Hausa Novels

Lu’u Lu’u 31

*31*

 

Wajen Ayam kuma d’aki suke ita da Juman inda ta tambayeta a tsanake “Mah, a game da lamarin ruwan garin nan, yau nayi magana da wasu daga cikin talakawa sun fad’a min komai, ya zanyi na taimakesu akan haka?”

A tsanake ita ma tace “Ayam ai maganar ruwan nan kasuwanci ya shiga cikinshi, duk da gwamnati na iya yin ta, bana jin zaki iya wani abu tunda baki da abu biyu.”

Da alamar tambaya ta kalleta tace “Kamar ya Mah?”

Numfashi ta sauke tace “Na d’aya baki da kud’i, na biyu baki da iko.”

Da mamaki tace “Idan ina da su kenan zan iya taimakon al’umma?”

Jinjina kai tayi tace “Tabbas, idan kina da kud’i zaki iya taimaka musu, idan kina da iko zaki mallaki dayawa daga cikin masu fad’a a ji.”

Shiru tayi tare da fad’awa kogin tunani, sai ta ga bata da wad’annan abubuwan, da sauri ta rik’o hannun Juman tace “Mah, ke fa? Ai kina da iko saboda ke ce sarauniyar k’asar nan, kuma nasan kina da kud’i ma.”

Murmushi tayi ta girgiza kai tace “Bana da ko d’aya yanzu Ayam, sanda mahaifinki ya jefani kurkuku ya datse min asusun bankina, gaba d’aya masarautar nan yanzu ba zan iya saka baki a abinda ya shafeta ba.”

Da mamaki a fuskarta tace “Saboda me Mah? Na d’auka yanzu ai kin fito.”

Sake fad’ad’a murmushi tayi tace “Ayam kenan, kafin ya fito da ni saida aka fad’a min na wucen gadi ne.”

Cike da alhini a fuskarta tace “Mah…na kasa yarda Pah duk yake wad’annan abubuwan, har yanzu bana jin wani iri a jikina idan na ganshi.”

Lak’ace hancinta tayi tace “Saboda yana mahaifinki ne mana, soyayyar dake tsakaninku ba zata bari tsoro yayi tasiri a kan ki ba.”

Ajiyar zuciya ta sauke bata sake cewa komai ba, haka ita ma Juman ba tayi magana ba, saidai dukansu da abinda suke tattaunawa a zuk’atansu.

*08:30* Na dare ta fito cikin wasu had’add’un kaya na masarauta wanda suke jan k’asa har da babban mayafin da aka d’ora mata a kai amma ya sauka a baya, karo na farko a rayuwarta da aka shafa mata jan baki kalar leb’enta pink, bayan yau kam bata tab’a sakawa ba, tana dai shafa man leb’e amma ba jan baki ba.

Sanyayyan k’amshinta ne ya fara sanar da su tana zuwa, suna juyawa a tare da sauri Haman ya mik’e tsaye dan sak sarauniyar Khazira idonsa suka gane masa, hakan yasa shi saurin mik’ewa da girmmawa yana neman gaisheta.

A b’oye Umad ya ja rigarsa ya d’an motsa labb’ansa yanda ba kowa zai gane ba yace “Kula fa, kar ka kwafsa.”

D’an gyara tsayuwarshi yayi ya saisaita kanshi ya dakata daga hard’ewar da yake shirin yi ya rusuna mata, da k’ayataccen murmushi ta k’araso a nutse zauna tare da nuna masa zai iya zama, zaune sukayi a tare inda ta d’an k’yallara idonta ta kalli Umad.

D’auke kai tayi ta kalli hadiman da suka rakota, a nutse kamar wata sarauniya ta furta “Zaku iya tafiya.”

Saida suka rusuna kafin suka nufi hanyar fita, saida ta ji sun rufe k’ofar sannan ta kalli Umad dake tsaye bayan Haman k’ik’am, sauke k’arar data d’ora kan d’aya tayi ta gyara zamnta cikin yanayinta data saba tace “Me ye haka yallab’ai? Duk wannan shirin na miye? Me ye wani neman aure na da kuma mai tsaro?”

Haman kam mik’ewa yayi ya koma kusa da Umad yace “Zai miki bayani, duk shirin sa ne wannan.”

Kamar a rashin sani ta mik’e tsaye tare da wurgawa Umad wata harara, takawa tayi har zuwa inda suke tsaye, da yatsa ta shiga masa k’wak’waran kashedin “Ka ga yallab’ai bana so, bana son wannan bibiyar da kake min, idan har gaske ne rayuwata na cikin had’ari, to ka barni na mutu bai dameka, amma ka sani idan har wani abu ya samu mahaifina a zuwan nan na ku, wallahi Allah sai ka gane kurenka.”

Jujjuya d’an k’aramin bakinta tayi ta juya ta barsu tsaye baki sake da mamaki, bugo k’ofar da tayi bayan fitarta ne yasa Umad sakin wani lallausan murmushi yana girgiza, wai shi ta kalla duk da matsayinshi a gareta, da kuma matsayin da Allah ya masa kasancewarsa mai jiran gado, bata duba kasantuwarshi na malaminta ba ta kalleshi ta nunashi da yatsa sannan ta ce wai *zai gane kurensa*.

Shafa sumar kanshi yayi ya zauna kan kujera yana furta “Zakanya, ni ne zan gane kure na?”

Jinjina kai yayi yace “Zan gani.”

Da sauri Haman ma ya zauna yana fad’in “Ka ga Umad dan Allah ka fad’a min me ye shirin ka? Ni wannan shirun da ka min ina bin uamrninka bana son shi wallahi.”

Kallonshi yayi fuska a had’e yace “Zan fad’a maka, ka k’ara hak’uri kawai.”

Jinjina kai yayi yace “Shikenan zan jira.”

Tana komawa d’aki ta samu Juman ta shiga fad’a tana fad’in “Mah ni wannan kayan sun isheni, cirewa zanyi.”

Dariya tayi tace “Zaki fara sabawa da zaran kin zama sarauniya.”

Kallonta tayi kamar zatayi kuka tace “Haba Mah, ki daina fad’a mana.”

Jinjina mata kai tayi tace “Na ga wannan ranar Ayam, na ga haka a mafarkina, saidai nasan ba lallai mafarki ya zama gaske ba.”

K’ala ba tace ba saida ta cire kayan nan ta d’auki wata sassauk’ar riga a cikin wanda aka kawo mata ta bacci ta saka, warware gajeran gashinta tayi wanda har yanzu yake tohowa ta sakeshi dan ya sha iska, kan gadon ta kwanta ta kalli Juman tace” Mah, yau na farko a rayuwata ina so na kwana tare da ke kaina a kan k’irjinki.”

Dariya tayi tace” Baki da matsala gimbiyata, ni ma zan so hka duba da yau zan yi bacci a nutse hankalina kwance.”

Da mamaki tace” Saboda me Mah?”

Cikin rad’a da fara’a a fuskarta tace” Saboda Umad na gidan nan, ganinshi ya bani k’arfin gwiwa, duba da shekarun dana fara had’uwa da shi da kuma yanzu.”

Girgiza kai tayi ta buga hannunta akan cinya alamar” Haba mana Mah.”

K’yalk’yalewa tayi da dariya tace” Da gaske nake fad’a miki.”

Turo baki tayi tace” Ni da yanzu mana fad’a masa ya daina bibiyata, ni sam ban wani yarda da shi ba.”

Kallon tuhuma ta mata tace” To da kike jin haka a game da shi, me ya hana ki fad’awa mahaifinki?”

Jim tayi sai kuma ta d’aga kafad’a alamar bata sani ba, matsawa Juman tayi kusanta ta ja dogon hancinta tace” Ko dai ko dai? Ko dai akwai abinda k’aramar yarinyata ke b’oye min ne?”

Rik’e hannun Juman d’in tayi data ja mata hanci da shi tana k’yalk’yala dariya tace” Mahhhh…hancina fa, ni ba wani abu da nake b’oye miki, d’azu ma ba’a gabanki na saka kaya ba?”

Janye hannunta tayi daga hancinta sai kuma ta shiga mata cakulkuli tana fad’in” Ban yarda ja’irar yarinya, fad’a min me kike ji a kan shi? Da alama idan baki zama sarauniyar Khazira ba zaki zama sarauniyar Giobarh.”

Cikin farin ciki suka dinga wasarsu har Juman ita ma ta canja kayanta suka kwanta, daga kwance ma duk abubuwan da zasu anfaneta a cikin addininta ta dinga sanar da ita, k’aramar wayar da Ayam har ta manta ta ta ce sak’o ya shigo, d’auka Juman tayi ta mik’o mata tace “Wayarki.”

Karb’a tayi tana duba wayar dan har ta manta wace kala ce ma, bud’e murfin tayi ta duba sak’o gajere kamar haka _”Ki ji magana ta, bayan d’akinki da na mahaifiyarki ki kwana a ko ina ki ke so, idan kuma kina son kasancewa cikin tsaro, to ki kwana a k’ark’ashin kulawar Umad.”_

Tashi tayi zaune tana sake karanta sak’on, me hakan ke nufi kuma? Wa ye ya turo mata sak’o haka? Gashi dai lambar ma a rufe take, tsaki tayi kawai ta rufe wayar ta aje gefe ta koma ta kwanta.

Cike da kulawa Juman ta kalleta tace” Lafiya? Me ya faru?”

Ba yabo ba fallasa ta amsa da” Ba komai.”

D’ora mata tayi daga inda suka tsaya ta ci gaba da fad’in” A duk wani hadisi daya tabbata kuma ya zo daga iyalai ko sahaban manzo (S. W. A) babu wanda ya nuna Annabi Muhammad yayi wankan tsarki wanda ba cikakke ba, ma’ana wankan da bashi da alwala, amma magaba sun inganta wanka da baya da alwala ma, wasu daga ciki sun ce ko da a cikin kogin ruwa ka tsumbula da niyyar wankan janaba to yayi, haka ma idan a buta ne ka d’aga ka kwarara a kan ka shi ma yayi…”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button