GOJE

GOJE 21 and 22

FREE PEGE

21&22
Hakika baka sanin amfanin mutum a rayuwarka sai ranar da wata musiba ta sameka, ya taimakawa rayuwarta, ita kuma ta daukeshi a matsayin abokin gabarta! tayi masa mummunar fahinta duk da irin taimakon da yake akanta, ni a ganina idan shi din macuci kamar yanda kullum take kiransa ba zata kai labari ba, domin da tuni ya keta mata haddi ya yasar da gawarta a dajin. koda yake kowane dan adam da irin tunaninsa, har yanzu ita tana shakku akansa cewa bashi ne ya sato ta daga gaban iyayenta ba.

Kwanciyarta da kamar minti goma mugun k’aikaiyi ya tasheta, ashe tsutsar data sauka kan kafad’arta tana da dafi! kuma ta cijeta a gurin har ya kumbura sai tsuko! yake mata, yatsunta biyar tasa a gurin tana aikin sosawa amma kamar ‘kara angiza kaikaiyin take, fatar gurin tayi jajawur! saboda susa duk ta kwaile.
Hawaye kawai take tana jan hanci! daga wannan sai wannan! ciwuka a jikinta iri-iri! sosai take kuka tana kiran innalillahi-wa’ina ilaihi raji’un!

Ya rage shi kadai a waje yana kai kawo a gurin, har yanzu zuciyarsa taki aminta da gurin, yana ganin kamar idan yaje ya kwanta wata matsalar zata faru! zagaya gurin yake karnukansa na binsa duk inda ya nufa sai koke-koke suke………Alba ya cimma inda yake tsaye cikin girmamawa yace.”Maigida yarinyar nan fa tun dazu ta ishi mutane da kuka.”
Yace.”Me kukayi mata.”?
Da sauri yace.”Wallahi maigida babu abunda mukayi mata kawai dai munji tana kuka shine nace bari na sheda maka.”

Ya girgiza kansa da fadin.” Jeka gani nan zuwa.” da sauri ya juya ya tafi.

D’azu ta ‘bata masa rai! ya hakura ya shanye amma baya tsammanin yanzu zata kawo masa shiririta ya saurara mata.

Ya sameta sai gursheken kuka take gabad’aya ta cire rigar dake jikinta sai breziya sai soshe-soshe take.

Ganinta a haka ya ‘bata masa rai! rashin kamun kanta yana bashi haushi, idan ba hakaba ta san da cewa ita kadai ce mace a cikinsu mai yasa ba zata suturta kanta ba, kullum shike k’okarin ganin ya suturta ta a matsayinsa na namiji amma ita a cikin maza! saboda rashin sanin darajar kai take bude tsaraicinta.

Tsaki mai karfi yaja ya juya yana kallon gurin da ya yaransa ke zazzaune! akwai tazara a tsakanin inda take, baya kuma tsammanin zasu hangeta saboda kafin ya fita sai da ya katangeta.

Murya a sama! yace.”Mayar da rigarki.” ido gaja-gaja da hawaye! ta kalleshi, ya murtuke fuska! ko alama bata bashi tausayi ba, ya bude mata dukkanin idanuwansa! umarni ya sake bata, a dashe tace.” Ka daina yi min tsawa! ko ka san abinda yake damuna.”?
Yace”Babu abunda ke damunki sai hauka! da gidadanci! idan ba haka mai zai sanya ki cire riga cikin maza.”

Wani abu mai nauyi ya tsaya mata a wuya! wai ace wannan gantalallan ne yake kiranta da mahaukaciya.

Nauyin abunda ya tsaya mata a wuya ya hana ta magana sai uban hawayen dake tsere a saman fuskarta, abu biyu ne suka dameta a halin yanzu.

“Mtswwww! tsaki mai tsayi yaja kafin ya fita da gurin, ya dawo da fitila a hannunsa sai da ya rage karfinta sannan ya tunkari inda take.

Ta sake takure jikinta tana kallonsa yana dube-dube a gurin, rigar ya mika mata da fadin.” Kar’bi kisa ko kuma yanzu nayi abinda ba kiyi tsammaninsa ba.”

Ta tsira masa ido! da jin shakkar maganarsa, ganin babu alamun wasa a fuskarsa yasa tasa hannu ta kar’bi rigar amma bata sanya ba, ta rike kawai a hannunta tana cigaba da sosa gurin dake mata ciwo.

Ya haskata da fadin.” Cire hannuki a gurin! da sauri ta cire! tsigar jikinsa ta tashi! ganin yanda gurin yayi jawur! har da kumburi! zuciyar musulunci, duk sai jikinsa yayi sanyi haka kawai baya so wani abu ya cutar da ita, burinsa bai wuce ya kaita gaban iyayenta lafiya lou ba.

Sassauta murya yayi yace.”Sannu yaushe hakan ya faru.”? a maimakon ta bashi amsar tambayarsa sai kawai ta sake rurucewa da kuka!!

Yatsansa yasa saman bakinsa da fadin.” Shiiiiii.” kukan bashi da amfani kiyi shuru zan taimaka miki.”

Ba tayi shuru ba kuma bata daina kallonsa ba, yace.”Kina bukatar hakan ko.”?

Kamar wata sakarai ta daga mai kai!

Yace.”To ki zama jaruma! ki daina yawan kuka bashi da fa’idah.”!

Taji kamar ta kai masa duka! ta’ina zata iya daure wannan azabar!

Fita yayi da kamar minti biyar ya dawo da magani a hannunsa. yayi zaman ra’kuma a gabanta cikin muryar da ya saba rarrashinta ya mi’ka mata maganin da fadin.” Jarumata! kar’bi maganin ki shafa a gurun zai daina miki ciwo.”

Maganin ta kar’ba ta lakato a yatsanta, can bayan kafad’arta gurin ciwon yake ta daga hannu sosai tana kokarin shafawa hannunta ya gaza kaiwa!
Ganin haka yasa ya kar’bi maganin daga hannunta ya lakato kan yatsansa, ya kalleta da fadin.” Kin bani izini.”?
Shuru tai masa.

Ya sassauta murya yayi da sake maimaita maganarsa.

Kai kawai ta iya daga wa gabadaya jikinta ya mutu! ya lalubi gurin yana shafa maganin a hankali yana sake kwantar mata da hankali da cewa gurin zai daina ciwo insha Allah!

Ido kawai ta lumshe tana jin maganganunsa sama-sama a cikin kunnanta, har ya gama shafa maganin fuskarta ya dan kalla sai yayi sauri ya janye idonsa jin yanayinsa na neman sauyawa, gefe ya matsa tare da sassauta murya ya kirayi sunanta………… GIMBIYA! a kasalance ta bude idonta! tana kallonshi , tana masifar son taji ya kira ta da wannan sunan. yace.”Sannu ki kwanta ki huta na shafa miki maganin.” Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta zame ta kwanta tana tattakure guri daya, Shima ajiyar zuciya ya sauke kafin ya lalubi wani zani mai kauri ta fara k’okarin rufa mata a jiki akayi rashin sa’a gwiwarsa ta zame ya fad’i kanta! fuskarsu ta hadu! da sauri yayi gaggawar rabuwa da jikinta yana bata hakuri! uffan ba tace ba asalima lokacin da hakan ya faru idonta a rufe yake.

Ganin tayi shuru ba tace masa komai ba yasa a gaggauce ya fita yana auziyya a zuciyarsa, be san me yasa ba kullum zuciyarsa take kwadaita masa wasu gurare na jikinta, a duk sanda zasu kasance a guri daya yakan rasa nutsuwarsa.

Itama anata bangaran hakane, har yanxu idonta a rufe yake ta rasa abinda yake mata dadi! yanda yake sassauta murya yana rarrashinta yakan karya mata garkuwar jiki, tana jin dadin hakan sosai, a rayuwarta tana masifar son namiji wanda ya iya soyayya, bayan haka kuma bata san lusarin namiji tafi son tsayayye shiyasa wasu lokatan yake birgeta domin dik ya tara abubuwan da take bukata.

Ajiyar zuciya ta sauke tare da jan zanin daya rufa mata ta rufe gabadaya jikinta harda fuskarta, addua take a zuciyarta Allah ya sa bacci ya dauketa. Cikin ikon Allah kuwa bacci mai nauyi ya dauketa…………….

Kamar a mafarki! ta dinga jin ihu!!! da hayaniya tare da kukan karnika! da karar wu’ka’ke! a firgice ta tashi tsaye! tana bin gurin da kallo, babu kowa duk sun fice! yanda ‘kura! da guguwa! take shigowa har gurin da take shi tabbatar mata da cewa babu lafiya!

Fitowarta daga gurin yayi daidai da tashin bomb! gabadaya gurin ya kacame! ya hargitse! da hayaki! da rarrafe ta koma katangaggen gurin ta takure guri daya tana kiran sunan Allah.

Ta jima a haka kafin ta dago kanta, still tana jiyo hayaniya da kuwwa! tare da kukan karnika! ga wani irin b’akin hayak’i! da ya turnuke! a gurin!

Hannu tasa ta toshe hancinta tare da sake takurewa a guri daya jikinta in banda rawa babu abunda yake, bakinta sai motsi yake adduar yaye masifa takeso tayi amma bata iya ba, sai kawai ta dingi nanata innalillahi da karfin gaske!

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button