GOJE 15 and 16

Tsaf yake cikin shirin fita, ya sauya rigar jikinsa doguwar jallabiya ce browan mai gajeran hannu sai ya sanya dogon wadon jens kanshi nannad’e da bakin yadi yayi gammo sosai! idanuwan nan rad’au! da bakin kwalli! kafad’unshi rakwacam! da tarin kayan farauta, har da irin doguwar bindigar nan, hakanan wuyanshi da damtsan hannuwansa wasu irin abubuwa ne a d’aure.! kafafunsa sanye suke da wani irin takalmi mai tarin igiyoyi a jikinsa.
Tunda ya tsaya a kanta take kallon kafarshi, mamakin kyawun kafar take, bata ta’ba kallon kafarsa ba sai yau, faratanshi tas babu kazanta sai kananun gashi dake kwance saman yatsun kafar.
A tsorace ta dinga sauke ajiyar zuciya tana kokarin kawar da idonta daga kan kafar. taji muryarsa cike da wani irin amo!! “Tashi zaune.”
Yanda ya fadi maganar babu wasa yasa ta tashi tana kallon fuskarsa, babu fara’a yace.” Zanja ragamar yara na wani aiki a cikin dajin nan, ina so ki kula da kyau! kada kiyi kuskuran barin gurin nan! ki kiyaye! mutukar kina so ki cigaba da rayuwa a duniya.
Kuka tasa tana kallonsa da fadin.” Me yasa ba zaka tafi dani ba, saboda tsabar mugunta shine zaka had’a kan yaranka ku tafi ku barni ni kad’ai! bayan ka san dajin bashi da kyau komai yana iya faruwa da rayuwata.”
Yace.” Nan gurin yana da tsaro bayan haka kuma gurin da zamu shiga yana da had’ari shiyasa na yanke shawarar barin ki anan sai yafi miki kwanciyar hankali.”
Ta girgiza kai tana shakar hanci tace.”Aa nifa ba zan zauna ba wallahi ko kun tafi sai na biyo bayanku.”
Yanda tayi maganar babu alamun wasa a tare da iya yasa yaji shakkar tafiya ya barta.
Ya kalleta a lokacin da take kokarin mi’kewa. “Na fad’a miki abinda yake da akwai kina kuka ko.”?
Hannu ta d’aga masa da fadin.” Nifa ba zan zauna ni kadai a wannan gurin ba.” Tana gama maganarta ta kama tana tafiya babu takalmi a kafarta, ga kanta babu dankwali.”
“Ki tsaya nan nace.”! Cikin tsawa yayi maganar. taja ta tsaya ba tare da ta juyo ba.
Yaja tsaki tare da komawa baya, takalmi ya lalobo mata tare da wani farin yadi.
Ya karasa inda take da fadin.” Kar’bi wannan ki rufe jikinki dashi.” ba tayi musu ba ta kar’ba, ta lullube jikinta har kasa. Ya bata takalmi ta tsuguna tana kokarin sawa, ganin tana ‘bata masa lokaci yasa ya tsuguna da kansa ya d’aura mata takalmin sosai yanda duk wuya ba zai fita a kafar ba.
Hannunta ya rike a cikin nasa suka nufi inda ayarin jama’arsa suke tsayuwar jiransa, ganinsa tare da ita ya basu mamaki! amma babu wanda yayi magana a cikinsu, yayi gaba suka rufa masa baya.
karnuka wasu a gaba wasu a baya, sai kuma bushe-bushe da gangi! da ya cika dajin!
Free pege ya kusa ‘karewa a hanzarta biyan kudin karatu.
0542382124…Binta umar gtbank a tura sheda ta wannan number…… 07084653262
Ayi kokari a duba wannan馃憞馃徎
Mijina baya bani kulawa bayan kafin muyi aure yana bani kulawa da duk wata soyayya
Watakila kece kika janyo faruwar hakan, na farko dai namiji yana da bukatar kulawa, ta kowane fanni, watakila kafin kuyi aure ke din ‘yar gayu ce mai tsafta, bakya rabo da kwalliya kamshin turare ako da yaushe, sai bayan auranki kuma ki mayar da kanki jakar mata, da kuruciyar da komai ki shiririce wanka ma sai kiyi kwana biyu ko uku ba kiyi ba mussaman a cikin wannan lokacin, sai kiyi kwaskwarima ki shafa mai akan dauda kina tsamin hammata! to me zai hana namiji bai kyamace ki ba, babu mummunar mace, kuma komai shekarunki mutukar kina da miji to kada ki zauna a lalace domin hakan zai janyo miki bacin rai mai tsanani mussaman idan kina da abokiyar zama to zaki zama koma baya ta kowane fanni, tsafta jigo ne a cikin zamantakewar aure don haka ki kula da wannan abubuwan.