GOJE 17 and 18
FREE PEGE
17&18
UBAN DABA!
Ya gagara! yayi shura! a harkar ta’addanci! ya addabi ‘kasa da jama’ar dake cikinta, ran mutum abun banza ne a gurinsa, da yawa jami’an tsaro suka shiga sassaninsa, basa fitowa da rai! idan anyi sa’a wasu su fito a raye to za’a samu muggan raunika a jikinsu, shekaru bakwai kenan daya kafa sansani a cikin dajin dashi da jama’arsa, manya manyan bishiyun kuka ciki suka fafake ya zama makwancinsu, duk abunda yake faruwa a cikin gari yana samun labari akwai redio a tare dashi, bayan haka kuma yakan tura yaran sa suyi badda kama su dauko masa rahoton abinda kasa take ciki.
Masana sunyi hasashen cewa Gurin da ya kafa sansani akwai albarkar kasa a gurin, irinsu gold da man fetur da sauransu, wannan dalilin yasa shima ya tsaurara matakan tsaro a gurin, babu wanda yake amfana da albarkar dake gurin sai shi da jama’arsa, duk sanda suka haqo gold din akwai wani hamshakin dan kasuwa dake zuwa ya saya. cikin dare ya kan shiga dajin kar’ba! ya basu kudi da kayan masarufi, sannan a duk sanda sukayi ra’ayi zasu badda kama su shiga cikin gari suyi siye-siyen abunda suke bukata.
Mashekin daji! Hatsabibin mutum ne wanda yake da suddubaru! duk sanda hukuma ta tura jami’anta binkice a dajin, basa nasarar ganin sansaninsa amma kuma shi da jama’arsa suna ganin duk irin d’auki ba dadin da jami’an tsaron keyi a kok’arinsu na ganin sun ga mafakarsu, wannan damar suke samu su karkashe wanda sukayi ra’ayi, sai dai a fito da gawarsu.
GOJE! Ya jima da jin labarin hatsabibancinsa, kullum tunaninsa ya za’ayi ya kawo karshen ta’addancin daya ke a kasa.
Kafin ya yanke shawarar tunkarar inda yake sai da ya zauna da yaransa domin yaji ra’ayinsu, da yawa daga cikinsu jikinsu ne yayi sanyi domin dai sun san tunkarar mutumin babban al’amari ne! dalili shi akwai kayan aiki a tare dashi da jama’arsa, duk da suma suna da dabaru amma a ganinsu tunda sojoji da ‘yan sanda suka kasa samun nasara a kansa to waye zai iya .
Ganin jikinsu yayi sanyi yasa ya karfafa musu gwiwa da fadin.” Su cire tsoro a cikin ransu, kada su sanya a ransu cewa masheki da jama’arsa zasu samu nasara a kansu, idan sun yarda da kansu cewa sunfi karfi wuka da bindiga to tunkarar inda yake abune mai sauki bayan haka kuma su dauka cewa wannan aikin da za suyi kamar jahadi idan ma Allah ya kaddara mutuwarsu a gurin aljanna ce makomarsu.
Wannan maganar da yayi ya sanya suka samu karfin gwiwa, suka kwanta da shirin tunkarar masheki ba tare da k’asa ta san abinda suke shirin aikatawa ba.
Tafiya suke tsakankanin bishiyu da manyan tsaunika, gami da kwazazzabe, gabadayansu, babu alamun gajiya a tattare dasu, tafiyar suke suna bushe-bushe tare da farautar duk wata dabbar data gilma a gurin, ita dashi ne a gaba, yayin da jama’arsa ke take masu baya, tayi masifar galabaita! bakinta ya bushe cikinta in banda qugi! babu abinda yake, ba komai ke damunta sai yunwa,
kallonshi tayi kamar tunda aka halliceshi be taba dariya ba, tunda ya rike hannunta da zasu tafi be sake kallonta ba ballantana magana ta had’asu,
Magana takeso tayi masa amma tana jin shakka! don yanayin sa kadai dole ya baka tsoro! sai taja ta tsaya cakk! tana sauke wani irin numfashi!
Kallonta yayi na minti biyu, kafin ya juya yayi masu magana da ido, sun gane abinda yake nufi, sai suka samu guri suka zazzauna wasu kuma suka fara hawa kan bishiyu suna kad’o ‘ya’yan itace.
Kan wani ice ta zauna tana kallonsa sai kai kawo yake a gurun……….”Ina bukatar ruwa da abinci.” tafada tana dam hararar bayansa. Yana jin maganarta amma be juyo ba.
“Ina magana fa.”! tafada kamar zata fashe da kuka.
” Alba.” sunan d’aya daga cikin yaransa kenan. Yayi saurin zuwa gurin, yace.”Ka bata ruwa da abinci.” Yace.” An gama maigida.
Gabanta ya k’araso da wata ‘yar jarka ruwane a ciki, ya mika mata da fadin.” Kisha yanda kike so”
Cike da k’yan’kyami take bin jarkar da kallo, ‘ya’yan wasa sun tashi a cikin ruwan.
Tsaki! taje cikin tsawa! tace.”Wuce ka ban guri waye zai sha wannan kazantaccen ruwan.”
Maganar ta dauki hankalinsa ya juyo yana kallonta, shi kansa Alba d’in ransa ya baci da jin irin tsawar data buga masa.
Ya kalleshi da fadin.” Jeka kawai.” Ya girgiza kai, da fadin” Angama.” Gurin ya bari. Shi kuma ya juya mata baya, tunda ba zata sha ruwan da kowa yake sha ba sai ta zauna a haka.
Ranta ya baci ganin ya juya mata baya tace.” Wai me ake nufi ne.”?
Ba tare da juyo ba yace.” Ya kike so ayi miki? an baki kince bakya so akwai wanda kike so ya zama ruwa a cikinmu kisha.”?
Tace.” Ruwan fa bashi da kyau, bayan haka ya za’ayi na hada bakina dana wannan ‘kazamin.”
Ya girgiza kai da fadin.” Sai ki zauna da ishirwarki .”
Kuka! ta fashe dashi! da fadin” Allah ya isa tsakanina da kai mugu azzalimi.”!!
Ya juyo da fuskar bacin rai yana kallonta…..Alba dake kokarin zuwa gurin yace.”Oga wannan yarinyar fa tana da matsala wallahi! da zaka bani dama sau daya dana koya mata hankali .”
Ya kalleshi na minti biyu kafin yace.” Ko bana guri ban amince da hakan ba amana ce a gurina.” da sauri yace.”Allah ya huci zuciyarka.”
Ya gyada kai da fadin .” Wanke lemon ka bata.” Da sauri yayi abinda aka umarceshi, ta kar’ba tana yatsine fuska.
Yana kokarin barin gurin yace.”Bani wannan jakar ruwan ta hannunka.” Ya mika masa, a gabansa ya bude murfin ya zubar da ruwan ciki. Ya bar gurin da ita a hannunsa.
Ita dashi duk suka bishi da kallo yana tsallake manya duwatsu kafin su daina ganinsa, gabanta ya tsananta fad’uwa ganin baya gurin, ta dora idonta kan Alba dake tsaye yana zazzare mata jajayen idanuwansa, saurin sunkuyar da kanta tayi, tsoro takeji kada yayi mata wani abun, sai da ya gama cije-cije kafin ya bar gurin.
Ya kasance sai ita kadai a gurin, sai motsi da maganarsu da takeji a saman bishiyu, ta daga kai tana so ta hangesu, amma ta kasa ganinsu,
Dajin ta dinga bi da kallo, kanta yana juyawa, manya dutsina da tafka-tafkan bishiyun dake gurin sun juyar mata da kai.
Da sauri ta kama hanyar da taga yabi, tana tafiya tana waiwayen bayanta.
Sai da yayi tafiya mai tsayi sannan ya cimma ruwa yana gudana daga kasan wani tsabtataccan dutse gare-gare dashi………Ya haura wasu manya duwatsu kafin ya samu nasarar d’ibar ruwan.
Yana juyowa kibiyar ta gilma ta gefan fuskarsa, da alama saita shi akayi Allah be bada nasara ba…….Da mugun sauri ya daga kanshi sama, can ya hango su saman wani dutse sun kai su biyar, yayi gaggawar fitowa daga tsakanin ruwan.
Suma basu fasa harbinsa da kibiya ba.
A gaggauce ya fara kurd’awa inda jama’arsa suke baya su cimma inda suke ba tare da shiri ba. sai dai me! biyoshi sukayi suna sakar masa harbi ta ko’ina!!
K’aro sukayi da juna!! ya rike hannunta tamau! bayan wata bishiya suka ‘buya, suka ‘karaso gurin suna sassare matattatun itacuwan da suke gurin.
Hannunsa dake cikin nata yake kokarin cirewa ta rike da kyau! tana girgiza masa kai! wai kada ya fita, ya sake yunkurin cire hannunsa ta rike! hawaye masu tsananin zafi suka wanke mata fuska, bakinta tasa a kunnansa, a hankali tayi magana “Kada kaje.”
Jajayen idonsa ya tsira mata! ta marairaice fuska, tana ro’konshi da idanuwanta.
Tausayi ta bashi ganin yanda jikinta ke wani irin karkarwa, cikin zuciyarsa yace.”Ba yanda za’ayi yana ji yana gani nasara ta kufce mai wannan ce hanya mafi sauki da zai tunzura zuciyar abokin gabarsa.