GOJE 15 and 16
FREE PEGE
15&16
Sosai ta kwanta jinya sakamakon artabun da sukayi ita dashi, jikinta yayi mugun tsami! ta shar’be! a guri guda da kyar take iya motsa hannu saboda tsabar sanyi da jikinta yayi, al’amarin bai tashi tsananta ba sai da dare ya tsala tukkuna, ta kasa rintsawa gabadaya jikinta ya dauki ciwo! ga wani irin kaikayi da ciwukan jikinta keyi.
Kuka ta dinga yi tana jan hanci! ita kam wannan bala’i bata san ina zata kai shi ba.
Can cikin baccin daya dan fizgeshi ya dinga jin shashshekar kukanta, zumbur ya mike zaune, dama babu wata tazara a tsakaninsu, ya d’auki fitilar dake gefansa ya kunna yana daga inda yake zaune yake haska gurin da take.
Hannu tasa ta kare fuskarta ta sake takure jikinta tana cigaba da zubar da hawayen azabah!.
Ya karaso gurin da fitilar a hannunsa, ya dudduba ko’ina babu wani abu. tsugunawa yayi a gabanta yana duba fuskarta, hannu tasa ta doke fitilar ta fadi. a take ta mutu gurin yayi duhu! ya lalubi fitilar yana kokarin gyara batir din, amma ina ta rikice! yayi-yayi ta kama taki, haka ya hakura ya ajiyeta kafin yace.” Kukan me kikeyi ko wani guri yana miki ciwo a jikinki.”? Shuru tayi masa, ya sake maimaita maganarsa, uffan ba tace masa ba.
Sai ya yun’kura da niyyar barin gurin tayi saurin rike gefan rigarsa, a rikice tace.”Jikina ne duk yake ciwo ko’ina babu dadi.”
Yanda yaji tana magana a rikice da alamun kuka ya sanya ya gazgata maganarta, bece komai ba ya sake yunk’urin tashi. Ta rike gefan rigarsa da kyau! yaja! taja! sai ya juyo yana kallonta, da k’yar ta mike zaune kafin tace.”Kada ka tafi kayi wani abu wallahi zan iya mutuwa.”
Yana da tsananin tsausayi mussaman akan ‘ya mace! sai duk jikinsa ya mutu, ya koma ya tsugana yana dan ganin shatin fuskarta duk tayi wani iri idonta yayi jajawur! fuskar duk ta kumbura!.
Be iya tausasa murya ba, amma sai ya tsinci kansa da sassaita muryasa yace.”Yi hakuri ki sake min rigar na samo miki magani.”!
Hanci taja kafin ta sakar mai rigar ya tashi, tabi inuwarsa da kallo tana sauke ajiyar zuciyar wahala.
‘Daya daga cikin yaranshi ya umarta daya had’a masa maganin ciwon jiki, da yake duk suna tafe da guzurinsu, ba tare da anja dogon lokaci ba, ya harhad’a komai ya nufi inda take dashi a hannunsa.
Samun ta yayi tana rawar d’ari, domin lokacin sanyi asubah ya fara sai zazzabi yake kokarin rufeta, sai datse hakoran bakinta take.
Cikin wani irin yanayi ya mika mata maganin da fadin.” Kar’bi kisha wannan za kiji sasaauci sannan zaki samu bacci.”
Kasa kar’ba tayi saboda halin da take ciki kawai ido ta tsirawa fuskarsa hawaye na sharara! jikinta gabadaya yaki tsayuwa a guri daya saboda karkarwa!.
Ya ajiye maganin hannunta ya lalubo ya rike a cikin nasa, nan yaji zafi rau!! ya sake shiga damuwa da ya fahimci zazzabi ne a jikinta.
Sosai ya zauna a gurun ya kama dukkanin hannunta cikin kokarin sassaita muryarsa da sigar rarrashi yace.”Zazzabi ne ko.”?
Sai ta fashe da kuka! mai karfi! kamar me jiran kiris! da sauri yasa hannu ya rufe mata baki yana girgiza mata kai!
Hannunsa ta cire tana me cigaba da janyo kukan dake cin zuciyarta.
Kawai sai ya tsinci kansa da janyota jikinsa, ya sata cikin katuwar rigar dake jikinsa, ya san nauyin rigar zai zame mata garkuwa gurin karkarwar da take.
Da yake taimako take nema ba tayi wani turjiya ba mussaman da taji ta kan faffadan kirjinsa dake cike da gargasa ga wani irin dumi da ya fara ratsa jikinta, luf tayi ta kwanta sosai tare da sanya hannu a bayansa ta rikeshi kam! tana sauke ajiyar zuciya daki-daki.
Sai da ya fara jin saukar numfashinta a hankali sannan ya dan gyara zaman shi, cikin wannan muryar daya aro yace.” GIMBIYA! Yanda ya kira sunan yayi masifar kassara mata gabobin jikinta.
Taji shi sarai! tayi shuru motsin kirki ta kasa mamakin ma take yanda akayi ta saki jikinta a kirjinsa ba tayi tsammanin zata yarda numfashinta da nasa ya hadu ba sai gata a kwance a kirjinsa male-male maimakon taji wari! ko wani abu makamancin haka na fita a jikinsa sai taji akasin haka, jikinshi baya fitar da wari! ko kad’an sai ma wani irin dumi! da takeji na ratsa ta, nutsuwa da kwanciyar hankali na sauka a sassan jikinta.
“GIMBIYA.” Ya sake kiran sunan daya sanya mata a lokacin, koda yake daman Gimbiyar ce shiyasa shima ya ara ya yafa.
Dan motsi tayi amma bata amsa ba, kuma bata sakeshi ba, ya dan ja numfashi, jin yanayinsa yana sauyawa, ya fara kokarin cireta daga jikinsa. Ta dage! harda gyara kwanciya kamar wacce take kan katifa.
Mamaki sosai ya rufeshi, tunda yaji tayi shuru kuma numfashinta ya daidaita ya san ta samu sassauci bayan haka kuma jikinta ya daina karkarwa da alamar zazzabin yayi nasa a guri, amma meye amfanin abinda take.
Namijin kokari yayi ya cireta daga jikinsa, babu kunya ta zuba masa ido kamar wanda yayi mata laifi.
Ya saisaita yanayinsa kafin yace.”Sannu kina bukatar magani ko.”?
Shuru tai na minti biyu kafin ta kalli hannunsa, maganin ne yake kokarin sanya mata a baki. Tasa hannu ta buge kwaryar maganin gabadaya ya zube kasan gurin da jikinsa
Cike da takaici da bacin rai yake kallonta, ta ‘bata rai da fadin.” Wane irin magani ne wannan me wari zaka sa min a baki.”
Ya hadiye b’acin ransa wannan karan bai sassauta murya ba da yanayin maganarsa yace.”
Ke ki kace jikinki na ciwo maganin karfin jiki ne.”
Ta’be baki tayi da fadin.” Bana bukata.” Bece komai ba ya tashi daga gurin tare da jin takaicin abinda tayi.
Ta kalleshi da fadin.” Ka bani aron wannan rigar ta jikinka na rufe jikina da ita tana da d’umi.”
Uffan bece mata ba ya bar gurin, minti uku ya dawo da irin rigar a hannunsa. Ya mika mata, ta kalleshi da fadin.” Ta jikinka nake so.”? Yace.”Duk daya ce da wannan din.”
A yamutse tasa hannu ta kar’ba tana kokarin sawa a jikinta ya bar gurin .
Sai kace suddabaru! hankalinta ya gaza kwanciya koda tasa rigar ta kwanta domin jin d’umi kasa nutsuwa tayi ta tashi zaune tana rawar jiki…….Me yasa ta kasa samun abunda takeso a jikin rigar! ita a tunanin kaurin rigar ne ya saukar mata da nutsuwa sai taga akasin haka. “Ba rigar bace mai rigar ne yasa miki nutsuwa da kwanciyar hankali.”
zuciyarta ce take mata wannan maganar.
Da sauri ta k’aryata zuciyarta ta sake rurrufe jikinta da rigar tana korar abinda zuciyarta ke raya mata, babu yanda za’ayi ta amince da cewa wannan gantallalan ne zai zama garkuwa a gareta.
Daya daga cikin yaranshi ne ya kawo mata ruwa da asuwaki da abin kari. ganin yanda maigidansu yake bata kulawa ya sanyashi gaisheta, bata amsa ba sai wukalantaccan kallon da take masa shida tarkacen da ya ajiye a gabanta. Girgiza kansa yayi baki a cije! ya bar gurun ba don kar ya dauki mataki akan yarinyar ya samu matsala da maigidansa ba, da sai ya fasa mata baki domin yaji ciwon kallon banza da tayi masa.
Har gari yayi haske sosai tana takure cikin rigar har yanzu ta kasa tantance a wane iri yanayi take,
Can ta hangoshi yana zuwa inda take, ido kawai ta tsira masa babu kiftawa sosai take mamakin tsananin kamar da yake da jarumi(Barbahs) tana bala’in son jarumin saboda jarumtarsa da iya soyayyarsa idan yana abu a film kamar gaske, zazzafar ajiyar zuciya ta sauke tana kokarin karyata abinda zuciyarta ke raya mata a kansa.