GOJE

GOJE 13 and 14

     FREE PEGE

13&14
Sosai yayi namijin kokarin tunkarar inda take kafin ya karasa ya cire duk wani kawazucin dake cikin zuciyarsa yana isa ya bude mata wuta sosai yana mata fada tare da nuna mata illar abinda ta aikata.

Tsaye ta mike tana masa wani irin kallo kafin tace.”Wai shin ubana ne kai da zaka zo kana min tsawa ina ruwanka da rayuwata, idan har baka san ganina a haka to kayi gaggawar mayar dani inda ka daukoni.”

Ya nuna ta da yatsa kamar zai tsole mata ido Yace.” Banyi ra’ayin haka ba kuma ke baki isa kisa na tafi ba tare dana shirya tafiya ba, idan kina san kanki da arziki ki dauki rigarki kasa a jikinki.”

Ta nuna masa jikakkiyar rigar dake yashe a gefe, ya kalleta da fadin.” Meye manufarki na jika rigarki da ruwa ko kinyi hakane don kija ra’ayina akanki.?

Wulakantaccen kallo tayi masa kafin tace.”Allah ya kiyaye meye abin sha’awa a tattare da kai da har kake wannan maganar.”

Ya zuba mata jajayen idanuwansa yana kallo, ta gyada kanta idonta a soye a kansa tana kara tabbatar masa da maganarta.

Yace.”Idan babu abin sha’awa a tattare dani to ni naga abinda ya burgeni a jikinki kuma ke zaki janyo na aikata abinda ba shikkenan ba.”

Gabanta ya fadi da jin furucinsa, amma bata saduda ba, ta ya mutsa fuska da fadin.” Da kuwa nayi maka illah! domin ka kuskura ka keta min haddi wallahi sai ka dawwama a daure. a kurkuku.”

Leb’ansa yasa a bakinsa ya dan ciza kafin ya furzar da wani irin huci! yace.”Baki san ni bana d’auruwa ba? ko ba kiji sunana ba GOJE! nake ko kuma ki kira ni da MAI DAWA! Babu wani mahalukin da ya isa ya tunkari inda nake ban ci Uwarsa ba!”

Sai ta tsargu! ta nuna kirjinta da hannu da fadin.” Ni kake zagi ko? shin ka san su waye iyayena a fadin kasar nan kuwa”?

Ya gyda kansa da fadin” Babu ruwana da ko su waye iyayenki ni na fada miki wanene ni! babu wanda ya isa ya daureni ba tare dana rikirkita masa al’amuraba.”

Ta dinga kallonsa tana mamakin furuncinsa, babu wanda ya isa ya daureshi ba tare da ya rikirkita masa al’amuraba ba.”

“Kana nufin kafi karfin hukuma kenan.”? tafada idonta a tsaye a kansa.

Tsaki! yaja mai karfi kafin ya nuna kirjinsa da fadin.” Ni nan! ni ne hukuma! duk wani mai bukatar kwanciyar hankali a kasar nan to kada ya ta’boni.”!

Cike da Izzah! da jin kai ya fadi maganar, kai daga jin yanda yake magana kasan akwai abinda da ya taka.

Ta sunkuyar da kanta tana mamakin furucinsa wato shi bai yarda ma akwai hukuma ba! to bari ta ta’bashi taga abinda zai yi.

Yanke shawarar zaginsa tayi, ta dago kai suka hada ido, yana tsaye kikam! a kanta, tsoro ta cire
Cikin turanci ta fara zazzzaginsa tana kiransa da sunayen dabbobi…….. Iyakacinsa secondary skull turancin nata yayi tsayi sosai da kyar ya fahimci wasu kalmomin mussaman sunayen dabbobin da take kiransa dashi.

Bahagon mari! ya kifa mata a fuska a take taurari masu haske suka gilma, ta rintse idonta hawayen azaba na zuba!

Tana cire hannunta daga gurin shatin yatsunsa suka fito radau!

Ta tsira masa ido gabanta sai faduwa yake, tunda take a duniya babu wanda ya taba fitar da hannu ya tsinka mata mari sai shi.

Ta dinga bin sassan jikinsa da kallo, shi kuma yana dogare a kanta yana tsuma! da alama tsumin ne ya tashi.

Kafin kiftawa da bismillah tayi wani tsalle sai kace aljanna ta fizge kaifaffar wukar dake soke a gaban rigarsa.

Ta rike da kyau! tana kallonsa da fadin” Sai na zubar maka da jini yau! GOJE! kake ko? har kana Ikirarin cewa wuka bata huda ka, bayan haka yaranka suna kumbura maka kai kana d’aukar kanka wata tsiya! to yau ni zanyi ajalinka.”!!

Da gaske take domin hannu bibbiyu ta ri’ke wukar da kyau sai huci take! tana mazari! kanshi tayi da wukar zata yankeshi, ya kauce! tabi iska! a sukwane ta sake kai masa sarah! ya kauce ta sake bin iska! dariya ta kusa kufce masa ganin yanda ta dage! wai dole sai ta yankeshi da wukar wanda duk kokarin da take a banza bata samu damar saka wukar a jikinsa bama ballanatana ta fitar mai da jini.

Haka suka dinga bugawa ya dinga watangaririya da ita yana bata wahala! ta galabaita mutuka gumi duk ya jika mata jiki shi kanshi tsumman data daure cinyoyinta dashi ya kwance,ribbon din data d’aure gashinta dashi ya cire ya fadi kasan gurin, kafafunta sunyi bududu! amma saboda tsabar karfin hali taki saduda!.

Yana sane ya dinga bata wahala sai da ya tabbatar data galabaita sannan ya murde hannunta ya kwace wukar! faduwa tayi a gurin tana wani irin kukan bakin ciki!

Tausayi ta bashi! wannan artabun da sukayi koda namiji ne zai ji jiki ballantana mace irinta da bata saba da wahala ba, yayi mamakin karfin halinta mutuka.

Kusa da ita ya tsuguna yana duba kafafunta duk ta taka k’ananun k’ayoyi, hannu yasa domin cire mata k’ayoyin ta harbeshi da kafa daya, kallonta yayi cikin zafin nama! ta ciko hannu da kasa zata watsa masa ya kautar da fuskarsa, ta watsawa iska. tana daga kwance tana nishi ta cigaba da cin mutuncinsa da turanci, hakan be dameshi ba tunda ya kaita kasa bukatarsa ta biya.
Duk buge-bugen da take bai hanashi ciccire mata kayoyin da suka huda kafafunta ba, ya cire rigar jikinsa ya rufa mata a jiki.
Da sauri ta cire ta jefar da ita.
Yace.” Ni zan iya kawar da kwadayina akanki amma kika yarda wata dabbar ta gilma ta hangi tsaraicinki ba zaki kai labari ba, bayan dabbobi akwai aljanu a gurin nan kiyi hattara.”
Jin maganar aljanu yasa jikinta mutuwa idan akwai abinda take tsoro a duniya aljan ne! hakura tayi kan dole ta karbi rigar sa tasa.
Tana share hawaye ta mike tsaye, ya kalleta yana jimanta karfin halinta, wai dashi za tayi fada, dariya yayi wacce ta dauki hankalinta ta kalleshi tsantsar kyawunshi ne ya bayyana a lokacin, ganin tana kallonsa yasa ya gimtse fuska yaje ya dauki rigarta da tsumman ya bar gurin dasu a hannunsa,


Yau ma da wuri ta isa gidan, ta sameta ta shirya tsaf domin fita! A gabanta sabbin atampopi ne irinsu nicham hartget da makamantasu, cike da ladabi suka gaisa, tace.”Kinga sabbin atampopi ne Rakiya ta kawo min na saya wai itama a cikin gari ne aka bata su shine nakeso nayi musu kudi a ganinki duk daya za tayi nawa.”?

Hamra’u ta kalli atampopin kafin tace.”Uwale ke kin kasa yi musu kudi ballanatani ni da ba sana’ata ba.”

‘Yar dariya tayi kafin tace.”Don kar nace da ita dubu uku taga kamar wulakanci ne abun amma iyakacin abinda zan iya siya kenan.”

Cike da mamaki tace.”Uwale dubu uku a tamfa turmi hudu haba Uwale kiyi adalci mana shiyasa jama’a suke zaginki har suna kiranki da mummunan suna.”

Ta ‘bata rai da fadin.” Sun jima basu zageni ba! ai Hamra’u a wannan duniyar idan zaka dauki maganar mutane to wallahi babu abunda zaka tsinana, amma meye laifina don na saya dubu uku, itama ai kyautarsu a ka bata.

Tace.”Duk da haka dai sunyi arha da yawa duka cotton ne babu leda a ciki maimakon ki saya dubu biyar gabadaya.”

Tace.”Aa ba zan iya saya dubu biyar duka ba, dubu uku zan saya kuma ke da kike surutu ai idan na saya to tanadi nake miki kayan lefanki ne.”

Murmushi tayi kafin tace.”Uwale nifa jikina yayi sanyi sai nake ganin kamar burina ba zai cika ba.”
Murya na rawa ta karashe maganar.

Tace.”Aa ki daina sanya damuwa a ranki insha Allahu ba zakiyi zaman banza ba UMARU zai aureki koda baya sonki to ni zan umarceshi ya aureki.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button