rabu dani gabadaya kenan..?Umhm..Shikenan ai Barrister Asma”u bazatayi kwantamai ba Zan samu Mijin Dayafisa komai da komai Tunda shi Daada ta shiga Tsakanina dashi ita da su Mustapaha..!
Take fada Tana Hawaye kallo Daya Zakayi mata kasan bata cikin Hayyacinta Surutai kadai take yi bata san me take fada ba Damuwar take cinta ne take Furta batare Data sani ba
Ance Uwa uwace ko da kuwa Mahaukaciya ce,Tuni Tsausayinta ya Sarke Sajida duk da kuwa Tana Fushi da ita Tun bayan Faruwar Lamarin ammh ganinta Cikin Wannan Halin Tana kuka ya karya mata Zuciya Rauninta ya bayyana ta Rungume Mamin Tana Fadin”Mami u are not Well..Bakya samun barci muje asibiti a Dubaki plz..!
Mami Asma”u na kuka Share Share kukan da Tuntuni take son tayi bata samu Kafadan da Zata Kwanta Tayi kukanta ba,Tabbas Tayi Rauni ta kuma gaza Duk kuwa da Taurin kanta wannan karon ta gaza ta yardan ma kanta Mijinta da ya”yanta ne Duniyarta Da kuma su take Takama yau da basu Tare da ita Rayuwarta ta Zama cikin Wani Hali Halin kakanikanin da bata Taba Tsammanin Zata shigesa ba batama Dauka abubuwan zasu Dakule mata haka ba.
Sajida kuka Mami Asma”u nayi Kafin Sajida ta Tsagaita da kukan ta ta Share Hawayenta Mamin na Bukatarta a wannan Lokacin,Fiye da yadda ita take Bukatarta.
Mikewa Tayi Tana Fadin”Mami Tashi muje asibiti a dubaki..Bakya barci Idanuwanki sun kumbara..!
Mami Asma”u batayi gaddama ba bata Barci,Ga ciwon kai Datake kwana Dashi batayi ma Sajidan Musu ba ta Jirata ta sako Mayafinta Ta Riko Hannunta bayan ta Rufe Dakin…
Specialist Hop suka je inda suke da Fayel Dr.Barau ya Duba Mami Asma”u ya Tabbatar mata da jininta ya Hau Saboda Damuwa da Rashin Barci ya Rubuta mganguna sosai da Shawarwari ga Mamin,Bayan an dubata ta Mtsa Sajidan ta Zauna itama a Dubata ta ki yarta tace ma Mamin itafa bakomai Strees ne na Karatu kawai ba Domin Mamin ta yarda ba ta kyaleta sai da Mamin ta koma ta Maida Sajida makaranta Kana ta Tuka kanta zuwa Gida.
Da hajiya Turai ta ganta ta Dawo Cikin wani yanayi shine take Tambayanta tace mata Wajen Sajida Taje Daganan ta Rakata asibiti taga Likita Jininta ya hau.
Hajiya Turai ya kyabe baki Tana Fadin”Uhmm..Asma”u kenan kaza mai ya”ya..Ai kulafacin Kabiru da ya”yansa Kadai aka barki ba Jininki ne bane zai Hau ba har Bugawar Zuciya Zaki iya samu..yarinya kina Wahala kanta bata sani ba..Ta Debeke ta Watsar ke kuma kin kwashi jiki kin Bita kamar itace Uwar..Wannan Bakin Halin na Fulanin Dukku sun kwasoshi Wajen Ubansu shi kuma ya kwaso wajen wannan Kafaffiyar Tsohuwar..!
Mamin dai na jinta bata Tanka mata ba ta Shige Ciki gabobinta sungaji so take ta kwanta Maltina ta Dauko ta sha ta Sha mgani ta koma ta kwanta Tana Sauke Numfashi sai kuka Allah Sarki Rayuwa yau ina Brr Kabiru..?ina Khamis..?ina Sajida..?ina Umaima..?
Basa Tare da ita Sai ita kadai Tayaya ko Zuciyar Karfe ce da Barrister Asma”u bazata Raunana ba Ya”yanta da Mijinta fa sune Duniyarta.