GOJE

GOJE 13 and 14

Tace.”Aa Uwale ni nafi so ya aureni dan yana sona bana so muyi irin wannan auran da iyaye suke hadawa daga baya a samu matsala.”

Tace.”Insha Allahu ba za’a samu matsala ba, domin ni kaina na gaji da ganinsa a haka babu aure sa’anninsa sun jima da aure da ‘ya’yansu amma shi yana zaune a haka, idan za’a biye masa to zai kare rayuwarsa a haka wannan dalilin yasa zan tilasta masa auranki.”

Hawaye ta share tana girgiza kai, itafa kwata-kwata bata son irin wannan auran tafi so da bakinsa ya furta mata kalmar so, amma dole haka zata hakura tunda yaki gane irin son da take masa. watakila idan Allah ya kaddara auran nasu Allah ya sanya masa kaunarta a cikin zuciyarsa.

Tace.”Ki goge hawayenki ki daina kuka mutukar ina raye to kamar kin auri UMARU kin gama, shiyasa duk tsumi da tanadina ya kare akanki gashi cikin ikon Allah na kusa kammala hada miki lefe, kinga sai komai yazo da sauki.”

Tace.”Nagode Uwale Allah ya tabbatar mana da alkairi” Ta amsa da “ameen” tana kokarin tashi, Rakiya tayi sallama, gabadaya suka amsa, Uwale tayi saurin fadin.” Yanzu nake maganarki a cikin raina nace har gida zanje na kai miki kudinki.”

Tace.”To ai baki fada min nawa kika sayi atampopin ba.”

Ta ya mutse fuska da fadin.” Gabadaya dubu uku na saya domin dai kema kin san atampopin naki an daina yayin irinsu bayan hakan haka kuma sun jima a ajiye sai warin ajiya suke.”

Rakiya ta mika hannu da fadin.” Ban siyar a hakaba bani na kai inda za’a saya da mutunci.”

Baki ta bude da fadin.” Rakiya ina zaki kai a siya da mutunci bayan nan, kin san dai idan kika kaiwa Delu siyan banza za tayi miki gwara ki tsaya mu sassanta.”

Taja tsaki da fadin.” Ai har gwara Delu a kanki Uwale sai kace kayan sata zaki saya dubu uku duk daya a kasuwa dubu biyu da dari biyar ce, idan sayan mutunci zakiyi ina laifi ki saya dubu biyar gabadaya.”

Tace.” Oh!oh zan dai saya dubu hudu idan kin sallama min a haka.”

Jim tayi kafin tace.”Na siyar miki amma kada ki tsinka min kudi ki bani kudiba cif.”

Tace.”Maganar kike so Rakiya ai a inda ba kasa anan ake gardamar kokawa da ban shirya ba ai ba zan karbi kayanki ba.”

Rigar jikinta ta daga ta zuge zif din lalitar dake daure a jikinta kudi ta fito dasu, a dukunkune yawanci duk ‘yan dari biyu ne, duk sun ya mutse, Hamra’u tasa hannu suka lissafa dubu hudu kudin me kayan ta mika mata da fadin.” Gashi maganin karya hallara ki lissafa a gabana na san halinki kada ki dawo kice min basu cika ba.” Rakiya ta dangwali yawun bakinta ta fara lissafa kudin ta kalleta da fadin “Sun cika.” Tace.”To masha Allah idan an samu wasu kayan ina bukata.” Tana kokarin fita tace.” To shikkenan idan an samu zaki jini.”
Bayan fitar Rakiya daga gidan itama Uwale kayan dillancinta ta dauka ta fita, ya rage saura ita kadai a gidan, ta jima tana sakawa da kwancewa kafin ta tashi cikin sanyi jiki ta gyara gidan tsaf ta kulle da kwado, gidan Tasallah ta shiga ta bayar da mukkulin kafin ta kama hanyar gidansu, salo-salo take tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki………”Hamra’u.” da sauri ta juya jin muryar kawarta Zabbah, taja ta tsaya tana wasa da karan dake hannunta har ta karaso gurin da faratin goro da lemon tsami a kanta.

Zabbah ta karaso inda take da fadin.” Daga ina kike haka naga duk jikin a sanyaye.”?

Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace.” Daga gidan yayar mahaifina nake kullum ina zuwa nayi mata aiki kafin ta fita.

Zabbah ta fashe da dariya irin ta shakiyanci kafin tace.”Hamrau kenan wai kenan kina kamun kafa ko? wallahi kina wahalar da rayuwarki domin kaf cikar karkarar nan banga wata mace da zata ja ra’ayin GOJE! ba

Tace.” To ke Zabbah waye ya fada miki ina kamun kafa da Uwale a matsayin uwa take a gurina laifi ne don naje gidanta.”

Zabbah ta tabe baki da fadin.” Hamra’u bari na fada miki abunda baki sani ba, kaf ‘yan matan garinan babu wacce bata san halin da kike ciki akan GOJE! ba kowa ya san kece kike sonsa baya sonki kullum sai kinji kinyiwa kakarsa aikace-aikace sai kace baiwa bayan haka ance idan yana gari kece kike masa wankin kayansa ki goge ki wanke masa takalma saboda rashin hankali irin naki kin mayar da kanki yar aiki bayan baki da tabbacin zai aureki.

Tace.”Zabbah! duk abinda kika fada hakane babu karya ina san UMARU kuma ina rokon Allah yasa ya zama uban ‘ya’ya na, bayan haka kuma duk wata bauta da nake masa ra’ayi na duk surutun da jama’a za suyi akan hakan bai dameni ba.”

Ta girgiza kai da fadin.” Shikkenan ai tunda kinyi nisa duk abinda zan fada miki a yanzu ba zaki fahimta ba, saboda haka muna zuba ido muga yanda za’ayi wannan auran.

Shuru kawai tayi bata sake magana ba, ita Zabbah ce keta surutu tana bata labarin saurayinta wanda zata aura uffan bata ce ba har suka rabu da juna.

Cikin kunci da damuwa ta shiga gidansu, nan ma ta iske wani bacin ran don mahaifiyarta fada ta rufeta dashi sosai tace.”Ina ji ina gani kinfi karfina Hamra’u! saboda kulafucin namiji kullum da gari ya waye hankalinki na wani guri kisa kafa ki fita ki barni da aikin gida, kina can kina bauta a wani gurin, to wallahi nagaji ba zan hanaki ba tunda ke ki kasa kanki amma ba zaki kara fita ba sai kin gama min aikin gida.”

Daki kawai ta shige tana kokarin danne kukan dake kokarin kufce mata, wai shin da wane bala’in za taji? ko’ina babu sassauci, bata samun nutsuwa da kwanciyar hankali sai a gurin Uwale ita kadai ce ke kwantar mata da hankali, amma ita kanta wacce ta haifeta kullum habaici take mata akan wanda ta kwallafawa rai! kowa yana ganin laifinta bayan itama ba ita tayi kanta ba, Allah ne ya halliceta ya sanya mata soyayyar wanda bai san ta nayi ba, dole idan ya dawo ta cire kunya ta sameshi da maganar ko ta san matsayinta..

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button